Showing 69001 words to 72000 words out of 95282 words
Chapter 24 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
ba Amma yanada yakinin boka yace Masa Afiyya ba zata Dara ko Ina ba daga Ringim, so Dole ya maida auren ta da Junaidu Dan ya samu abinda yake so. Haka ya cigaba da tunani har suka Isa, Bai ma bi ta Tasha ba se kawai ya samu napep ta Kai shi kofar gida, Hanson ya bashi ya wuce ciki, tun daga kofar gidan yake jin muryar kubra
" Wallahi ba se anjima ba, yazunnnan ki tattara ki koma gidan mijin ki, Nima nan zaman umarni kawai nake, Amma Babu wadda zata kashe auren ta ta dawo gidannan, Nima naji da nauyin kaina"
" Ummaah wallahi Allah Ummaah bazan iya cigaba da aurennan ba, Dan Allah ki barni, nayi tunanin nan gidan mu ne, nayi tunanin kowanne lokaci na dawo Ummaah zaku saurare ni, zaku tsaya kuji meye matsalata, wa nake dashi Bayan ku? Ummaah na gaji da aurennan bazan iya ba Kuma"
Ummaan su ta Kara hayayyako Mata ba tareda Tama gane me Siyama ke fada ba,
" Duk abinda zai faru, ko me ake Miki Dole ki hakura ki zauna, kowacce mace a gidan mijin ta hakuri take. Yanzun tashi ki fice min a gida"
Siyama ta dinga kuka Wanda yasa jikin Kawu Sa'idu yayi sanyi, a hankali ya saka kanshi cikin gidan ba tareda yayi sallama ba, so gaba daya su biyun bama su lura da shigowar shi ba, seda Siyama ta mike tana share hawayen tana fadin
" Ummaah Zan tafi..."
Bata karasa ba ta ci Karo da Kawu, ta saki jakar hannun ta ta saki ihun kuka tareda durkusawa tace
" Baba ka dawo!"
Lokacin kubra ta hango shi, ta taho Babu wani Abu ta rungume shi, sede yadda yaga gidan ya canja tun daga kofar gida, maganganun su, yanayin kubra da ramar da tayi yasan suna cikin bakin talaucin da ya guda tun farko.
Ina kwanciya bacci me dadin gaske ya dauke ni, I felt new and relieved. Se nake jin Kamar na fara sabuwar rayuwa ne, I felt so happy da a Banda mafarkin farin ciki Babu abinda nayi, I'm sure da cewar da zaa haska fuskata da zakaga murmushi ne kawai a kwance akai. Sallar asuba ta sa na tashi nayi sallah sannan nayi wanka, dakin Mom na wuce Dan nasan Dad na masallaci Bai dawo ba. Tana zaune har lokacin bata tashi akan sallaya ba. Na gaishe ta se kallona take tana murmushi nasan tana tunanin abinda ya sani farin ciki har Haka ne. Ban wani Jima ba na koma na dakina Ina tunanin abinda tace min
" Yayanki zai Yi breakfast nan, bansan me yake so ba, Zan fito zuwa anjima se mu fara ko?"
Na gyada Mata Kai, tana nuna min na tambaya me yake so hakan yasa na kunna data na fara chatting Nads up, ta dinga dariya jin tambayar da na mata, se ta fada min daga karshe. Tareda Mom mukai Gama, wajen tara Ina zaune a daki Nanny ta shigo tace nazo inji Mom, na kalla kaina yau atamfa na saka riga da skirt na daura dankwalin bayan na saka sweater a sama saboda sanyin da aka tashi dashi. Fuskata tayi fes se glowing take kamar Rana, na fito cikin nutsuwa da wayata a hannu Ina karbar korafin Yaya Hasher da yace nayi bacci jiya without even saying goodnight, yau na tashi ban ce Masa Good morning ba. Banyi replying ba saboda karasowa ta parlor, se na saka wayar a flight mode na zauna kujerar Dake kallon tashi, yeah shi fa Yaya Shehu ya karaso. Da murmushi fuskata nace
" Good morning! How's London?"
