Showing 81001 words to 84000 words out of 95282 words

Chapter 28 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6666

gayyace su ba, Haka na dauka na fita anan inda muka zauna dazun na ganshi shi da Dad in a serious conversation kamar yadda fuskokin su ya nuna, na hadiye yawu Dan kawai jikina na bani something is fishy, akwai Dole abinda yake faruwa a Nigeria, ban wani maida hankali ba na fadawa Dad inda zanje sannan na wuce, ban Jima ba na dawo dukda Sheriffa kamar zata yanka ni saboda ban fada Mata ba, nace Mata Nima na manta gaba daya da hakan. Ina dawowa mukai dinner sannan na zauna kujeran Dake kallon wadda yake zaune yace

" 2am ne flight dina"

Confusingly nace

" Zuwa Ina kenan?"

Yace

" Nigeria, Dad yace min jibi zaku taho ko?"

Na gyada Kai trying hard Kar na nuna na damu so kawai muka Shiga hira yau da gobe Bai ce min komai ba balle Kuma ni da bansan ma abinda ke faruwa ba. A Daren ya wuce airport banma rakashi ba saboda na gaji ga bacci se kawai na kwanta Bayan munyi sallama. Washegari ya kasance duk hada Kaya ne, ranar Monday da sassafe karfe shida jirgin mu ya tashi zuwa Malaysia Dan se mun fara trans in acan kafin Kuma mu wuce gida wato Nigeria. Abinda yafi min dadi a wañnan tafiyar kasancewar dukka zamu hadu acan su Rooks ma sun riga da sun wuce.

Agogon hannun shi ya kalla sannan Kuma ya samu guri ya zauna gefen Ummiey wadda ke kallon duk wani Abu da yake Yi, daga ita se shi a gidan Dan Nads da Harith sun tafi gidan su Rooks sarki da Daddy Kuma suna fada. Ummiey ta dube shi tace

" Yaushe ne saukar su Afiyya din? Na zata zakaje Kano taho dasu"

Yayi dariya yace

" Ai Kawu Tijjani zai dakko su shiyasa"

Ta gyada Kai tace

" So da kaje Lancaster kayi Mata magana akan Hasher dinne?"

Ya girgiza Kai yace

" Ni ban Mata ba, bana son taji maganar a bakina Amma munyi magana da Mummy da Kuma Uncle Babawo yace min wai wannan tsohon mijin nata shima yazo Wai da family dinsa..."

Da sauri Ummiey tace

" Wai Junaidu? Amma ma dai a gaida Tijjani me karfin zuciya shi wannan yaron har ya Isa ayi Masa second glance."

With lot of humor a muryar Shehu yace

" Ummiey ni nasan afiyy ba zata taba zabar wani miji Bayan ni ba, so shiyasa banma bi takan maganar ba shi Kuma Hasher yayi contacting Dina akan maganar nace Masa ni bazan Yi fada da kowa akan ta ba nasan idan har ita zata zaba mijin ta Bata da wani se ni se Kuma idan Allah ne Bai nufa ba"

Ta Dan bugi kafadar shi kadan tare da gyada Masa Kai tace

" You have so much faith in her"

Yayi murmushi Yace

" I believe in her Ummiey"

Ta musu adduoi sannan ya wuce daki Dan ya huta kafin karasowar su Afiyya.

Karfe Tara na dare muka shigo garin Ringim, tun daga gate din legal nake ta kalle kalle ko Ina se Ina tuna memory that's lingered a wañnan gurin, har seda muka shigo cikin gari mukai parking kofar gidan da yake mallakin na uncle Babawo ne. Shekara biyu kenan da na bar garinnan gashi na Kara dawowa, sede I'm no more that naive girl wannan din wata sabuwar yarinya ce wadda ta Kara fahimtar rayuwa da Kuma zaman duniya. Muka fito zuwa ciki a matukar gajiye, Ina shiga nayi daki na fada Kan gado ko veil Dina ban cire ba, nayi shiru Ina lumshe idanuna a take kuwa bacci yayi gaba dani, nasan Ina baccin naji shigowar Mom da Nanny Amma banji fitar su ba, se Sha biyu sannan na farka idanuna har lokacin akwai bacci, na tashi na gyara kwanciyata na cigaba da bacci.

