Showing 36001 words to 39000 words out of 95282 words
Chapter 13 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
shiru bacci ya daukeni daga nan.
Jin motsi yasa na rufe card din na aje na samu turaren na fesa kamshin so sweet, nayi murmushi Ina jin duk wata kewa da nake ta ragu. Da yamma Ina zaune gaban Miya da maburgi a hannuna naji sallama, Ummaan su ta dubi Hafsa dake gefen ta tace ta duba waye, kafin ma ta Kai ga fita, Sega masu sallamar sun shigo, Yan Mata ne guda biyu sun Sha kyau abinsu, Ummaan ta fara musu barka da zuwa, su Kuma se kalle kalle suke suna yatsina fuska kamar sunga kashi, but ba se an fada maka ba kana kallon su kaga yayan masu kudi, ta kalleni tace
" Se nace a kawo tabarma?"
Na aje maburgin hannuna na nufi daki Dan dakkowa naji daya daga ciki tana fadin
" No need kawai! Sako aka Aiko Wai a bawa Afiyya!"
Na juyo na kallesu da kyau lokacin na fahimci ai nasan daya daga ciki, she's called Shahida na Dan taba ganin ta gidan su Rooks sau daya. Umman su najin Haka ta Bata fuska tace
" Se ku Bata ai gata nan!"
Na dube su nace
" Sako from where?"
Dayar da ba Shahida din ba tace
" Istanbul"
Suka Mika min katuwar Leda, na karba na musu godiya suka juya Suka tafi, Nima na nufi daki Dan ajewa tace min na dawo na kawo ledar, ko musawa banyi ba na aje Mata ledar na juya na koma aikin burge miyar, ko Kara kallon gurin banyi ba, idan da sabo ai na Saba, shekara uku da wani abun ba kwanaki uku bace ba. Ina jin yadda Hafsa ke exclamation na kyan only God knows what! Na sauke miyar na juye gawayin a gaban rijiya na kashe sannan na tattara na aje inda nake adanawa, na dawo Zan wuce naji sallamar Yaya,cikin sauri na juya fuskata dauke da murmushi nace
" Yaya!"
Ya kalleni Yana min wink tareda sakar min tattausan murmushi Amma Bai amsa ni ba, se ya nufi wajen Babar shi, ta riga ta hade kayan kafin ya karaso ta kalleni tace
" Zo ki dauke tsiyar ki!"
Na karasa na dauki ledar na nufi daki Ina jin kaifin idanun Yaya da ya bini dasu, na zauna na fara Ciro kayan dake ciki, waya ce me kyau kirar infinix sabuwa dal cikin kwalin ta, se turarrruka masu kyau Wanda kwalin kawai abin kallo ne. Se abaya da takalmi a ciki. A kasan kayan Naga small paper
It's your graduation today, you know that u always in my thoughts for a second I never forget you. I hope you will like the gift. Please give me a call after! Shehu Matawalle!
Nayi murmushi Ina Kara kallon kayan, shi Bai manta Dani ba na ayyana cikin raina, gashi ni tsakani da Allah na manta dashi gaba daya. Ture kayan nayi daga gabana na aje paper, Hafsa ta shigo ta zauna gefena tace
" Saurayin ki ne ya Aiko Miki?"
Nayi dariya nace
" Wai ke ba gidan Siyama naji ance zakije ba"
Ta mike tana zumbura Baki tace
" Na tafi!"
Na Bata sakon ta gaida Siyama wadda daga baya tayi aure tana zaune acan sabon gari. Bayan sallar maghrib na samu na sulale na fita kamar yadda nakeyi, daga can gefe Yana tsaye Yana kallon kofar gida na Isa inda yake tsaye nace
" Yayana!"
Ya juyo Yana kallona fuskar shi dauke da murmushi me kwantar min da hankali yace
"Afeey ta! Congratulations know that wannan shi ne starting point, Inshaaa Allah Zan tsaya Miki Naga kinyi karatu"
Nayi murmushi nace
" Zanyi farin ciki kuwa, saboda Ina son cika burin Abbuna, I've received your gift I'm grateful"
Yayi min murmushi yace
" Inshallah! Kayan meye Ummaan mu ta baki dazun Dana shigo?"
