Showing 78001 words to 81000 words out of 95282 words

Chapter 27 - AFIYYA BOOK COMPLETE DOCUMENT By A'ishatu.txt

Ayshatuu   

16 Jul 2024

6656

Ni Amina ta iyayen mijinta daya, tana gidan mijin ta"


Se lokacin Ambaby tace


" Anty Afiyya muke nufi"


Wani mummunan kallo ta fara musu tace


" Nan yayi muku Kama da gidan su Afiyya ne ko meye, malamai ku fitar Mana a gida"


Ta fada tana Jan tabarmar kamar zata jirkice su, Siyama dama na tsaye tacw


" Haba Ummaah..."


Kallon da tayi Mata yasa tayi saurin rufe Baki, tuni sun mike Siyama tace


" Ai Afiyya batayi sati biyu ba a garinnan ta tafi London, inaga sede kuje kano gidan Kawu Tijjani"


Su Ina Suka San wani Kawu Tijjani, Haka Suka fice ransu a bace suna iya jiyo muryar Ummaah na zazzagawa Siyama fadan ta kulasu itama ta bisu tunda nan ba gidan aurenta bane, ita kuwa tayi shigewar ta daki ta Mata kunnen uwar Shehu! A kofar gida hakan ce ta faru Dan Kawu Sa'idu kamar zai daki Junaidu ya nuna Masa shi ne silar lalacewar komai, munafurci ya dawo dashi. Wannan kenan




A bangare na, na dawo gida washegari na fara exams sede dukkan wani Abu da nakeyi Ina tunani shi ki nakeyi kamar nayi tsuntsuwa naje gare shi, har na gaji da tambayar Nads ko ya karaso, sede tayi dariya tace ita kuwa taha ta kanta. Na fito daga paper Primary health care se ga Kiran shi ya shigo cikin sassanyar murya nace


" Honey!"


Yayi murmushi Wanda naji sautin shi yace


" Damsel kinata jirana ko? I'm sorry se yanzun na karaso ko gida ban karasa ba"


Naji wani irin farin ciki ya lullubeni so I'm that important na tambayi kaina, yace


" Are you there?"


Na saki ajiyar zuciya nace


" Ina jinaka ka karasa gida ka huta zamuyi magana. Allah ya huce gajiya my regards to everyone at home"


Daga mukai sallama na wuce gida, bamu Kara waya ba se dare har nazo Zan kwanta, mun Sha Hira se can nace Masa


" Honey waye Nusaiba?"


" Hello!"


Ya fada Wai ni zai nunawa Bai jiba, nace


" I know you heard so I'm not repeating myself my Dear!"


" Were you eavesdropping?"


Na saki ajiyar zuciya Ina murmushi kadan nace


" Mhmmm...Yes!"


Yayi dariya ya fara min bayanin ta da komai sannan yace


" Kinsan ke nake so ko? Please ki cire sunanta a ranki"


Nace


" Anya zan iya? Why did she call you then?"


Ya Kara min bayani sannan nace


" I was very mad at you! Daga yau don't talk to her again"


" I promise you!!"


Ya fada immediately sannan na Masa sallama dukda yaso mu cigaba da magana Amma na nuna haushin shi nakeji.






AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.
[15/02, 23:10] +234 703 364 5886: 56




















Duk wani abu da ake Babu abinda muka san Yana faruwa, rayuwar mu kawai muke not knowing it's a mess down there in Nigeria. Bayan anyi Babu dadi tsakanin Kawu Sa'idu da su Junaidu duk dasu Basu kulashi ba, Dole suka juya zuwa kazaure. Junaidu was more than depressed bayan komawar su gida. Kamar wanda zaiyi karamin hauka Haka yakeji. Ranar Yana zaune gaban Hajja da carbi a hannun shi ya dawo daga dakin Malam Wanda ya daura Masa karatu kamar yadda suke dukkan Rana. Yanzun ya tasar ma watanni uku da dawowa Kan track dinsa. Ya rame yayi Baki, gashin Baki da baya Tarawa da yake askewa yanzun duk sun fito saboda bama shi da nutsuwar zuwa wajen askin. Ta dubeshi tace


