Showing 72001 words to 75000 words out of 95282 words
Chapter 25 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
har kaina, yace
" Saboda Ina son ki! I can guess abinda kikeyi ta muryar ki. I can tell Koda numfashin ki ya canja, I can sense that!"
Na gyada Kai kamar Yana gabana ina ayyana ok wannan shi ne ake Kira soul connection kenan. Tabbas souls dinmu are connected, mun Dan taba Hira inata Hamma yace
" Awwww! Se yawning kike kamar Zaki hade ni. Oya sleep kinji?"
Ba lumshe idanuna nace
" To se yaushe zaka kwanta Kai Kuma?'
" Immediately after na Gama tura mail dinnan kinji?"
Na gyada Kai nace
" Zakazo breakfast gobe?"
" Noo Damsel zanje office da wuri am not sure idan Zan shigo"
Se naji banji dadi ba, na Dan pouting lips dina nace
" Ok then Good night"
Yayi murmushi yace
" I'm sorry, Zan so school da zarar na samu time. Sleep well Damsel"
Daga Haka ya kashe wayar na kwanta Babu jimawa bacci ya daukeni ba tareda na kara tunawa da maganganun da Yaya Hasher yayi ba. Washegari da wurwuri na tashi Dan kuwa inada lecture da karfe takwas na safiya. Kitchen na shiga na daura tea sannan na fara hada noodles da prawns. Na Gama se zuwa lokacin Mom ta fito sanye da sleeping wears se katon veil data daura a sama, ta dubeni Ina zaune Ina kurban tea da wayata hannu Ina duba pharmacodynamics da pharmacokinetics saboda suna Dan rikita ni suke, Zama tayi na gaishe ta tace
" Ya gajiya jiya Kun Sha yawo, I've seen pictures masu kyau har da videos"
Nayi kasa da kaina, Ina sakin murmushi nace
" Kai Mom"
Ta danyi dariya tace
" Feel free ni din nance fa, your friend. Kina son shi?"
Na Dan dago Ina kallon ta ta gyada min Kai hakan yasa nace
" Mhmm! Amma tsoro nakeji'
Ta Dan kalleni da alamar tambaya tace
" Tsoron me? Kada abinda ya faru ya maimaita Kan shi? My dear Inshaaa Allah Kim Gama kunci a duniya, ai Junaidu da Shehu mutane ne mabanbanta, hallayr su, dabiun su, wayewar su, sanin Allahn su. Da bakin ki Kika ce baya sallah, Wanda Bai Kare hakkin Allah ba ta Yaya zai Kare hakkin mutum? Shikam dai kinsan Shehu kinsan waye shi, tun ranar da na fara ganin ku tare naji how I wish shi din mijin ki ne to Amma akwai yadda Allah ya tsara komai, follow your heart and pray!"
Na fahimci dukkan abinda take nufi Kuma Nima Ina jin hakan, na Dan langwabar da Kai nace
" To Mom Yaya Hasher fa?"
Kafin ta bani amsa muka ji fitowar Dad, ya karaso inda muke zaune ya tsaya daidai kanta Yana fadin
" Me ake cewa Babu ni?"
Mom ta dube shi ni Kuma na Mike Ina gaishe shi, ya amsa Yana murmushi yace
" Princess Ina zakije? Kije ku karasa maganar ki"
Na girgiza Kai nace
" I'll be late to school"
Daki na wuce bayan na leka kitchen na gaida Nanny sannan na wuce dakina na shirya na fito da backpack sabe a bayana, Dad na cin breakfast, Mom na zaune ta tattara dukkan hankalinta akan shi, da alamu magana suke me muhimmanci, na tsaya nace
" Zan tafi"
Mum ta dubeni tace
" Wanne irin Zaki tafi, breakfast din fa?"
Na yatsina fuska nace
" I've took tea, se na dawo"
Dad ya bani kudi sannan na juya na nufi kofar naji muryar Dad yace
"Princess kinsan me yasa Yayanki Bai shigo ba?"
Na juyo nace
" Mhm! Dama zai je office ne shiyasa"
Ya gyada Kai yace,
" You call him for lunch ok? Kinsan saboda ke yazo garinnan ko?"