Na gyara tsayuwa ta na fada Masa daga gurin Yaya Shehu ne, ya Bata fuska yace
" Ai nace Zan siya Miki waya ko ba Haka ba?"
Na Dan rausayar da kaina nace
" To ai bani nace ya kawo min ba, he felt like ya aiko se kayi godiya Mana"
Ya Kara tamke fuska yce
" Kinsan I don't like you with that guy ko?..."
Nayi saurin katse shi nace
" Because?"
" Saboda yadda yake kallon ki Yana nuna sonki yake, Kuma I'm sure kin fahimci hakan kawai pretense ne."
Yanayina ya Dan canja nace
" To ai shikenan!"
" And what's that? Kenan kinsan Yana son naki ko?"
Na hade hannayena alamar gajiya da maganar nace
" Please Yaya! Kai kasan Kai nake so, Kai kadai nake kulawa, so kana ganin zaka hana wani yace Yana Sona ne? It will not be, Abu me muhimmancin shi ne Kai nake so ba wani ba!"
Ina Gama fadar hakan na juya na wuce gida, Ina jin shi Yana Kirana na Masa banza, matsalata dashi kenan Babu dama wani yayi min magana ranar Haka zai wuni Yana fushi, yayi ta mita kenan. Ina zuwa tsakiyar gidan aka kawo wuta, gaba daya tsakar gidan ya dauki haske gani Kuma a tsakiyar gida sanye da hijabi, Ummaan su na zaune kofar dakin ta, ta zuba min idanu tana kallona!!!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 First bank of Nigeria A'isha Hassan kwalam, send evidence of payment to 09063467258.26
Ban taba jin tsoro ba kamar yadda naji a wannan lokacin ba, idanuna a warwaje na zuba Mata idanu Ina jiran abinda zata ce, nasan na kade Tau har ganyena. Ta mike tana kallona har ta karaso inda na tsaya na kasa motsawa, kafin na ankare ta dauke ni da Mari Wanda saukar shi seda tasa na matsa daga gurin saboda it landed unexpected
" Dama so nake na Kama ki da kaina, ai nasan kina fita. Gidan uban wa kike zuwa?"
Nayi shiru Ina rike da kuncina, Ina zance Mata naje? Ko Ina Wasa da wuta bazan ce gurin Yaya nake zuwa ba, balle ko na fada ma nasan bazata yadda ba. Jin nayi shiru ta Kai min wani dukan, na tsugunna a gurin na saki kuka, tasa kafarta ta hanbare ni
" Shiru shiru dake kamar ba Zaki aikata ba, dama nasan wannan nunkunfurcin da kike bana Allah bane, Zakici ubanki a cikin gidannan!"
Jan takalmin da naji yasa na Kara sakin kuka Dan nasan na Gama yawo Kawu Sa'idu ne, ba zai taba daga kafa yayi tafiya yadda ake Yi ba, sede ya dinga Jan takalmin sharaf sharaf, nayi saurin mikewa tasa kafarta ta maida ni , saboda yadda ta taka kafar tawa yasa naji zafi ya ratsa jikina har na saki karamar Kara.
" Gata nan! Dama na fada maka fita take Yi kaki yarda, gata yanzun dai ka ganta da hijabi, to shigowar ta kenan daga yawon ta zubar!"
Banma San meye yawon ta zubar din ba Amma nasan tabbas ba Abu ne decent ba, tsugunnawa yayi Yana fuskanta ta yace
" Ina Kika je?"
