Showing 69001 words to 72000 words out of 98220 words

da alkairi
Sannan ina addu'an Allah ya sauqeki lafiya ya albarkaci duk abinda zaki haifa
Idon Ameera cike da kwalla ta shafa cikin ta da ya fara fitowa tace "Ameen ya Rabbi yaya AMJAD"
Murmushi Amjad yayi mata
Haka kaman karsu rabu suka yi sallama Ameerah har da yar kwallanta suka baro ta a gida dan Daddyn Little ne ya kaisa har motor pack ya sashi a Motorn Bauchi ya biya kuษ—in motorn sannan ya basa wasu a hanunsa duk da ya nuna a'a
Jakan da tun ran da ya buge sa ya ajiye yaje motor ya ษ—auko ya miqa masa bros ga jakan kayan ka nan sannan ya buษ—e yasa masa kuษ—in a ciki sun riga sunyi exchange na number. Sanda motornsu ya tashi kamun Daddyn Little ya ja nasa Motorn yabar tashan ya wuce wajan aiki
Amjad na zaune cikin Motorn suna tafiya shiru yayi dan ya fara jin kewan mutane masu halaccinnan dan baya tunanin azamanin da muke ciki ana samun mutane haka
Wasuma in sun buge mutum guduwa suke kamun ataru a kansu
"Allah ka datar damu, su kuma Allah saka masu da mafificin alkhaeryh".




