Showing 48001 words to 51000 words out of 95282 words
Chapter 17 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
musu su shirya zasu unguwa, kowacce da murna Dan ba fita suke sosae ba Suka tafi shiryawa. Tana yafa mayafi taji sallamar Jidda matar Jazuli yayan Junaidu, ta shigo kamar yadda ta Saba se ta fara shigowa gurin ta kafin taje wajen Hajja ma, wannan Hajja ta koya musu girmama Hasiya. Hajja sukaiwa sallama sannan Suka fita, Jidda nata tambayar inda zasu je, Malam ya Basu kwatancen gidan Suka tafi.
Bayan na Gama binciken da banma San me na gani ba, na dawo parlor na zauna na tafka uban tagumi Ina tunanin yadda rayuwa take zuwa ma mutane, ni dai tawa bansan yaushe Zan bude shafin da zanyi dariya ba, bansani ba ko bazan Yi dariyar ba ko Kuma se nan gaba. Kwankwasa gidan yasa na Mike Ina mamakin waye, katon clock din dake manne jikin bango na kalla karfe biyar da mintina, daki na wuce na dakko bakin veil din dana riga na fito dashi, na yafa sannan na fita zuwa bakin kofar nace
" Wannene?"
Dukda jira nake naji muryar me gidan yace ubanki ne, Dan nasan wannan karamin aikin da zai iya ne. Muryar babbar mace naji tace
" Kannen Junaidu ne"
Who's Junaidu? Na tambayi kaina, se lokacin kaina ya tuna sunan me gidan kenan, cikin hanzari na bude kofar tareda Dan ja da baya Dan na Basu guri su shigo, wadda ta fara shigowa Gwoggo ce wato Hasiya, se Kuma Yan Mata biyu sannan Anty Jidda. Na saki fuskata dukda murmushin da nake Bai Kai zuci ba Amma dai naji dadi da wasu Suka nuna sun damu Dani. Jidda ta kulle gidan na musu sannu da zuwa sunata Bina da kallo har muka shiga parlon, Ina jin yadda suke gasping na tsananin kyan da parlon yayi, na musu tayi su zauna sannan na zauna saman carpet
" Ina wuni?"
"Lafiya Lau"
Ta amsa ni Ina iya ganin tsanin farin cikin da take ciki, sauran Suka gaishe ni na amsa Ina Wasa da hannuna
" Ina Junaidun?"
Nayi Dan Jim kafin Kuma nace
" Mhm ya fita"
Ta gyada kai, Anty jidda tace min
" Ya sunan ki?"
Ina Dan murmushi nace
" Amina sunana"
Ta gyada Kai sannan na Mike Ina tunanin yadda Zan samo musu abinda zasu Sha, na nufi kofar da nake tunanin kitchen ne, na tura nan na samu carton din ruwa lode, wata ajiyar zuciya na sauke ba tareda na bi takan kallon kitchen din ba na dakko glass tumblers na kawo musu, sunata min sannu. Na dubi ta gefe na nace
" Ya sunanki?"
Tace
" Sadiya, wannan Ambaby mu kannen shi ne, wannan Anty jidda ce ita matar yayan mu ce, ya girmi mijinki. Wannan Kuma Gwoggo ce "
Na gyada kaina na fahimta nace
" Nagode!"
