Showing 24001 words to 27000 words out of 95282 words
Chapter 9 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
sallama a bakin kofa, cikin sauri na Mike Dan Babu tantama muryar Rooks ce, tana ganina ta taho da gudu tana sakin ihu
" Afeey darling!"
Na rungume ta a jikina Ina fadin
" Rooks darling welcome"
Ta sakeni tana Kare min kallo na samo Mata kujera ta zauna gefena ni Kuma Ina tuka tuwo, ta kalleni tareda matsar da kujerar ta tace
" Baki jin zafi? Bazan iya Zama anan ba"
Ta tashi ta koma can nesa Dani, nayi murmushi Ina tuna da can lokacin da nake da gata ko suya ake a kitchen bana shiga Wai kada ya fallatso min, gani a gaban murhu Ina tuka tuwo.
" Ya hanya? Ina Mummy?"
Tayi murmushi tace min
" Mummy da zamu taho tare se tayi bakuwa, matar yayar Abbah ce tazo wannan ta Istanbul din"
Bansan ta ba Amma Ina jin ta a bakin Rooks, na gyada Kai muka fara Hira har na Gama kwasar tuwon, ta rkeni idanun ta sun kada tace
" You do all this everyday?"
Na langwabar da Kai nace
" Yeah! And I'm fine our little secret darling"
Na fada Ina Mata wink, ta biyo ni daki hannuna cikin nata, anan taga su Mino Suka Mata magana ta gaida su sannan tace min
" Me yasa komai se kice it should be secret, you are suffering fa"
Nayi dariya na dauki hijab na fito Dan tun safe Kawu Sa'idu yace idan Mummy tazo na tafi gidan ta. Na fito Ummaan su ta fito ta dubeni, wani skirt da riga ne a jikina ya dage saboda jikina ya fara karbar hormonal changes, atamfar tare Uncle Babawo yayi Mana da Rooks wani zuwa da yayi, Ash ce Kuma kunsan atamfa Ash nada saurin kodai so duk ta kode,
" Ki wuce ki canja Kaya, ki saka na wannan akwatin naki"
Na juya nace Mata
" Ai duk kin daukar wa hafsa, saura kadan Zan saka da biki"
Ta daka min tsawa Rooks tayi gasping saboda tsorata da tayi ta kalleni taga ki gezau banyi ba , na koma na dakko wata atamfar blue na saka na fito muka tafi.
" Afeey Dan Allah haka kike rayuwa? Kingan yadda Kika koma kuwa? Nidai gaskiya Zan Fadi gaskiya"
Na girgiza Mata kaina nace
" Zan daina yadda dake, idan na fada me Zan canja Rooks? Bazai canza komai ba sede bacon rai, Nanny tace min watarana komai zai wuce and I also believe in that!"
Hakan Dana fada se yasa tayi shiru kawai muka cigaba da tafiya har muka zo gida, a parlor mukaa samu wasu Yan samari suna zaune, tunda muka shiga hankalin su ya koma kaina, Rooks ta karasa tana fadin
" Yaya nd Yaya shehu sannun ku da zuwa!"
Suka amsa Mata, ta dubeni sannan ta dube su tace
" My cousin Afiyya"
Na gaishe su Suka amsa da murmushi a fuskar su, dayan ya gyara Zama Yana kallona da niyyar yimin magana se ya fitowar mummy da bakuwar ta ya katse mu
" Abin kunya ai naku be da Baku San inda yarinya take ba, dangin uwa da aka sansu da jin Kai Amma ku kuka Yi fatali da yarinya marainiyar kwaya daya, abin kunya akanki ya Kare Mariya"
Mummy ta fada tana huci
" Nidai na fada Maryam, Kun kasa rike yarinya kwaya daya Kun barta tana watangaririya a Ringim, kunci amanar zumunci.."
"Ku me kuka ci! Ke kin Isa ma kiyi zancen zumunci, kinada Baki? Ai Baki da bakin fadar wannan"
Duka muka Yi shiru muna kallon su, ni ba maganar su nakeji ba se kallon matar da ke ta kumfar Baki nake, so nake na tuna fuskarta, why does she look so much like me? Babban Wanda shi ne Sarki ya karasa gefen mahaifiyar shi ya rike hannunta Yana fadin
" Ummiey ku Bari Mana Dan Allah, mu tafi"
Ta kwace hannunta tana fadin
" Zaki San ni Kika fadawa magana Maryam"
Mummy tayi tsaki tace
" Kije da borin kunyar ki dai!"