Yayi murmushi me kyau yace
" Not bad Amma akwai sanyi"
Na gyada Kai na Mike na nufi kitchen Dan Taya ta kawo abinci. Tare muka ci suna Dan Hira yayidan jefi jefi na Kan yi murmushi ko dariya. Bayan mun kammalla na kwashe kayan na Kai kitchen anan Mom ke cemin zasu fita itada Dad se yamma zasu dawo, Nima nayi changing my fita da Yaya Shehu na Dan nuna Masa gari.
I'm sorry, Dan Allah kuyi hakuri my exams is starting on Monday Inshaaa Allah, shiaysa kuke jina shiru, I've lots of documents da ko budewa banyi ba. Amma inshallah zanyi typing 50th page tomorrow se Kuma na Gama exams. Thank you for understanding!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 50
Na Jima tsaye gaban wardrobe din nawa Ina tunanin abinda Zan saka, dama ta barni da atamfar jikina Amma nasan idan tasan da atamfa na fita se nasha fada. Haka nan na dakko black trouser da pink top na saka na taje gashina in a bun sannan na saka bakar hula. Socks na saka na dakko sabon sneakers Dina pink da ya kawo min jiya na saka, na fesa mist sannan na dakko katuwar jumper na saka na fito bayan na dauki wayata da credit card din da nake amfani dashi. Yana zaune shi da Nanny suna Hira, Ina rufe kofa dukkan hankalin su ya dawo kaina, Nanny nata murmushi ganin fitowa ta, yayin da shi Kuma ya zuba min idanun shi Yana kallo na lokaci zuwa lokaci Kuma se ya Dan lumshe idon shi, a hankali na tako inda suke na dube shi nace
" Yaya muje?"
Ya mike Yana sighing na dubi Nanny nace
" Nanny se mun dawo na siyo Miki ice cream?"
Ta harareni tare da fadin
" Tsofe tsofe Dani me zanyi dashi, Allah ya kiyaye. Me Borno kada kuyi dare"
Ya juyo Dan har yaje bakin kofar fita Yana murmushi yace
" Inshaaa Allah Nanny"
Daga nan ya fice Nanny ta dubeni tare da fadin
" Wuce Mana se yankare Baki kike"
Na turo bakina Ina juyawa na fice ba tareda na sake magana ba, Yana zaune a mazaunin driver Yana kallon wayar shi, cikin nutsuwa na bude side din shi na shiga, ya dago Kan shi daga Kan wayar yace
" You look beautiful Damsel"
Nayi murmushi Ina jin Dadi a raina Amma bance komai ba, ya tada engine sannan yayi reverse muka hau titi sannan ya fara magana cikin nutsuwa
" Wanne course kike a school din?"
Nace
" Nursing nakeyi"
" Why? Nursing is stressing"
Na kalleshi Naga alamar zolaya a fuskar shi hakan yasa nace
" Law ma ai is stressing"
Yayi dariya wadda tasa na shagala kallon shi, ya Dan daki steer wheel din kadan yace
" Kin Rama kenan? But can you do that tedious work?"
Na danyi Jim nace
" Zan iya"
Yace
" Ok! All the best then. Kinsan cewar I got your back ko? Komai Nene kike so Zan tsaya Miki, I just want you happy"
Ina murmushi da ya fitarda hakorana na dube shi, I felt some gush of feelings cikin jinina, nace
" Na sani and thank you"
Ya girgiza Kai Yana kara maida Kan shi Kan titi yace
" Meye na godiya, a husband should all this to his wife"
Idanuna a warwaje nace
" But you're not my husband ai"
Yayi dariya tareda Kai hannun shi ya lakuce min hanci na yace
" See you I'm trying to be, ai wannan Karan zaa bani chance ko?"
