Showing 93001 words to 95282 words out of 95282 words

Chapter 32 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6668

tashe ni ba ya kyaleni shima da ya idar da sallar se ya kwanta mukai bacci har Sha daya sannan na tashi a gigice, nayi bandaki da sauri nayi alwala nazo nayi sallah. Ya fita ya kawo min abinci Dana kalleni a madubi naga duk na rame kamar na Yi kwanaki Ina jinya. Na zauna muka ci sannan mukai wanka muka shirya nayi packing kayan mu danma bamu bude ba. Hudu na yamma muka dauka hanya da daddare muka Isa Lancaster. I felt really at home. Muna Isa seda muka biya gidan su Sheriffa ya karbo key sannan muka tafi. Tun a kofa na fara admiring gidan, ya saka key ya bude na Shiga sannan ya shigo da kayan mu. Kana shiga se siririn corridor anyi painting walls din da favorite colors dina, se shoe rack an jera takalmana da nashi a ciki. Da siririn carpet da zai kaika a parlon Wanda ya hadu da wasu sofas masu kyau. Bai da wani girma Amma ya ishe mu muyi rayuwar wucin gadi. Dakuna biyu ne masu toilet a ciki, se Kuma study room daya da kitchen, ta baya akwai karamin garden da akai shuke shuke masu ban shaawa, kallon gurin kadai is a therapy. Mukai wanka muka shirya sannan yace na Bari zai samo Mana abinci, ni Kuma na kwashe kayan da muka zo dashi na juye cikin built-in wardrobe. Na wuce kitchen na dudduba abubuwa tare da maida su inda ya dace. Ina kitchen din ya dawo muka ci abinci sannan muka fara hira. Cikin aminci da albarka zaman mu ya daure bawai na daina ciwon cikin ba, kullum se nayi Amma se nata daurewa Dan kada na tada Masa hanaklain shi. Ranar da muka cika wata daya da aure na tashi da ciwon kai me tsanani na balla magani nasha sannan naje na kwanta shi a ranar ya fita aiki ni Kuma ban koma school ba. Su mom cikin satin suka dawo dukda Nanny kadai tazo ta ganni. Bayan wani lokaci se bacci ya daukeni akan gado, nayi abuna cikin baccin naji ciwo a cikina kamar a mafarki, nayi ta juyi cikin rashin jin Dadi har na farka, Ina mikewa Dan nufin dakko magani nasha se kawai Naga jini kacakaca akan gadon, na dubi kayan jikina shima duk blood stain dinne. Na yamutsa fuska na ayyana se yau period din ya ga damar zuwa kenan. Na yaye bed spread din na shiga dashi toilet na Dan wanke gurin sannan na jefa cikin washing machine dina, na cire kayan jikina na dauraye sannan na fito. Doorbell naji hakan yasa na kalli agogo sure lokacin dawowar shi yayi, nayi saurin zura riga na tafi bude masa, Yana tsaye da suit dinsa sakale a hannu Yana Jirana, Ina bude Masa ya riko ni tareda fadin


" You're sick?"


Na gyada Masa kai, ya taimaka min na zauna sannan ya shiga ciki Bai Jima ba se gashi ya dawo ya mikar Dani muka fita se asibiti. Muna zuwa aka karbe mu na fada ma doctor din duk abinda ya sameni, ta kalleni sannan ta danyi rubutu tace akai ni O&G. Muna zuwa aka min scan, sannan aka kwantar Dani ta dubemu ni dashi tace


" She was three weeks pregnant!"


Da confusion yace


" Was?"


Ta gyada Kai ta Masa bayanin wannan magungunan da Nasha shi ne ya lalata cikin


" I've seen incidences da ciki ke zuwa da ciwon Mara, our ladies usually thinks it's menstrual cramps, they go on with taking anlgesia Wanda in most cases ke harming fetus din. Is same as your case"


Ta shafa kaina ganin har na fara kuka, ta furta


" I'm sorry, we need to do evacuation, if you ready please do come and sign"


Na damke hannun shi inata kuka, wani zafi nake ji dama ciki ne dani nayi ta bankan magani bansani ba. Ya zauna gefena yace


" Kiyi shiru kinji, ai Baki sani ba shiyasa. I'm sorry for the pains you've gone through"


Ni ko jinshi ba nayi kukana kawai nake Haka ya barni yayi signing sannan suka zo zasuyi min sannan ya fita ya Kira Mom ya fada Mata. Ai kafin a gama ma har ta iso itada Nanny. Suna shigowa ta rungume ni tana fadin


" Ya Isa kinji? Kiyi hakuri Allah zai kawo wani"


Na share hawayena ta ta tasheni zaune na karba tea nasha sannan ta dinga min nasiha ai ba wani Abu bane ba, I'll still concierge again, Kuma Banga ita ko haihuwar ma Bata taba Yi ba. Maganarta hit my hard, why am I not been grateful? Ita ko conceiving na Bata taba ba balle taji dumin a jikin ta. Na lumshe idanuna bacci ya fara kokarin dauka ta. Kwana biyu nayi na warke sosae aka sallame ni, gida muka fara zuwa a wañnan ranar Dad ya dawo daga Manchester. Ina ganin shi na sake Baki na fara kuka, se ya fara murmushi Yana kallon Yaya Shehu dake tsaye Yana kallona yace


" Afiyya ta Zama shgwababiyya! Ya Isa Haka Allah ya Kara sauki kinji?"