Ni ban taba ganin manya na fada ba, se Naga scene din banbarakwai, ta juya tana huci ko lura batayi Dani da nake tsaye ba, tana fita shehu ya bi bayanta, na zauna Ina gaida Mummy wadda lafiya kawai tace min tana kuka, Rooks ta dawo gefena ta zauna idanunta sunyi ja itama, waya ta dauka ta fara fadin
" Babawo kazo ka sameni Ina gida, ku taho da Tijjani yanzunnan. Afiyya ta gama Zama gidan Sa'idu tunda shi Maci amana ne!"
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria. Send evidence of payment through 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: 20
Kamar yadda yayi min alkawarin cewar zai zo da yamma hakan ce ta faru,sede shi kafin yazo Yaya ya riga shi zuwa. Muna daki ni da Rooks ni Ina kwance Ina kallon frozen cikin system ita Kuma tana ta ciye ciye. Me aikin su ta kwankwaso sannan ta shigo tace Mana a parlor Yaya yazo. Nayi saurin mikewa Wanda yasa Rooks kallona tace
" Meye abin sauri kamar Zaki Fadi?"
Nayi murmushi nace
" Ba Dadi jira"
Ta tabe baki ta cigaba da tauna popcorn din da take ci, na zauna Ina yarda hijab din hannuna nace
" Rooks naaa! Muje Mana"
Ta kalleni tana murmushi tareda fadin
" Ban taba ganin kina gaggawa akan Abu ba"
Ban ce d ita komai ba na zura hijab dina na nufi kofar fita a bedroom din, tayi saurin mikewa ta biyo bayana, a parlor muka same shi an jera Masa drinks kamar wani bako, Mummy dama ta fita tun dazun ta Shiga fada, kamar yaji footsteps Dina ya juyo ya zuba min idanun shi , na Dan kalleshi briefly Ina murmushi sede idanun nashi bazan iya kalla na tsawon lokaci ba, Zama nayi har lokacin I felt his eyes akaina nace
" Yaya tun jiya baka zo ba?"
Ya danyi murmushi yace
" Haba dama kina nemana ne?"
Na tura bakina Wanda yasa shi dauke Kai ya maida Kan Rooks dake faman tambayar Ina yaje tunda tazo Bata ganshi ba. Nan muka hadu munata Hira wadda mostly ma shida Rooks dinne, se shi ne yake sako ni a ciki. Mun fi minti talatin se ga sallamar Yaya shehu, na daga idanuna Ina kallon shi, he looks so much like baban su Rooks, kana kallon shi ba se an fada ba kasan he's a royalty, tafiyar shi ma kawai cikeda Isa yake yinta, a fuska zakaga tamkar Yana da girman Kai Amma idan ka zauna dashi zakaga ko kadan he's simple as what you can't imagine, kyakyawa ne musamman idanun shi Dan ni dai su suka fi burgeni dashi, se Kuma leben shi. Kullum idan Yana magana lips dinsa kawai nake kallo yadda yake motsa su a hankali. Yana da tsawo kana kallon shi zakasan Yana zuwa gym yadda abs dinsa ke fitowa musamman idan kayan jikin shi sun Kama shi, he's a man to kowanne gaba. Muna hada idanu ya sakar min murmushi, na mayar masa har ya zauna ya bawa Yaya hannu suka gaisa, Rooks tace
" Ya shehu wannan sunan shi Yaya, gidan su Afiyya yake Kuma cousin dinmu ne"
Ya Shehu ya saki fuska ya Kara Mika Masa hannu a Karo na biyu suka gaisa, Rooks ta dubi Yaya tace
" Yaya Shehu, Afeeys' cousin and also my cousin!"
Yaya ya tsira Masa idanu kamar zai ce wani Abu kawai se ya Mike, Ina ganin hakan Nima na tashi Ina fadin
" Yaya tafiya zakai?"
