Showing 3001 words to 6000 words out of 95282 words

Chapter 2 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6654

Akai akai yake kaini Ringim Dan na Saba dasu, Yan uwan Mama Babu Wanda ya taba zuwa ya ganni Dan haka Abbu yace shima bazai kaini ba, har na Isa yaye aka daina feeding Dina da Madara se aka koma solid food. Ban Jima da yaye ba na cika shekara biyu, Abbu ya kaini creche, so ni dai as far as am concern tunda nayi wayo a makaranta nake, karatu nake, Dan hakan karatu a cikin Raina yake, shekarata ta farko bani ma da wayo bazan iya tuna komai ba, seda nayi shekara biyar sannan na fara sanin kaina, mutum daya na gane matsayin uwata da ubana Abbu, shi kadai na sani kowa as preliminary nake ganin shi,duk Wanda na Kira da Baba to Kara ce kawai,Dan Babu Wanda ya yimin abinda Abbu yayi min.




Saboda yadda na Shiga makaranta da wuri yasa kankanin lokaci na gama. Munje Ringim Ina kwance akan cinyar Hajiya Abbuna ya shigo Dan tun isowar mu fada ya fara zuwa ya gaishe da sarki sannan ya fito mutane Kuma suka tareshi kowa na fada Masa financial complain dinsu Dan ya taimaka musu. Da kyar na yadda na shigo gida shima Yaya na gidan Kawu Sa'idu ne ya lallaba ni muka shigo cikin gidan dashi, Ina ganin Hajiya se na saki hannun shi na nufi inda take zaune ta mike kafafun ta na kwanta Ina ce Mata


" I was waiting for you, you didn't come to my house and I missed you!"


Ta dungure min kaina tace


" Ni bana jin wannan yaran nasarar da Baban ki yake koya Miki, yimin hausa"


Yaya dake gefe yayi ta Mana dariya sannan ya fassara Mata abinda nace, ta rungume ni Yana cemin ita ta tsufa ba zata iya zuwa har can capital wajena ba. Tana ta tambayata abinda zanci ne Abbuna ya shigo, nayi saurin tashi na koma kan cinyar shi, murmushi yayi ya zaunar Dani Yana gyara min hular kaina suka gaisa da Hajiya, Yaya ya Mike Dan yasan ya kamata ya Basu guri, hannu ya Mika min yace


" So muje na kaiki gidan mu"


Na kalleshi sannan na kalla Abbu, ya gyada min Kai tareda mikar Dani tsaye, har na tafi na dawo na rungume shi nace


" I'll mish u"


Yayi dariya yace


" My Princess go"




Na wuce hannuna cikin na Yaya muka nufi gidan su dake can gefe duka a cikin Ausar ne. Muna zuwa duka suna zaune ita Ummaah na gaban murhu tana rabon shinkafa da Mai da yaji, su Kuma suna zaune an shimfida katuwar tabarma na bogaji suna jiran a Gama kowa ya dauki nashi. Muna sallama suna ganina Mino ta mike tana fadin


" Afiyya oyoyo! Ummaah Kinga Afiyya tazo"


Ta juyo ta kalleni ni Kuma naje kamar yadda Abbu yace min idan Naga babba na gaishe shi na tsugunna nace Mata Ina kwana, ta tabe baki ta fara fadin


" Kanwar uwarki ce Afiyya da Zaki dinga wannan ihun? Shashasha kawai"


Jiki a sabule ta zauna, shikam Yaya Zama yayi yace


" Ummaah Baki amsa Mata gaisuwar ba"


" To uban shishiggi Kai Kuma, Wai ita wannan Afiyya din Yar gwal ce, bazan amsa ba"