Daga Haka mukai shiru se can Suka Mike zasu tafi, na Mike na rasa me Zan Basu, se na tuna ai Naga containers din gara a kitchen, cikin sauri naje na babbude na diba musu me yawa na kawo musu tareda musu rakiya har bakin kofa, nace da
" Dan Allah ki dinga zuwa. Gwoggo nagode sosae"
Na fada Ina jin tun bayan rasuwar Abbuna ga Wanda suka nuna min kukawar su. Ciki na koma Ina ayyana nayi Saar in-laws ina fatan Zan iya Zama dashi, Ina fatan halayen shi zai gyaru. Ruwan da Suka Bari na tattara na Kai kitchen na shiga bandaki nayi alwala jin har an fara Kiran maghrib, nayi sallah sannan na zauna Ina tunanin inda Zan samu fitila na haska, Dan duhu ya fara Shiga, Allah ya kalla sincere zuciayata se gashi an kawo NEPA, nayi sauri na Mike Ina hamdala, wata Leda na hango a kasa, alamar Ina janyo Kaya ta fado, nayi sauri na Mike na dakko ledar a take naji farin ciki ya mamaye ni ganin waya sabuwa a ciki, na dakko na saka caji sannan na zauna gefe Ina jin yadda cikina ke kugin Yunwa, har wani ciwo ciwo yakeake min. Wasa Wasa har ishai banji shigowae shi ba, hankalina ya fara tashi ga Kuma Yunwa ga tsoron ni kadai ce a gidan. A lokacin wayar ta cika hannuna na rawa na kunna ta, hatta Sim da komai is set, na Shiga contact Dina number mummy na gani da sauri nayi dialing Babu jimawa ta katse Sega kiranta ya shigo, hannuna karkarwa yake na Kara kunnena nace
" Mummy!"
" Daughter? Ya kike? I'm very sorry I failed you again"
Na danyi murmushi me ciwo na gaishe ta tana ta bani hakuri tace min
" Ban San yadda zamuyi ba Afiyya Amma ban taba ganin tashin hankalin irin na yau ba, kiyi hakuri kiyi addua itace mukai sake bamuyi ba, itace sakacin da mukai har Sa'idu ya samu ya dinga controlling dinmu, Ina son kiyi addua ni Kuma I'll do whatever it's in my power Naga na raba aurennan!"
Motsin da naji yasa nayi saurin Mata sallama, nayi silencing wayar na fito, yana tsaye a parlon Yana kallon kofar dakin Dana fito daga ciki, na karaso Adan dadare nace
" Sannu da zuwa"
" Kawo min ruwa"
Na juya na dakko Masa ruwa da tumbler na dawo na sameshi ya zauna cikin daya daga cikin cushions din da Suka kawata parlon, na aje Masa tareda Zama can nesa dashi Ina rarraba idanu ganin ko ya shigo da abinci, can nace
" Dazun Gwoggo tazo da...."
" Wacece Gwoggo? Uban waye yace ki bude min gida mutane su shigo min?"
Gabana nata faduwa nace
" Kannanka ne"
" Nace Miki inada dangi ne? Wallahi wannan shi ne na karshe da Zaki budewa wasu gidannan. Tashi ki bani guri"
Na mike Babu musu na kwashe kayan gaban shi na Kai kitchen sannan na dawo, Yana nan zaune nayi ta maza nace
" Banci abinci ba!"
Ko kallona baiyi ba balle na saka ran ko yaji abinda na fada, nayi Dan Jim sannan na nufi daki Amma se naji idan nayi bacci da wannan yunwar to kilan mutuwa zanyi. Na mike na cire kayana nasa kayan bacci na zumbula hijab na fita parlon. Yana nan inda na barshi, na Kara matsawa nace
" Banci abinci ba!"