Ya gyada min Kai yace
" Ai Naga kunyi bako, Zan dawo anjima"
Banji dadi ba Sabida ganin shi ma ko bazan Yi magana ba nutsuwa yake saukar min, Haka Ina kallo ya tafi na dawo na zauna Ina duban Ya Shehu da yake kallona admiringly yace
" Afeey Babu magana! Ko na tafi I'm not welcome?"
Na girgiza Kai na zauna na gaida shi, ya Bata fuska yace
" Seda ma na roka"
Na danyi shiru Ina kyabe fuskata kamar zanyi kuka, yayi dariya wadda tasa na shagala Ina kallon shi yace
" I got you exactly where I wanted to! Wasa nake come on bani labari"
Nima se nayi dariya na gyara zamana nace Masa ni banida labari, se yace min zai bani Mai dadi, Rooks dake gefe tace
" A'a ya kamar Kun manta Dani ne?"
Ya kalleta Yana harar ta da Wasa yace
" Shut up my Friend! Tashi anan"
Haka ta Mike Ina Mata dariya tace Masa ita tafi son Sarki tasan da shi ne bazai taba korar ta ba not ever, yace yaji taje, abinda na lura dashi they're close gaskiya sun Kuma Saba sosae. Tunda ta tafi se mukai shiru se shi yace
" Ok tell me, me yasa Baki taba Neman Ummiey ba"
Se na kalleshi sannan na dauke kaina daga kanshi nace
" Ta Yaya Zan nema ta bayan ban santa ba!"
" Hakane Kuma! I hope kin yafe musu?"
Nayi dariya nace
" Basuyi min komai ba fa! Stop making it sounds somehow"
Ya gyada Kai. Kwanaki suka cigaba da tafiya kullum Yaya Shehu se yazo Haka Yaya sede Basu Kara haduwa ba, idan Yaya yazo se yayi ta complain shi baya son yawan cousins gaskiya, ranar har na Dan ji haushi nace Masa ko baya son na shirya da dangin Mama ta ne, se ya fara kame kame shi ba Haka yake nufi ba kawai dai shi tsoro yake ji, banma tambaye shi tsoron me yake ba saboda hankalina baya gurin, Yana tunanin dalilin da yasa har yanzun Ummin su Bata neme ni ba. Da daddare na samu Mummy a daki ana gobe zaa fara bikin Mino, tana ta ware Mana kayan da zamu saka na biki na shigo da sallama, ta aje rigar hannun ta tace
" Afiyya ya akai? Kinci abinci?"
Na gyada Kai na sannan na zauna Dan nesa da ita nace
" Mhmm Mummy...mhm"
" Menene? Fada min"
Nayi kasa da kaina Ina Wasa da fingers Dina nace
" Mummy Ina son naje gurin Ummin su Yaya Shehu"
Ta Dan kalleni for some seconds sannan tace
" Ki Kira Rooks ta raka ki"
Wani dadi naji a raina Amma har na tashi Zan tafi se na dawo nace
" Mummy Amma bakiji haushi ba ko?"
Ta kalleni ta sakar min murmushi tace
" Banji haushi ba, you need to meet her tuntuni. A gaida su"
Tana zaune Kan makeken gadon ta , tayi kwalliyya cikin doguwar riga ta lace, fuskarta Babu kwalliyya Amma tayi ado da jewelry set masu tsada da daukar hankali. Hannunta da kafarta yasha kunshi Banda kamshi Babu abinda ke tashi, gefenta sarki ne se Shehu dake zaune akan bed table.
" Ummiey wannan fa ba dalili bane gaskiya, saboda Kuna fushi da babanta se ku sauke akanta? Haba Ummiey ke me zumunci ce fa wallahi kunyar yarinyar nakeji, idan Kika zauna da ita she's so much in pain".
Ta kalleshi sannan ta maida kanta Kan tab din dake hannunta yace
" Kenan ganging kukai kunzo kuyi min fada?"
Shehu yayi saurin dariya Yana daga hannu, yayinda sarki yace
" No Ummiey ba Haka bane ba,kawai munji ya kamata mu fada ne"
Tace
" Naji! Dakko min veil Dina ku rakani na ganta"
Shehu yayi saurin mikewa Yana fadin
" Ko kefa Ummiey!"
