Showing 15001 words to 18000 words out of 95282 words
Chapter 6 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
Nanny a gida!"
Seda na fada naji idanuna sun ciko da kwalla, itama a yanayin yadda tayi min magana nasan jikinta yayi sanyi, na danyi murmushi me ciwo nace
" I've to live Rooks ko Dan nayi ma Abbu da Mama addua, I've a reason to live"
" Yawwa Afeey, kiyi addua komai zai zo da sauki. Yanzun kin fini class!"
Nayi dariya na gama tsokanar ta, cewa ya kamata ta fara Kirana senior, I'm not match for her Dan kuwa na fita aji yanzun. Haka muaki sallama Raina fari Kal, duk gajiyar Dana kwaso se naji ta Dan tafi. Na Mika masa wayar Ina murmushi nace
" Thank you Yaya!"
Yayi murmushi Yana kallona so intense yace
" Ya makarantar?"
Na amsa da alhamdulillah sannan nace Masa Zan shiga gida bayan na kara Masa godiya, I felt his eyes trailing on me har na shige gidan. Ina shiga na tarar dukka sun dawo, da sallama na shiga, Mino ta amsa min tana fadin
" Ina Kika tsaya?"
Na danyi shiru Ina tunanin abinda zanyi cooking, se nace
" Mhmm! A hankali na dinga tahowa"
Ta gyada kanta na shiga ciki na cire kayana sannan na fito nayi wanka, tunda naji gidan shiru nasan Ummaan su Bata nan, Nima ban tambaye ta ba Dan idan Bata nan gidan yafi Dadi. Abinci muka ci sannan nayi shara na dawo na fara kwafar note, sallamar Ummaan su naji, na daga labule na Mata sannu da zuwa, ta amsa sannan tace na aje littafin nan nazo na Mata wanke wanke, na bude baki da niyyar ce Mata ai nayi tawa sharar tunda dama shi ne aikina, Amma se nayi sealing bakina kawai na tattara littatafan na aje na fito, dogon hannun rigar dake jikina na nannade na hada kayan wanke wanken guri daya na zauna, na fara a hanakli kamar me wanke Raina, nayi nisa ta leko daga daki ta kwalla min Kira, bafa Afiyya take cemin ba sede tace min
" Ke!"
Shikenan Kuma Dole na amsa, hannuna na dauraye, kafin na karasa dakin naji sallamar Yaya Yana kwalla min Kira, na tsaya tareda juyowa kawai se Naga Nanny a Bayan shi, na cire slippers din kafata na ruga a guje na fada jikinta, na kankame ta kamar Zan koma cikin ta, ta rungume ni itama, na saki dariya wadda take so genuine and sincere nace
" Nanny!"
Ta Kara rungumeni, bana tunanin Zan manta farin cikin da naji a wannan ranar, da na sake ta Kuma se na fara Kuka me ciwo, na tuna gida na tuna beautiful moments din da mukai tare, na tuna Abbuna. Na rike hannun ta na dinga kuka Ina jin tamkar Ina shading dukkan bakin ciki, da gajiyar Dana kwasa a wannan kwanakin. Ummaan su ta fito dasu Mino dake daki, ta hade Rai tana hararata da ni bama lura nayi ba. Lallashina ta shiga Yi sannan na dakko Mata kujera nace ta zauna, se lokacin ta lura da Ummaan su Suka gaisa ni Kuma na koma kan wanke wanken da nake, Ina wanke wanken Ina Mata tambayoyi tana amsa ni, su kansu nasan Basu taba sanin inada surutu har haka ba. Na Gama wanke wanken tana ta Bina da kallo har na Kai kwanukan kitchen tana zaune, fuskarta na nuna tausayi da Kuma mamakin wata daya yadda na koma wata daban, tana zaune na hura wuta kafin ta Gama kamawa na leka nace da Ummaan su me zaa dafa, tace na Kira Mata Mino na tafi gurin Nanny. Ina Shiga daki da Nanny Sega Yaya, ya shigo hannun shi da Leda ya bani, ruwa ne me sanyi da carbonated drink, nayi murmushi na Masa godiya, na bude Mata na Bata Amma se kallona take, na riko hannunta nace
" Nanny naji dadi da Kika zo, kullum se nayi addua ko ke ko Uncle Babawo wani yazo, Allah ya amsa addua ta"
Se Naga hawaye suna sauka daga fuskarta, nace
" Me yasa kike kuka Nanny, kin tuna Abbuna ko? Ina Masa addua kullum bana mantawa"
Ta riko hannuna tace
" Me yasa Kika rame? Baki cin abinci ne? Ko aiki kike da yafi karfin ki?"
