Showing 60001 words to 63000 words out of 95282 words
Chapter 21 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt
samu Nanny ta Jima da bacci. Maimaikon bacci se kawai na dakko kur'ani nayi tilawa sannan na kwanta Ina tabbatar da nayi blocking dukkan channels din tunani na, ya kamata wannan abin su tsaya a Haka, Dole nayi bacci me dadi!
Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam to First bank of Nigeria, send evidence of payment to 09063467258.
Please can I have your prayers?43
Daga emirate council din Ringim suka kaimu Kano, tun sassafe muka kammalla breakfast da sauran abinda ba zaa rasa ba. Na kalla kaina jikin fuskar wayata idanuna da sukai can ciki duka sun fito, wannan unexplained ramar da nayi a fuska ta cike se abinda bazaa rasa ba, jikina ne dai nasan wannan se a hankali dukda shima ya fara karbar canjin. Na saki ajiyar zuciya Ina Kara nanata kalmar alhamdulillah, na sani ba wayo na bane ko dabara ta yasa na Zama Haka ba, yasa na fita hannun wancan azaaluman ba, Allah ne yayi miracle dinsa da Haka dukkan godiya a gareshi take. Hijab na saka na fito da wayata a hannu Ina gyara zaman sandal wedge din kafata. Nanny na zaune alamar ita ta kammalla, tare muka wuce can parking space inda already motar ke jiran mu. Har na Shiga se Naga Hafsa tamkar an jefo ta, Uncle Babawo ya dube ta Dan shi Bai riga ya shigo ba, ta gaishe shi da murnar ta, inata kallon ta she's so carefree, nasan yarinya ce Amma tasan dukkan abinda ke faruwa, but she chooses to act naive and neutral. Bayan ta gaisa da kowa ta karaso inda nake ta tambayeni zancen kayan jiya, se na maida hankalina Kan Anty Nafisa wadda ita na bawa akan tasan yadda zaayi a aika ma Hafsisi din. Anty Nafisa tace ta bayar zaa Kai Mata gida, se ta rungume kaina Dan fito dashi ta window a kunne na ta rada min
" Kar ki yafe musu!"
Nayi saurin janye kaina Ina dariya itama tana Taya ni, na gyada Mata Kai nace
" Ki gaida Mino sosae, kice na tafi Amma idan na dawo har gidan ta zanzo"
Daga Haka ta wuce mu Kuma muka dauki hanya, leaving behind my oppressed life! Na bude sabon shafi cikin rayuwata. I know it hard, kafin wancan shafin ya Kare zaka Sha wahala but Amma Dole dai zai Kare, to every hardship anyi Mana alkawarin ease, ni dai inada yakinin nawa ya karaso. Tunda muka shiga airport naji wani irin yanayi, naji tamkar Ina juyawa zanga mahaifina, na tuna lokacin da airport a gurina tamkar zuwa kasuwa ne, na kalla yadda a shekaru uku da doriya an Kara gyara airport din. Muka zauna har seda jirgin su Rooks ya tashi Bayan harda kukan rabuwar mu ni Kuma Ina dariya, bana tunanin as simple as rabuwa da Rooks zai saka ni kuka, da dai da ne nasan se nayi to Amma yanzun na fuskanci abubuwan da kwakwalwa ta Bata son tuna su!
Muna landing a Abuja wannan yanayin ya Kara lullube ni, na damke hannun Nanny da itama yanayin ta ya canja, na Kuma San tabbas ta tuna Abbuna da Mama ne, na tsaya jikin wani popcorn stall inda anan Abbu ke siya min, mutumin Yana nan abin shi, ni Kuma Abbuna ya rasu! Se kawai na saki kuka me daci, dukkan su suka juyo suna kallona, uncle Babawo ya saki hannun Anty Nafisa ya karaso inda nake tsaye na rufe fuskata da hijab inata sheshekar kuka yace
" Me ya faru? Me akai Miki?"
Nace cikin kuka
" Abbuna na tuna! Abbu..."