Na girgiza kaina sede bazan iya cewa komai ba, yasa hannun shi ya kwada min Mari Wanda da farko nayi tunanin fuskata ta fashe, na saki Kara Ina jin wani dum! A kunnena, ya Kara matsowa ni Kuma nayi saurin Jan jikina bayana yace
" Ina Kika je? Iskanci Kika fara? To baa gidana ba muna tausayin maraicin ki Ashe ke Baki tausayin kanki, to aure zanyi Miki tun kafin ki dakko min abun kunya"
Yadda kalmar aure zai min ta dake ni na Kuma ji zafin saukar ta bana tunanin naji zafin Marin da Suka min, na fara kuka sosae Ina fadin
" Wallahi Kawu ba abinda kuke tunani bane! Allah kofar gida kawai naje. Allah Kawu ka yarda Dani"
Ni kaina kukan da nake was breaking me, zuciyata ji nake kamar an watsa min ruwan zafi, tun farkon da nake sneaking nake fita to meet Yaya nasan I was making a lot big mistake Amma saboda yadda nake son shi ban mayi kokarin danne zuciyata ba, shi yace min Yana son abun ya Zama a little secret between us saboda yasan iyayen shi zaiyi wuya su amince da maganar auren mu, plus yana ganin idan maganar ta fito zasu ga ai har na Kai shekarun da zanyi soyayya, kenan na Isa aure!
Duk tambaya daya se ya mareni, saboda mugunta se ta rike min hannayena ta baya yadda bazan iya karewa ba, tun Ina kokarin kwatar kaina har na daina se hawaye da ya dinga bin kuncina, naji fuskata ko Ina radadi kawai yakeyi kamar an zuba min borkono. Se daya ji marin ya ishe shi sannan yace ta sakeni, ta sakeni na kallesu tsabar su ta Kara nunkuwa cikin zuciyata, yanayin fuskar Ummaan su kawai na kalla nasan farin ciki take.
" Ba Zaki tashi ki bace min anan ba?"
Nayi saurin mikewa Zan nufi daki naji Ummaan tace
" taje Ina Kuma? Ai asibiti zaa kaita amata gwajin ciki, ta Yaya na fada maka wannan ba shi ne Karo na farko da take fita ba, na kyalleta ne Naga gudun ruwanta!"
Se Naga Kawu ya kalleni fuskar shi da wasi wasi Amma Dan ya faranta ran matar shi Haka ya Jani ya tasa keyata muka tafi wani Rahma clinic dake nan kusa damu, Banda kukan fili Dana zuci Babu abinda nakeyi, Muna zuwa Babu mutane Dan haka na shiga dakin scan din, likitan na zaune da wayar shi a hannu alamu sun nuna ya Jima Babu patient. Kawu ya samu guri ya zauna tareda fadin
" Likita zargi muke tana da ciki saboda yawon banza da take..."
Babu shiri doctor ya dubeni sannan ya dubi kawu da yayi dare dare a kujera, hawaye Suka Kara gudu akan fuskata, baa taba cimin mutunci irin wannan ba. Doctor y dubi Kawu Sa'idu yace ya bamu guri, bayan ya fita yace na hau gadon Babu musu na hau ya zuba min gel cikin bare cikina Wanda seda taikar jikina ta tashi saboda sanyin shi, ya dauki pointer ya dinga gogagwa akan gel din da ya bawa light rays din damar penetrating cikin cikina, seda ya Gama ya Mika min tissue na goge cikina naja rigata sannan yace
" Amina! Waye wancan mutumin? Me ye hadin ki dashi"
Nayi mishi shiru se kawia kallon shi da nake a raina Ina saka meye amfanin fada Masa? Maganin me zai min? Yayi yayi nayi magana naki, se kuka da nakeyi Wanda Ina jin azabar ciwo da kaina keyi, zugin da fuskata takeyi da Kuma dum da kunne na yayi, har na mutu bazan manta da wannan ranar ba. Ganin ba zanyi magana ba ya fita ya bawa Kawu Sa'idu sakamakon sannan yace Masa ai alada ma nakeyi, ya Kuma San Babu yadda zaayi me ciki tayi period. Daga Haka muka juya zuwa gida, a hanya yace min
" Ba dai abin kunya Zaki jawo min ba, to aure zanyi Miki! Aure Zan Miki se kije ki dandana abinda kowa yakeji"
Bance Masa komai ba Dan banida bakin maganar, plus ban masan me zance Masa ba, roko na riga na roke shi na Kuma fada musu iyakar gaskiya ta, kuskure nasan nayi Amma I don't deserve abinda akai min. Muna zuwa gida na tarar da Yaya, Baba da Hafsa da umman su sunyi cirko cirko kamar zakaru. Muna hada idanu dashi na Kara sakin kuka, Kawu yayi tsaki ya fada Mata sakamakon scan din da nayi, ta tabe baki tace
" Ni fa bazan taba yarda fitar da yarinyar nan take ba shagon wani namijin take zuwa ba! Yadda kace kawai kayi Mata aure shi ne maslaha!"