" Yarona kaga yadda kake komawa kuwa? Ba zaka sanyawa zuciyar ka salama ba"


Ya aje carbin idanun shi sun Kara kadawa sunyi ja, tamkar ba wannan Junaidun da kowa ya sani ba, gaba daya wannan ya sususuce ya Zama wani iri, a hakan Wai sallah na dawo Masa da nutsuwar shi. yace


" Hajja zanso wani yaji yadda nakeji, kilan da kunmin uzuri, Ina jin zuciyata tayi min nauyi duk abinda nake tunanin ta nake, bana bacci me dadi se Ina ganin lokacin da nake dukanta nake azabtar da ita gashi yanzun Bata nan balle na nema yafiyar ta na Mata tayin soyayya ta!"


Hajja cikeda tausayin Dan nata ta Raya Allah ke sakawa Afiyya ta hanyar darsa Masa sonta cikin zuciyar shi, ta sauke ajiyar zuciya tace


" Babu Kuma Wanda ka sani nata? Amma ance tanada Kawu a Kano ko?"


Se lokacin ya tuna tabbas tana da Kawu a Kano shi ne Wanda Kawu Sa'idu ke yawan cewa dolo ne da ace shi ke da dukiyar Afiyya da tuni an Gama zancen Amma da yake hannun Uncle Babawo take shiyasa suka kasa banbara. Cikin sauri ya fara tuanain yadda zaiyi ya samu address din Kawu Tijjani Bai kuwa wani Sha wahala ba ya samu. Washegari suka nufi Kano bayan Hajja ta saka jamilu ya raka shi yayi aski, ta sashi a gaba ya shirya ya Dan dawo hayyacin shi sannan Suka tasarma gidan Kawu Tijjani. Lokacin da Suka Isa ya fito Dan rakiyar bako, da yake bashida zafi ko kadan yasa ya tarbe su har cikin parlor ga Kuma daraja da kimar Malam da ya gani. Bayan sun gaisa an jajanta abubuwa se Kuma Malam ya fada Masa abinda ya kawo su. Kawu Tijjani ya kalli Junaidu Wanda yayi kasa da kanshi sosae mamaki ya Kama shi lallai Allah shi ke shiryawa gashi nan shekara da wasu watanni ko Kai waye baka Isa Junaidu ya sauke Kan Shi ba Dan Kuna magana sede ya zuba idanun shi cikin naka Amma abin mamaki yanzun shi ne yake kasa da Kai alamar Jin nauyi.


" Ni da kake gani banida ikon yanke hukunci akan Afiyya, Babawo shi ne babanta shi muka bawa dukkan dama a kanta, balle Afiyya yanzun ko zatayi Aure musulinci ya Bata damar zabar mijinta da kanta tunda ba auren farko bane. Ina saka ran zasu dawo karshen wani watan se kayi kokarin daidaita kanka kaje ka Nemo yafiyar ta, zancen aurenta Wanda kukaga ya fita yanzun shi ma Neman aurenta yazo Dan Haka lissafi ya rage naka"


Ko Babu komai maganar da Kawu ya Masa cikin tattausan lafazi yasa ya danji hankalin shi ya kwanta sede Kuma ya fara jin tsoro saboda yasan indai Afiyya ce zata zabi mijin ta ba zata taba zaben shi ba Haka wannan kawun nata me masifar bin diddigi, dama Yana ta adduar ba hannun shi take ba Amma adduar shi Bata ci ba.