Na gyada Kai na Ina murmushi Wanda ke saka min nutsuwa cikin Raina, ya gyada Kai tareda shafa kanshi yace
" That's my Damsel"
Daga Haka se mukai shiru, motar tayi shiru Nima na Dan lumshe idanuna tamkar me yin bacci Amma bashi nake ba Ina tunanin rayuwa ne da yadda take canjawa, Ina daukar rayuwa tamkar littafi Dake kunshe da chapters Wanda kowacce chapter baka San menene a ciki ba, se idan ka bude, farin ciki da bakin ciki Basu dawwamma Dole akwai canji Haka ma akai Mana alkawari, ba lalle rayuwa taxo maka yadda kake so ba ko Kuma yadda ka tsarata ba Amma Kuma lokuta da dama canjin idan yazo zai Faye maka alkhairi saboda Allah shi yasan menene kake bukata kaima kanka lalube kake a cikin duhu. Na saki ajiyar zuciya tare da bude idanuna jin yayi parking, se Naga min iso kofar wani katon mall ne, ya dubeni yace
" Let's go in! Ke ace ki nuna min gari Amma Naga alamar ba inda Kika sani"
Nayi murmushi nace
" Itama Mom tasan fa ba inda na sani se school Amma tace Wai na rakaka"
Yayi dariya tace
" She wants us together shiyasa"
Na Dan tabe baki nace
" Idan bana so fa?"
Se Naga ya tsaya da unbuckling seat belt dinsa yace
" What? Me Kika ce?"
Na juyar da kaina dayan bangaren Ina kallon yadda mutane ke zirga zirga a ciki da wajen mall din, ya saka hannun shi ya juyo da fuskata Dan na kalleshi, hakan yazo min a bazata na ture hannun shi, shima se ya sauke Amma still fuskar shi a Babu annuri but he looks Charming, exactly Ina kallon shi naji tamkar charm nayi saurin cewa
" Nifa ba Haka nake nufi ba! Ni fa bana son kaga ko Zan soka Dan wani relationship we have, no I want to love you for who you are"
Wannan Murmushin da yayi Yana kallona tamkar wani karamin yaro da ake Mika Masa alawa, he was so happy as I can see, nayi saurin bude kofar motar na fita Ina gyara moppler dake wuyana a zagaye, kaina a kasa Ina tuhumar kaina da sakin bakina har na fada Masa abinda na boye tuntuni nake tunanin Kuma yaushe Zan bayyana shi, but wannan Charming looks din nasa yasa na furta abinda banyi niyya ba. Nayi shiru har ya karaso ya kalleni Yana Murmushin da Bai bar fuskar shi ba yace
" Muje Damsel!"
Na gyada Kai har lokacin kaina a kasa yake, yayi dariya da tasa na kalle shi ya dage min girar shi, munyi yawo cikin mall din sosae na ware duk abinda na gani Ina so se na dauka takama ta na taho da credit card Dina, shima idan yaga girly Abu zai dauka nayi tunanin Nads yake Siyama seda muka je biya na Mika nawa credit card shima ya Mika nashi, na dubi cashier Dake kallon mu nace
" Use mine please!"
Hannun shi yasa ya karba nawan sannan Kuma ya bada nashi aka Mana packaging muka saka a mota, ya daukeni zuwa Bayan mall din Wanda yake kamar garden ga swings dasu wheels a gurin, kasancewar weekends ne couples da yawa da Kuma Yara sunzo gurin. Na hau Kan swing na kasa swinging seda yazo ta bayana ya tura ni sanann na fara Yi with full force, ya dawo gabana Yana min video,inata dariya tun karfina, har cikin zuciayta nake jin tsananin farin cikin da nake ciki. Se bayan laasar sannan muka fara kokarin komawa gida, Amma Kuma Ina Shiga mota Sega Kiran Aisha kawata, course mate Dita ce, na dauka muka gaisa tace min na zo school akwai tutorials da zaa fara in 10 minutes, na kalleshi dukkan hankalin shi na kaina, na girgiza Kai saboda na gaji ruwa kawai nake son naji a jikina dukda sanyin da ake ciki, na
" Ba lallaii nazo ba gaskiya, kiyi min jotting down seki turon ko ta telegram ne please"
Daga Haka mukai sallama, ya dubeni yace
" Whatsup Damsel?"