Na gyada Kai Ina saka hannuna a baki kamar wata doluwa, Anty Nafisa tana murmushi tana Kara juya Masa tea din gaban shi
" Treat him kindly he's your guest!"
Nace
" To Dad!"
" Good girl!"
Na juya Ina murmushi, a raina nace idan naki Yaya Shehu I'm sure yadda mutanen nan ke son shi akwai damuwa. Ba jimawa na Isa makaranta, mukai test akan pharmacology sannan na fito na kunna data ta ready to face Yaya Hasher. Aikuwa dai da sakon shi na fara cin Karo, hakan yasa na bude kafin na karanta Kiran shi ya shigo ta WhatsApp, na sauke ajiyar zuciya na dauka, muryar shi so down na gaishe shi ya amsa yace
" Kin Gama guje gujen kenan?"
Na Dan Bata Rai nace
" Nifa ba gudu nake ba"
" To me kikeyi? Tun yaushe na Miki magana Babu reply"
" I was busy ne fa"
Na fada straight away, yayi shiru har seda nayi tunanin bazai Kara cewa komai ba yace
" Been busy Bai hanaki fita da Wanda kike so ba ko?"
Na danyi tsaki siriri nace
" Yaya Hasher let's stop this please, Yaya Shehu came all the way daga Istanbul to Lancaster, just for him to see me, kaga Dole Zan kashe komai nawa na bashi lokaci"
" Saboda ni ban zo ba kenan. Amma kinsan Ina son ki ko?"
Na girgiza Kai kamar Yana gabana nace
" Bansani ba saboda you've never mentioned it"
" But I showed you all the signs ko? Zakice Baki sani ba, Zaki nuna min Baki gane cewar Ina sonki ba"
" Yaya Hasher kasan me? I'm thanking you for giving me your shoulders to cry on, bazan taba manta alkhairin ka ba, Amma Ina son kasan cewar nidin bansan kana sona ba saboda gaskiya bana daukar signs, for me to understand se idan mutum ya fada wannan kalmomin daga karkashin zuciyar shi zuwa bakin shi. Yaya Shehu ya fada tuntuni tun kafin nayi aure. We're just rekindling love din"
Wata nannauyar ajiyar zuciya ya saki yace
" Amina dama kina da Baki har Haka, what are you trying to tell me, kin zaba Shehu akaina? Just think about us mana"
Nayi shiru kaina har ya fara ciwo, se nace Masa Zan Kira shi I need to eat, Ina aje wayar na dago kaina na gan shi tsaye akaina hannunsa cikin aljihun suit din jikin shi, he looks handsome wallahi, se naji kamar na boye shi kada wasu su kalleshi. Ya zauna gefena Yana sakar min murmushi yace
" Whatsup? Waye yake Baki hard time a waya?"
Na kalla wayar na kalleshi nace
" Yunwa nake ji"
Ya mike da sauri yace na wuce ya samo min abinci, tare muka ci sannan ya raka ni class ya tafi akan zamu hadu da daddare, da dukka ba zamu samu yin lunch a gida ba.
AFIYYA is not free, pay 300 to3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 52
A hankali idanun shi Suka sauka akan mutanen dake zaune gaban massalaci, bawai a zazzaune suke ba, yawanci butoci ne a hannun su suna yin alwala kasancewar an Kira sallar laasar, ya kalle su ya dauke Kai tareda kokarin wucewa Amma se ya gagara wucewar, wani irin abu yaji a cikin zuciyar shi tare da amsa kuwwar maganganun Afiyya acikin kunnuwan shi, abin ya zame Masa tamkar wani nightmare, kowacce sallah idan aka Kira Yana zaune se ya dinga Jin tamkar wani nauyi cikin zuciyar shi. Ya karasa a hankali for the first time a abinda bazai taba tunawa ba ya dauki buta ya ciko da ruwa ya zauna a wani dakali can gefe ya fara alwala a hankali, kamar yadda yaga anayu, dukda Babu coordination Amma Yana yi din dai. Yana gamawa aka tada ikama Dan shiga sallah, wani farin Gaye a gefen shi ya Mika Masa hannu yace
" Zaa Shiga fa"
A hankali Junaidu ya saka hannun shi cikin na gayen suka shiga massalaci, wata irin nutsuwa yaji tana shigarshi, ya tsaya yaga yadda mutane ke ta hada sawu, suna jeranta kafafun su tareda hade duga dugunsu, se yaji zuciyar shi tayi taushi har danshi danshi ya fara bin fuskar shi, a karon farko ya fita
" Astagfurillah!!!"