" To ki cinye ni Mana idan ke mayya ce! Kin ishe ni fa"
Nayi saurin ja da baya saboda yadda hargagin shi ya tsoratar dani, nayi saurin juyawa Zan tafi daki se na tuna kayan gara na bude kitchen na dauki diblan da alkaki naci sannan na koma daki na zauna naci nayi brushing sannan na kwanta, banma kawo zai zo dakina ba Dan hakan na saki jiki nayi bacci!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[05/01, 14:34] +227 98 36 59 34: 33
Juyi kawai nake saman gadon dan Babu wani bacci ma da yayi kokarin zuwa ya dauke ni, na Jima a Haka da wayata a hannu Ina ta bubbude social media accounts, na bude WhatsApp da Wattpad, se Sabin Gmail account. Inata tunanin yadda Zan yiwa kaina Shirin zaman wannan gidan, da dukkan alamu Babu wani zaman lafiya ko farin ciki a cikin tarayyar mu. Ga daga farawa har an fara da horon Yunwa kenan an gudu ne baa tsira ba. To idan hakane se nace gwara zaman gidan Kawu Sa'idu akan wannan. Can wajen biyu Naga to da wannan tunanin da nake zaifi ace Allah na kaiwa karar dukkan abinda yake faruwa. Na mike nayi alwala na dawo na kalli gabas na fara sallah, dake shedan babban makiyi ne se na fara Hamma Ina jin bacci, Haka na Dan kwanta Ina tasbihi bacci ya daukeni, bani na farka ba seda ana iqama, cikin hanzari na sake alwala sannan nayi sallah na Kara bingirewa nayi bacci a gurin. Wajen bakwai ringing din wayata ya tashe ni, na bude idanuna a hankali se Naga garin yayi haske hakan yasa na Mike da hanzari na dauki wayar, bakuwar number ce tunda dama banyi registering contact din mutane ba, seda na fara wanka sannan na shirya cikin wata atamfa skirt da riga ban daura dankwalin ba se na saka hijab na fito parlon, Babu alamar an fita Haka Babu alamar ya tashi, kitchen na shiga na wanke tumblers din da nayi amfani dasu jiya kafin na fara tunanin me zanci, Yunwa nake ji kamar zanci Babu. Tukunya na dakko na daura ruwan zafi na fito na tsaya nayi shiru ina tunanin ko dai na tashe shi nace Masa Ina jin Yunwa, se na tuna yadda mukai dashi jiya, yace min idan ni mayya ce to se na cinye shi, idanuna suka ciko da kwalla na tausayin kaina, Amma se Naga me yasa Zan fara kuka tun yanzun? Idan har na fara to tabbas zuwa nan da wani lokaci lacrimal gland Dina zai daina secreting tears. Kitchen na koma nayi shiru Ina kallon yadda komai ya tsaru a ciki, komai ka kalla kasan an narka kudi, na goge hawayena, dama da wannan abin da kudin da suka kashe Wanda nasan daga aljihun su yake inama tsayawa sukai akaina, Suka zaba min rayuwar da zanyi farin ciki, Dan Ina da tabbacin duk abinda aka siya min ba daga gadona bane nasan daga aljihun su ne, mistake daya sukai na barina hannun Kawu Sa'idu Wanda shi ne dalilin lalacewar komai a rayuwata!
Kan fridge na hango wani tray an jera gwangwanin Madara da sauran kayan tea, yadda kuka San anyimin albishir da Shiga aljanna Haka naji, na dakko na aje Kan kitchen island din sannan na zuba tea bag a ciki ya Kara tafasowa, Ina tsaye Banda murmushi Babu abinda nake, tunda aka fara bikinnan Babu abinda yayi min farin ciki irin ganin kayan tea dinnan, na hada shayi me kaurin gaske Wanda rabo na da Nasha me kaurin shi tun Ina gidan mu. Na zauna na dakko cake cikin kayan gara naci sannan na zuba Masa a flask na fito dashi parlor na aje. Kitchen na koma nayi gyare gyaren abubuwa har lokacin Bai fito ba, na dauka cake na saka cikin transparent dish na kai Masa. Ina bincike a kitchen din Naga stew cikin bucket ai tuni na Nemo tukunya na juye ta nayi warming sannan na Nemo container na juye na bar wadda zanyi amfani da ita a tukunya na zura cikin fridge. Motsi naji a parlor hakan yasa nayi saurin fitowa, shi dinne ya fito cikin coffee jallabiyya, fuskar shi a murtuke Yana kokarin hada TV, na karaso na zauna can nesa dashi nace
" Ina kwana?"
Bai amsa ba Haka Bai juyo ya kalleni ba, har seda ya gama sannan ya zauna na kalle shi nace
" Na hada maka tea"
Ya gyada kai, na karaso na hada Masa tea sannan na bude mishi cake din, ya kalleni cikin Isa yace
" Meye wannan?"
Na Dan hadiyi yawu nace
" Cake ne!"
" Ba zanci ba!"