Na gyada kaina seda mukai lunch sannan muka tafi gidan mu. A mota hannuna cikin nashi yace


" Why were you crying? Har yanzun kukan Babyn ne?"


Na Kara Bata fuska zanyi kuka yace


" Sorry, we will make another baby ko?"


Na Dan kwantar da kaina a hannun shi, ya fara murmushi Yana cemin kunyar me nakeji. Na Jima Ina kallon post na Mata a IG Akan complain na sure, yawanci they always complain and spit d bad side of auren, Amma Ina son na fadawa Wanda basuyi aure ba da kada wannan ya tsorata su, kada wannan ya Sagar musu da gwiwa, akwai good stories about aure that are untold. I believe Babu wani Abu da bashi da matsala, ko menene kaui seka samu matsala but ya kamata muna tuna a cikin matsalar akwai Abu me dadi. They said marriage is not all bed of roses and so it's not all bed of thorns!


Da farko bamu fadawa kowa ba se dai ya fadawa Yaya Sarki shi Kuma ya fadawa Ummiey, ni Kuma na fadawa Rooks ta fadawa Mummy. Dukkansu seda sukai fadan bamu fada musu ba, da Ummiey zata zo muka ce Mata ai naji sauki seda Dad ya Mata magana sanann ta hakura ta zauna. Na koma makaranta, tun safe na tashi na samu Yana wanka, se na wuce kitchen na hada Masa breakfast Ina Yi Ina gyara gidan har na gama, Ina zuwa daki na samu har ya Gama shiryawa, na riko hannun shi nace


" Ina kwana?"


Ya langwabar da Kan shi yace


" Se yanzun? Kin tafi ko tayani shiryawa bakiyi ba"


Na danyi murmushi nace


" To ai abinci nake hada maka fa"


Ya saki hannuna Yana tayani ninke duvet din sannan muka je yaci abincin Yana tambayata yaushe Zan dawo nace


" Se yamma!"


Yace lokacin ya gama shima na jiar shi a makaranta. A Haka muka rabu na Gama duk abinda zanyi na tafi school. Two muka shiga lecture dinmu ta karshe a ranar, epidemiology in nursing, ranar zamu fara course din, Ina zaune Ina duba slides din se kawai lecturer ta shigo, da sauri na dago na kalleta Jin murya kamar ta Anty Falmata, na kalleta tare da saurin tashi tsaye, se Naga tana kallona tace


" What?"


Nayi saurin girgiza kaina na zauna tayi introducing kanta as Zainab Othman, she's Ethiopian Amma tace Mana tana lecturing anan, nayi shiru har ta Gama Ina tunanin yadda zaayi na Mata magana, I remembered ance kakata ta koma Ethiopia da ciki a jikinta, inata kallon ta Ina Kara auna kammannin ta da Yan uwan mama. Har ta fita ko definition din epidemiology din banma Yi picking ba. Tana fita na Mike da jakata mukai sallama dasu Maryam sannan na fito na Isa inda Zan jira shi, nayi shiru very deep in thought Dole ita ce, Yar uwar Mama ce.


" Damsel!"


Nayi saurin sakin murmushi Ina duban shi ya karaso tare da Mika min hannu, muka gaisa sannan muka dauki hanya, yadda yake min Hira Ina yin shiru yasa ya dinga tambayar ko inada damuwa ne, na girgiza Kai nace Yunwa nakeji. A waje mu kaci abinci sannan muka wuce gida, daki na wuce da kayan mu a hannu na fara lalubo wani tsohon diary din da Abbu ya bani, I remembered reading something similar to wanann. Inata flipping har na samu gurin da ya rubuta sunje Ethiopia shi da Mama, aka ce Mata babarta ta Haifa zainab amma tana UK tayi aure Amma basuda contact dinta. Na rike littafin a hannuna har ya shigo ya karbe yace


" Are you ok? Me yake damun ki?"


Na zauna na fara fada Masa seda na Gama tas yace


" Are you handling this alone? She's my Aunt also. We're in this together"


Na saka hannuna Ina zana Masa soothing circles a fuskar shi, hannun ya karbe ya zura a bakin shi wanda yayi sanadin sending wasu waves of vibration cikin jikina, na lumshe idanuna na kwantar da kaina a kirjin shi nace


" I love you Darl! Kullum kana sawa Ina jin sonka nake Kara Yi"


Ya dube ni da pouted lips yace


" So akwai space a zuciyar ki da ban Gama cikewa ba kenan?"