Ya karasa a hankali ya jera da Yan uwan da musulinci ya hada dasu, suka tad sallah, kafin raka'o'i hudu su kammalu fuskar shi ta jike da hawaye, Bai taba jin wannan peace din cikin rayuwar shi ba kamar yadda yaji a wañnan lokacin. Aka idar kowa yayi addua ya fice, shi Kam kasa Koda tashi yayi se ya zauna ya cigaba da shiru da zurfi cikin tunani. Dama abinda ya Bari kenan? Dama Haka musulin ci yake d haske? Dama Haka sallar take da yayi neglecting iya rayuwar shi? Yana nan zaune har aka Kira mghrib, gaba daya yayi laushi ya taushi tubus, fuskar shi kawai zaka kalla kasan cewar akwai babban Abu a tare dashi, he looks pale and down, abubuwa sun Masa katutu kunya take ji Yana Kuma ganin tamkar dukkan zunuban shi a rubuta shi a Kan goshin sa shiyasa ya kasa daga idanun shi balle ya kalla wani. Yayi alwala yazo akai jamin maghrib,Bayan an Gama Malam wato limamin yazo ya fara nasihu kamar yadda yake duk Bayan sallar mgahrib da ishai, a wañnan ranar yayi nasiha Akan abinda ya Zama rampant rashin bin iyaye, ya dakko ayoyi da hadisai sahihai Wanda suke supporting dukkan bayanin shi, Wanda baibi iyaye ba to ya kamar Bai bi Manzon Allah SAW wanda baibi annabi ba kuwan yasan ya dakko gagurimin rikici tsakanin shi da Allah! Gaba daya jikin shi yayi sanyi tamkar an sassara Masa jiki Haka yakeji, a karshe yace shawara ce yake bawa dukkan mutanen dake sauraren shi indai har akwai rift tsakanin su day iyayen su to suje su daidaita tsakanin su tun kafin lokaci ya Kure musu. Kafin wani lokaci se tsiraru a cikin massalacin kowa ya Kama gaban shi, Haka nan ya cigaba da Zama har lokacin da akai sallar Isha wadda ya Kara yin nasiha akan zamantakewa da alumma, ya nuna cewar Allah yafi kowa sanin menene a zuciyar bawan shi Amma Dan ya nuna Mana muhimmancin exhibiting halaye masu kyau, shiyasa idan ka mutu se malaiku su dinga bin chamber chamber ta mutane suji shedar da zasu maka, Kuma wannan shedar zaayi amfani da ita wajen Yi maka hisabi, shiyasa idan ana maganar ka to ka dinga duba kanka, A known sociologist Charles Cooley yace looking Glass self, "The looking-glass self theory suggests that we come to know ourselves by reflecting on how others see us" Yadda kake daukar kanka ba lallai Haka kake ba, ya kamata kana duba ya mutane suke kallonka lokuta da dama shi ne ainahin yadda kake. Yana fitowa a massalacin ya samu napep, Yana Shiga me napep ya tambaye shi Ina zaije for unknown reason kawai yace a kaishi asalin gidan Malam, me napep ya kada napep se kofar gidan Malam, ya tsaya a kofar gidan Yana ganin irin mashahurin canjin da Suka samu, gidan Kan sjo ya canja, shekaru sun tafi Sha biyar tunda ya baro gidan Kuma Bai Kara komawa ba, ya tsaya Yana tuna lokacin yarinyar su day jamilu, lokacin da yake cin zalin yaran mutane, lokacin da ake Kai karar shi Hajja Kan ce suyi hakuri yarin ta ce, yaayinda shi Kuma Malam ke cewa Dan shi jarumi ne, w Haka ya tashi da zuciyar cewa shi he's superior to everyone he came across, ya Zama Wanda Babu Wanda zai iya tankwara shi se dai yayi abinda yayi niyya a lokacin da ya ga dama. Wannan shi yasa da suka zo tankwara shi se Suka kasa. A hankali ya dinga tuna rayuwar da yayi a wañnan gidan, kamar picture Haka suka dinga wucewa ta idanun shi, hannunshi ya dunkule in a fist kafin Kuma ya juya Dan he knows he looks pathetic bazai iya Shiga a Haka ba. Cikin sauri ya juya Dan barin gurin Amma se yaji wannan muryar me cike da dattako, dijantaka, hakuri da sanyi yace
" Junaidu Ina zaka je Kuma?"
