Showing 27001 words to 30000 words out of 98220 words

Chapter 10 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt

sannan kice in sai maki waya da kuɗi na? Maha yaushe zaki girma ne?. Tace "Ummeyh kiyi haquri bazan sake ba." Good inkin so ki sake kuma in yamaki in kinje can en ma kiyi ta masu rashin ji, kinji wallahi tsab ina zuwa xan shirya na maida ke Adamawa wajan su Ardo ku fama dan shi ne dai-dai ke. Ido cike da hawaye Maha tace "Ummeyh kiyafemun kiyi haquri Allah zan dinga ji, kawai uhmm sai tayi shiru bata qarisa ba." A'a qarasa inajinki kawai me? Announcement da akeyi na kowa ya samu wajan zamansa ne ya tsayar da maganan nasu, suka jaa trolly nasu suna ɗagawa mahaifiyar tasu hanu. Allah tsare hanya tace masu tana qara jaddada masu su nistu suji magana, bayan sun shige jirgin motor ta koma ta shige amma bata tafi ba sanda taga ɗagawan jirgin su Mahreen ɗin. Lumshe ido tayi tana "zanyi kewanku yaran albarkan Allah tsaremun ku ya kare ku Ameen ya Rabbi". Ta tada motor tabar airport en.
Zaune suke a cikin jirgin Maha ce kusa da window Mahreen a gefen ta. Yaya Mahreen kiga Ummeyh taqi sayamun waya fa. Mahreen tace "ke ɗince bakya ji ko kaɗan Maha, amma karki damu in muka isa muka yi waya da Abbeyh sai ki faɗa masa ko."Caɓ lallai ma yaya Mahreen Abbeyh kam zai ce yaushe ya sayamun wacce ta ɓacin kuma kinsan Abbeyh da faɗa gwanda dai na lallaɓa Ummeyh. "Allah shiryaki Maha, sai kiyi haquri har ki daina rashin ji Ummeyh zata sai maki" inji Mahreen. Maha tace "yaya Mahreen nikam fa ba zani Adamawa ba yaya mus'ab mugunta, dan gwanda ya habeebu Ni ke stokanan sa". Zakiji dashi kuma zuwa Adamawa dole Ni dai inason ganin Arɗo dan haka zani Adamawa, kema in dai Ummeyh tazo kinsan dolen ki kije. Maha tace "yaya Mahreen ai Arɗo dan yaga sunan matar sa gareki shiyasa ke yake raga maki, Nima da mijin Kakus na nan nasan ni zai fi so tunda nice mai sunan matar sa." Murmusawa Mahreen tayi!! Qanwata Maha rigima...
Driving Ummeyh take har ta iso haɗaɗɗen gidan nasu, horn tayi mai gadin yazo ya leqa ganin ita ce da wuri ya buɗe gate en. Shigowa da motorn tayi, rufe gate en mai gadin yayi yabi motorn da gudu yana Hajiya sannu da dawowa ayi haquri na zaga ne. Murmusawa tayi ba komi malam idi, ta faɗa ta shige cikin gidan. Komawa wajan zaman sa yayi ya zauna yana magana shi kaɗai "gaskiya wannan matan ta huta duniya da lahira ba ruwanta da masifa yaran ta haka, Alhaji ne kawai yake taɓa wa Allah Alhamdulillahi wasu kuɗi bai rufe masu ido ba, Allah sa ku gama da duniya lafiya Allah bawa yaranki mazaje na gari."
Ko da ta shige palourn nasu ganin gidan tayi ya mata girma, tun yanzu ta fara jin kewan ƴaƴan nata gashi ɗan Autan nata yana makaranta bai dawo ba da tabbas dashi za'a yi wannan tafiya dan rigiman sa. Ajiye mayafin nata tayi da handbag nata ta zauna a ɗaya daga cikin manya manyan kujerun da ke babban palourn nasu. Waya ta ciro a jaka tai dialing number, kashewa akayi ko da qiran ya shiga. Ganin an kashe Murmusawa tayi Abeeyh rigima har gobe bazaka dinga ɗaukan qira na ba sai dai a kashe a qirani, bata gama idasa tunanin da take ba call en nasa ya shigo da murmushi ta ɗauka ta sa a kunnen ta. "Assalamualaikum wa Rahmatullahi wa Barkatuhu ranka ya daɗe ɗan fulani"ta faɗa fuskanta shumfiɗe da qayataccen murmushi mai taɓa ran duk mai kallo da saurara!! Bayan ta saurari amsar da aka bata a ɗayan ɓangaren cewa tayi "Abeeyh gani a gida kam ni ɗaya ba kai ba yara gidan har storo yake ban, saurara wa tayi tana sauraron abinda ake faɗi a ɗaya ɓangaren, sa wayan tai a handsfree ta ajiye a hanun kujeran da take zaune kai tana warware ɗan kwalin kanta. "Hajiya ta da girmanki gida ya baki storo Autan naki bai dawo bane?" Faɗin Abeeyh. Abeeyh ina Auta ya dawo da na gansa ai da sauqi, kuma ma wanne girma ne garen? Murmusawa akayi a ɗaya ɓangaren yace "Tom Hajiya ta a samu a huta ko we'll talk later". Tom ranka ya daɗe mijin Hajiya sai naji ka ko Allah taimaka ayi aiki lafiya, Abbeyh yace a ɗayan ɓangaren "au wai mijin Hajiya ko hhhh wata ta jiyoki ki kasheman kasuwa afasa aurena ni da ke ne." Byee ranka ya daɗe mijin mata huɗu, ta faɗa ta kaste wayan tana dariya! Miqewa tayi ta shige bedroom.
Bayan ta shige bedroom toilet direct ta wuce ta wasta ruwa ta fito. Zaunawa tayi bakin dressing mirrow ta janyo wayanta tayi dialing layin da akayi saving da habeebi Auta akai, sanya wayan tayi a handsfree ta ɗaura akan mirrow desk en jin layin na tafiya. "Hello Ummeyh ta" abinda aka faɗa a wayan wanda ke nuni da wanda ta qira ya ɗauka. Habeebin Ummeyhn da ya akayi? Ya kuke? Ya gida ya gajiyanka? Shagwaɓe fuska yayi kaman yana gabanta "Ummeyh ta kowa lafiya sai nine ban da laafiyah". Da yanayin damuwa tace "Habeebee me ya sameka?" Cewa yayi a ɗaya ɓangaren "Ummeyh gajiya kuma inaso na ganki" ajiyan zuciya ta sauqe! ta ɗan murmusa habeebin Ummeyh soon Ina zuwa ko tunda kaikam kaqi biyowa kawuce gida direct abun ka, yanzu ma qannen ka suna hanya duk inda suke insha Allahu nasan jirgin su ya kusa landing ka qoqarta ka ɗauko su ba dan halin su ba. Shikkenan Ummeyh ta Allah iso dasu lafiya kema yaushe zaki zo? Habeebin Ummeyh surprise zan maku amma nakusa kaji, yace "Tom Allah kaimu ya kawoki kema lafiya Ummeyh ba na tashi na shirya kamun su iso byeee Ummeyh ta" ya kashe wayan. Cigaba da shafa mai Ummeyh tayi ta tashi ta saka dogon riga dai-dai mara nauyi tabi lafiyan gado ta kwanta cike da kewan yaran nata da kuma mijin nata....


