Showing 54001 words to 57000 words out of 95282 words
Chapter 19 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
ni kowa ya huta, na Jima a tsaye se naji an bude gate an shigo daga baya na daina jin ihun shi, agogo na kalla Naga karfe hudu da rabi, jakata na dakko na ciro warpper 200 wadda mummy ta bani na saka katon hijab na dauki wayata na fito ba tareda na kulle dakin ba, Ina zuwa Naga saboda rikicewa a bude ya bar gidan, ga jini kacakaca tunda ga parlo har waje, na fice daga gidan na fara tafiya ba tareda nasan inda zanje ba, Ina zuwa Naga napep nace Tasha zai kaini zanje Kano, Ina Hawa ya kaini har lokacin nayi blocking duk wata channel din tunani a kwalkwalwata, Ina zuwa Tasha na samu mota baa Jima ba ta tashi se lokacin komai ya fara dawo mini, what if idan ya mutu kenan na kashe rai Zan mutu kafira, me yasa banyi hakuri an raba auren a hankali ba. Se na fara kuka Ina jin tsoro Yana ratsa ni, Ina ganin kamar kamani zaayi. Ta gefena se hakuri take bani tana lallashi na Dake datijuwa ce. Dake Babu nisa sosae se gashi mun so Kano, na kirga kudin na bashi sannan na samu guri na zauna Ina tunanin inda zanje, nasan Mummy Bata tafi ba, Amma sunyi tafiya kamar yadda Rooks tace min, su Ummiey basa nan, shi Kuma Kawu Tijjani bana son zuwa gurin shi Dan matsoraci be, se kawai na tuna uncle Babawo na saya airtime na saka na fara Kiran shi kowanne bugu na Kara bugun zuciyata! Seda na fitar da ran zai dauka sannan ya dauka
" Princess!"
Se na saki kuka jikina na rawa tamkar mazari,
" Me ya faru? Ya akai? Kina Ina nake jin hayaniya?"
Na kasa magana se kuka nake, gaba daya ya tada hankalin shi se roko na yake na fada masa menene, se can nace
" Na kashe shi! Nasan kasheni zaayi!!"
" Junaidun?"
Ba gyada kaina, hankalin shi ya tashi yace na tsaya yanzun zai taho kazauren, se nace ai na baro kazaure Ina Tasha a Kano, Allah ya taimaka shima Yana kanon yace Yana Hanya na jira shi!
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.39
Koda alkawarin da sukai min Basu cika ba,wannan Abu daya da sukai min se naji duk wani haushin su day fushi da nake dasu ya yaye, ko Babu komai wannan lokacin shi ne hardest moment of my life, da ace Bai kawo min dauki ba sede nayi ta watangaririya a titi tunda nasan Babu Wanda zai kula Dani Kuma. Kawu Tijjani yayi min alamar naje daki akan zasu Yi magana, na kuwa Mike Ina jin tamkar anyi min bushara da aljanna na koma dakina, na samu Anty Nafisa tana jera min Kaya cikin wardrobe. Na Isa gareta nace
"Ki kawo nayi Dan Allah!"
Ta juyo ta harareni tace
" Dama haushin ki nake ji.."
Gabana ya fadi na marairaice fuska Ina jin to meye hakan Kuma
"... Wai Kika tashi da sassafe ki kafa shara da wanke wanke bayan nace kiyi bacci da yawa"
Na sauke ajiyar zuciya nayi tunanin nan dinma wani Abin Zan fuskanta Kuma, nayi murmushi nace
" Kai Anty ni bazan iya Zama idle ba, bana komai. Lokacin Ina gidan su Yaya tun asuba nake fara aiki Kuma Haka nake yini Ina Yi, Kinga aiki ya zame min jikina"
Dana fada sunan Yaya se na tuna dashi, Allah kenan komai cikin tsari yake tsara shi.
" To Banda abin ki ai nan ba gidan Yaya Sa'idu bane gidan favorite Uncle din ki ne, kede ki huta da kyau Dan zai fara nema Miki admission ba dadewa ba"
Na Kara gyara zamana nace
" To Anty waec din ya fito ne?"