Na Gama exams har munyi hutun sati uku Wanda sati biyu a NY nayi shi, naje na tarar Rooks tayi kiba ta Zama babbar mace kamar Amina Abubakar Rogo, ni ce dai Yar firit a cikin su. Wannan sati biyun da nayi na Yi shi cikin farin ciki da Jin Dadi, na dawo gida Dan daura sabuwar semester. Tsakanina da Yaya Shehu soyayya me karfi kullum ke Kara shiga tsakanin mu, shi din aboki nane, shi din masoyi name Wanda nake jin son shi a dukkan sassan jikina, wani lokacin na Kan auna wani Abu ya raba ni dashi nakan ji hankali na ya tashi iya ayyanawa da nayi. Shi din Rabin jikina ne Wanda na samu solace a tare dashi. Shi din wani bangare ne na rayuwa ta Wanda bazan iya ba se dashi,ban taba jin son Abu kamar yadda nake son shi ba, how I wish Abbuna da Mama ta suna raye suga namiji guda daya ya tsaya min a rayuwa. Ni dashi cikin aminci muke soyayya min riga min fahimci junan mu so deep,nakan Yi mamakin a lokaci kankani yadda ya fahimce ni Nima na fahimce shi har Haka. No matter what, duk abinda ya faru zamuyi magana Koda chat ne bana tunanin akwai watarana da tazo ta tsallake bamui magana dashi ba Wanda ya assassa Kara shakuwar mu dashi. Bangarena da Yaya Hasher ya daina kulani wani lokacin na Kan duba last seen dinsa and idan Naga Yana online Bai kulani ba se naji Babu dadi, ko Babu komai ya nuna min kulawa lokacin da nake bukatar hakan, wani lokacin se na aje pride Dina na Masa magana but yadda yake replying Dina ke Bata min rai se na tattara shi na watsar dashi Nima, I know ni ban yaudare shi why will I be accounting for zargin da yake min.




Wani yammaci min kammalla abincin dare na dawo daki Dan returning call din Yaya Shehu, ya kirani nayi picking nace Masa Zan Kira shi I was a bit busy ne. Dakin nawa wajen study table Dina duka a hargitse saboda exams da nake, karatu nake ba na Wasa ba. Na zauna na fara Kiran shi se ya kashe ya kirani yace na kunna data muyi video call . Na kalla kaina I was clad in skirt da riga na atamfa, ta wajen hips din ya kamani soosae Wanda ya tabbatar min na fara kiba Nima, Amma saboda yadda nake son kayan yasa naki cirewa, veil nayi draping saman kafadata ya lullube duk inda ya kamata sannan na kunna data Wanda immediately Kiran shi ya shigo, Yana zaune a office he looks tired, nayi murmushi nace


" Somebody is tired!"


Ya shafa Kan shi yace


" Extremely Baby! Ya exams din?'


Na haska Masa study table Dina Ina jin shi Yana dariya kafin na dawo da wayar inda nake, muka Dan taba Hira se na Mike na fara tattara books din, se kawai naji yace


" Mashaaa Allah! Damsel kiba kikeyi, kin sani?"


Nayi saurin Jan veil din Dan ya rufe min hips dina Ina pouting se yayi dariya tareda lumshe idanu yace


" I'm sorry zamuyi magana da daddare ko?"


Na gyada kaina har lokacin kunyar yaga abinda nake ta boyewa nake shi Kuma ya Mike ya tattare kayan shi ya tafi. Muna zaune muna cin abinci wayata Dake cikin pocket Dina ta fara ringing, nayi saurin hadiyewa na Ciro wayar se Naga Kawu Tijjani ne, na Kora apple juice din dake cikin tumbler sannan na Kara wayar a kunnena cikeda farin ciki yace


" Daughter ta"


"Abiey! Ina Basma"


" She's here, Ina Dad dinki?"


Na kalla Dad da ya meda hankalin shi Kan broccoli salad din da yake ci nace


" He's here"


Se da muka gaisa yace na bawa Dad ya kira shi Bai sameshi ba, na Mika Masa wayar Ina fada Masa Kawu Tijjani ne.


" Man! Wallahi wayar na daki I'm having dinner ne"


" You want to talk to me! Ok..."


Daga Haka ya Mike ya nufi bedroom dinsu ni Kuma na maida hankalina wajen cin abinci.