Se naji ya saki ajiyar zuciya, Anty Nafisa ta hadani da jikinta tana nuna min it's ok Dan nayi kuka saboda tasan tuna shi nayi, Amma ya kamata duk lokacin da na tuna shi na Masa addua har Mama ma da bansan ta ba shi ne kawai abinda suke bukata daga gurina. Na gyada kaina Ina share hawayen nawa sannan muka cigaba da tafiya, Uncle nama Nanny fadan biye ni da tayi tana sharar kwalla. Tunda muka doso hanyar Gwarumfa kaina kamar zai cire Dan kallo, kowanne titi muka shiga se memories din gurin ya dawo min a Haka har muka Isa gidan Uncle dake cikin wani sabon estate. Su kadai suka Shiga no dashi kawai juyawa mukai zuwa embassy Dan mu fara neman visa din. Munje muka ciccike formalities sannan aka ce mu dawo washegari. A gajiye tikis muka fito daga embassy ya tambaye ni ko akwai abinda nake so na girgiza Masa Kai se kawai ya tsaya wani ice cream parlor ya karba min scoops da frosted cake.
Muna zuwa gida na samu har sun Gama gyaran gidan ta Gama girki suna zaune suna Hira, tana jin sallamar mu ta mike ta rungumo uncle wannan aladar ta ce Babu ruwanta ko waye a guri kuwa, saboda yawanci tana da aladun westners kasancewar a cikin su ta tashi. Farkon zamana dasu kunya nakeji Amma a hankali Naga su Basu ma damu Dani ba se ya zamana I admire their love da suke ma junan su. Seda ta gama pecking dinsa kafin ta dawo kaina, na tura Baki Ina cire sandals din kafata nace
" Ni Baki murnar ganina ba kenan"
Me zasuyi Banda dariya, uncle ya wuce ciki suna gaisawa da Nanny dake dariyar wauta ta, Anty Nafisa na kokarin hugging dina na ture ta na wuce irin nayi fushi dinnan, ta Dan daga muryar ta tace
" Darling kaga abinda ka jawo ko?"
Shi dai dariya yake har lokacin ya wuce daki, na zauna na fara cin cake dina. Kwana biyar mukai a Abuja visa ta samu da komai da komai na Shirin tafiya. Da yamma na gama hada dinner, Ina fitowa na samu Anty ta nufi kitchen din, na tsaya tace
" Princess din Darling, Wai Zaki iya tuna kawar ki ta garki?"
Na gyada Kai na ta Yaya ma Zan manta childhood friend Dita Amina Abubakar Rogo. Se tace min yace na shirya su kaini muga ko tana nan. Aikuwa a guje na wuce daki, Dan Nanny seda ta min fadan Wai za taga ranar da zanyi hankali. Na tura Baki nace
" Duk nutsuwa ta?"
"Ke Kika sani. Ni Kam kin Kira mamarki Bintu?"
Na girgiza nace Zan kirata idan na dawo Dan ranar ta kirani ban Kira ba kuma. Cikin sauri na shirya na fito das Dani Nanny ta Kara kwatanta musu gidan sannan muka wuce, se Naga hanyar na dawo min tiryan tiryan, har muka Isa kofar katon gate dinsu, muna parking na fito se Naga an bude gate alamar fita zaayi, katuwar mota Lexus me numfashi ta fito, se Kuma Naga anyi parking an bude kofar da sauri, kafin na Gama tantance komai naji an rungume ni tamkar zaa balla ni, dodon kunnena har amsawa yake Sabida ihun da takeyi. Se data Gama sannan ta sakeni tareda riko hannuna, anan na Kare Mata kallo sure Amina Abubakar Rogo ce, ta Zama budurwa sosae, tayi kiba dukkan jikin ta sun cika ba zaka taba comparing dinta Dani that's skinny ba Kuma har yanzun jikina is developing.
" Amina Afiyya innanlillahi Ashe we're bound to meet again? Kawai kikai vanishing into thin air"
Ina murmushi sosar da ya bayyana hakorana nace
" Amina I've missed you!'