Tayi murmushin jin Dadi, sede kafin ya fita Nadia ta shigo tana fadin
" Ummiey ga Afiyya tazo"
Tayi saurin mikewa jikinta har Dan rawa yake tace
" Da gaske?"
Bata jira amsar su ba tayi waje, Shehu ya dubi Sarki yace
" She longs for her Amma saboda dlili marar tushe tana punishing kanta"
Sarki yayi murmushi ya dafa kafadar Shehu Suka fito parlon. Ina tsaye Harith na ta cemin sufa sunyi fushi dani, se gata ta fito. Rooks ta Kama hannuna muka karasa ciki, fuskarta da dariya ta bude min hannayenta, Babu musu na shige jikinta ta rungume ni, Yan kwanakin kam they were one of the happiest days of my life! Bayan ta sakeni na gaishe ta tana ta kallona tana fadin mamakin girman da nayi takeyi, time sure flies! Duk yadda take Jana da Hira se na kasa sakin jikina se hirar ta koma tsakanin ta da Rooks, seda Yaya Shehu yazo sannan na saki jiki mukai ta hira dashi, se bayan Sha daya na dare aka raka mu gida. Daga nan aka fara bikin Mino, anyi biki Babu laifi sede son barka, kwana biyu aka daura aure da dare yayi aka kaita gidan ta anan Sabin fegi.
" Maryam ya akai?"
Kawu Sa'idu ya tambayi Mummy lokacin da suka hadu duka suka je gidan, Bayan an nutsa da bikin. Ta dago ta kalleshi cikin idanu kamar yadda yake kallonta shima cikin idanu, gaba daya se taji ta duburburce ta fara stammering, uncle Babawo yace
" Yaya Sa'idu dama zamu ce ne zata tafi da Afiyya can NY!"
Ya Kara dago idanu ya kalli Uncle Babawo yace
" A'a! anan zata zauna"
Gaba daya suka hada Baki duka su ukun sukace to! Ya Mike ya fice ya barsu zaune tamkar ruwa ya cinye su, Mummy tayi zumbur ta mike tare da Dora hannunta akai tace
" Me ya faru? Menene wannan?"
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258
[15/12, 10:38] +227 98 36 59 34: Muka zauna mukai jugum jugum mussaman ni da nake ganin ni ce na Zama silar fadan uncles dina, se lokacin na fahimci maganganun da Mummy da wannan matar suka dinga exchanging, wato tazo tana Mata fadan sun kasa rike ni kenan? To idan haka me wannan matar ita ce Yar uwar mamata da akai auren su tare, na Kara zurfafa tunanin da nake nace tabbas biri yayi Kama da mutum, no wonder yaranta ke kallona kamar alien, Nima Kuma nake kallonta tamkar an cira fuskar ta an saka min, shiyasa Mummy ke ce Mata sune Suka ci amanar zumunci kenan! Ina wannan tunanin naji sallamar Kawu Tijjani da Uncle Babawo, shi banma San da zuwan shi ba Kuma dama tun asali shi dinne nafi Jin haushin shi, saboda Ina ganin shi yafi kowa kusa da inda nake Amma bai taba zuwa yaga inda nake ba. Ganin Mummy a zaune ta hade Kai da gwiwa tana ta kuka yasa duka sukai kanta Basu ma kula da gaisuwar da muke musu ba, na Mike tsaye na Kama hannun Rooks muka tafi kitchen
" Me ya faru Anty Maryam wallahi kin tayar min da hankali"
" Ta Yaya bazan tayar maka da hanakli ba Tijjani? Kai da Zan tafi bayan rasuwar Yaya me nace maka? you should be checking on Afiyya lokaci zuwa lokaci, Amma me? Kayi, bakayi ba, Kai da zaka saka idanu akan yadda take rayuwa baka masan wanne Hali take ba balle mu da muke wata uwa duniya! Ta Ina zamu sani?"
Uncle da yayi shiru yana sauraron ta yace
" Mom Rooks! Duk tone tone bashida amfani kowa yayi laifi a cikin mu, bamuyi zunmunci ba Amma yanzun ba lokacin wannan bane ba, kawai let's decide ya zaayi da Afiyya?"