Washegari da wurwuri mukai gyaran gida komai ya koma muhallin shi sannan nayi wanka naci abinci na koma daki ko wayata ban nema ba na sake komawa bacci. Wajen daya na farka nayi sallah sannan na fito parlor nayi kicibis da Nads da Rooks, suka yo kaina kamar zasu kayar Dani na fara musu ihun su sake ni Zan Fadi kafin Kuma na zauna

" Mom dinki ta fita tun dazun kema tashi zakiyi mu tafi"

Nace

" Ina zamuje?"

Nads race

" Gidan Ummiey mana!"

" Ummiey fa? A'a wallahi bazan je ba"

"Kunyar surukai!"

Na wuce daki na canja Kaya sannan na fito muka fita, iska na kadawa a hankali muka nufi gidan Mummy kamar yadda nace musu sede da mukaje Bata gidan, na Ciro wayata na saka Sim Dina na Nigeria sannan muka fara Hira se tsokana ta suke Wai jikin su na Basu kafin a Gama hutunnan zaayi min aure. Nayi dariya nace

" Da an rage min wahala wallahi dama so nake na kasance da Honey kullum"
.
Rooks bakin ta kamar zai yage Dan mamaki yayinda Nads ke fadin

" Lallai in law kice a matse kike"

Na Harare ta

" Ke Nads I'm your elder sister yanzun stop teasing me"

Kafin ta bani amsa wayatta tayi ringing ta dauka Babu jimawa ta dubeni tace

" Dad dinki na Neman ki acan gidan Waziri"

Nace

" Toooo!"

Na mike Ina musu kashedin su jirani na dawo sannan su sayo Mana Dan malili muci idan na dawo se suka ce kawai idan na Gama na same su a gidan mu can zasu koma. A hankali na cigaba da tafiya har nazo kofar gidan Kawu Sa'idu, na tsaya ba tareda na shiga ba Amma se kallon zauren gidan nake rayuwa kenan. Komai ya wuce se tashin labari,na tuna lokacin da nake ganin rayuwa ba zata taba komawa daidai ba, na tuna lokacin da nake ganin Babu wani Jin Dadi a rayuwa , lokacin da nayi giving up akan rayuwar ma Baki daya lokacin gani nake banida wani hope na kara samun yancin but Allah ya nunamin shike da iko bani ba. Na juya na cigaba da tafiya nayi niyya Zan Shiga Amma ba yanzun ba se na dawo daga Kiran Dad. Na danyi nisa kadan naji muryar Hafsisi tana kwala min Kira, a sukwane na juya ita din ce kuwan da Sahib a hannun ta yaron Siyama, na saki murmushi lokacin da ta karaso tana fadin

" Afiyya kin ganki kuwa?"

Nace

" Me nayi?"

Tace

" Innanlillahi se wani haskawa kike kin Kara kyau"

Nayi dariya nace taje gida zanzo yanzun jirana ake, ta ruko hannuna tana tambayata kp da gaske zanzo nace Mata ai alkawari nayi.sannan na samu ta tafi ni Kuma na hanzarta naje. Shima gidan an gyara shi sede Ina iya hango guraren da mukai wasan kasa, guje gujen da komai, Allah sarki Hajiya kakata. Kofar parlon takalma me sunfi biyar hakan yasa gabana faduwa Amma na daure bakina dauke da sallama kaina Kuma a kasa na shiga, Mummy ta fara fadin

" Mashaaa Allah Afiy xo nan"

Na saki murmushi na Isa gareta tare da rungumar ta nace

" Mummy Ashe kina nan? Ina wuni?"

Ta amsa sannan na gaida Dad da Kawu Tijjani, Ina daga kaina Naga Kawu Sa'idu a zaune ya zuba min idanun shi, nayi saurin janye nawa na gaishe shi a ciki ciki kafin Kuma na Kai idanuna kan sauran occupant din, subhannallah! Kadan ne zuciayata Bata fito ba ganin Junaidu wani dattijo da Kuma wasu su biyu da ban San su ba. Gaban ya Fadi na dubi Mummy se Naga ta min alamar na gaishe su, bakina na Dan rawa na gaishe su, dattijon yace

" Amina kece?"