Na rungume ta nima, lokacin Yan gidan su da nawa Suka fara gaisawa. Na saketa na gaida Mom da Dad da Basu manta ni ba se kannenta guda biyu. Itama ta gaida uncle da Anty. Babanta yace ai Kano zasu tafi yanzun saa mukai muka same su, yanzun flight dinsu baifi hour da wani Abu ba. Haka mukai exchanging contact nace Mata London Zan tafi kawai zamuyi magana. Ranar nayi farin ciki na Kuma Kara tabbatar da kokarin Uncle nasan ya dawo min da komai da na rasa, sede BAHAUSHE yace baa Bari a kwashe daidai.
Muna Isa gida na cire kayana mukai dinner tun a table na ishi kowa da labarin Amina Abubakar Rogo, Amma Haka Suka dinga saurarao na seda na kware tukun kowa ya samu lafiya. Ina komawa daki na tadda call da wata Turkish number, jikina ya bani ko Ummiey ko Kuma Nads, hakan yasa na fara kokarin returning Kiran Amma se wani ya Kara shigowa nayi saurin dauka se kuwa naji muryar Ummiey
" Congratulations daughter! Se jiya nake jin abinda ke faruwa wajen kawun ki, naji Dadi Ina fata yanzun Babu abinda ke damunki"
Na fara gaishe ta sannan nace Mata Babu komai, ta Jima tana min nasiha tareda shiwa uncle albarka sannan ta bani Nads muka gaisa kamar nace Ina Yaya Shehu se na Bari kawai. A wañnan Daren se past 12 nayi bacci munata waya da chatting da Amina Abubakar wadda tuntuni sun Isa Kano, ta fada min yadda suka ta nema na har Ringim sukaje Basu San wanne family nake ba se juyawa sukai, na Bata labarin auren da akai min har da kukan ta. A kwana na goma muka nufi airport Dan wucewa Lancaster. Muna boarding flight din wayata ta fara ringing, Truecaller tayi identifying Kiran daga Istanbul ne sede ba Ummiey bace ba Kuma Nads bace. Na fara kokarin picking naji ana kowa ya maida wayar shi flight mode, ayi fastening seat belt, plane about to take off!
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 A'isha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.45
Ko baiyi magana ba kasan Yana cikin farin ciki, a ganin shi a wañnan lokacin Ummiey ta Gama Masa komai duniya da lahira. He'll surely use the time perfectly. Yana fitowa sukai Karo da Daddy da shigowar shi kenan, ya Dan matsa Yana bawa Daddy hannu sukai musabaha, ya kalleshi yace
" You seems happy what's the news?"
Ya shafa Kan shi yace
" Daddy sannu da zuwa"
Ya bugi kafadar shi a hankali Yana murmushi yace
" Sannu ya naka office din?"
Yace
" Alhamdulillah not bad"
Daddy ya gyada Kai ya shige ciki Yana Masa fatan alkhairi, hannun shi ya dunkule In a fist yayi wani juyi tareda sakin murmushi yace
" Yes!"
Nads Dake tsaye duk abinda yake tana kallon shi, duk a su hudun ta fison Shehu saboda sun fi dasawa, halayen sui sunfi Mata, Dan Tasha fada race da aure ya hallata tsakanin su tabbas shi zata aura, Kuma se yazo yayi rashin Saar Nusaiba, Dan ita a ganin ta ba karamar rashin saa bace kace Wai zaka aura Nusaiba, ita kanta da take mace ba taga abin burgeea a tattare da ita ba. Ta matso ta Sha gaban shi tare da Mika Masa hannu tayi crossing kafafun ta, ya kalleta cikin rashin fahimta yace
" What?"
Ta turo Baki tana wani sly smile tace
" Payment!"
" For?"
" Afeeys' contact na London!"
Yayi dariya sosae har ta Bata Rai yace
" It's already in my upstairs! Ummiey ta rigaki!"
Ta buga kafarta tace
" To ka biya na Mata magana ta saurareka Mana"
Ta fada tana bin Bayan shi Dan Yana Gama fada Mata yayi hanyar parlor. Bai kulata ba har ya zauna gefen Sarki dake kallon su, ta zauna itama tare da riko hannun shi stubbornly tace
" Dan Allah Mana!"