---------
A Nigeria kuwa bayan soja ya gama waya da Ummeyh har zai bi gado ya kwanta sai ya tuna ba marar kunyan bace kaɗai zatazo har da mutumiyar sa Mahreen. Dira yayi a kan gadon ya shige toilet, a gaggauce ya wasta ruwa ya fito ɗaure da towel ɗaya ɗayan kuwa yana qoge suman kan sa. Shiryawa yayi cikin qananun kaya army t-shirt da jeans, fesa turare yayi. Sanda ya qarewa kansa kallo a mirrow kamun ya fice a ɗakin ya ja qofan side nasa ya kulle kamun ya qaraso cikin main palourn nasu, bai tarar da kowa ba a palourn shiru har ya juya zai fice yaji muryan mai aikin nasu na cewa "adawo lafiya Autan Umma" amsawa yayi har zai wuce da ya tuna dai ba marar kunyan bace kaɗai kar su iso ba abun ci sai ya juya ya mata magana "yauwá mama nace ba a ɗan tanada abinci mana Umma nada baqi daga jidda, mai aikin tace "ba dai su mai sunan amarya ba?" Eh mama sune amma kar afaɗawa Umma in ta tambayi ko Kinga fitana kice mata eh naje anguwa. Shikkenan Autan Umma adawo lafiya Insha Allahu zan tanadar masu dan mai sunan Amarya mutumiya ta ce, taɓe baki yayi yace "shikkenan sai mun dawo" ya faɗa yana ficewa a palourn.
A tsakar gidan ya hangi Little na ball da wani soja, har ya juya zai yi hanyan parking lot sai yaji muryan Little en "unkui where are you going?" Big bruh anguwa zani kayi ball naka okay. Da gudu ya bar Ball en yazo ya riqe qafan sa yace "nidai a'a unkui anbika anguwa anfaca baii en". Murmushi soja yayi yace "shikkenan let's go bruh" wajan motor suka wuce suka shiga, key yawa motorn mai gadi ya walgale gate en da gudu yafice a gidan suka yi hanyan KADUNA STATE AIRPORT.
Isar su airport yayi dai-dai da lokacin da jirgin da ya taso daga jidda yayi landing, bayan wasu mintuna mutanen da ke jirgin ne suka fara futowa. Yana zaune daga cikin motorn Yana kallon mutanen dake fitowa a jirgin carabb idonsa ya sauqa a kanta tana sauqowa a jirgin, gyalen rigan jikinta iska ya ɗauke wanda hakan ya bawa gashin kanta kwantacce dogo baqi daman bayyana, siririn tsaki yaja ya fito a motorn yana faɗin "yarinya sai rawan kai". Hango mutumiyar sa da rolling tana sauqowa a nuste ya sanya shi ɗan murmusa wa! Idonsu ne ya haɗu bayan ta ɗauko gyalen nata ta qara yafawa da murmushi ta yo wajansa tana qoqarin rungumesa ya dakatar da ita "ke malama tsaya, bayan kingama tallata wa duniya cinyayyen kan naki ne kikeso kuma ki taɓani ace wai Nima banda hankali irin ke? Tom ki nistu, tunda ke ko a cikin jama'a sai kin raba halinki."
Murguɗa baki tayi ta kuma yin qwafa, da alama ranta bai yi daɗi ba! kai kuma ba'a maka gwaninta.
Wucewa tayi Inda yai parking motor ta buɗe gidan gaba ta shiga.
Mahar ce ta qaraso da murmushi! Afuwan mun sanya ya soja jiranmu, kallon ta yayi Au kema sojan zakice ko? murmusawa tayi tana kama kunne noo ya habeeby. Wajan Motorn suka nufa, Hajiya Maha na ankame a gaba haka Mahreen ta buɗe back seat ta shige shikuma ya shiga mazaunin driver yaja Motorn suka nufi hanyan gida. Mahreen da ke zaune a baya ce tace "ya habeeby ɗan wa ka samo? Kyakkyawa kaman ni haka". Dariya Maha da ke gaban Motor ta sanya, wai yanzu har zaki ce kyakkyawa kaman ke yaya Mahreen kyau ne dake? Kallon da habeeb ya aika mata dashi shi