AFIYYA is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 09063467258.57




Har muka gama cin abinci Babu alamar fitowar Dad, ni Kuma naki tafiya saboda I was waiting for my phone, na tabbatar Honey will call. Nayi shiru Ina kallon TV Amma ko kadan bani comprehending abinda ake Yi balle abinda ake fada. Itakam da Nanny Banda hirar su Babu abinda suke yi, can na Mike na nufi daki na dakko system dinta Dan washegari inada mental health exams da Rana, na saka slides din a gabana na kura idanu, yawancin ban Faye son course din ba especially Schiz dinnan dukda Yana da sauki Amma wannan positive and negative symptoms ke Dan confusing dina, mum ta dubeni Lokacin I was going through OCD tace


" Karar TV Bai damun ki ne? Ki tafi daki indai karatu kike so kiyi"


Na Dan Yi pouting nace


" Wayana a gurin Dad"


Nanny tace


" Nayi mamakin abinda ya zaunar dake Ashe shalele ce hannun Alhaji"


Duk lokacin da tace Alhaji se Abbu ya fado min , na murza hannuna a idanuna Ina fadin Allah ya jikanka Abbuna I so much missed you! Mum ta mike Babu jimawa se gata da wayata ta Mika min na amsa da sauri tareda duba call log dina, na saki ajiyar zuciya ganin Bai Kira ba, na tattara system Dina na wuce dakina. Ban Dade Ina karatu ba bacci yayi gaba Dani. Washegari I woke up to calls dinsa da nayi missing, Ina kuwa idar da sallah na Kira shi Bai dauka ba se kawai na cigaba da sabgar gabana. Na fito na samu Babu kowa a parlon se na wuce kitchen Dan duk tuanani na Basu tashi ba, Ina shiga kitchen na hada tea na fara Sha sannan na fara hada brown yam da tuna sauce, ba jimawa na Gama na fito se Naga Nanny, Mom da Dad sun fito a tare daga dakin Nanny, Mom fuskarta ta nuna alamar tashin hankali Dake ita Haka take Bata iya boye damuwa a tattare da ita, Nanny Kuma tana kallona with my sympathy a idanunta. I was like irin eh! Meye Haka? What are these people doing together this early morning? Na cigaba da kallon su har suka karaso parlon kafin na Dan tattaro courage na gaishe su Dad ya fara amsawa sannan sauran biyun. Na juya na hado komai na karyawa sannan na dawo parlon. Mum na min murmushi ni Kam duk jikina yayi sanyi, what's happening? Dole akwai wani Abu da zaisa da sassafe su kafa meeting kamar wasu UN. Na dai zauna Ina yake Dad ya dubeni yace


" When are you writing your last exams for this semester?'


Na aje cup din hannuna nace


" Yau ne!"


Ya gyada Kai tareda fadin


" Se ku Zama cikin shiri we will be flying back to Nigeria cikin satinnan. Ai hutun ki da yawa ko?"


Na gyada Kai tareda bawa Mom questioning look se ta dauke kanta daga kallona ta mayar Kan abinci, a take naji abincin ya fita daga raina, naji ko kadan bazan iya cin komai ba, na karasa shanye tea Dina lokacin takwas da rabi na wuce daki nayi wanka se school Kuma har lokacin shima Bai kirani ba. Na jima da wayar a hannuna Ina tunanin what kept him this long baiyi returning call ba se gashi ya kira, na Dan Bata fuska kamar Yana gabana sannan na dauka nace


" Nayi fushi"


" I'm sorry Damsel! Was a bit busy. How have you been?"


Na Dan yatsina fuska Dan na haddace wannan gaisuwar tamu nace


" I'm fine alhamdulillah! Na Gama exams!"


Yayi Dan karamin squealing na Taya ni murna sannan yayi min addu'oin nasara yace na tafi gida idan na Isa na kirashi zamuyi magana. Hakan kuwa nayi Ina kashewa nayi sallama dasu Janet da Maryam na nufi gida, dukda sun so muyi pictures naki nace musu sauri nakeyi. Ina Isa gida tun a Hanya na hanga Nanny tana Shiga gida, ta fita strolling na ayyana a raina, bayan na shiga gida na tarar Babu kowa a parlon, mamaki ya Kama ni ganin ko minti biyu cikakke baiyi da Naga shigarta gida, na cire veil din na Yar Kan sofa sannan na bishi na danne tareda lumshe idanuna Ina jin wani ease a jikina, se kawai naji muryar Mom na fadin


" Surprise Afiyya!"


