Showing 84001 words to 87000 words out of 95282 words

Chapter 29 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6667

kuwa. Dad ya dubi Kawu Sa'idu yace


" Ban zo gurinnan Dan na hada aure ba, nazo na bawa yata kariya ne, ni ne ubanta ni ne me hakkin zaba Mata abinda nake ganin ya dace da ita. Junaidu kace kana son ganin Afiyya gata Ina sauraronka"


Naji dadin maganganun shi, naji karfin gwiwa da Kuma Jin Dadi a raina. Junaidu ya taso yazo ya tsugunna har gabana inda nake zaune ya dira gwiwar shi biyu a kasa sannan ya fara roko na na yafe masa, yasan ya cutar dani...bla..bla...bla...


Tunda ya fara magana nake kallon shi, he seems moody, dukda dama bantaba ganin faraar shi ba Amma nasan da gaske shi din se a hankali, but yanzun akwai sabon Abu a tattare dashi. Kaina na girgiza nace


" Duk abinda ka min, son ranka ne ban maka komai ba, Amma kayi min komai, Dan Haka yafe maka bakai zaka ce ba ni ce Zan gani idan ka cancanci hakan."


Kowa yayi tsit nasan mamaki suke, Kawu Sa'idu ya fara kokarin magana Dad ya dakatar dashi


" Right dinta ne idan taga zata yafe to? Ni bazan matsa Mata ba saboda ita kadai tasan wahalar da Tasha"


Kawu Tijjani ya gyada Kai yayinda na dubi Junaidu he looks disturbed abin tausayi kawai Baki daya, da idanu na pleading I'm sure da su zaiyi amfani wajen plead din, na dauke kaina se naji muryar Dad na fadin


" Ni fa na Gama magana ba zata koma gidan shi ba"


Malam da se lokacin yayi magana yace


"Aji ta bakinta tukunna"


Dad yayi dariya yace


" Afiyya Zaki koma gidan Junaidu?"


Kafin ya karasa na girgiza kaina na Kuma bude Baki nace a'a Dole Haka Suka tashi Sika tafi sannan Dad yace min Hasher yazo musu da batun Yana sona, Yana son na nutsu sub bani kwana biyu na zaba ko Hasher ko Shehu, banma motsa ba kaina a kasa nace


" Yaya Shehu na zaba!"




Afiyya is not free pay 300 to A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
59






Labban Dad sukai curving alamar sakin murmushi da yayi a ranshi Yana ayyana Afiyya my daughter, na kalli kowa naga yadda dukka suke kallona Mummy ma mamaki ne kwance a fuskarta Amma Kuma she looks impressed. Ka u Tijjani ya dubeni yace


" Know that wannan din is final, ba Zaki zo kice wani Abu ba Kuma"


Na gyada Kai na nace


" Na yadda Abiey"


Yace


" Tashi kije"


Nayi musu godiya fuskata dauke da murmushi na fito zuwa tsakar gidan Ina shakar numfashi me dadi, Ina jin tamkar nayuwa kaina babban zabi, se yau naji inada yanci da aka barni na zaba abinda nake muradi da kaina. Ina zuwa kofar gida Junaidu ya taso tare da nufo inda nake, ganin ya Sha gabana se kawai na tsaya tare da kallon shi fuskata a hade nace


" Menene?"


Yace cikin marairaice fuska


" Amina ki bani dama Dan Allah na Kara Zama mijin ki a Karo na biyu, wallahi bazan Kara yin abinda nayi ba"


Nayi mishi wani mugun kallo me cikeda tsana, I can't deny the fact that I hate him, seeing him makes me sick, irin sick dinnan fa, yanzun ma da nake tsaye dashi nasan se nayi zazzabi ko mura, nasan Rukayya Amin zatace samun guri, to Amma Rayyanatu tasan cewar ko lokacin Ina gidan shi bana son shi bana kaunar shi kawai Ina jurewa ne saboda a lokacin banida mafita, Kuma lokacin shi din mijina ne Dole na Masa biyayya!