Sanin halinta yasa ya guntse bakin shi ya Mike yace min na zauna yanzun zai dawo, na Mike na Kama hannun shi Dan kada ya tafi, Mino yasa ta daukeni haka na Dan zauna a dadare saboda rashin sabo, abinci kowa yaje ya dauki nashi, Nima aka Miko min wani Dan mitsitsi cikin karamin roba, na karba na aje Amma naki ci saboda bana ma jin Yunwa, suna Gama ci Siyama ta janyo nawa ta cinye, Mino na Mata magana Ummaah tace ta barta dama ni na xo na datse musu abincin su. Yaya ya dawo da kifi a Leda ya dauki abincin shi yace nazo naci me kifi, ni Kuma since from childhood bana ketare tayin kifi saboda yadda Abbu ya Saba min cin kifi kullum se mun ci a dinner. Ina ganin Kifin naje na zauna Siyama ma ta taho ya dinga bamu muna ci har ya Gama naje nace ma Ummaah ta wanke min hannu, ruwa kawai ta zuba min na cuda tace naje, nace Mata ai se an saka detergent sanann zai fita, se ta koreni Wai Ina Mata iyayi. Ban wani Kara sakewa ba saboda karnin da hannuna yake na dameshi ya maida ni gurin Abbuna.


" Jarabar ka tasa ka dakko ta,seka maida ita ai"


Ya Mike ya Kama hannuna muka tafi, Ina zuwa na samu Abbu ya fita, se na zauna wajen Hajiya Ina Mata hirar school, se dare ya dawo da Kifin shi. Naci nayi bacci, bayan fita ta Hajiya ta nuna Masa lallai ya kamata ya kaini maiduguri Koda su Basu neme ni ba to shi ya kamata ya Kai ni na gansu, idan sun cigaba da nemana kansu idan Basu Kara ba shi dai ya sauke wannan nauyin. Washegari muka tafi Kano muka bi flight zuwa maiduguri, ya kaini na gaida kakkani na duk sunata borin kunyar Wai Basu San min koma Abuja ba, se zuzzuta yadda na girma nake Kama da Mama suke. Akazo zau tafi na dinga kuka bazan zauna ba hakan shima ya hakura muka tafi tare. Kawata Dana fara Yi a school namesake Dita ce, sunan ta Amina Abubakar Rogo, gari kadai ya banbanta sunan mu. An tashi school drivern mu duka Bai zo daukar mu ba, muna zaune inda muke Zama mu jira na Bata book Dina Wanda tsayin shi bazai Shiga cikin backpack Dita ba haka itama, inda water dispenser ke aje naje na tsiyayo ruwa nasha sannan nayi discarding cup din sannan na dawo na karba book Dina, kafin na zauna Nanny ta shigo cikin sauri, nayi sauri na nufe ta Ina rungume ta nace


" Nanny!"


Ta shafa kaina ta karba book Dina, da food box dina da Kuma backpack Dita nayi waving Amina muka tafi. Tun cikin mota nake Mata complain Yunwa nake ji, tace ai ta Gama abinci, nace Mata Abbuna ya dawo tace ai yace se dare zai dawo. Muna zuwa gida na wuce dakina da gudu na dauki waya nayi dialing wayar office din Daddy, Yana picking nace Masa yaushe zai dawo yace nayi hakuri naci abinci zai dawo da daddare, ba yadda naso haka na yadda mukai sallama. Akazo wanka nace ni fa da kaina zanyi da kyar na yadda Nanny tayi min.


Ina zaune Bayan maghrib a dakina na tasa drawing book a gaba dasu pencil colors da water color Dole se na zana picture Mama da Abbuna dake rungume Dani on my first birthday,


" Where's my princess?"


Naji muryar Abbu Yana tahowa dakina, na yadda drawing book din na taho a guje gurin shi na rungume shi, ya daga ni sama ya wulla ni ya cabe nayi dariya na rungume shi. Tare mukaci abinci sannan na raka shi yayi Dan walk cikin compound dinmu sannan Muna dawowa Nanny ta min wanka yazo ya zauna gefena Yana tambayata yadda school ta kasance a hakan nayi bacci sannan ya tafi. Haka yake min kullum indai Yana gida to zai zauna side bed Dina har se nayi bacci. My father my world!








AFIYYA is not free, pay 300 into 3091721807 A'isha Hassan kwalam, first Bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258.