Yarinta ce tsagoro a tare dani, ga wautar Yan fari, ga gabuntar autanci na zauna na fada Mata duk halin da nake ciki, na Kara cewa
" Nanny Babu dadi anan, komai Babu dadi, rayuwar gaba daya Babu dadi, dama haka kowa yake komawa idan baban shi ya rasu ko Kuma ni ce Kawu Sa'idu baya so?"
Ta girgiza Kai Amma ta kasa magana, se ta rungume ni a jikin ta, mukai sallah, a Jakarta ta fito min da foiled kaza, na kalleta na Kara rungume ta, na zauna naci nayi nak, Dan haka da aka bani jollof din taliya nace na koshi. Guntun lemon da tayi na shanye, wa yaga komai se da dalili Kuma an Dade Baa hadu ba. Ranar bacci nayi me dadin gaske, dukda katifar ta matse mu Amma ban damu ba. Da sassafe kamar kullum na tashi na fita shara na hura wuta sannan na gama nayi wanka na dawo na tarar ta bude akwatina na, ta dubeni tace
" Ya akai duk kayan datti a ciki?'
Nace
" To Nanny bazan iya wankewa ba"
Ta gyada kanta kawai, ta fito dasu, wankakkun kadan kawai Suka rage!
AFIYYA is not free, pay 300 through 3091721807, first Bank of Nigeria Aisha Hassan kwalam, send evidence through 09063467258
Shatttzzzx
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Karfe biyu daidai ya tashi daga baccin da yake, lokacin da kowanne Dan Adam dake neman dacewa a wajen mahillicin shi Yana ibada, ko Kuma kowa na kwance na hutawa daga gwagwarmayar da aka Sha da rana, shi Kam Junaidu lokacin ya fito inda yasa salama tun dare ta hada Masa wuta a Mangal yasan zuwa Daren ba lallai ta Gama cinyewa ba, Yana zuwa ya tono anan ya samu har lokacin wutar akwai saura. Ya diba ko tsoro baya ji, baka jin motsin kowa se iska dake kadawa da Kuma karnuka dake haushi, se wild kukan tsuntsaye dake wucewa, ga garin yayi duhu kasancewar watan ya Kai karshe. Ya Gama fifita wutar sannan ya dauka ya shiga dakin sa ya duba lokaci yaga yayi daidai, ya dakko kaso na biyu na maganin ya fara ambulawa a ciki. Hayaki, tukuki duka Suka gauraye dakin, haka ya Gama yayi kwanciyar shi. Da safe ya tashi da wurwuri Dan yasa ran shi zaije makaranta, Dan hakan da wuri ya fita a gidan ba tareda ya nemi kowa ba kamar yadda yasan hajja Huwaila ce kawai zata nemeshi. Yana zuwa makaranta ya zauna bakin aji, ko Ina ya canja Dan yafi wata rabon shi da ya shigo cikin makarantar, idan ka kalleshi ba zaka taba ganin alamar fitina a tare dashi ba, idan ka kalleshi sede ka ga gentle guy with promising future amma a badini bazaka kawo shi ke tantirancin da yake ba. Yana nan zaune har mutane suka fara zuwa, Yan ajin su na asali tuni suna ss2 Amma shi baima San wanne aji yake ba. Yana ta zaune har makamai Suka fara Kora a shiga aji, shima ya Mike kamar na kirki ya nufi aji. Can karshe ya samu ya zauna, Wanda suka lura da zuwan shi a ajin suka dinga zuwa suna gaisawa Kuma suna jajen ya Jima Bai leko ba, sede ya danyi murmushi yace abubuwa ne Suka Masa yawa. Yana zaune sauran gang din shi Suka karaso,suna hango shi suka fara ihu suna hailing din shi, shikam Banda murmushi Babu abinda yakeyi, Jarma yace
" Shegen! Amma ko jiya bakace zaka zo makaranta ba"
Ya shafa Kan shi da hannu yace
" Kawai na tashi naji ya kamata nazo"
Malam yayi dariya yace
" Wai baka ga admin block Bari daya ya kone ba? Ko ka tambaya"
Junaidu ya Dan leka da mamaki ya fara binsu da kallo yace
" Guys badai ku..."