" Junaidu inaga baka ma fahimce ni ba ko? Ka kalla idanuna kaga me Nene a cikin shi. Ka sani wancan Lokacin da na zauna da Kai Babu yadda zanyi ne, ni idan ni ce Kai emphasizing zanyi akan na yafe maka Amma ba Wai kokarin maida ni ba, ni din na maka nisa"


" Amina Dan Allah ki bani dama na gwada Miki yadda son ki yayi tasiri cikin zuciyata, a dalilin ki na gyara halayena..."


" Ina maka murna"


Na fada Ina waving hannuna me wayata a rike, juyawa nayi na wuce Dan na gaji da Jin maganganun shi. Har na like Yana tsaye Yana kallona yayinda nake tafiya cikin nishadi da farin ciki. Wayar shi Dake cikin aljihun shi ta fara kara alamar Kira ya shigo yayi saurin Ciro ta sede number ma baayi saving dinta ba, ya kura ma lambar idanu kafin Kuma ya dauka Yana sallama se Kuma ya Kara marairaice fuska Jin muryar Safiyyu,


" Mutumin se ka fito ka bace a duniya! Ko tambayar wanne Hali nake bakai ba"


Safiyyu ya fada cikeda nishadi, Junaidu yayi wani furza yace


" Ba kanta fa alamura sun rincabe anan din"


Cikeda rashin fahimta Safiyyu yace


" Me ya faru? Badai wani abun bane Kuma"


Junaidu ya Dan jinjina Kai yace


" Akan Amina ne..."


" Wacece Amina? Tukun yaushe ka Bari har mace ta Shiga rayuwar ka har kake tunanin ta. Kaga wannan maganar mu hadu a kazaure kawai"


Ya kashe wayar, Junaidu yayi shiru yana kallon wayar wani irin azaba yake ji cikin zuciyar shi, gani yake matsawar Afiyya ta kubce Masa to zauce wa zaiyi, Dan Haka yake ganin kawai zai amsa tayin zuwa ya hadu da Safiyyu, Dan yasan zai sama Masa shortcut din komai.




Ban Jima ba na karasa gidan mu, tun daga gate nasan Hafsisi da Mino na gidan, Nima da farin ciki na na shiga bakina dauke da murmushi, a tare suka zo suka rungume ni Ina yin sallama, Nima na rungume su, seda muka zauna Nads tace


" What a reunion"


Nayi murmushi na zauna muka gaisa nace


" Mino Ina Siyama? Ita ya bata zo ba"


Ta tabe bakinta tace


" Tana gida auren ta ya mutu"


Na jajanta musu da gaske har Raina banji dadi ba, mun Jima muna Hira kafin Kuma Suka min sallama Suka tafi, na dawo wajen su Rooks a daki na zauna Ina kallon Nads nace Mata


" Nads Kan Yaya Hasher daya yake kuwa? Me yasa zaije yace Yana Sona Bayan na fada Masa Honey nake so"


Nads ta kalla Rooks tace


" Ke Baki San waye Yaya Hasher ba, su fa Haka Yan gidan su suke. Kinsan brother din shi Ya Hussein Haka ya so Yar Anty Ya Kaka, do you remember her?"


Na gyada Kai na, ta cigaba da fadin


" Asiya wadda ta fada mishi ita tana da Wanda zata aura Amma da yayi blowing maganar a family seda kowa ya fara ganin laifin ya Asiya har yau zancen da nake Miki Basu shiri"


Nayi tsaki nace


" Tabdi ni Kam I'm no match for that nonsense, ko a gaban waye zan fada nace Honey.."


Ban ma karasa ba Sega wayar shi ta shigo, na saki murmushi me ainahin kyau daga karkashin zuciyata na dauka


" Ni nayi fushi ma! Tun jiya baka neme ni ba"


Ya Dan marairaice fuska yace


" I'm sorry my Darl! Kin dawo a gajiye nasan kina bukatar hutu shiyasa. Where are you? Can I see you?"


Na kallesu kowacce hankalin ta akaina yake nace Masa Ina gida , se yace to zai zo zuwa yamma. Babu jimawa Mom da Dad har Nanny Suka dawo, Dad ya kirani dakin shi gashi gani ga Kuma Mom yace


" Can you find a soft place a zuciyar ki ki yafawa Junaidu?'