Mahreen, Maha da kuma Soja sun dawo gida bayan satan nin da suka yi a bauchi, suka dawo cike da kewan mutan Bauchi da surutun kakar tasu
Umma taji daษ—in ganin yaranta sosai sosai
Inda gefe ษ—aya kuma da Umman da su Mahreen en duka ido suka zuba ganin ikon Allah yaushe Ummeyh kuma zata iso kullum ina hanya na kusa zuwa amma shiru
Mahreen ce in ta tashi qorafinta sai ta tura baki, tace "wa yasan ko jiddahn ya koma bangon duniya ne".
Tsakanin Maha da Little kuwa soyayyace ba kaษ—an ba In ka gansu sai ka ranste itace uwarsa yacce yake maqale mata
Mahreen ke kwance a ษ—akinsu tana aikin da ya same ta na waya
wayanne a maqale a kunnenta sai narkewa take "nide ya Abdoul ka dena bana so
Ta ษ—ayan ษ“angaren ne naji ya Abdoul yace "nifa da gaske nake ba wasa ba zanwa su baba magana am eager to see you as my wife, I seriously need you by my side, Ina kallon wannan kyawawan idanuwanki masu tafiyar da tunanin mai kallonsu"
Lumshe idon tayi
Yace "and 1 thing kinsan me?
Tace "uhm uhmn yayana ban sani ba sai ka faษ—a"
nifa in baki daina cemun yaya ba duk randa na kama bakinki hmmn
Turo bakin tayi kaman yana gabanta nide uhmn
Dariya yayi kaษ—an kede kinji kunya ko tom shikkenan in zaki aje kunya agefe ki aje inba haka ba nifa baza'a qwareni ba bari kiji. I love you Queen
Muahhh! blowing mata kiss yayi ta wayan
saurin cire wayan tayi a kunnenta ta kashe tana murmushi ita dai ta rasa ya Abdoul wani iri ne ko kaษ—an bai jin kunyan ta komi yaga dama faษ—a mata yake
Rumgume fillow tayi inasonkaaa sosai nima yayana.
Maha ce zaune a palourn tana kallo
Litlle ya futo daga ษ—akin soja yana bubbuga qafa yana anci boi na anci boi na (Aunty ball na)
Kallon sa tayi babyna ball naka a ina?
Nuna mata ษ—akin soja yayi a akin unkui Tace mass "Ina uncle en
Kuma tom?
Fara buga qafa yayi unkui ayanan boi na aunci
Dafe kai tayi ba yacce ta iya haka ta tashi ษ—aukansa tayi suka shiga ษ—akin
Wow ษ—akin tuzurun soja kenan komi na dakin white colour ne ษ—akin ya haษ—u iya haษ—uwa ga tafkeken gadon da zai ษ—auki mutum 4, tunda suka shiga sashin take qare ma palourn nasa kallo har suka shiga cikin ษ—akin gaba ษ—aya kaman ba'a Nigeria part nasa yake ba bare ace maka a cikin gidan Abba ka yarda dan ya haษ—u iya haษ—uwa san da ta gama santin sa dan bata taษ“a shiga ba kamun ta wuce yin abinda ya kawo ta
Suna shiga ษ—akin ya sauqe sa shi kuma ya nuna mata qasan gado wai yana ciki ball ษ—in
Sunkuyawa tayi dan ta ษ—auko masa har ta miqa hannu sai taji motsin an buษ—e qofan bayi
Innalillahi wa inna ilaihirraji'un shine abinda ta furta a zuciyanta dan tabbas tasan yau ta gama yawo little ya jaza mata dama wasan ษ“oyel ษ“oyel suke da marar kirkin nan yanzu gashi ta kawo kanta har ษ—akin sa daษ—in ya kashe ta ya ษ“oye wuqan ko ya dakata har tayi laushi ba wanda ya sani bare ta karษ“e ta tama rasa yacce zata yi
shi ko gogan naku ya fito wanka zuciyansa ษ—aya 1 little ne kawai a ษ—akin daga shi sai guntun towel white wanda be kai guiwansa ba faffaษ—an qirjin sa a buษ—e da kwantattun gashin da ruwa ya jiqa su(abinka da soja)
Wajan mirror ya wuce bai ko kalli Little dake tsaye gefen gado kaman mai jiran abu ba, yana share jikinsa kaman ance ya kalli can ai kuwa karaf ta cikin mirrow idonsu ya haษ—e
Saurin rufe ido tayi tana duk addu'an da yazo mata a zuciyanta
shi kuwa haษ—e fuska yayi daga baya kuma yayi murmushin mugunta
Tana nan wajan qasan gadon idonta a rufe a storace take sanda har ta qarisa futowa daga qasan gadon wajen qofa ta nufa da rarrafe wai dan kar ya ganta bata kai ga isa ba taji an riqeta
Juyowa tayi zata kwala ihu
Hanu yasa ya buge mata bakin
Dama wa yasa ki shigomun ษ—aki? renin daki kamun har yakai haka ko
Bata ce ko qala ba ganin dai tana hannu idanuwan ga a rufe dan storo har jikin ta na rawa
Sake ta yayi yana faษ—in "qaramar mara kunya fice mun a ษ—aki kamun nayi ball dake ta yacce ko qashinki baza'a iya ษ—aurawa ba idiot kawai"
Ai kuwa kaman jira take ya sake ta tana hamdala ta fita tana haqi da sauqe ajiyan zuciya yacce ya habeebu ya fusatan nan in yakaiman bugu 1 ai bani ba labarina amma Little ya jamun kwandon bala'ee
Hararan hanyan ษ—akin sa tayi ta shige dakinsu da gudu tana ga kaman zai biyo ta
Little da ya samu Ball nasa dama palourn ya gudu yana yi dan inyayi a ษ—akin unkui zai zana sa
Bayan fitan ta murmushi yayi yaci gaba da abun da yake yi hankalin da kwance ko bai dake ta ba dai yasan ta storita




Motorn su tafiya yake shi kuma da yake zaune a gaban motorn ya zubawa hanya ido, idon shi nakan hanyanne amma tunaninsa gaba daya yana gida Ummansa kawai yake misalta irin yanayin da take ciki gashi baisan taya za'a yi yayi magana dasu ba duk sunqi riqe waya daga ita har Abba
1 month basu yi magana ba bata kallesa ba sai yanzu ma yake jin haushin rashin riqe wayan da Umma da Abba suka yi
Shima kuma dama bawani damunsa wayan yayi ba shi yasa bai matsa masu ba dan bai tava kawowa zai yi irin wannan tafiyan har haka ya jima beji Umman sa ba
Tafiya suke tun da hansti har har sune basu isa bauchi ba sai can tsakiyan dare dan ma Allah ya taimake su driven bai yi zagaye ba kuma an gyara hanya
Sun shigo gari ga dare yayi gashi besan kowa ba
Gaba ษ—aya ya rasa ya zeyi haka de wani bawan Allahn da suka zauna tare dashi a motorn suka wuce gidan sa suka kwana kamun da safe ya nemi abunda ya kawosa bauchi.