Tace
" Ya fito Mana, printout din ki na gurin Darling bara ya Gama ya Baki, bakiga yadda Kika ci ba"
Na saki hamdala Ina murmushi me kyau na Jin Dadi, Ina nan zaune ta Gama gyarawa tas sannan ta zauna gefena tareda bani jaka tace min
" Kinsan me yasa wanann abubuwan duka Suka faru? Kunyi sakaci da addua dukkan ku daga ke har su Darling din bakwa addua, Dan Haka yanzun addaua zakiyi sosae, duk dare Zan dinga zuwa Ina tashin ki kiyi sallah ki roki Allah mafita, this is not the end of it har yanzun akwai aurenki akan Junaidu"
Na gyada kaina tabbas hakane, addua mukai sakaci da ita shiyasa abubuwa da dama suka lalace cikin rayuwata, dukda nasan kaddara akace ta riga fata Amma wani lokacin na kanji bamu ma fahimci concept din kaddarar ba, it's prewritten shiyasa akace muyi addua, wannan adduar can make a great change a cikin rayuwar mu, Idan da ace Babu abinda yake canja kaddara da bazaa ce muyi addua ba!
JUNAIDU
Kafin yankan da Afiyya ta ma Junaidu, cikin satin abubuwa da dama nashi suka fara lalacewa, a wañnan safiyar da ya fita, main source din kudin Junaidu wannan garage ne na gyaran motoci da Saida spare parts, se Kuma shaguna a jere guda biyar da yake dasu a Kano inda ya zuba Yan haya. Sauran duk yawancin kananan kadaru ne, Amma Kuma har lokacin Yana drug dealing dukda ba sosae ba kasancewar shi Bai fiya son risking safety din shi ba, Amma wani lokacin Safiyyu idan yaga chance Yana saka shi Dole se yayi tunda ba karamin kudi suke samu ba. Yana fitowa ya fara Kiran Safiyyu Dan sunyi akan zasu je asibiti saboda drugs din aka bashi akan matsalar shi sun Kare, Doctor yace Masa zai Sha maganin na kimanin sati kamar biyar kafin ya Kara gwadawa aga ko zaa dace dukda nerves din dake gurin anyi damaging dinsu sosae beyond repair! Safiyyu ya karaso Suka shiga mota Dan tafiya kamar yadda Suka shirya, se ga Kira a wayar Junaidu daga manager shi akan gobara baa San daga inda ta taso ba ta mamaye gaba daya garage din, Kuma ba guri daya ba ta barbazu ne cikin garage, a take Junaidu ya saki kara cikin tashin hankali yace
" Ku Kuma Kuna me da har hakan ya faru? Dukiyata wallahi baa Isa ba!"
Ya kalla Safiyyu da ya riga ya nufi inda garage yake can farkon gari kafin a kawo kanti, yace
" Kaji Dan hauka sun bar gurin ya kone! Dukiyata, takama ta !!"