" Ni Zan tafi da ita wannan Karan Bai Isa ya hanani ba, yasa anzo har gida an gaggaya min magana, Dan hakan Zan wuce da ita ta koma hannuna"
Kawu Tijjani da se lokacin yayi magana yace
" Mom Rooks kiyi hakuri nasan I've failed you, tabbas banyi abinda Kika cemin ba Amma Kuma akwai abinda na kasa fahimta, ni bansan yaushe Yaya Sa'idu ya Zama abin tsoro ba, nazo Ringim say da yawa na Kuma San halin da Afiyya take ciki Amma idan na sameshi zanyi Masa magana se na kasa...."
" Shirme kenan! Waye shi Sa'idun? Bai Isa ba wallahi yayi kadan daga yau Babawo kada ka sake tura Masa kudi, idan ya ga dama kada ya ciyar da ita, you've been sending kudin makaranta, baka taba inquiring makarantar whether Afiyya tana zuwa ko Bata zuwa, ka dinga tura mishi kudi yarinya ko abinci say uku ba taci. Ka bani kunya! Duk Ina plans dinka?"
Sudai hakuri suka bata, har ta sassauta, Muna daga kitchen Ina jin komai da suke fada, Mummy ma nada laifi ya kamata ta dinga Kira tana jin yadda nake Amma shiru itama sede tabbas laifin su yafi nata yawa a nawa ganin kenan. Rooks ta dakko juice daga cikin fridge ta zuba min cikin glass cup ta aje min, itama ta tsiyayawa kanta tace
" Ina fata Mummy zatayi nasara mu tafi dake"
Nayi murmushi bance komai ba, Haka kurum jikina ke fada min kada na saka Rai da yawa akwai sauran lokaci. Daga nan se maganar ta lafa, na cigaba da harkokina gidan su Rooks, da daddare Abban ta ya dawo yayi murnar ganina, seda suka kebe da Mummy yake ce Mata
" Afiyya kamar ba ita ba, da farko fa ban gane ta ba"
Mummy sarkin kuka se ta fara matse hawaye ta fara fada Masa duk abinda ya faru tsakanin ta da Ummin Istanbul, seda ta gama yace
" To kiyi hakuri, tun farko Dana Bai dace ku barta anan ba gaskiya, I'm sorry to say Sa'idu ko gamawa yaranshi baiyi ba balle yayi shouldering needs din Dan wani. Se a kiyaye gaba, ita Kuma Hajiya Mariya kada ki Kara kulata har ta Bata Miki rai, kawai kiyi abinda ya dace."
Washegari da wurwuri kamar yadda na Saba tashi na fito, gidan yayi shiru kowa na bacci na dakko tsintsiya na fara shara dukda Babu koami a parlon se Dan kura, akwai lokutan da nake ayyanawa idan har na bar gidan Kawu Sa'idu ko tsintsaiya ba Zan Kara kalla ba, Amma jikina is groomed da hakan yanzun da na kwanta nayi bacci sosae se naji jikina ciwo yake min, in no time na Gama gyara gidan nayi wanka na dakko sabon kayan da Mummy ta bani tun jiya nasa a jikina. Na saka hula na zauna nayi shiru Ina tunanin yau da gobe, a raina Ina adduar Allah ya zaba min mafi alkhairi, Zan iya binsu su Rooks din idan akwai kaddarar se na Sha wuya shima gidan su bazan ji Dadi ba, Allah shi kadai yasan me ya tsara min a rayuwata, Dan haka komai yazo min Zan karba.
Sosae Mummy tayi mamakin gyaran da nayi, ta kalla Rooks tace
" Ba abinda Kika iya malalaciya"
Abban ta yayi dariya yace
" Itama ba Haka aka so ba"
Ta kalle shi tareda fadin
" Wallahi kua! Allah sarki Yaya Allah ya jikan shi!"
Muka amsa Amin sannan muka bita kitchen Dan yin breakfast, Muna gamawa muka hadu muka ci, na kalla table din dukda munyi girki Amma seda aka kawo daga fada, na dauki mug na hada tea me kauri na fara sha, Mummy ta zuba min wajen dishes uku cikin