Cikin ko in kula na mashi bayani ya girgiza Kai yace
" No you're going, muje na kaiki will wait for you har ki Gama kinji?"
Ba yadda zanyi na gyada kaina muka dauki hanya, Babu jimawa muka Isa, tare dashi muka Shiga har venue din ya samu guri ya zauna, yayin da Aysha ke cemin
" Kince da ba Zaki zo ba Kuma?"
Na danyi murmushi nace
" I changed my mind ne"
Tace ai gwara da Kika zo, gurin shi naje nace
Bari mu fara, ya min murmushi tare da dunkule hannun shi na bani courage na koma na zauna, duk inda na kalle shi se Naga ko dai Yana kallon wayar shi ko Kuma Yana kallona a Haka muka Gama sannan muka fito, Yana gaba Ina biye dashi se few of my friends da muka fito tare dasu. Aysha ta dubeni tace
" That guy a Bayan class kamar ba Dan class dinmu ba ko?"
Na gyada Kai nace
" Tare muke dashi"
Ta zaro idanun ta tace
" OMG! Amina he's so cu.."
Da sauri nayi cutting dinta Dan Kar ta Fadi abinda zanji haushin ta ko Kuma nan gaba taji kunya nace
" He's my fiance, shi Zan aura idan mun Gama level 2. Muje ku gaisa"
I can see kunyata a idanun ta, Naja hannun ta har sauran ma, Yana tsaye Bai shiga motar ba, nace
" Honey! My friends"
Ya dube su da fuskar shi wadda ke dauke da Murmushin kullum yace
" Is nice meeting you! How's studies?"
Duka suka amsa, ya dubeni inata murmushi Nima yace
" I'm taking my Damsel away hope you don't mind?"
Janet tayi dariya wadda kusan dukkan su dariyar suke tace ba karamin matching mukai ba, we look beautiful together, idan bazai damu ba zata Mana hoto. Na Dan matsa kusa dashi dukka hakoran mu a waje akai Mana, ta min waving wayar akan zata turon, mukai sallama sannan na shiga shima ya zagaya ya shiga ciki ya tada motar, a hankali yake tafiya tamkar a kafa muke tafiya yace
" Da gaske after level 2 zamui aure?"
Na dube shi da sauri nace
" Ya akai kaji?"
Ya nuna min kunnen shi Yana dariya, na dauke kaina yace
" It will be coming soon kenan, na kusa Nima nayi owning abinda tunda na fara ganin shi ya hargitsa min lissafi, how will it be having you as my wife Damsel?"
" It will be lovely ko?"
Na fada Ina dariya ya girgiza Kai yace
" Abu ne da ni kaina bansan yazan kwatanta shi ba, Ina fata komai yazo cikin sauki ko?"
Na gyada Kai. Munata Hira har muka Isa gida, ya kashe motar ya fitar min da kayan sannan ya bani key din akan zaije yayi wanka ya dawo dinner, Ina tsaye har ya kule kafin na shigo ciki da Kaya Niki Niki, dakin Mom na Kai Dan har lokacin Basu dawo ba, kitchen najee na samu tana burabusko, na zauna bayan mun gaisa na hada coffee na Sha sannan na barta Dan hutawa kafin dare ya karasa Yi.