Bai karasa ba sukaji shigowar principal, sergeant, senior Master da sauran kuso shin school din, sergeant rike da zabga zabgan bulali daga bishiyar maina, kowa a ajin ya tashi in chorus Suka gaishe su sannan, principal yace su zauna, kowa gaban shi faduwa yake kada ma Malam da Jarma suji labari.
" It's with dismay that I'm announcing to you the expulsion of some of student in this class. They tempered with the rules and regulations of the school, bullying junior student, coming to school late and leaving school before closure. With all this they went ahead and burnt some part of the administrative block to ashes. Junaidu Ibrahim, Hafizu muhmmad Jarma, Idris yakubu, huzaifa hannafi, I want you out here!"
Junaidu ya kalle su duka Suka Mike, malam yace
" Guy kace kawai baka nan, Babu yadda zaayi ka karba punishment din mu"
Ya girgiza Kai yace
" A'a komai tare muke Yi Dan hakan wannan ma tare zamuyi"
A tsakiyar makaranta aka saka su sukai lie down flat, sergeant ya dinga dukan su kamar Allah ya Aiko shi, Banda ihu Babu abinda suke, seda bulalaen suka karye kafin kowa aka damka Masa expulsion letter dinsu Suka tafi! Kowanne class ka gani zakaga sun leko suna kallo, Yara da yawa fuskokin su kamar gonar auduga Dan farin ciki. Haka Suka dakko jankunkunan su suka fita daga makarantar jiki duk tsami. Malam ke ta kuka Dan yasan irin nashi iyayen, irin yadda dama suke cin kaniyar shi akan rashin jin shi da Kuma bad guys da yake bi. Shikam goga ko a jikin shi Banda jikin shi dake tsami Amma tun a kofar gate ya faffalla takardar ya yaga, a ranshi yasa tunda aka koreshi to kuwa ya Gama makaranta har abada. Zama sukai suka saka Malam a gaba suka dinga lallashin shi tareda nuna Masa is not necessary se ya fada a gida kawai kullum yayi Shirin makaranta ya taho se suje gareji su koyi aiki, idan time din waec yayi suje wani garin suyi. Da haka ya Dan kwantar da hankalin shi.
A bangarena Babu abinda ya canja, kullum wahala Kara Sha nake a gidan, kafin wani lokaci na rame nayi zuruzuru, lokaci zuwa lokaci nakan dauki tab dita idan Babu kowa nayi chatting Maryam. Seda nayi sati na uku sannan ranar Monday da sassafe min tashi kamar kullum. Na kwashe shimfida ta, na fito tsakar gida na dauki tsintsiyar na fara shara, yanzun na iya Babu wannan tsihin, dan Dole ma seda aka saka na koya, seda ya zamana safiya da yamma ni ke shara saboda na kware, ga dundun da Babu fashi matsawar nayi messing Kuma tana gurin. Tun inayi Ina hawaye har ya zamana na ma daina. Na fara shara a hankali kamar yadda yake a jikina, ni ba mutum bace me sauri and I'm not too slow. Na Gama na hura wuta Siyama ta daura abincin safe seda suka Gama wanka sannan ni na shiga a karshe, uniform Dina Mino ta Miko min wani Jan wando farar riga da Kuma Jan hijab, se bakin sandals kwaya daya da stockings daya. Na kalla na kalleta idanuna sun washe nace
" Makaranta zanje?"