ya hanata qarisa sauran maganan ta juyar da kai tana magana qasa-qasa.. Mahreen ce tace "ya habeeby ɗan waye?" Yanzu zakiceman baki gane Little ba Reeyhn? Zaro ido Mahreen tayi tana ɗaga Little da ke shan baccin sa cikin kwanciyar hankali tace "don't tell me yaron Adda Ameera ne wannan ya habeeby?" so now anyi mumyn zamani tunda dai baki gane ɗan ki ba. "A'a fa ya habeeby kasan dai rabon mu da Nigeria tun Auren Adda Ameera bamuzo ba da ta haihu a waya kawai nake kallon sa, yanzu dai wannan kyakkyawan saurayin yaronmu ne wow ya habeeby soon zamu zama surukai" Mahreen tafaɗa tana murmushi ganin Little ya buɗe ido. Little ne yace "unkui my head" kwantar da shi Mahreen tayi a jikinta sai yaqi yasa kuka ya miqawa unkui habeeb hanu, big bruh Ina driving ne zaka zauna jikina what's wrong with you? Juyowa Maha tayi ta miqa masa hannu tana murmushi, ba ko gardama ya yarda ta ɗauke sa, lallashin sa tayi yai shiru ya qanqame ta kaman itace maman sa. Kallon su habeeb yayi yace "hali yazo ɗaya dole aso juna ai" Maha murguɗa baki tayi batace komai ba, motorn shiru ba qaran komai sai na AC dake tashi.
Suna isa gida Maha ko tsayawa a gyara parking batayi ba, little en ma ko tsayawa ɗaukan sa batayi ba da gudu tayi cikin gidan tana "ayoyo ummata ayoyo ummata ayoyoo ummata".
Kaman daga sama haka umma taji muryan Maha, aikam Mahan ce dan tana shigowa palourn jikin Umma ta faɗa. "Ikon Allah ashe kuna hanya doter, ayoyo sannun ku gajiya ko" ta faɗa tana rungume Maha. Maha tace "Umma i miss you wallahi" miss you more doter yanzu kam ba gaki ga Umman ki ba ƴar kirki. shigowan soja da Mahreen ne da Little da ke kukan Maha ta tafi ta barsa ya sa Umma ɗago kai tana washe baki tace "Lale marhabun da yaran kirki" Mahreen tazo ta rungume umman tasu itama. Maha jawo little tayi ta lallaɓa sa tayi shiru, Kallon habeeb Umma tayi "wai dama Auta kasan ƴaran nan na hanya baka faɗa mun ba Gwaggon ku ma bata sanar da ni ba, na tambayi mama wai kace mata kaje anguwa, yanzu kai zaka nemo masu abinda zasuci a take kamun adafa ko?" sosa qeya yayi Umma nima fa bansan suna hanya ba kuma ai mama ta dafa masu abinci.
Mama mai aiki ce ta shigo palourn da sallama riqe da tire a hanunta mai ɗauke da abun sha da kulolin abinci, kallon ta Umma tayi "wai mama kinsan da zuwan su ne kema tunda naga har da abinci" murmushi mama tayi tace "Hajiya ai mana afuwa ni da soja fitan sa nagani yace zaije ɗauko su shine nai sauri haɗawa ƴan ɗakina abin taɓa wa nasan tafiyan hanya akwai sa yunwa" Umma Murmusawa tayi "au wai Ni kawai kuka wa surprise shikkenan ai sannun da aiki mama, Auta sannu da gajiya, yaran Umma sannunku da zuwa sauqo kusha ruwa ko" ta faɗa tana kallon Maha da Mahreen. Sauqo wa suka yi dan shan ruwan, mama ta masu sannu da hanya, da murmushi duka suka amsa barin ma Maha dan mutumiyar mama ce sosai.
Habeeb yace "Umma ba na shiga ciki nikam yau Little yaga mai irin halin sa yaqi ni" Umma ta kallesa zaka fara ko? Tura baki Maha tayi, hararan ta habeeb yayi ya nufa hanyan sashen sa, bin bayan sa Maha tayi da harara. Kallon su duka Umma tayi ta girgiza kai kawai cewa take a ranta "Allah shirya mun ku ya nunan randa zaku zauna lafiya".