Na dubi Yaya da gaba daya fuskar shi tayi turning pale saboda tsabar tashin hankali, idanuna na saka cikin nashi Ina rokon shi ya fada musu gurin shi nake zuwa, amma se ya kaudar da kanshi gefe, karshe ma daki ya tafi abin shi ya barni nan tsaye. Na bi Bayan shi da kallo cikeda madaukakin mamaki, how do you want me to believe cewar Yaya ya juya bayan shi a kaina, ya kasa fitowa yace dashi muke haduwa , in fact shi ya kawo shawarar Ina fita Dan mu hadu. Zuciyata naji tana bugawa da karfin gaske tamkar zata balla kirjina ta fito, hawayen dake ta suntiri a fuskata na neme su na rasa, what's the worst feeling better than been betrayed? Ina ganin shi ne worst feeling Dana taba ji a rayuwata. A wannan Daren nayi kuka kamar Zan cire idanuna, at some point na tuhumi rayuwa da yin walagigi da ni, nayi kuka na rashin madafa, na rashin gata, na rashin abinyi!
Afiyya is not free pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment through 0906346725827
Bana tunanin na taba ganin dare me tsawon wannan Daren, har so nake gari ya waye tunda nasan bazan iya bacci ba. Kukan ma ya daina zuwa, there are times a cikin rayuwar ka da kake jin komai baya tafiya daidai Kuma baka saka ran wani relief zai taba zuwa, to Haka naji, naji zuciyata ta bushe, naji I was equal and ready to whatsoever comes up, menene a rayuwa? Kin Dadi to ni nasan na Gama jin Dadi. Na mike na duba tab dita da na dakko nake amfani da ita a boye Naga biyu da rabi na dare se kawai na fita tsakar gida nayi alwala, na Jima a tsaye Ina jin iska me dadi tana kadawa, a raina nayi wishing, Ina ma dai ace matsalolina zasu bi iskar nan su tafi? Na dubi sama yadda tayi blue me kyau, ga taurari da Suka cika ta Suka kawata saman. A lokaci daya na furta subhannallah! Se naji karfin gwiwar yin addua ya kamani, na koma daki na tada sallah amma Dana idar zanyi addua se na gagara yi, na fara kuka cikin zuciyata abubuwa tari ne barkatai a ciki, da tarin bukatu a ciki, Amma bakina se yayi nauyin furta Haka, Abu daya ya kwantar min da hanakli nasan Allah yafi kowa sanin bukata ta.
Kada na cika ku da wannan maganar,asuba nayi a kunnena na fito nayi sallah sannan na gyara dakin, I wanted something to distract my mind away. Nayi shara nayi wanke wanke sannan na kunna murhi nayi dumamen tuwo na dama koko. Ta lungun dakin ta anan gawayi yake se na tafi dakkowa Dan na Kara na daura musu ruwan wanka, tun a kofar dakinta nasan Kawu Sa'idu Bai fita ba saboda takalman sa na gurin. Na Gama dibar gawayin naji tana fadin
" To ya zaka cewa Yan uwanka, kasan Dole zasu ki maganar auren"
Ya saki dariyar da naji tamkar ruwan zafi take cikin zuciyata yace
" Zance musu maza take bi, shiyasa"
" Ba zasu yarda ba, kaima ka sani! Shi mutmunin da kake fada zaka aura Mata yaushe zai zo?"