Tana murmushi ta gyada min Kai, na rungume kayan Ina jin Dadi a cikin raina, it doesn't matter to me ko wacce makaranta aka kaini indai Zan cigaba da karatuna that's what matters to me. Cikin sauri na shirya, na dakko body mist Dina da ya rage baifi feshi biyu ba na fesa a hankali sannan na mayar cikin kayana, da tuni na yiwa Abbu dogon list, komai nawa ya kare, Abbu bama ya jira se Abu ya Kare, da zarar wata yazo karshe to Nima zai kaini shopping na saya duk abinda nake so. Na girgiza Kai Ina share hawayen da ya fara min tsartuwa a fuska, na furta
"I've missed you Abbuna, Allah ya Kara rahmarsa gareka"
Na fito na same su suna karyawa, na zauna na gaida Ummaan su ta dubeni ta tabe baki tace
" Meye kike ta dariya da sassafen nan se kace an Miki albishir"
Nayi murmushi Wanda inaga tunda nazo it was the genuine smile da na Yi, ta tabe baki ta dangwara min kofin bakin tea din da aka dafa, na karba na fara Sha aka yago min bread na fara ci a hankali, remembering yadda indai bread ne is either toast ko akwai spread din mayonnaise, jam ko chocolate spread Amma ni ce nake yagar shi haka. Har na Saba da abincin da nake ci a gidan, na hakura da komai Dan it's not changing no one is rescuing me. Mun Gama duka muka tashi Dan tafiya, na dauki bag Dita me Asalin kyau tun days Dina na Yar gata, books din kwaya Tara ne Wanda nasan idan js3 ne to tabbas subject din yafi hakan. Kawu ya fito sanye da jallabiyya, na tsugunna na gaishe shi, Suma suka gaishe shi, ya dubeni yace
" Uwata se makaranta ko?"
Na dago Ina murmushi nace
" Eh Kawu"
Ya gyada kai Yana murmushi dake Bata min Rai, Dan fuska biyu ne dashi Yadda yake nuna min tamkar Bai masan yadda nake rayuwa a gidan ba Amma ni nasan ya sani, I might be a little naive girl but am not stupid, kwalkwalwata is very sharp, kallonka kawai zanyi I can see through you.
" To ayi karatu da kyau"
Na gyada Kai na juya na bi bayan su, makarantar da Dan tafiya daga Ausar haka mukaje a kafa, kafin mu karasa ba karamar gajiya nayi ba. Ina zuwa mukaje office din principal ni da Mino, ya dubeni yace
" Amma Malam Sa'idu baice min yarinyar karama bace sosae"
Mino ta dubeni ta kalla principal din Amma batace komai ba, Dan Bata San yadda sukai da principal da kawu ba. Haka yasa ni a gaba ya kaini class, mutane da yawa a cikin class din, banbancin dake tsakanin makarantar Dana Bari da wannan abin ba zai auni ba. Yace nayi introducing kaina ma Yan class din na fada musu, sannan ya Samar min guri a gaba na zauna, ya Kira wata Sauda yace ta Zama kawata. Na zauna a seat din Ina rarraba idanu a ajin. Yan kusa dani sunata kallona yawanci mamakin kankanta ta suke. Ban Jima ba first period ya shiga, wani malami ya shigo, duka muka tashi Dan gaishe shi ya amsa yace mu zauna, duka muka zauna ya rubuta physics a board, anan na fara wondering kenan ss1 aka kawo ni, ni js3 Zan Shiga fa!