Na gyada Kai yayi murmushi yace


" Can I ask a favor?"


Na sunkuyar da kaina nace


"Babu favor Dad, just order me I'll comply"


Yayi murmushi na Jin Dadi yace


" Zanyi fixing date din aurenki kafin mu koma Lancaster, saboda wannan abubuwan sun fara damuna, bana son yadda kowa ke cewa Yana son ya aureki"


Na Dan kalleshi saboda abin yazo min a bazata ban Yi planning aure kwana kusa ba, Amma ya zanyi hakan yasa nace


" Dad duk yadda kayi is ok!"


Ya gyada Kai yace


" I'm sorry yazo abruptly, mutane na threatening position din Shehu, so zamuyi magana dasu duk yadda ake ciki Zaki jini"


Na gyada Kai na fita na samu Rooks zasu tafi gida hakan yasa Mom tace na bisu tasan Zan Dan ji dadi, Babu musu na bisu Amma se na kasa fada musu abinda aka ce. Muna zuwa mummy ta Gama girki tasa aka zuba Mana ta zaunar damu muka ci kafin ta kirani dakin ta


* Hope baa takura Miki ba zancen auren?"


Na girgiza kaina nace


" A'a Mummy kawai banyi expecting din shi close Haka ba"


Tace


" Eh, muma ba Haka muka so ba, Kinga shi Shehu ba yaro bane, na tabbatar aure yake so but Yana Kara ne, idan ma Istanbul zaku zauna we can transfer you makarantar ki can, se Kuma Kinga Junaidu har yanzun ban aminta dashi ba ke har Sa'idu they can do and undo,dukda muna addua Amma ya kamata mu Zama wary of them. Kiyi addua nasan banida matsala da Shehu Ina Miki fatan farin ciki me daurewa Afiyya, Inshaaa Allah burin mu na ganin rayuwar ki ta inganta ya a dab da cika"


Ta fada tana bude hannunta Babu musu na shiga ta rungume ni, se naji na Dan ji sanyi a raina, Kuma Nima Ina hango idan baayi auren ba kamar na shiga hakkin shi da yawa, all what matters to me shi ne naga Yana farin ciki.






" Nadia ya na ganki ke daya Babu Rukayya balle Afiyya"


Ummiey ta fada lokacin da Nads ta koma gida ita daya, ta cire veil dinta ta aje ta dubi Shehu da ya fito rike da hula me glass, Yana sanye da wani yadi me laushi fari tas hatta aikin da akai fari ne, hannun shi ya samu ado da kyakyawan silver agogo, fuskar shi Banda annuri Babu abinda take fitarwa, ya karaso Yana jin Nads na fadin


" Rooks zatai bako ne, ita Kuma Afiy kinsan Yaya Shehu dai ya rabaki da yarki"


Shehu ya kalleta kamar yadda Ummiey ke kallonta


" Ban gane ba"


" Ba kace zaka aureta ba, tana can kunya takeji. That girl should be sent back to 18cents. She's too local"


Se Jin duka tayi a hannunta yace


" Afiy yayarki ce, you should know this"


Ummiey ta mike tana fadin


" Zo mu tafi, I need to see her"


Shehu yace


" Wai Ummiey Ina Zaki? Gurin Afiyya Wai?"


" To da Ina? Kasan yaushe rabon da na ganta?"


Ya Bata Rai sarki na ta dariya yace


" Ummiey Zaki Bata Masa shiri, ki Bari gobe se kije kawai"


Ta dauki mayafi tayi gaba tana fadin


" Sede shi ya fasa, Ina son azo a tukani"


Shehu ya kalli sarki yace


" Bro talk to your mother naaa"


Sarki ya kwashe da dariya yace


" Man just follow her kasan ba ji zatayi ba!"