Na Dan gyada kaina kadan sannan Kuma na sunkuyar da kaina. Kawu Sa'idu Dake gefe yace

" Tunda tazo se mu Basu guri Dan su sasanta kansu ko?"

Da mamaki na dago cikin sauri na kalla Kawu Sa'idu, na kalla Junaidu da yaki dauke idanun shi daga kaina, se lokacin na lura da sauyi a tattare dashi, Naga wata irin nutsuwa da ban taba gami a tare dashi ba Amma duk ba wannan ba meye Kawu Sa'idu ke fada Haka? Ni da way zamu sasanta? Haba ba dai Junaidu ba wannan mafarki ne ma, mummunan gaske ma kuwa. Dad ya dubi Kawu Sa'idu yace

" Ban zo gurinnan Dan na hada aure ba, nazo na bawa yata kariya ne, ni ne ubanta ni ne me hakkin zaba Mata abinda nake ganin ya dace da ita. Junaidu kace kana son ganin Afiyya gata Ina sauraronka"

Naji dadin maganganun shi, naji karfin gwiwa da Kuma Jin Dadi a raina. Junaidu ya taso yazo ya tsugunna har gabana inda nake zaune ya dira gwiwar shi biyu a kasa sannan ya fara roko na na yafe masa, yasan ya cutar dani...bla..bla...bla...

Tunda ya fara magana nake kallon shi, he seems moody, dukda dama bantaba ganin faraar shi ba Amma nasan da gaske shi din se a hankali, but yanzun akwai sabon Abu a tattare dashi. Kaina na girgiza nace

" Duk abinda ka min, son ranka ne ban maka komai ba, Amma kayi min komai, Dan Haka yafe maka bakai zaka ce ba ni ce Zan gani idan ka cancanci hakan."

Kowa yayi tsit nasan mamaki suke, Kawu Sa'idu ya fara kokarin magana Dad ya dakatar dashi

" Right dinta ne idan taga zata yafe to? Ni bazan matsa Mata ba saboda ita kadai tasan wahalar da Tasha"

Kawu Tijjani ya gyada Kai yayinda na dubi Junaidu he looks disturbed abin tausayi kawai Baki daya, da idanu na pleading I'm sure da su zaiyi amfani wajen plead din, na dauke kaina se naji muryar Dad na fadin

" Ni fa na Gama magana ba zata koma gidan shi ba"

Malam da se lokacin yayi magana yace

"Aji ta bakinta tukunna"

Dad yayi dariya yace

" Afiyya Zaki koma gidan Junaidu?"

Kafin ya karasa na girgiza kaina na Kuma bude Baki nace a'a Dole Haka Suka tashi Sika tafi sannan Dad yace min Hasher yazo musu da batun Yana sona, Yana son na nutsu sub bani kwana biyu na zaba ko Hasher ko Shehu, banma motsa ba kaina a kasa nace

" Yaya Shehu na zaba!"58

Bamu dawo gida ba se yamma Dan Muna shigowa ko Zama bamuyi ba aka fara Kiran sallah, na wuce daki nayi alwala nai sallah na zauna bare gift dina, na Dad da Mom da Nanny se Kuma nashi, kowanne content din yayi min kyau ba ma kamar nashi. Na Adana komai sannan na fito Jin Nanny na Kirana, na rungume ta Ina Mata adduar kyautar da tayi min, tace Mom Dina ke Kirana. Tana Kitchen na sameta tayi packaging slice cake da sauran finger foods tace na dauka na kaiwa su Sheriffa tunda ban gayyace su ba, Haka na dauka na fita anan inda muka zauna dazun na ganshi shi da Dad in a serious conversation kamar yadda fuskokin su ya nuna, na hadiye yawu Dan kawai jikina na bani something is fishy, akwai Dole abinda yake faruwa a Nigeria, ban wani maida hankali ba na fadawa Dad inda zanje sannan na wuce, ban Jima ba na dawo dukda Sheriffa kamar zata yanka ni saboda ban fada Mata ba, nace Mata Nima na manta gaba daya da hakan. Ina dawowa mukai dinner sannan na zauna kujeran Dake kallon wadda yake zaune yace

" 2am ne flight dina"

Confusingly nace

" Zuwa Ina kenan?"