Yace
" Kin dame ni fa! Ki kyaleni"
" To biyana kawai zakai nida Rooks mu kafa maka kujera"
Ya Mike yace
" Yaya Sarki just warn your sister ta isheni"
Sarki ya dube su sannan yace
" Da alama ka kusa tafiya London kenan?"
Ya gyada Kai Yana Kara bude bakin shi saboda murmushi yace
" Sure, gobe Dana fita Zan fara neman visa!"
Ya gyada Kai yace
" Take care of her, she's suffered a lot"
Yace
" Inshaaa Allah!"
Satin mu biyu na fara fita zuwa makaranta, bamu da wani nisa sosae da famous University of Central Lancashire. Ranar Monday tun asuba Dana tashi dauki Bai bar ni na koma ba, nayi wanka sannan nayi sallah na fito parlor, kitchen na wuce Mom ta fada min abin breakfast Dan Haka na fara hadawa, banana pancakes ne se tea. Ina gamawa na Dan ci kadan na koma daki na Ciro wani black trouser na saka da farar top sannan na saka hula Bayan na taje gashin kaina, open abaya green na daura a saman na danyi buttoning dinta sannan na dauka books Dina da system na fito parlor. Lokacin duk sun fito Suma, na gaishe su Mom tace
" Kinyi bacci kuwa?"
Nayi dariya nace
" Mom nayi fa! Me Kika gani?"
Tace
" Ai Na zata dauki ba zai barki ba"
Lokacin Dad ya fito shima ya Gama Shirin, Bayan mu Gama gaisawa ta Masa serving pancakes na zauna saboda tare zamu fita dashi. Kara naji alamar shigowar message, na dauka thinking Nads ce jiya ta barmin message akan taji Yaya Shehu zai zo London, Dan Allah nace ya taho da ita, shi ne nace Mata yaushe zaizo, nayi missing din shi sosae. Ita Kuma da taga ko kula maganar su taho tare banyi ba se tayi fushi tace ba zata Kara updating dina ba. Nads rikici!
Message din Yaya Hasher ne
Yaya Hasher: Good morning beautiful! Ya Kika tashi?
Nayi murmushi Ina Dan jin dadin beautiful din da ya kirani dashi
Me: I'm fine alhamdulillah! Kai fa?
Yaya Hasher: Ina son na ganki, ya zaayi?
Nayi shiru Ina tunanin possible yadda zaayi mu hadu, were millions of kilometers away, se nace
Me: kazo London Mana!
Yaya Hasher: Kinsan se nabi protocols da yawa kafinnan and I want to see you now please"
Na danyi shiru Ina tunanin how's that possible ya ganni yanzun kawai se nayi offing data ta na saki ajiyar zuciya, Dad na gamawa muka wuce se school. Bana tunanin a Nigeria akwai irin wannan hadaddiyar campus din, tundaga gate komai yayi kyau environment din is so conducive. Karfe takwas calss din mu ya fara, Ina zaune kusan a gaba, lecturer ya shigo kana kallon shi kasan bature ne, yayi introducing Kansa as Mr James zai dauke mu intro to human biology. Seda ya samu dukka mukai introducing kanmu, anan na gane akwai wani guy da Kuma wata Yan Nigeria. Sauran Kuma yawanci British dinne, se yan across su uku making us six. Kafin ya fita ya karba email address din mu akan zai tura Mana soft copy na lectures din. Bayan nan se muka je breakfast muka dawo mukai Use of English shima wani British dinne, nayi enjoying class din sannan muka Kara lecture daya Mika tashi. Ina fitowa ana laasar nayi sallah naji Ina jin Yunwa, Amma se na daure na Kira Dad nace na tashi yace shima Yana Hanya zai karaso mu wuce. Ina nan zaune yazo muka tafi Yana ta tambaya ta yadda school din take nace Masa ai da dadi, lecture ma Babu wuya.