A Haka ya tsaya Bai motsa ba sede dukkan jikin shi a sanyaye yake, har wani rawa yakeyi. Malam ya karaso tareda saka hannun shi ya ruko na Junaidun Wanda Yana juyowa ya rungume Malam din, ya saki ajiyar zuciya Malam ya Kashi Suka shiga ciki Kan shi a kasa kana kallo kasan a takure yake ga Kuma kunya me tsanani data lullube shi.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 53
Babu kakkautawa alarm din da aka seta a wayar ya cigaba da ruri Wanda yasa Kara dunkukunewa cikin quilt din , ganin alarm din bazai kashe Kan shi ba yasa ta zuro hannunta Wanda yasha artificial nails an painting dinsu da white nail paint da wasu stones a jiki da a zahiri ita ya kawata ta Amma a gaskiya it looks dirty. Wayar ta janyo har lokacin bata fito da fuskar ta ba, tsaki ta buga tare da tashi ta zauna Wanda hakan yasa quilt din yin nashi guri Wanda ya bayyanata, she looks disheveled, gashinta dukka a barbaje kamar wata bishiya, fuskarta tasha Mai Dan kuwa ba se an fada maka bleaching take ba. Jikinta sanye da bum short da half vest. Wayar ta dauka tareda karawa a kunne Ashe bama alarm din bane Husna kawarta ce ke kiranta, tunda taga lokacin da ta Kira tasan definitely something is up,
" Husna bacci nakeyi"
Ta Dan yatsina fuska tace
" Me zanyi a Whatsapp Kuma? Just tell me"
Ta Dan Kara sakin tsaki tace
" Ok Zan duba, I'll get back to you!"
Daga Haka Nusaiba ta kashe wayar tare da sakko kafafunta ta zura cikin wani soft bedroom slippers, toilet ta Shiga ta wanke fuskarta tayi alwala tayi brushing, tana fitowa ta samu har an canja spread din gadon, sallayya ta shimfida ta hau Bayan ta saka jilbab Wanda ya rufe duka jikinta, agogo ta kalla har Tara saura, hakan yasa ta yatsina fuska ta tada sallar asubar da batayi ba akan lokaci. Seda ta idar ta dauki coffee din da aka aje Mata a gefe, ta juya tana ta hura hanci ta dauki tea spoon tana juyawa ta fara Sha a hankali sannan ta cewa me Mata gayran dakin ta Bata wayar, ta Miko Mata cikin ladabi, ta karba ta kunna data sannan ta jira komai yayi settling kafin ta duba message din Husna da ya shigo, tana dubawa taga pictures ne da yawa se videos Haka, ta shiga budawa tana jin ko menene tabbas Yana da muhimmanci da Husna zata Mata sharing. Yana Gama budewa da wannan video namu na swing ta fara cin Karo, idanun ta ta ware sosae tana kallo har ya Gama cikin sauri ta Kara kunnawa tana zooming fuskata, ganin bazai Yi ba ta bude sauran pictures din, wani Wanda Janet ta Mana a bakin mota ranar da ya raka ni tutorials school, tayi zooming tana kallon fuskata da wani farin ciki da yake a kwance bama ya bukatar se an fada. Aje login coffee din tayi ta bar wayar a gurin ta Shiga toilet, har ita Shehu zai ciwa mutunci? Yayi karya Bai Isa ba wallahi, wannan karya ne ta dinga ayyanawa bayan ta sakar ma kanta ruwa me dumi, cikin hanzari ta Gama wankan ta fito ta shirya a gaggauce cikin wando da riga ta daura jacket wadda iya karta kugunta, ta yafa wani firirin mayafi hade da saka takalmi wani high wedged sandals. Fitowa tayi rike da wayatta saboda yadda ranta ke bace Bata ma ga alamar Kiran da Husna tayi Mata ba. A parlor ta tadda wata dattijuwar mace, itama kana kallonta kasan Yar duniya ce, fuskarta is wrinkled Amma alamar shafe shafe Yana nan tattare da ita.