_There goes my heart beating_
_Cuz you're the reason_
_I'm losing my sleeping_
_Please come back now_
_There goes my mind racing_
_And you're the reason_
_That I'm still breathing_
_I climbed every mountain_
_Swim every ocean,_
_Just to be with you_
_Fix what I've broken oh_
_Cuz I need you to see that you're the reason!_
Banbi ta Kan wayata ba seda nazo kwanciya, Ina Hawa WhatsApp Naga dukkan cousins Dina sun updating story dinsu, na Nads na fara dubawa tun kafin na bude Naga caption din " Love birds...let the feelings speak". Se ga hoton mu a garden ni dashi, na tsura ma fuskokin mu Idanu da suke fitar da annuri, you don't have to ask kinsan ba karamin so mukewa juna ba, na cigaba da dubawa har da aunties Dina ma sun daddaura, na fara kokarin duba nashi se na tuna ai banida contact din shi ma gaba daya. Na duba Rooks wadda tayi dogon sharhi akan picture din, yawanci tana nuna how much I meant to her, da Kuma adduar Allah yasa wannan shi ne farin cikin da kowa kemin adduar samu. Na kasa replying se kawai na koma chat Dina nan Naga messages, na Yaya Hasher Dake da yawa na fara dubawa, he sent me the picture da Kuma wani video lokacin munje wani guri da suke culture show, an bani Abu Ina kadawa Ina dariya yayi min video, a raina nace how on Earth abinnan ya fita Haka? Nasan shi ya daura kowa ya samu ya dauka ya daura, I'll be the hottest topic of gist kenan, tunda ba kowa yasan aurena ya mutu bama. Na sauke ajiyar zuciya na fara karanta messages dinsa
*Dama shi ne dalilin da yasa Kika ki kulani yau kenan? You opened Chats Dina Amma Baki bani amsa ba, Wait tukunna meye tsakanin ki dashi? Do you want to rush again, yaushe auren ki ya mutu ko shekara bakiyi ba fa.*
Na dafe kaina Ina jin kaina ya fara sarawa, Amma dukda Haka na cigaba da karanta na kusa dashi
*Kinsan Ina son ki, kinsan da gaske nake son ki Amma ta Yaya Zaki ma soyayya ta Haka ta hanyar nunawa duniya Baki ma lura ba...*
Ban karasa ba na aje wayar so confused...
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 51
Na dafe kaina Ina tunanin a yaushe ya nuna cewar Yana Sona da har zaice na nunawa duniya bani bukatar shi, na matsara da wayar gefe tare da furzar da iska daga bakina, yeah I actually know Yaya Hasher ya kula dani lokacin da nake cikin tsananin damuwa da matsala, lokacin da na ke bukatar Wanda zai kula Dani, Wanda Zan saka kaina Kan kafadar shi nayi kuka akai shi din ya zame min hakan,sede ko kadan ban kawo cewar Wai Yana Sona bane. Shiru nayi ba tareda nayi replying ba Dan ban ma San me zance Masa ba, a cikin zuciyata babu wani namiji da ke da matsayi irin na Yaya Shehu a raina, bazan taba manta abubuwan da yayi min ba, he was there for me when no one was there, he lend a helping hand, yaso kubutar Dani a lokacin da Wanda nake Kira iyayena Suka kasa min komai, Suka hakura suka made hannun su I remembered Bai hakura ba har seda yaga Babu yadda zaiyi sannan ya hakura, he kept telling me zai gudu Dani, ya Kuma nuna min na gani, bawai Ina returning favor din da yayi min ba, a'a zuciyata tayi naam da shi ta Kuma karbe shi hannu bibbiyu saboda shi din ya cancanci na soshi. Na numfasa na kashe data tareda kwantar da kaina Kan pillow a hankali Ina jin jikina Yana min Dadi Dan kowacce gaba ciwo take min, wayar na janyo jin alamar Kira Yana shigowa, na Dan tsirawa numbers din idanu kafin Kuma nayi sliding tareda karawa a kunnena, kafin nayi magana yace
" Damsel"
Take na fahimci shi ne, na saki murmushi jin nutsuwa tana Shiga ta, I felt kamar I'm safe a tare dashi,
" Bakai bacci ba?"
" Se kace ke wadda am sure yanzun kina Kan gado zakiyi bacci ko?"
Na saki murmushi nace
" How do you know? "
Yayi dariya wadda naji ta