Shi dai Safiyyu Bai ce Masa komai ba Dan Bai masan me zaice ba, suna Isa kafin ya Gama parking Junaidu ya fito a gigice yayi gurin da uban mutane suka taru kowa na tofa albarkacin bakin shi, Amma abun mamaki duk yadda suka taru Babu Wanda ya dauki Koda ruwa cikin kofi Dan ya kashe wutar, gaba daya sun zagaye gurin se Allah ya Kara suke wasu na fadin dama ai dukiyar jinin mutane ce dole zata kone kuwa. Ya ratsa ta cikin mutanen ya shiaga garage da already inda main heart din garage yake ta Jima da konewa, yayi wani ihu Yana kallon Safiyyu dake contacting fire service akan su kawo dauki, Junaidu Allah kadai yasan irin susucewar da yayi kafin zuwan Yan kwana kwana, Koda suka zo 3/4 na abinda yake ciki ya kone se gini Haka ya dinga faduwa yif Amma ko sauran da suke makwabtaka dashi wutar Bata taba ba. Safiyyu ya rike shi saboda fizge fizgen da yakeyi, mutane sunata binsa da Allah ya Kara sauran ma zasu kone sannu a hankali, da kyar Safiyyu ya tafi dashi daga gurin Amma ba karamin asara ya tafka ba, abin tashin hankalin ma shi ne akwai motocin mutane, Kuma yawancin mutane suna Kai Masa gyara ne ba Wai Dan wani Abu ba se Dan Babu karya sun kware wajen aikin su. Safiyyu ya kaishi gida ya samu ya kwantar dashi tareda karanta Masa wasu spells a take bacci ya dauke shi, Bai farka ba se wajen uku anan Safiyyu ya masa bayanin cewar ai akwai damuwa Dan matsawar Afiyya na rayuwar su Kuma Bai kusance ta ba to abubuwan shi da rayuwar shi Baki daya ta dakko hanyar tarwatsewa, cikin fushi ya nufo gida da nufin yayi ma Afiyya dukan da ko Bata mutu ba to se ta nakasa ko ta jigata, ni Kuma na fito da shirina Allah ya bani saa na yanke shi.
Safiyyu already ya biyo bayan shi Dan yasan definitely zaiyi wani silly Abu ne tunda ranshi kuwan a bace yake, Yana shigowa ya dinga jin ihun shi, shi ne fa ya shigo ya dauke shi zuwa asibiti, fada Masa yake ya kulle gidan kada na gudu kafin ya dawo, yau se ya kashe ni yaga uban da ya tsaya min. Ba karamin jini ya zubar ba, Dan kafin su karasa har ya Suma, ana zuwa tunda case of assault ne yasa aka Kira police, yazo ya shaida komai sannan aka dinke gurin it was so deep Dan na taba Masa artery shiyasa bleeding din yayi yawa. Aka Kara Masa jini duk Safiyyu ke ta wannan Kai kawon kafin Kuma aka samu ya farfado, da furucin se ya kashe ni shi ne abinda ya fara fada, dan sandan da case din ke hannun shi ya dubi Safiyyu yace Yana son magana da Junaidu, Dole Safiyyu ya fita Yana nuna Mai alamar yasan me zai fada.
" Waye ya yanke ka?'
" Mata ta ce"
" Kunyi fada ne?"
Ya gyada Kai, Bai San dalili ba kawai bakin shi yace
" Dukanta nake shi ne a kokarin kare kanta ta yanke ni har Haka"
Shi kanshi Bai San me yasa ya kareni ba dukda a ganina ba kareni bane ba ai gaskiyar ce, Dana tsaya na Bari ya dakeni kamar yadda ya saba sede Kuma Rooks idan ta haihu ta tuna tana da Yar uwa me sunana tayimin Kara ta mayar da sunan! Dan sandan ya fadawa in charge din emergency unit din akan kada suyi discharging Safiyyu har se an sanar da nan police station din.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.40
Tunda na tashi Ina daki ban fito ba, se addua nake Allah yasa komai yazo karshe, tun karfe uku saura na tashi na dare shi ne har yanzun ban koma ba, Anty Nafisa tazo ta tasheni da kanta, seda na tashi taga nayi alwala na hau Kan salayya kafin ta koma dakin su, nayi sallah sosae cikin nutsuwa da Mika Kai, da saka ran cewar Allah ya riga ya karba addua ta. Ita ta koya min yadda ma zanyi adduar, nayiwa Allah kirari da dukkan kalmomin da suke nuna girma da Kuma rahma, nayi salatin annabi yadda Zan iya sannan nayi istigfar, abinda nake bukata ya biyo baya, iyaye na da sauran alumma. Nayi na Gama sannan na koma karatun kur'ani na Gama na Kara sallah zuwa lokacin alfijir ya keto nayi rakaatanul fajr sannan nayi sallah abuna. Na Jima Ina zaune nayi azkhar na karanta suratul Yasin sannan na fada tunanin yadda abin zai kasance, dukda ban taba jin nutsuwa da sanyi irin Wanda naji ba, Ashe Haka addua take? Se nake jin tamkar face to face nayi magana da Allah, I felt so much relieved, naji tamkar lokacin da nake rayuwa ni da Abbuna da Nanny, lokacin banida wata damuwa ko matsala, Amma kalleni at 16years I'm exposed into abinda wata Yar shekara arabain din Bata taba fuskanta ba. Na mike nayi wanka na gyara gadon na shirya cikin skirt da riga na shadda brown, kasancewar ni ba fara bace yasa kayan Suka min kyau sosae, sede da na kalleni se Naga ramar da nayi ta fito da yawa, na shafa wuyana Ina turo bakina alamar rashin jin Dadi Amma dukda Haka na danyi kyan gani akan shekaranjiya. Knocking naji softly jikin kofar hakan yasa na dubi kofar se naji sallamar Anty, ta shigo har lokacin kayan bacci ne jikinta Bata cire ba se Dan veil data daura akai, ganina na shirya fes Dani yasa ta saki murmushi tana fadin
" Kinyi kyau Princess din Darling"
Nayi murmushi me kyau na gaishe ta ta amsa
" Muje kitchen ko?"