" Mama zanje Law firm din Usman"
Maman ta kalleta tace
" Meye Kuma hadin ki da Usman? Ina ce maganar ku ta tashi"
Ta girgiza Kai tace
" Idan na dawo Zan Miki bayani, I need to go"
Daga Haka ta finciki Jakarta tayi waje, maman tayi murmushi tace
" Banda wauta ki samu miji kamar yaronnan lokaci daya ki juye kice ba Haka ba. Allah ya kyauta"
Nusaiba na fita office din Shehu ta nufa, tun da ta Isa Secretariat shi tace Mata ai baya nan, kwana biyu Bai zo ba Yana hutu. Ko amsa Bata Bata ba ta juya tana fadin
" Yau har gidan su zanje, ta Yaya zance na bar Abu sannan wani ya dauka, ai idan na bar Abu bazai cigaba ba sede ya lalace!"
Lokacin da ta Isa kofar parlon, sarki na kokarin fitowa daga gidan, ya kalleta ya Kuma kalli kayan jikinta ya matsa ya Bata guri ba tareda ya Mata magana ba, he hates yarinyar to the square of infinity, ya ga wautar Shehu da ya kalleta yace Yana sonta, the girl is so artificial, komai nata jabu ne. He was so happy lokacin da ya fara ganin hankalin shehun ya fara rinjaya wajen Afiyya yasan definitely zai bar Nusaiba ya koma can, se kuma aka samu akasin wannan auren Amma dukda Haka yasan Dan uwanshi Bai hakura ba, yasan a zuciyar shi burin shi auren Afiyya ne. Ya ficewar shi Bai koma ba Dan yasan Ummiey will handle everything squarely, tana shiga ta samu Daddy da Ummiey na karyawa, tunda Ummiey ta amsa Mata sallama taji kamar ta koma, dama Basu taba haduwa da juna in person ba, sede kowa Yana da labarin kowa, Ummiey ta dubeta tace
" Zauna Bari a Kira Miki Nadia"
Ta girgiza Kai tace
" Gurin Usman nazo"
Ummiey tayi shiruu tana tunanin waye Kuma Usman se ta tuna Ashe ubanta ne Usman din, ta Kara kallonta kafin Kuma ta tura kujerar ta baya ta dawo parlon tana Kare Mata kallo, Daddy shidai Bai ce komai ba se abincin shi da yake ci Yana Kuma sauraron su,
" How are you two related keda Usman Dina?"
Nusaiba ta kalli Ummiey sannan ta Dan fara Wasa da hannunta ba tace komai ba
" Bakiji ba? Meye tsakanin ku keda Shehu? I mean Usman"
Ummiey ta Kara maimaita Mata, Nusaiba ta dubi Ummiey tace
" Ni budurwar shi ce"
Ummiey ta zaro idanun waje yayinda Daddy dake cin abinci ya kware, cikin sauri ya tsiyaya ruwa ya fara sha, Ummiey ta dubeshi sannn ta maida hankalin ta Kan Nusaiba tace
" Are you Nusaiba? Kece?"
Ta gyada Kai tana jin dama wannan ce uwar Shehu, ai ita Bata taba tsayawa gaban wani ba ta kasa yin abinda tayi niyya ba, sewannan matar ta kasa Koda kwakwarran motsi. Ummiey ta Kara kallonta tace
" Look! Duk ranar da Kika koyi descent dressing you can come back here, wuce ki tafi!"
Nusaiba kamar ta hantsila Haka ta fice ranta a mugun