Nayi dariya nace


" Not at all! Gaba daya cikin zuciyata is filled with you, only you Darl"




Baya gajiya da Jin shi din nawa ne, wannan satin ya Kare akan bincike akan Mrs Zainab Othman, se hasashen mu ya tabbatar Dan shi Yana ganinta yace wallahi ita ce. Haka mukai kundunbala muka same ta a office, he clearly explained everything to her, ya Nuna Mata pictures din su Anty Falmata da sauran su, tana ta kallon mu hawayen da am sure hawayen farin ciki ne. Ta hada mu ta rungume mu tace she have waited ko mutum daya yazo nemanta har ta gaji tunda mahaifiyar su tace Mata zasu Neman ta. Haka muka Kira Ummiey muka fada Mata ai a satin se gasu sunzo akai karamin reunion. Na samu sabuwar uwa.




Rayuwa ta cigaba da tafiya cikin aminci, kauna da Kuma zaman lafiya, ban Jima ba na samu cikin da nayi ta kukan zubewar wancan, I feel safe ga Mom, Nanny ga Kuma Mamaa kamar yadda nake Kiran Anty zainab. Duk wannan rashin uwar da ake ganin banida shi ta kulle dukkan gaps, a Haka munata turawa cikina ya Kai term Nanny ta dawo wajena, da daddare na fara labor muna zuwa asibiti akace tip of finger, na kalla nurse din nace Mata ciwo nakeji tace eh false labor ne, kamar na daketa Amma Nima na sani a literature. Wasa Wasa seda na Kara sati kafin true labor yazo, anan na ganne tabbas wancan false labor ne. Mukaje asibiti na kusa 12hours Ina Abu daya kafin Allah ysa na haihu yarana biyu. Dukkan su Mata, na saki ajiyar zuciya lokacin da na rike su cikin hannuna, honey Yana sahafa kaina yace


" Sannu Darl kinyi kokari"


Nayi murmushi Ina kallon su, Ina jin kaunar su har cikin kaina. Mummy sasu Ummiey duka Suka zo lokacin ana Shirin bikin Hafsan Kawu Sa'idu zata auri cousin din su Rooks ta wajen babanta, Nads zata aura Dan Anty Yana Bulama karami, Rooks Kuma bansan yaushe Suka hade da ya Hasher ba se daga baya nake jin labari me dadi, Yaya Sarki Kuma zai aura Amina Abubakar Rogo. Nayi farin cikin wannan Abu. Yara akai suna aka saka Halima da Mariya.










Epilogue!






Bayan shekara biyar cikin katon prison Dake lagos, Junaidu ne na zaune a wani karamin daki hannun shi dauke da kur'ani da matasa sun taru Yana musu karatu. Wani lokacin mukan Yi tunanin wani hukuncin yayi tsauri not knowing hanyar shiriyar mu ce a hakan, it's a laid down path for us to walk on. Tunda zaa tafi dasu zuwa Lagos da Malam ya same shi ya bashi takaddu ya nuna Masa yayi amfani da damar shi wajen tuba da Kuma kusantar Allah, sannan ya sanshi yayi amfani da abinda ya sani din. Haka yayi kuwa Bai Jima ba ya samu wani dattijo ya nanike Masa kafin shekara ya haddace kur'ani ya Gama littatafi sosae, a shekara ta uku malamin masu ya rasu se kawai ya gaje shi, shi Kan shi idan ya ga Yana huduba a massalaci da yadda ake karrama shi se yayi ta Dana sanin abinda yayi. Kawai Kuma se aka zo anyi lifting sauran shekarun da zaiyi anyi Masa afuwa. A cikin satin zaa sallame shi. Bayan sun Gama karatun ya zauna yayi shiru yana tuna every bit of his life, yayi sujadda ta godiya sannan ya dauki niyyar daurawa daga inda ya tsaya, ba zai cigaba da Bata rayuwar shi Akan duniya ba!!!














Cikin lokaci na Gama karatuna na Zama kwararriyar Nurse me licence to practice, yarana sun girma har na Kara samun wani cikin na Haifa Abbu na. Duk abinda na kalla se naji ya wuce, nasan Nasha wahala Amma yanzun na manta no ce wannan yarinyar a gidan Kawu Sa'idu da tayi bauta kamar baiwa a lokacin da, wadda aka Mata aure da Wanda Bata sani ba, na shafa fuskata da Banda kyallu Babu abinda take, na tuna Mari da nasha kala kala akai, na dubi masoyi na, farin ciki na nutiswata Yana koyawa Hisham rubutu yayinda Ayaan ke rubutu cikin karamin littafi se hairan a makale a jikina, sune farin ciki na su dinne rayuwata. Kowacce da take ganin rayuwa ba zata daidai I'm gonna tell you that at the end of tunnels there's light!






There goes my hands shaking
You're the reason
My heart keeps beating
I need you now!




If I can turn back the clock
Make sure the light defeated the dark
I'll spend every hour of every day
Keeping you safe!


I climbed every mountain
Swim every ocean
Just to be with you
Fix what a broken
Cuz you need to see that you're the reason!






Alhamdulillah!!!








AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria. Send evidence of payment to 09063467258.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login