Ya fada Yana ture dish din Wanda Banda na rike Babu abinda zai hana shi fashewa, why is he so aggressive? Na tambayi kaina, dauka nayi na koma kitchen ban Kara bi ta kanshi ba, daki naje na zauna na tarar da calls din da nayi missing, Mummy na fara Kira muka gaisa ta fada min inda kayan gara ta suke wato foodstuffs, ta Kara koya min dabarun Zama da Kuma hakuri. Ina gamawa Uncle Babawo ya kira mun Jima muna waya sannan Rooks dasu Nads Suka Kira, Nads nata tambayar yadda first night Dina ya kasance, takaici yasa na kashe wayar, se daga baya Rooks ta kirani
" How's it over there? Ina fatan Babu matsala"
Na danyi murmushi marar sauti nace
" I'm fine! Zaki zo ?"
" Mummy tace zamu zo kafin mu koma, akwai abinda kike so ne?"
Na gyada Kai na kamar tana gabana nace
" I need contraceptive pills please"
Da mamaki tace
" Planning zakiyi? Akwai abinda ya Shiga tsakanin ku ne?"
Na girgiza Kai nace
" A'a Babu Amma I want an armor, yadda Zan Kare kaina"
Cikin rashin fahimta tace.
" But why Afeey?"
Nace
"Ba Zaki gane ba Rooks life is not what it's seems! Duk yadda zanyi Miki bayani ba Zaki gane ba, Amma ni dai bazan iya hada zuria dashi ba"
" Ke!!!"
Naji maganar shi Yana tahowa towards dakina, na Yi saurin Yi Mata sallama akan zamuyi magana na aje wayar na fito , wani irin kallo yake min na rashin mutunci irin ni banza dinnan ce, nace
" Gani!"
" Ke bakiji Ina kiranki ba? Ke dabbar Ina ce"
Na dauke kaina gefe cikin kasa da murya nace
" Ni ba dabba bace"
OMG! Ashe ya jini kawai se ji nayi taf ya wanka min Mari,
" Keeee! Baki San ni waye bane ko? Waye dabban idan bake ba Dan uwarki?"
Na mishi banza na dauke kaina, fuskata ya juyo dashi Ina fuskantar shi yace
" Waye dabban?"
Na fara kici kicin kwace fuskata, ya da hannun shi tun karfin shi ya hankade ni na tafi ta baya na buge kaina da abin shoe rack dina, na rike kaina naki dagowa saboda yadda nake jin azaba a cikin kaina, yaja tsaki sannan ya juya ya bar wajen, na Jima a gurin Ina kuka sannan na koma daki na wanke fuskata, na kwanta nayi shiru Ina jin daci a cikin Raina har cikin bakina. Wajen azahar na daura shinkafa nasa cikin flask sannan na zuba nawa Amma da na dauki spoon se na kasa ci, na rufe fuskata na saki kuka, meye makoma ta a cikin wannan auren?
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258
[05/01, 14:34] +227 98 36 59 34: 34
⭕Matured content!
Ina ta juya abincin Wanda yayi sanyi sosae, da na tabbatar ba zanci abincin ba se kawai na rufe na fito parlon, dama tun kafin azahar ya fita, jin ana kwankwasa kofa yasa na wanke fuskata da sauri Baki na dauke da adduar Allah yasa su Ambaby ne. Fitowa nayi sanye da hijabi, banma tambayi waye ba saboda na sawa zuciyata kawai ita din ce na bude kofar, na samu wasu Yan kananan Yara ne Basu fi shekaru goma zuwa Sha biyu ba, na matsa musu suka shigo sannan na maida kofar nayi jamming, tare muka Shiga parlor Suka zauna na tambaye su daga inda suke a amsar su na fahimci daga yaran neighbors Dina ne. Na zuba musu abinci sannan na koma kujera na zauna deep in thoughts. Bayan laasar na fito daga daki na idar da salla nazo na cewa yaran bazasu tafi gida ba saboda kada a neme su, Naga mutum a tsaye, jikina har rawa yaso farawa saboda tsorata da nayi, nayi kokarin danne tsoron da nake ji saboda nasan zai iya using wannan tsoron da nake mishi ya gallazawa rayuwata, tunda kwana biyu kawai nayi Amma Ina jin tamkar I'm living in a hell! Yana tsaye ya zura hannayen shi a aljihu Yana kallon yaran da I'm not sure idan sun San da shigowar shi ma, na karaso jikina a sanyaye Dan banso ya samu yaran cikin gidan ba saboda warning din da yayi min akan barin mutane su shigo.