Na gyada Kai Ina tambayar ta ko Uncle ya tashi, tace ai tun asuba Bai ma shigo ba da yaje masjid se yanzun ya kirata akan Yana shigowa kazaure zasu wuce, na gyada kaina. Kusan karfin hada breakfast dinma ni ce, tunda ita ba ta da sauri, mun kusa gamawa mukaji sallamar uncle Babawo ya dawo, da sauri ta dauki towel ta goge hannunta sannan tace min bari ta ganshi, na gyada Kai Ina murmushi, a raina nace she's so lucky tana zaune cikin farin ciki. Hanzarta gamawa nayi na fito bayan ba Dan gyara gurin na same su zaune suna magana, Yana kallona ya saki murmushi Yana fadin
" Princess har kin tashi?"
Nayi murmushi na karasa na gaishe shi, ya amsa da faraar da Yana Kuma bani reassuring look, a gurin mukai breakfast Yana bani labarin then lokacin Yana karatu a Lancaster Banda dariya Babu abinda nake, saboda yadda labarin yake so funny, gaba daya Suka tsaya suna kallona, ganin sunyi shiru yasa na tsagaita dariyar Ina murmushi na cigaba da tauna plantain din dake bakina, Anty Nafisa tace
" It's nice seeing you smiling again!"
Na Kara sakin murmushi bance komai ba, uncle Babawo ya wuce Dan yin wanka, ni da Anty muka kwashe kayan muka gyara tsaf kafin muka fara Hira, me aikin ta na ta gyara gidan. Kamar daga sama naji sallama kofar parlor, wata irin mummunar faduwar gaba ce ta ziyar ce ni, nayi saurin mikewa hannuna har rawa yakeyi, ta kalleni sannan ta dubi kofar daidai shigowar Kawu Sa'idu afijajan, na kalleshi kamar yadda yake kallona, Anty Nafisa tayi saurin zura hijab din da take ajewa standby tana kallon shi Wanda shi Kam duk hankalin shi Yana kaina, ta rike hannuna tana kallon shi tace
" Yaya sannu da zuwa"
Ya karaso cikin parlon ya Kai hannun shi zai riko hannuna nayi saurin komawa bayan Anty Nafisa Ina kankame ta, ya saki hannun ya bude baki zaiyi magana se mukaji fitowar Uncle daga daki, nayi saurin sakin Anty Nafisa na koma bayan shi Ina rike hannun shi, Ido cikin Ido suke kallon juna, Uncle ya riko hannuna ya dawo Dani gefen shi yace
" Sannu da zuwa, dama yanzun nake son zuwa gida na sameka"
Ya dube shi yace
" Dama tana nan? Dama Kai ka boye ta kenan? Kasan me tayi?"