Shatttzzzx
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Na Kara runtse idanuna Ina kokarin dadira wukar a wuyana, many thoughts running through my mind, idan na kashe kaina kowa zai huta, tunda suna ganina tamkar liability ce gare su to gwara kawai na kashe kaina zaifi sauki. Ina dirzawa naji wani irin azabar zafi saboda wukar ko yanka albasa seka dirza balle kashe Kai, na yarda wukar na saki kuka tareda durkusawa a gurin, se Kuma wani tunanin yazo min, idan na kashe kaina Allah a wuta zai saka ni, Ina kallo Mama da Abbu zasu tafi aljanna, I can't be able to reunite with them, ko Kuma Kawu Sa'idu da Ummaan su Mino da ta cuce ni suje aljanna ni da aka cuta saboda na kashe kaina na tafi wuta! Da sauri na Mike Ina girgiza Ina fadin that's not possible I've to live, na dauki wukar na fito tsakar gida, akwai wata tsohuwar rijiya a gidan na jefa wukar ciki, danma kada na cigaba da ganinta suicidal thoughts din Yana zuwa min. Na koma daki na kalla kayana se Kuma na fara tunanin ko dai na gudu ne? Na Shiga duniya kilan na samu wani Mai imanin ya dauke ni! What idan na fada mugun hannu da yafi su Kawu Sa'idu? Na ayyana hakan. Zuciyata se taci galaba a kaina, na bude trolley karama na dauki necessary na saka hijab, I've made my mind I'm leaving this house. Na fito Ina zuwa zaure mukai kicibis da Yaya, ya tsaya Yana kallona Nima Ina kallon shi, hawaye na sauka Kan kuncina, ya kalleni tun daga kasa har sama, mamaki sosae a fuskar shi, ya bude baki zaiyi magana nayi saurin ketare shi Zan wuce Dan ya Gama Bata min budget, hannuna ya kamo hakan yasa na tsaya Ina kicinayar kwacewa,
" Ina Zaki je Afiyya? Me ya faru dake? Me akai Miki?"
Duka a tare ya jero tambayoyin, na kwace hannuna daga tsatsauran rikon da yayi min, Amma kafin na Kara daga kafata na bar gurin tuni ya rike hijabi na, jawo ni yayi har cikin gidan, inata turjewa Amma seda ya maida ni, na tsugunna a kofar dakin Ina jin shima haushin shi nakeji, kaina kamar zai fado saboda kukan da nakeyi, ga jikina dake ciwo.
" Kina ganin idan kin gudu shikenan kin Gama Shan wahala? How will you even think of this? Wa Kika sani Ina Zaki je?"
" Ka rabu Dani na tafi, na gaji da wannan rayuwar gwara naje ko Ina ne tunda kowa baya Sona!"
" Wayace Miki ba a sonki? Muna son ki mana, ni Rooks and your Nanny, you've to stay for us kinji?"
Ya Jima Yana lallashina seda yaga na hakura sannan ya barni yaje ya siyo min abinci a wani eatery ya kawo min naci sannan na shiga daki na kwanta wani bacci me nauyin gaske ya dauke ni.
ISTANBUL, TURKEY
Daddy ya cire glasses din idanun shi, tamkar cire glass din zai Kara Masa karfin jin sakon da yake amsa ta waya ne, Amma sede maganar da ake Masa tayi Masa nauyi a cikin Kan shi ya kamata yama bada hankalin shi gaba daya akan maganar.
" So yanzun Kai a Ina kaji wannan labarin da kake fada min?"
Daga dayan bangaren yace
" Ranka ya Dade bazan iya fada maka ba Amma yarinyar tana cikin matsala, Alhaji Abubakar Bai cancanci jinin shi yasha wahala ba, shiyasa na Kira na fada maka!".
" Wannan hakane na Kuma gode sosae!"
Wayar ya kifar ya Mike daga Kan kujera ya Isa jikin suit holder dake gefen shelf dinsa, ya dauka ya zura sannan ya rike kugun shi ya fada tunanin Abbuna, haduwar su ta karshe a ringim ne da sallah yaje gidan shi yake ce Masa
" Abubakar me yasa baka kokarin hada Afiyya da Yan uwan mahaifiyar ta"
Ya gyara Zama yace
"Mariya ta kawo karata kenan?"
Abbu yayi dariya yace
" Halima ta rasu, ta bar yarinya a kaida tunda princess karama ce to ya kamata su zasu dinga nemanta,