Shatttzzzx
[20/11, 19:31] +227 98 36 59 34: 💔 AFIYYA 💔


Four (Free)


✍️ Ayshatuuu






Karfe takwas malamin dake zuwa yimin karatun islamiyya yazo, an riga anyi min wanka nan ma se da akai rigima Dani Dan seda Abbu yazo yace yayimin alkawarin ranar birthday Dina ranar Zan fara wanka da kaina, I was super happy na yadda Nanny tayimin , ta shiryani cikin riga da skirt na lace, tea ta bani Nasha sannan ta rakoni parlor na zauna bayan na Gama gaida malamin, gaba daya karatun na one hour ne sannan ya tafi na cire hijab na dawo daki na tafi gurin Abbu. Na samu ya Gama shiryawa for breakfast so a dakin shi muka ci abinci. Bayan mun Gama yace na dakko home work Dina se muyi tare dashi, na wuce dakina na kawo backpack Dita da dayan littafin, Yana dauka yace


" Princess wannan ba littafin ki bane ai"


Na karba littafin daga hannun shi trying to confirm, dama ban iya spelling Ringim ba amma nasan six letters Suka hada ringim, ni Kuma gashi Naga four letters, sauran sunan irin nawa ne. Nayi shiru se can nace


" Abbu canjawa mukai da Amina da Zan Sha ruwa"


Ya dafe kanshi sannan Bai ce komai ba ya Ciro waya ya Kira class teacher din mu, ita ce ta fada Masa address din gidan su Amina, yasa Nanny ta canja min casual wears din jikina zuwa wata English gown, aka saka min hula da takalmi, tayimin packing chocolate kamar yadda Abbu yace a bani nakai wa Amina. A garki suke nan muka je, Abbu yayiwa security din bayani, Babu jimawa Sega wani mutum ya fito, Yana zuwa ya gaida Abbu yace mu shigo, Yana fada Masa su Basu ma gane cewar Amina ba book dinta ta kawo ba. Ciki mukaje tana ta Wasa da siblings dinta, seda ta ganni sannan ta taho hade da Jan hannuna nayi Wasa, Dole Abbu ya tafi ya barni a gida se yamma ya dawo ya tafi Dani, that's how Maman Amina ta Zama a figure a cikin rayuwata.


Duk Sunday Abbu zai kaini salon, zaa wanke kaina sannan a yanke min farce, ayimin kitso, idan na zauna Baku labarin yadda Abbu ya kula Dani Zan karar da duk wani karfina kafin na shiga gundarin labarin. Abbuna ya min duk wani Abu da uba da uwa zasu min, akwai abubuwan da kake rasawa kake samun makamancin su Amma nikam har na koma ga Allah nasan bazan samu madadin Abbu ba. Rooks cousin dita ce, mahaifiyar ta ita ce Mummy Maryam, kanwa wajen Abbu. Mijinta Dan sarkin Ringim ne Daddy. Tun da ta haifi Rooks ya samu aiki a NY se ya tafi dasu can dama field din daya karanta was international relations. Ban Santa ba se lokacin da nayi birthday Dina na shekara takwas Abbu yace zai kaini Newyork gurin Aunt dina. Banyi wani murna ba saboda ni nafi son kawai na zauna a gida Ina gannin Abbuna. Ya Mana Visa komai dasu passport ya zama ready mukaje Ringim nayi ma Hajiya sallama, se muka biya Kano wajen Uncle Tijjani Abbu ya kaini Naga Basma da Bata wuce 40 days ba. Tunda Naga yarinyar nayi tama Abbu shagwaba Nima se ya siyo min Baby, se da Anty Salma tace min naje idan na dawo zata hada Mata Kaya se na tafi da ita gidan mu. Bamu Kara kwana uku a Nigeria ba muka wuce NY, Mummy tazo airport ta dauke mu, Rooks na makaranta, inata kallon gidan, da dakin Rooks din komai na fulla ne yayi kyau sosae. Na dinga kalla with so admiration a idanuna Ina fatan inama nawa dakin haka yake. Mummy ta shigo tana min murmushi tace


" So daughter."