Yace

" Nigeria, Dad yace min jibi zaku taho ko?"

Na gyada Kai trying hard Kar na nuna na damu so kawai muka Shiga hira yau da gobe Bai ce min komai ba balle Kuma ni da bansan ma abinda ke faruwa ba. A Daren ya wuce airport banma rakashi ba saboda na gaji ga bacci se kawai na kwanta Bayan munyi sallama. Washegari ya kasance duk hada Kaya ne, ranar Monday da sassafe karfe shida jirgin mu ya tashi zuwa Malaysia Dan se mun fara trans in acan kafin Kuma mu wuce gida wato Nigeria. Abinda yafi min dadi a wañnan tafiyar kasancewar dukka zamu hadu acan su Rooks ma sun riga da sun wuce.

Agogon hannun shi ya kalla sannan Kuma ya samu guri ya zauna gefen Ummiey wadda ke kallon duk wani Abu da yake Yi, daga ita se shi a gidan Dan Nads da Harith sun tafi gidan su Rooks sarki da Daddy Kuma suna fada. Ummiey ta dube shi tace

" Yaushe ne saukar su Afiyya din? Na zata zakaje Kano taho dasu"

Yayi dariya yace

" Ai Kawu Tijjani zai dakko su shiyasa"

Ta gyada Kai tace

" So da kaje Lancaster kayi Mata magana akan Hasher dinne?"

Ya girgiza Kai yace

" Ni ban Mata ba, bana son taji maganar a bakina Amma munyi magana da Mummy da Kuma Uncle Babawo yace min wai wannan tsohon mijin nata shima yazo Wai da family dinsa..."

Da sauri Ummiey tace

" Wai Junaidu? Amma ma dai a gaida Tijjani me karfin zuciya shi wannan yaron har ya Isa ayi Masa second glance."

With lot of humor a muryar Shehu yace

" Ummiey ni nasan afiyy ba zata taba zabar wani miji Bayan ni ba, so shiyasa banma bi takan maganar ba shi Kuma Hasher yayi contacting Dina akan maganar nace Masa ni bazan Yi fada da kowa akan ta ba nasan idan har ita zata zaba mijin ta Bata da wani se ni se Kuma idan Allah ne Bai nufa ba"

Ta Dan bugi kafadar shi kadan tare da gyada Masa Kai tace

" You have so much faith in her"

Yayi murmushi Yace

" I believe in her Ummiey"

Ta musu adduoi sannan ya wuce daki Dan ya huta kafin karasowar su Afiyya.

Karfe Tara na dare muka shigo garin Ringim, tun daga gate din legal nake ta kalle kalle ko Ina se Ina tuna memory that's lingered a wañnan gurin, har seda muka shigo cikin gari mukai parking kofar gidan da yake mallakin na uncle Babawo ne. Shekara biyu kenan da na bar garinnan gashi na Kara dawowa, sede I'm no more that naive girl wannan din wata sabuwar yarinya ce wadda ta Kara fahimtar rayuwa da Kuma zaman duniya. Muka fito zuwa ciki a matukar gajiye, Ina shiga nayi daki na fada Kan gado ko veil Dina ban cire ba, nayi shiru Ina lumshe idanuna a take kuwa bacci yayi gaba dani, nasan Ina baccin naji shigowar Mom da Nanny Amma banji fitar su ba, se Sha biyu sannan na farka idanuna har lokacin akwai bacci, na tashi na gyara kwanciyata na cigaba da bacci.

Washegari da wurwuri mukai gyaran gida komai ya koma muhallin shi sannan nayi wanka naci abinci na koma daki ko wayata ban nema ba na sake komawa bacci. Wajen daya na farka nayi sallah sannan na fito parlor nayi kicibis da Nads da Rooks, suka yo kaina kamar zasu kayar Dani na fara musu ihun su sake ni Zan Fadi kafin Kuma na zauna

" Mom dinki ta fita tun dazun kema tashi zakiyi mu tafi"

Nace

" Ina zamuje?"

Nads race

" Gidan Ummiey mana!"

" Ummiey fa? A'a wallahi bazan je ba"

"Kunyar surukai!"