. Afiyya is not free pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.60














Duk wannan fara'ar da murmushi duka suka dauke yayi kicinkicin da fuska shi a Dole ta takura Masa, ita Kam Ummiey ko kallon shi batayi ba a ranta tana ayyanawa lalali Shehu ya girma, she battled with him akan ma ya yadda yayi budurwa lokacin Kuma da yayi budurwar se Kuma tazo a wadda Babu Wanda yake kallon ta dace ayi soyayya da ita. Ta sauke ajiyar numfashi tana fadin yanzun Sarki ya rage dukda shima ya tsayar Amma Kuma family yarinyar na ta Masa Wasa da hankali, Dan dai kawai Bata son shiga irin wannan shirgin da zata ce kawai ya hakura ya nema wata.


Kallon shi tayi lokacin da yayi parking kofar gidan mu, ya dubeta fuskar shi a sake, shi Haka yake Bai Faye fushi me tsaho ba yace


" Ummiey muje"


Ta fito sannan ya rufe motar Yana baya tana gaba, ni Kuma Ina daki na na Gama shiryawa cikin wani Jan material me tsantsi, jikin shi anyi embroidery da green din zare na kananan flowers. Dinkin riga da skirt. Inata kokarin daura dankwalin Amma tsantsin shi ya Hana ni na daura. Se kawai na dakko veil na yafa tun daga kaina Dan ya rufe bakin gashina. Body mist Dina na fesa sañnan Kuma na dauka wayata Dan fitowa Jin kwalla min Kira da Mom keyi, na samu na fito kafata sanye da wani flat shoe green Wanda aka Masa ado da clear Crystals a jiki. Ina fitowa mukai Karo da ita alamar gurina zata zo, nayi saurin ja baya ta dubeni tare da maida ni daki tace


" Ina kallabin ki yake?"


Na nuna Mata nace


" Na kasa daurawa yayi tsantsi da yawa"


Ta girgiza Kai tace


" Come let me help you, ya kamata daga yau ya ganki cikin kyawun yanayi saboda yau dinne akai officiating relationship din ku"


Ta fada tana daura min dankwalin in a turban wrap, na kalla kaina Naga yadda nayi kyau na saki murmushi nace


" Amma an fada mishi cewar auren is close?"


Tayi dariya tana kallon fuskata tace




" Su Suka nema ai, dama Uncle din ki na kokarin yin hakan se Kuma Suka ce suna so"


Na gyada Kai nace


" School Dina fa?"


Ta mike tace


" Idan yazo feel free ki tambaye shi duk abinda kike so , ok?"


Na gyada Kia ta fita tana fadin na zauna idan yazo zata saka a Kira ni. Wayata na dauka Ina karawa a kunne saboda Kiran da ya shigo, Yaya Hasher ne, mun Jima bamuyi magana ba dama Kuma Ina son Kiran shi naji yaushe na Masa alkawarin aure kamar yadda ya fada. A dakile yake magana kamar Wanda akai Masa Dole hakan yasa nima na amsa kamar irin ya dameni dinnan.




" Afiyya yanzun ke Baki ji kunya ba a tambaye..."




" Sorry I've to go Ina da baki"


Na fada tare da sauke wayar daga kunnena na dubi Nanny dake tsaye nace


" Nanny nayi kyau kuwa?"


Bakinta dauke da murmushi tace


" Sosae ma kuwa. Afiyyata ta girma gashi har zatayi Aure. Allah ya albarkace ki"


Na karasa na rungume ta nace


" Amin Amin uwata ta kaina"


Se ta fara dariya tace


" Sakeni kije Hajiya Mariya na jiranki"


Na juyo da mamaki nace


" Ummiey Kuma? Me yasa tazo?"


Bata bani amsa ba Mom ta fara kwala min Kira, na bubbuga kafata nace


" Bata San kunyar ta nake ji ba ko?"


Na fita kaina a kasa , tana zaune kamar kullum cikin lace anyi Masa dinkin bubu, she looks expensive like always, na kalleta kafin na Kara maida kaina kasa nayi sallama sannan na tsugunna gefen ta tayi saurin dago ni ta zaunar gefen ta tace




" Haba Afiyya ta Yaya Zaki dawo Baki zo kin gaishe ni ba, I'm hurt Afiy"


Mom tana murmushi tace




" Ai me Borno ya shiga tsakanin ki da yarki fa"


Ta gimtse fuska tare da fadin


" Kowa Haka yake fada min Maman Afiyya, gaskiya ni bana son Haka. Afiyya I'm your mother kinji? Ki saki jikin ki Dani"


Na gyada kaina na gaishe ta ta amsa sannan tace min


" Tashi kije gurin shi, I need to talk to your mom"


Na gyada Kai na sannan na silale na fice, Yana tsaye Yana kallon entrance din alamar Yana Jirana, Ina zuwa ya saki murmushi Yana fadin


" Here comes the Queen!"