Na matso inda take na zauna ta shafa kaina tana ta murmushi tace


" Feel at home, Rooks ba zata Jima ba zata dawo. Yaya yaje ya huta zai dawo kinji"


Na gyada kaina Ina rarraba idanuna na rashin sabo, abinci ta kirani naci a parlor, Ina fara ci se ga Daddy da Rooks sun dawo, da gudu ta shigo hannunta dauke da backpack dinta, ta rungume ta tana shafa kanta tace Mata


" Afiyya tazo"


Ta juyo ta kalleni sannan ta kalli mamanta, se Kuma ta wuce dakin ta. Abbu yazo da daddare har lokacin bamu magana da Rooks ba kamar she's not happy nazo gidan su, Abbu washegari ya tafi ya barni shima seda aka fita Dani Dan da ya dawo kuka nayi tayi Bai zo ba. Kwana biyu na sake jiki itama Rooks ta saki jikinta Dani, seda nayi sati uku anan kafin na koma gida,shi ne mafarin sabon da mukai da Rooks.














Rayuwa ta cigaba da tafiya, Junaidu har ya Kai matakin shiga karamar secondary, Babu Kuma abinda ya sani haka dai kawai akai gaba dashi ya bar makarantar ko Allah zaisa su huta. Babu jimawa karatu ya kankama nanma ya bude sabon babin iskancin shi, baya zuwa makaranta ko Kuma yazo a makare Kuma kafin a tashi ya sallami kanshi, anan ma ya fara hada gang na bad boys Yana koya musu duk abinda ya iya. Ana haka ya shiga aji biyu daf da karshen term akai fada a gidan su. Ya dawo da yamma ya cake da abubuwan da yake zuka, Yana shigowa gidan Ashe Fatima ta bawa yarta zainab ta siyo Mata kayan Miya, yarinyar wani ya karbe kudin a hanya tana zuwa gida tace ai Junaidu ya karbe kudin. Tunda taji zance tace ai wallahi ko kasa da sama zata hade se an biya ta kudinta ta gaji da dibar albarkar da yake musu a gidannan, jiya ya daki yayanta kawai darajar zaman tare yasa ba tayi magana ba, yau Kuma gashi ya kwace kudi a hannun yarinya, me ake da haihuwar irin su, da kamar Dan Allah bani, inama da akazo haifar shi barin shi akai... Maganganu marasa Dadi Hajja Huwaila na gefe tana bakace ko dago kanta batayi ba balle ta maida martani, a ranta fada take Dan kuka me jawo uwarshi jifa, Hasiya ta fito ta kalla Fatima da har lokacin Bata bar mita ba tace


" Ke kuwa kin tabbatar shi Junaidu ya karbe kudin, kinsan yarannan sun iya karya"




" To idan bashi ba waye, shi din bako ne a gidannan da ita zainab zata kasa gane fuskar shi?"


" Ba bako bane Fatima Amma maganganun da kike fada sunyi nauyi da yawa mahaifiyar shi fa ta nan, ai da kunya"


Ta tabe baki yace


" Wannan ku ya Dana, tunda ta Haifa se ta bada tarbiyya tunda ta gagara bayar wa se ta bude kunnuwa ta saurari me zamu fada kudina se an biya ni"




Kafin Hasiya tayi magana se Suka ji maganar Junaidu a zaure yana fadin


" Zan babballa kashin ki wallahi shegiya me Kama da mayu, kin tashi ko Sena hada Miki jini a fuska"


Da gudu salama ta shigo, tayi Bayan Fatima wadda ke tsaye tana jiran taga da wa yake, shigowa yayi a lokacin kana kallon shi kasan yasha wani abun, gaba daya idanun shi sunyi jawur tafiyar shi ma Babu nutsuwa, dakin Hajja ya nufa Fatima da ganganci se ta rike Masa riga,


" Allah ya Toni asirinka, se ka fito min da kudina kafin na mare ka a gidannan"


Ya kalleta sannan ya kalli hannun ta da ta Kama rigar shi ta rike gam yace


" Ke dallah sakeni, wanne kudi kike magana anan?"