Nayi saurin bude idanuna a take na hango cake anyi frosting dinsa, yayi kyau Ina tunanin 8 inches cake ne. Nayi saurin mikewa bakina wide into a wide grin nace


" Mom"


Ta shafa kaina tare da fadin


" Happy birthday! I wish all the beauties of life!"


Na rungume ta Bayan ta aje cake din se lokacin na lura da pastries din da aka jera a dining, har Raina na manta da wani birthday dina yau, na sauke ajiyar zuciya na wuce daki bisa umarnin na canja Kaya. Nan na samu gift Akan gado, na Dan daddaga Amma Kuma ban bude ba nayi changing zuwa wata flowing gown da tayi min kyau, na hada kaina in a ponytail sannan na dakko hair band na saka kalar gown din tareda makala 10 inches pointed high heels. Powder na shafa hade da khol sannan na feshe jikina da turare na fito, Nanny ta fara rungume ni, tareda riko hannuna tace


" Kamar yau ne aka haifeki, na tuna an aiko Mana Lagos cewar Waziri baya da lafiya shi ne abinda yasa mamanki ta Shiga labor da baa shirya ba. Gashi yau har kin cika Sha bakwai! Allah ya raya ki"




N rungume ta Ina Dan goge hawayen dake barazanar Bata min fuska nace


" Nagode sosae Nanny, nagode da Kika tsaya cikin rayuwata! Allah ya jikan Mama da Abbu"


Ta sharen hawayena tareda fada min nayi farin ciki. I was so happy da Ina yanka cake din, Mum tasa maid dinmu tayi videos da hotuna, can Naga Mom taje amsa call ba jimawa ta dawo tace na saka dankwali akaina zatayi Baki, Haka na saka karamin veil na yafa a take na Kara yin kyau, ga mamakina se kawai Jin sallamar Honey nayi, na Mike daga zaunen da nake cikin sauri na nufe ahi, kunsan Allah Banda ya kauce wallahi da rungume shi zanyi, baa taba min surprise me dadi irin wannan ba, na kalleshi yayi kyau cikin maroon din long sleeve top Amma Kuma ya nade hannun sama se Kuma wandon pale blue ne. Yayi kyau da wannan Charming smile din nashi, na tsaya se Kuma na Bata Rai na juya Ina kallon Mom Dake kallona with so much amusement a idanunta nasan tana weighing kaunar da mukewa juna ne. Na tsaya gefen ta Ina tura Baki nace


" Kinsan yazo ko?"


Tayi dariya tace


" He wanted surprising you!"


A waje inda wasu wooden chairs suke muka zauna, se kallona yake Yana murmushi yayinda na hade fuska Amma Kuma cikin zuciyata ji nake kamar nayi ihu na Kuma Yi rawa. He told me tun jiya ya taho Dan kawai ya kasance Dani a Rana ta Mai muhimmanci, ban ma Kara fushin ba na hakura da yamma muka fita yawo na manta da duk wata damuwa da matsala, shi kadai nake gani a duniya, Kai duniyar ma ji nake kamar daga ni se shi muka rage.












Afiyya is not free, pay 300 to 3091721807 Aisha Hassan kwalam First bank of Nigeria and send evidence of payment to 0906346725858






Bamu dawo gida ba se yamma Dan Muna shigowa ko Zama bamuyi ba aka fara Kiran sallah, na wuce daki nayi alwala nai sallah na zauna bare gift dina, na Dad da Mom da Nanny se Kuma nashi, kowanne content din yayi min kyau ba ma kamar nashi. Na Adana komai sannan na fito Jin Nanny na Kirana, na rungume ta Ina Mata adduar kyautar da tayi min, tace Mom Dina ke Kirana. Tana Kitchen na sameta tayi packaging slice cake da sauran finger foods tace na dauka na kaiwa su Sheriffa tunda ban

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login