Da daddare duka an tura Mana lectures din da akai na ranar, na Shiga daki na bi ta Kai na gane komai sannan na kunna data Dita, kamar Yaya Hasher na jira Sega WhatsApp voice call din shi. Na saki ajiyar zuciya Ina ayyana ya fiye naci, na sliding tareda saka shi a speaker
" Beautiful"
Se na samu kaina da murmushi nace
" Naam! Ina wuni?"
Ya saki ajiyar zuciya I can hear him sigh in relief yace
" Lafiya Lau, ya Dad and Mom?"
Suka Suna lafiya na bashi amsa sannan ya fara complain wai nayi shunning dinsa, yace Yana son ganina Amma naki bashi dama
" Yaya Hasher na baka option kazo London mu hadu, kace it's a bit of protocols. Ta Ina zaka ganni for goodness sake!"
" Face time, zoom, WhatsApp video chat duka ai zasuyi favoring dina"
Na danyi murmushi nace
" Kaga ba laifi na bane Kaine baka making abin easier ba, da se kace let's use this"
Mun Jima muna Hira dashi tun Ina jin bana enjoying maganar har na dawo na saki jiki sosae, seda Mom ta so Kirana akan zamuci abinci kafin na Masa sallama na tafi.
AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria, send evidence of payment to 090634672547
Cikin kankanin lokaci muka Saba da Yaya Hasher sosae, muka Zama so close da kullum se na fada Masa yadda rana ta ta kasance. Amma duk wannan shakuwar kullum karkashin zuciyata Ina tunanin se yaushe Yaya Shehu zai zo, Dan tun ranar da Nads tace min zai zo gaba daya nake anticipating zuwan shi, kullum idan na dawo daga school to see na tambayi Nanny ko munyi Baki, a Haka har sati ya wuce kullum amsar tata daya ce Babu Wanda yazo, da farko tana tambayata wa nake expecting, se nayi murmushi nace Mata Babu kowa. Ranar muna chatting Bayan na dawo daga school da Yaya Harith nake tambayar shi su Yaya Shehu yace min, ai Yana nan Yana ta neman visa Bai samu ba da tuni sede kawai na ganshi anan Lancaster, for that moment se na Dan ji Dadi da ba fasa zuwan yayi ba, se Kuma na fara adduar Allah ya sa ya samu visar da wuri ya zo na ganshi.
A bangaren karatuna munyi nisa, dake ni me naci ce I enjoyed every bit of it, bana Bari na tsani wani course, Dan nasan da zarar na tsana course din to I'm dead. Haka kulllum nake zuwa na dawo. Ranar Saturday na tashi Babu inda zanje dan banida class se tutorials da aka hada Mana, Kuma na tashi bana son zuwa, Haka na fito kamar ko yaushe duk weekend se na danyi relieving dinsu da aikin gidan. Ina zuwa kitchen na nufa na wanke hannuna sannan na fito da kayan da zanyi amfani dashi na saka apron na fara girki, Ina cikin Yi Nanny ta sameni, muka gaisa se kawai ta zauna muna Dan taba Hira
" Har yanzun kawun ki na a kulle fa"
" Eh Amma naji ranar Dad na waya Wai kamar zaa sake shi har sauran ma"
" Su Junaidu kenan?"
N gyada kaina nace
" Haka naji yace Wai anyi reducing sentence dinsu"
" Amma ke ya kike ji? Kinji ko irin haushi dinnan?"
Na danyi murmushi Ina ciccire parsley nce
" Haushin me Nanny? Ni kawai nasan ban yafe musu ba, cutata da sukai nasan Allah zai saka min Amma duk hukuncin da zaa musu a duniya bazan ji na gamsu ba"
Se ta gyada kanta kawai se muka cigaba da Hira har na Gama, a lokacin Mom ta fito ni Kuma na shiga wanka, ta biyo ni daki lokacin Ina shiryawa, ta zauna bayan mun gaisa tace Ina fesa turare jikin
" Yau Zaki fita ne?"
Na girgiza Kai nace
" A'a Mom Amma Zan fita zamuyi badminton