Zaune take gaban mai martaba kanta a qasa
Ibnateeyh yanzu kinsan in lissafina dai dai ne to yau saura wata 1da satanni bikin nan ko fatan kina sane?
Don haka za'a fara shirye-shiryen biki da komi sannan zanyi magana da mahaifin yaron
Insha Allahu ni ina ji a jikina ya kusa dawowa ma don haka kema ki fara shiri inaso gaba ษ—aya ki daina fita yanzu kinji ba
"Insha Allahu Papa Allah taimaka" shine kawai abunda tace
ganin kaman bata yanayi me daษ—i sai Mai martaba ya sallameta
Sannan ya aika da ษ—an aike akan a faษ—awa Abban Amjad yana nason ganinsa gobe in Allah ya kaimu


Umman Amjad ce zaune tayi tagumi tasa tuwo a gaba amma bata ko sa hanu ba shigowan Abba kenan daga wajan jin saqon qiran Sarki ya tarar da ita haka
Girgiza kai yayi bece komi ba
Zama yayi kusa da ita MARYAMA ki masa addu'a kinji Inshร  Allah alkhaery ne ya riqe sa kinji
Sai hawaye a idonta sharrrrr ta cire hannu a abincin ma kuka nason qwace mata
Saurin share mata hawayen Abba yayi
Kul Maryama na haneki da mawa ษ—anki kuka kibar zubar masa da hawaye dan hawayen uwa masifa ne akan ษ—an ta ba mutuwa yayi ba tafiya ce kuma Insha Allah yana hanyan dawowa kinji ko mutuwa yayi ma tsakaninki dashi addu'a dan shine soyayyan ki gare sa
Adduah zamu masa yanzun ma kinji a haka ya lallaษ“a ta da qyar ta yarda taci abinci
Nan ya fada mata yacce suka yi da ษ—an saqon mai martaba
Sun kuyar da kai Umma tayi tace "Ni wallahi duk ji nayi ma da ban kawo shawaran ya shiga gasar nan ba tsakani da Allah na fara dana.." ta kasa qarisawa sakamakon kallon da Abba ya jefa mata
Wai ke Maryam mai yake damunki ne kam? Ja kike dashi akan hukuncin da Allah yayi akan ษ—an ki? Kinsan zaki zo duniya? Ko kinsan zaki samu yaron? Mai yasa dan Allah ya qaddara abu akan yaronki kikeson butulce wa Allah ta hanyan nuna baki karษ“i wannan qaddaran ba? Lokacin samun damuwan mu yayi tabbas in dai bazaki gyara kalaman ki ba, ki godewa Allah dan bakisan iya alkhaeryhn da yake cikin wannan qaddara ba ki ษ—auki kanki ki kwatanta a matsayin da Sarauniya take ciki na rashin lafiya shekaru da shekaru in kece zakice haka? Tom inaso ki kasance mai yiwa Allah godiya dan yaronki kaman yanda Allah ya baki kyautan sa tom haka yake kyauta ga al'umman Annabi SAW kisa albarka a komi da ya shafi Amjad in dai kinason ki shirya da mahaliccinki akan kyautan da ya maki
"Kayi haquri Abban sa" shine abinda Umma ta faษ—a tana share fuskan ta
Abba yace "ba ni zaki bawa haquri ba ki nemi yafiyar Ubangiji tun da wuri"
Astagfirullah ya Rabb Allah Alhamdulillahi Allah ka kare mun shi ka basa sa'an abinda yaje nema ka bamu ikon cinye ko wacce qaddara tamu
Yauwa Abban sa nikam ya za'a yi da maganan shirin bikin ne tom kaga fa ya kamata ace iyanzu ankai kayan tambaya da sauran su ya rage kayan Aure da sadaki to su masu sarautane Mu kuma Alhamdulillahi
Murmushi yayi ai tun ษ—azu da wannan magana muke ai da yafi
Amma da kikace Alhmdlh kin gama zance shi wannan kalman yafi komi yanxu dai in Allah ya kaimu zuwa goben naje naji qiran akan mene ko ya ya ake ciki inyaso in na dawo mu kuma sai musan ya za'a yi mai ya kamata ayi ba
Musan ta ina zamu fara amma mudai Allah ya dawo mana da ษ—anmu lafiya shine babba a wajan mu dasu duka
Da "Ameen" Umma ta amsa
ayyah jarumin Ummansa Ummanka na kewan ka nasan kaima duk inda kake kana kewata
Fatam Allah ya tsare mun kai ya haษ—aka da mutane na gari Allah dawar dakai gida lafiya ya nuna mana wannan biki Alfarman fiyayyen halitta SAW.