Ya fada Yana kicinayar kwacewa, ta Kara rikewa tana fadin


" To meye Dan kace min dallah Naga uwar data haifeka baka gaishe ta, ka Zama Dan shayeshaye meye Dan ka zageni, kudi se ka fiton dashi"


Hannun shi yasa ya doke nata yayi gaba abinshi, Amma Bata hakura ba tabi shi ta Kara Kama shi, a zuciye ya juyo Yana juyowa ya hambare ta, aikuwa se gata a zube a kasa, har mamakin karfin Junaidu nake, yayanta sukai kanta, Hajja Huwaila ta mike itada Hasiya sukai kanta, bakinta da hancin ta se jini suke saboda makewar da yayi Mata. Dake salama tafi wayo tana ihu ta tafi ta Kira Malam dake dakin shi, aikuwa ya fito lokacin an maida Fatima daki se kuka take wallahi ba zata yarda ba, Malam ya shigo ya tsaya yayi Shiru ya rasa me zaice saboda yadda zuciyar shi take kamar zata fito ta bakin shi. Hajja Huwaila daki ta koma ta sameshi yayi daidai ya ware fanka Yana bacci, ta daka Masa duka, ya bude idanun shi yayi tsaki ganin ita ce, ya juya Dan gyara kwanciyar shi ta fara fadin


" Tashi ka fitar min daki na, kaidao Allah ya wadaran halinka, bakai halin arziki ba San"


Dake ba fada ne da ita ba,shi kanshi a sanyaye take fadar hakan. Ya Mike ya nufi tsakar gida zai fita sega Yan sanda sunzo Kama shi Wai Fatima yayanta Ashe DPO ne anan division din Kazaure.










Afiyya is not free, pay 300 through 3091721807, Aisha Hassan kwalam, First bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258






Shatttzzzx💔 AFIYYA 💔


Five (Free)


✍️ Ayshatuuu






DPO ya turo yaran shi akan suzo su tafi da Junaidu, kunsan yadda Yan sanda suke na Nigeria kamar haushi dama suke ji balle Kuma an tabo kanwar DPO Kuma kunsan se inda man su ya Kare, suna zuwa sukai handcuffing din shi Suka tafi dash, mutane suka taru a kofar gidan Dan ganin kwakwaf, malam Yana ciki ya tasa Fatima a gaba ya zuba Mata idanu, ita Kuma ta bawa banza ajiyar shi. Da ya tabbatar ba zatai magana ba se yace Mata


" Nayi tunanin hakurin da na baki zakiyi hakuri kiga hukuncin da Zan yanke, Amma kin nuna min kinada Dan uwa"


" To Malam Naga kaima dai Junaidu a gidannan ya gagare ka, kana kallon dukan da yayi min da da karar kwana sede a Kira ka ace maka na mutu"


Bai ce Mata komai ba ya fito daga dakin nata, Kan shi har juyawa take saboda yadda ran shi yake a bace, dakin Hajja Huwaila ya nufa ya sameta tana kuka Hasiya na gefen ta


" Hasiya ni nasan Junaidu Bata jin magana Amma nasan bazai karba kudi daga hannun zainab ba, idan sata ya fara daga dakina zai fara..."


Hasiya tace


" Yanzun duk wannan ba wani amfani, kizo muje mu samu Malam ayi bailing shi"


Ta girgiza Kai tace


" A'a gwara a barshi su daka yadda itama Fatima zata ga an Rama Mata, ni abinda ya Bata min Rai Sharron Sara, wallahi Dana haifi barawo gwara ace kaf garinnan yafi kowa shaye shaye"


Anan Malam yayi gyaran murya yayi sallama ya shigo, Hasiya ta Masa sannu sannan ta fara kokarin fita ya dakatar da ita, seda ya zauna sannan yace da Hajja


" Kukan me kikeyi? Addua Zaki Masa Allah ya shirya ki Amma kukan ki kamar karar shi kike wa Allah"


Ta goge hawayen ta amma Bata ce komai ba, ya dubi Hasiya yace ta Masa bayanin abinda ya faru, tiryan tiryan ta fada Masa, ya Gama ji sannan ya fito ya kwallawa zainab Kira, tana dakin Babarta ta fito, yace ta biyo shi daki. Idanunta sunyi raurau ta bi Bayan shi zuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login