---------
Amjad ya koma gida lafiya. Kaman koda yaushe sunci abinci tare da iyayen nasa da fara'a da dariya suna hiran su, inka gansu ba zakace iyaye da ɗan su bane.
(Ba kaman wasu iyayen namu ba a yanzu, in baka ja ɗan ka jiki ba wa zai ja maka? Mu gyara iyaye).
Umma ke stokanan sa "wato jarumin umma don anfara jin qamshin surkata shine aka kwana har biyu ajeji ba'a yi kewan Umma ba ko?" Ɓata fuska yayi yace "Allah Umma nayi kewan ki fa Kuma ni ba wacce zata sa na mance da Umma ta, Nifa Umma zakisa ma nafasa abun nan ma"( dukda aransa yarasa dalili yaji yanason yin gasan dan kansa
Amma yabar hakan wa son sauqe mata girman kan da takeji dashi na ba wanda ya isa yabuɗe mata fuska).
Umma tace "ah ah yi haquri jarumin ummansa baza'a yi haka ba ma kaji. Abba dai yana kallon su yana murmushi amma bai ce komai ba, A haka suka cigaba da hiran dukansu na dariya Amjad ya murmusa!
Dare yayi lokacin kwanciya kaman yacce suka saba kullum haka suka yi har ɗakin sa iyayen nasa suka rakasa Umma ta masa addu'a suka ka masa bargo suka yi sai da safe suka fito suka nufi nasu ɗakin. Bayan sun shiga nasu ɗakin alwala suka ɗauro suka fara nafila da niyan Allah ya bawa yaron nasu nasara in hakan alkhaeryh ne gare sa..
Amjad a ɗakin sa bayan fitan iyayen nasa juyi kawai yake yi ya kasa bacci, shi dai yasan baida damuwa da abunda zasu yi goben, amma yarasa mai yahana sa bacci, ya juya haka ya juya haka har dai ɓarawon bacci ya sace shi.