" Tunda yau Zaki fita na fada Masa ya zo gobe"
Jikina ya fara rawa nayi saurin barin gurin, da gaske ban kawo zai iya yimin aure ba, ban taba kawowa cewar Bayan wannan mummunar rayuwar da nayi ba Ashe akwai wata dake jirana ba. Na karasa komai nayi wanka na koma daki abincin ma ban ci ba Dan I'm not in the mood, bana ma jin yunwar. Ina zaune ta kwala min Kira tace min na daura abincin Rana saura Kuma idan na ga dama na Kara fita, abin da aikai min jiya ba komai ba me, sannan idan naga dama in Zama cikin shiri sati daya kawai ya rage a daura min aure. Wannan maganar ta girgiza rayuwa ta, a hankali na koma daki na zauna tareda runtse idanuna Ina tunanin aure zaayi min da gaske, nidai bana son auren tabbas, fada ma Bata Baki ne Amma Kuma ya zanyi. Motsi naji a kofar dakin Wanda yasa na juyo da sauri Amma ganin Yaya ne yasa na maida kaina kasa na bawa banza ajiyar shi. Ya zauna Yana facing Dina, Amma se yayi shiru ya gagara yin magana balle ni da ko kallon inda take ma banyi ba, na Mike Dan na fita na bar Masa dakin, bazan iya cigaba da kallon shi ba, ganin shi kawai zuciyata zafi take min, for some unknown reason se nake jin he doesn't worth me.
" They're planning to get you married, kin sani ko? Ya zamuyi ?"
Na ji muryar shi me cikeda rauni ta daki kunnena, na juyo na kalleshi he looks so pitiful, kallon shi kawai seda ya raunana zuciyata, na dauke Kai nace
" And so? Meye naka na auren da zaayi min? Ni kaina Ina mamakin dalilin da yasa na fara sonka, bansan har me na gani a tattare da Kai da yasa na soka ba..."
" AFIYYA!..."
Ya Kira da karfi tare da mikewa tsaye, Nima na katse shi da fadin
" Kar ka min ihu! Bari na Gaya maka you don't worth aurena, nayi tunanin duk inda zaaje ba zakaji tsoron ka fito kayi defending Dina Amma jiya se Naga akasin hakan, se ka kasa cewa gurin ka nake zuwa, akanka na jure abubuwa da dama Amma Kai ka kasa Kare ni a wajen iyayenka, Kai kuwa me zaka iya yimin idan na aureka"
" Afeey please kizo mu gudu, I can't imagine you with another guy..."
Ya ciji leben shi idanun shi sunyi jawur yace
" Zan Kira uncle Babawo right away na fada Masa halin da ake ciki"
Ya fada Yana Ciro wayar shi daga pocket din pants din dake jikin shi na tracksuit, na karbe wayar nace
" Don't blow up the matter so quickly Dude! Beside ni bana tunanin tunda iyayen ka Suka dage se sunyi min aure akwai Wanda ya Isa ya hanasu. Na mafi so su cigaba da daukar alhakina yadda Ina kallo zasu Shiga jahannama.."
Hannun shi ya daga a zafafe zai mareni na tsaya cak nace
" Mari? Mare ni Yaya,ai abinda ka koya kenan, sannan Dan Allah zo ka fita kafin mahaifiyar ka ta dawo tace na maka fyade!"
Ya kalleni idanun shi kamar zasu fito Dan mamakin maganganu na sannan ga bacin ran halin da muke ciki. Yana fita na saki kuka a hankali Ina rike kirjina dake barazanar konewa saboda zafin da nake ji, na Jima Ina kuka sannan na Mike na Ciro tab dita nayi connecting na Kira Rooks, kamar tana jira tayi picking fuskar ta dauke da murmushi tace
" Afeey darling!"
Na Dan saki faint murmushi nace
" Rooks darling! Ina Mummy da Abbah?"
" Wait me ya sameki, Afeey marinki akai? Me ya sameki?"
Na saki kuka da nake ta rikewa na fara fada Mata dukkan abinda ya faru, tayi shiru har na gama sannan tace
" Afeey bazan iya rike wannan