" Su waye wadannan?"
Na kalle su sannan na kalleshi na rasa me zance Masa saboda tsoron magana nake ma ya kaimin Mari, fuskata has had enough slaps. Ya daka wa yaran tsawa duka Suka fice har da me manta dankwali, jikina se ya fara rawa Dan nasan ni ce next, kafin ya ankare nayi saurin juyawa na nufi daki Amma Ina shiga Ina kokarin rufe koafr na ganshi a bayana, na ja da baya idanuna a warwaje kana kallon yadda kirjina ke kasa da sama, ya tura dakin ya rufe sannan ya matso inda nake tsaye Ina tunanin yadda zan Kare kaina, yayi shiru yana kallon fuskata wadda da ace shi me Imani me kamata yayi ya rungume ni ya shafa bayana ya rada min a kunne cewar everything will be ok? Ashe shi tunani yake lokaci yyai da boka ya fada Masa, idan ya kusanceni to tabbas burikan shi zasu cika. Ajiyar zuciya ya sauke tareda saka hannun shi ya angaza ni na fada Kan gadon, kaina ya bugu da katakon gadon wani azababben zafi ya ratsa kwalkwalwata da dukkan jikina, Babu shiri na saki wani ihu Wanda yasa yayi saurin sakina alamar ya tsorata, ganin ba wani Abu bane yasa Bayan hannun shi ya buga min a fuska a take hancina ya fara jini, saboda dukan ya kai. Na saki kuka marar sauti bani ma da karfin yin me sauti, ya dage skirt din jikina ba tareda wani romance ko wani Abu ba ya fizge pant din jikina, it's more like a rape than normal marital affair! Wani ihu na saki Ina kankame jikina, tamkar Zan hadiyi zuciyata Haka naji lokacin da naji bare skin din shi na gugar nawa bare skin din, ture shi nake Amma Ina Bai ma ji, se wajen minti uku naji banji komai ba se tsaki da ya saki tareda ture ni gefe, nayi saurin tashi nayi toilet na kulle na daura kaina kan sink na saki marayan kuka, kuka nake da karfi zuciyata da dukkan jikina kunci suke, kuka nake na rashin madafa, na rashin gata, na rashin sanin yadda zanyi, Ina jin kaddarar tayi min tsauri, a Haka Zan cigaba da rayuwa, I'm been molested, wacce irin rayuwa ce wannan? Nayi kuka har bansan iyakar lokacin da na dauka a toilet din ba, se a karshe na fito na samu baya nan. Tun daga nan na rufe kaina a daki na fara laluben cikin drawer inda nan Rooks tace min ta aje min sako. Wani Dan karamin diary na dakko daga ciki, na kalla diary take na tuna shi, why did I forgot about it? Na tambaya kaina da mamaki, na kalla buttons din na tuna a cikin jirgi yake cemin passcode din date of birth Dina ne, na kankame littafin na saki kuka Ina fadin
" Abbu I missed you, Abbu ka barni cikin wahala"
Na dinga kuka Ina jin wata irin kewar shi tana Kara mamaye Raina, iyaye sune komai lokacin da suna da Rai Babu abinda na rasa, kowa Sona yake, kowa kaunata yake, duk inda naje rubibi na ake Amma kalleni yanzun, ni dinnan dukka gata na cikin kiftawar idanu komai ya lalace, banida wani gata, banida wanda Zan saka kaina akan kafadar shi nayi kuka, wannan itace rayuwar? I'm been tortured a hakan yanzun Zan cigaba da rayuwa? Na Kara sakin kuka na bare