" Na sani ta sare shi a hannu, ya Suma an Kara Masa pint of blood, Amma kasan me? Naso kashe shi tayi. Ba boye ta nayi ba ta dawo gidan ubanta ne kuma no Zan kwatar Mata yancin da ka tauye Mata"
" Babawo ni kake fadawa Haka?"
" Na fada maka, I'm ashamed to call you a brother, you're a failure. Ka sani da na Gama dashi Zan dawo kanka, you don't have to waste your time coming, I'll come for you. Princess jeki daki"
Na saki hannun shi na nufi dakin a guje Anty Nafisa ta bi bayana, sun Jima Ina jin cecekucen su Amma saboda tashin hankali da nake ciki na kasa fahimtar abinda suke fada. Anty Nafisa ta sa nata nanata addua " Allahumma la sahla illa ma ja'altahu sahla..." Se naji uneasiness din Yana sauka.
Uncle Babawo ya leko yace mu fito zai sauke mu gidan Mummy, Dan Bai son barina anan Baki daya, har mun fito yace na koma na sako hijab Dani zaa tafi kazauren Dan ayu komai ya Kare, a cikin motar shi muka tafi, mukai branching muka dauki Mummy, se lokacin Naga Rooks, tana ganina ta taho Mummy ta dalla Mata harara tace
" Ai na raba wannan kawancen, Babu ke Babu ita, she's a bad friend!"
Nayi shiru jikina a sanyaye, ita Kuma ta fara kuka tana fadin
"Uncle kana jin ta ko? Ka Bata hakuri Dan Allah. Wallahi Afeey tace Kar na fadawa kowa"
Mummy kamar ita take wa magana tace
" Zanci ubanki a gurinnan, da ta fada Miki tace karki fada Mana ke mahaukaciya ce! Baki San she's indirectly telling you she needs assistance ba. Zaki sani"
Ta rike hannunta tana ta kuka, nayi saurin cewa
"Mummy wallahi..."
" Zan mareki a gurinnan! Kin zata na kyaleki ne? Ina son komai yayi burning down ne Zan dawo kanki kinji"
Uncle Yana dariya ganin nayi shiru tareda rike hannun. Shi, yace Rooks ta dakko hijab mu tafi, Mummy ta watsa Masa harara ta karba key din hannun sa ta fice, seda muka jira ta dakko sannan muka fito Uncle nace Mana
" Ku kyaleta zata sakko da kanta, she's a bully tun muna yara"
Rooks ta saki dariya tana Kara goge hawayen ta, ni Kam murmushi kawai nayi muna Isa, har ta tada motar, yayi saluting dinta Yana murmushi ta Harare shi, tana kallona tace
" Daughter zo nan ki zauna"
Gefenta na bude na Shiga na zauna su Kuma suka shiga baya abin su, kallon time tayi ta fara complain din min kusa makara hakan yasa tunda ta hau titi take gudu, yayinda suke Hira itada uncle dake fada Mata yadda sukai shida Kawu Sa'idu dazun, tace how she wish gidan ta yazo da se ta kwada Masa Abu akai. In less than an hour min shigo Kano, main office din hisba muka wuce, nan muka tarar da Kawu Tijjani yana jirna mu, muka gaida shi sannan muka shiga ciki, commander muka samu Dan time din baa fara hisba a jigawa ba, already jiya Uncle da Kawu Tijjani sun filing musu komai, nan aka Kara min tambayoyi na fada yadda komai ya faru. Sukai filing sannan muka wuce kazaure, kafin muje already Kawu Sa'idu ya riga mu zuwa tuni Kuma har yasa an tura case of attempted murder zuwa capital Dutse gadawur!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 0906346725841
Gaba daya na kasa gane abinda yake faruwa, already komai anyi documenting akan na yanke shi ne saboda Kare kaina akan Yana duka na, se Kuma report din da aka bayar a asibiti na yanke shi a hannu, Amma da muka je dutse se muka ga it's a total different case, ance na yanke shi a cikin shi har na taba internal organs dinsa, Haka Kuma ba Kare kaina nakeyi ba. I was so confused har jiri nake ji Bayan sun Gama magana da Kuma charges