Na wuce daki na canja Kaya sannan na fito muka fita, iska na kadawa a hankali muka nufi gidan Mummy kamar yadda nace musu sede da mukaje Bata gidan, na Ciro wayata na saka Sim Dina na Nigeria sannan muka fara Hira se tsokana ta suke Wai jikin su na Basu kafin a Gama hutunnan zaayi min aure. Nayi dariya nace

" Da an rage min wahala wallahi dama so nake na kasance da Honey kullum"
.
Rooks bakin ta kamar zai yage Dan mamaki yayinda Nads ke fadin

" Lallai in law kice a matse kike"

Na Harare ta

" Ke Nads I'm your elder sister yanzun stop teasing me"

Kafin ta bani amsa wayatta tayi ringing ta dauka Babu jimawa ta dubeni tace

" Dad dinki na Neman ki acan gidan Waziri"

Nace

" Toooo!"

Na mike Ina musu kashedin su jirani na dawo sannan su sayo Mana Dan malili muci idan na dawo se suka ce kawai idan na Gama na same su a gidan mu can zasu koma. A hankali na cigaba da tafiya har nazo kofar gidan Kawu Sa'idu, na tsaya ba tareda na shiga ba Amma se kallon zauren gidan nake rayuwa kenan. Komai ya wuce se tashin labari,na tuna lokacin da nake ganin rayuwa ba zata taba komawa daidai ba, na tuna lokacin da nake ganin Babu wani Jin Dadi a rayuwa , lokacin da nayi giving up akan rayuwar ma Baki daya lokacin gani nake banida wani hope na kara samun yancin but Allah ya nunamin shike da iko bani ba. Na juya na cigaba da tafiya nayi niyya Zan Shiga Amma ba yanzun ba se na dawo daga Kiran Dad. Na danyi nisa kadan naji muryar Hafsisi tana kwala min Kira, a sukwane na juya ita din ce kuwan da Sahib a hannun ta yaron Siyama, na saki murmushi lokacin da ta karaso tana fadin

" Afiyya kin ganki kuwa?"

Nace

" Me nayi?"

Tace

" Innanlillahi se wani haskawa kike kin Kara kyau"

Nayi dariya nace taje gida zanzo yanzun jirana ake, ta ruko hannuna tana tambayata kp da gaske zanzo nace Mata ai alkawari nayi.sannan na samu ta tafi ni Kuma na hanzarta naje. Shima gidan an gyara shi sede Ina iya hango guraren da mukai wasan kasa, guje gujen da komai, Allah sarki Hajiya kakata. Kofar parlon takalma me sunfi biyar hakan yasa gabana faduwa Amma na daure bakina dauke da sallama kaina Kuma a kasa na shiga, Mummy ta fara fadin

" Mashaaa Allah Afiy xo nan"

Na saki murmushi na Isa gareta tare da rungumar ta nace

" Mummy Ashe kina nan? Ina wuni?"

Ta amsa sannan na gaida Dad da Kawu Tijjani, Ina daga kaina Naga Kawu Sa'idu a zaune ya zuba min idanun shi, nayi saurin janye nawa na gaishe shi a ciki ciki kafin Kuma na Kai idanuna kan sauran occupant din, subhannallah! Kadan ne zuciayata Bata fito ba ganin Junaidu wani dattijo da Kuma wasu su biyu da ban San su ba. Gaban ya Fadi na dubi Mummy se Naga ta min alamar na gaishe su, bakina na Dan rawa na gaishe su, dattijon yace

" Amina kece?"

Na Dan gyada kaina kadan sannan Kuma na sunkuyar da kaina. Kawu Sa'idu Dake gefe yace

" Tunda tazo se mu Basu guri Dan su sasanta kansu ko?"

Da mamaki na dago cikin sauri na kalla Kawu Sa'idu, na kalla Junaidu da yaki dauke idanun shi daga kaina, se lokacin na lura da sauyi a tattare dashi, Naga wata irin nutsuwa da ban taba gami a tare dashi ba Amma duk ba wannan ba meye Kawu Sa'idu ke fada Haka? Ni da way zamu sasanta? Haba ba dai Junaidu ba wannan mafarki ne ma, mummunan gaske ma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login