Na saki murmushi, Ina ganin watarana idan dariya da murmushi zasu Kare to tabbas nawa zai Kare, hardly na hada idanu dashi banji Murmushi ya kubce min ba, he gave me every reason to smile and laugh, kusan dukkan abinda nake so Yana kokarin ganin yayi min, in fact we share and understand the same love language. Na karasa inda yake nace


" Ni nayi fushi da Kai fa"


Ya shafa fuskar shi yace


" Tun dazun nace kiyi hakuri fa. Kinga yadda kikai kyau kuwa. You're putting the stars to shame fa"


Na saki dariya Ina daga kaina na kalli kyawaawan taurarun da Suka kawata sama nace


" Am I that beautiful?"


Yayi murmushi ya dawo gabana ya tsaya yace


" You're beautiful, you're perfect Baby, I love everything about you"


Na rausayar da kaina Ina jin wani Abu Yana Kara shiga cikin zuciyata zuwa jinin jikina, I found myself falling for him. Wannan lokacin bamuyi ma hirar da mom tace ba se soyayya kawai da mukai, sede lokacin da muke Hira nake spotting wayar shi na haske saboda ya aje ta a saman mota, sunan da akai saving ya fara da NU ya Kare da BA. Banma nuna masa na gani ba saboda I'm really enjoying the moment. Seda Ummiey ta fito sannan mukai sallama Suka tafi. Ina dawowa na wuce daki ko abinci ban nema ba. Na cire kayan jikina Sega Mom ta shigo da waya a hannun ta Wai zamu zaba furniture, na marairaice fuska nace


" Can we leave it zuwa safe Allah na gaji"


Se ta gayda kanta kawai ta yimin sallama, na dauki wayata na fara Kiran shi Bai dauka ba ya katse ya kirani


" Har an fara kewata?"


" Wacece NUSAIBA? Is she that same lady?"


Na tambaya Ina tsatsare shi da idanuna, ku kwace wallahi Yana gabana. Ya sassauta murya yace


" Damsel ki tsaya kiji"


Nace


" A kwance nake Kuma shi ne dalilin da yasa na kiraka, I want to know who the hell she's, wannan Karo na hudu Ina tare da Kai tana kiranka, fada min wacece ita"


Jin muryata ta fara sama na tashi na zauna shi dinma se ya fara lallabani


" Ai na Baki labarin ta, she's in the past Damsel..!"


Nayi dariya nace


" Ok yanzun ma daga past din take Kira kenan? See Honey gaskiya idan you over her tell her karta Kara kiranka idan ba Haka ba ni Zan fada Mata"


Ko ta Ina zan iya? Waya ga cika baki a gurina, seda na tabbatar na hargitsa shi na Kuma saka Masa a zuciyar shi ni ba wawiya bace and I'm not into such nonsense sannan na kashe wayata gaba daya.






A wañnan yammacin Junaidu ya koma Kazaure, Yana zuwa ya Kira Safiyyu Wanda yace su hadu can wani guri gaba da Shaiskawa, Haka ya Niki jiki ya tafi har zuwa can ya sameshi a zaune shi daya. Bayan sun gaisa ya dinga Masa dariya Wai me yeya koma wani kamili, shidai Junaidu ya dakatar dashi ya fada Masa ainahin abinda ke faruwa Safiyyu yace a washegari zaije maradi ayi ta ta Kare. Junaidu ya tafi dukda Yana jin Anya yayi hakan ko dai ya Bari yaga abinda Allah zaiyi Amma Ina yasan aikin Safiyyu kamar yankan wuka take!






Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258


Afiyya is not free pay 300 to A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258[24/02, 13:22] +227 98 36 59 34: 61
















Junaidu ya samu abun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login