MASARAUTA
A can gidan Sarki kuwa gimbiya tayi-tayi duk iya yin ta amma ina mai martaba yaqi fahimtar ta ya dage dole aurenta nan da wata 4 huɗu, gashi gobe ne gasan da za'a kuma yi Insha Allahu. Gaba ɗaya ta rasa mai ke mata daɗi, amma duk da haka dai ta saka aranta Insha allahu basu isa suyi galaba a kanta ba




*WASHE GARI RANAR GUDANAR DA GASA**

Babban filin da ya kasance na gudanar da bukukuwan wannan masarauta, a cike yake fam da jama'a. Baqi da ƴan gari sun hallara a wannan babban fili mutane ne a cike ba masaka stinke, ganin yawansu zai sanya ka tsammanin ba kowa da ya rage a wannan Masarauta, saboda irin tarin jama'a dake wannan fili.
Manyan baqi da ya kunshi Sarakunan garuruwan da suke makwaɓtaka, manyan mutane daga qasashe daban daban sun samu daman hallattan wannan gasan kasancewar yacce Sarki ya furta na ko daga ina kake zaka iya shiga gasan sai hakan ya bawa labarin wannan gasan zagayawa har garuruwa da dama wanda ba'a tsammani ciki kuwa har da Nigeria, baqi ta ko ina anzo dan kuwa kusan zuciyoyin kowa cike yake da ɗimbin mamakin qarfi irin na wannan ƳAR SARKI...
Mai martaba kaman ko da yaushe yana wajan da yake tanade dan zamansa tare da fadawan sa in ana gudanar da wani shagali a garin nasa, baqi kowa na zaune inda aka tanadar dan baqi manya da sauransu. Gefe guda kuwa GIMBIYA MEHWISH ne zaune a kujeran da aka tanada domin ita, kuyangun ta ne zagaye da ita da sauran bayi maza.
Sanye take da kaya blue wanda colourn ya tafi da yanayin halittan qwayar idon ta, kayan riga da wando ne, wandon ya kasance mai ɗan faɗi wanda ba'a ganin yanayin jikinta hakama rigan bai kama ta ba sai dai ɗamaran da ta ɗaura a qugun ta wanda ya ɗan bayyanar da shape enta, ta rufe fuskan ta da baqin veil kaman koda yaushe ba abinda kake gani sai qwayan idon ta wanda yakan burge duk wani mai kallon ta. Irin shiga da haɗuwan da Gimbiya tayi da kyawun da wannan shiga ya mata, indai kana Kallonta tom kallonta kaɗai ya isa ya hanaka nasara akanta don haɗuwa kam Masha Allah!!


Gefen waɗanda za'a gwabza dasu kuwa Anwar ne a zaune tare da muqarraban sa, shiri

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login