Muje zuwa fan's โœ๏ธ


ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ



๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐Ÿ˜!!!


# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š
๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ


๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–


(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorl)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค


_______________________________________________________________




๐Ÿ…ฟ๏ธ 51&52



๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


**
๐™ˆ๐™–๐™๐™–
๐™„๐™จ ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™ง๐™–๐™—๐™ž๐™˜ ๐™ฃ๐™–๐™ข๐™š ๐™ฌ๐™๐™ž๐™˜๐™ ๐™ข๐™š๐™–๐™ฃ๐™จ
๐™†๐™ž๐™ฃ๐™™๐™ฃ๐™š๐™จ๐™จ๐™จ & ๐™—๐™š๐™ฃ๐™š๐™ซ๐™ค๐™ก๐™š๐™ฃ๐™ฉ
Maha is a name for ur baby girl's
**










Mahreen ce ta kalleta ganin ta shigo da gudu kuma tana waige sai tace "ke kuma daga ina Maha? Ke da waye wa kika stokano?
Maha tace "sai jero mun tambayoyi kike Ina ruwanki" ta wuce banษ—aki tayo alwala tazo tai Salla
Da ta idar ta ninke darduma ta wuce tayi ษ—akin Umma dan tana ga kaman zai iya biyo ta nan ษ—in ma
Ita dai Mahreen ido ta zuba mata bata kuma cewa komi ba har ta fice a ษ—akin taษ“e baki tayi ta tashi itama ta ษ—auro alwala
Assalamu'alaikum Ummata
Amsawa Umma tayi shigo mana ษ—iyar Umma kuma surkan Ummanta
Turo baki tayi Umma kema xaki fara ko zan koma inda na fito Allah
Murmushi Umma tayi zo ki faษ—amun waya taษ“amun ke Autan Umman ta
Kan gadon Umma ta haye ta kwanta uhmn Umma nazo bacci a ษ—akinki ne
Anya ba laifi kikai wa soja ba kika gudo doter?
Umma nidai bacci nazo yi banyi komi ba kuma ki tambayesa kiji
Tom ayi lafiya Auntan umma
Umma wayanta ta ษ—auka ta qira layin Ameerah ya shiga har ya yanke ba'a ษ—auka ba qara qira tayi haka ba'a ษ—auka ba san da ta qira ana uku kamun aka ษ—auka
Ameerah na ษ—auka tace "afuwan Ummana"
Ina kika aje wayan kika je? Umma na mance wayan a ษ—akine
Tom yayi kyau ya kuke?
muna lafiya Ummanmu
Ya mijinki ya baqonku?
Dukanmu lafiya lah Umma afuwan ban faษ—a maki ba ai jiya ya tafi
Umma da yanayin faษ—a tace "Ameera ya tafi kuma ban gane ya tafi ba?"
Umma yace abu zaije yi a bauchi tom tunda ya warke zai tafi
Ameerah ashe niba uwarki bace da baxaki faษ—amun ba ko Abbanku amma de ya maki kyau daga ke har mijin naki
Umma Kashe wayanta tayi ranta a ษ“ace
Ameerah ce ta qirata ษ—auka tayi tace "Yanzu kuma me kika qira kicemun?
Qasa tayi da murya kiyi haquri Ummata amma akwai phone number ensa a wajan Daddyn little
Shikkenan naji yanzu ina ya tafi? kwashe duk yacce suka yi da yayanta amjad en tayi ta faษ—a ma Umma
Yanzu Ameerah rashin hankalinku da rashin tausayinku yakai haka dama mutum besan kowa ba tunda Allah ya haษ—a ku ta sanadin hatsari ai seku temaka masa shima nan gaba sai kuga da ikon Allah ya temaka maku ko wa wani naku
Baisan kowa a Bauchi ba so kuke yaje yai ta tangariri agarin bauchi ko?
Nagode maku Ameera
Umma kiyi haquri Allah nace ya bari muzo tare yace a'a time nasa kaษ—an ne
shikkenan yayi kyau Allah tsare sa ya basa sa'a
Haquri Ameera ta qara bawa Umma
Umma tace "Bakomi" sallama suka yi ta kashe wayan ta
Numbern Abba ta nemo ta qira
ฦŠauka yayi "assalamualaikum hajiyata ya akayi ya gida"
Yallaษ“oi kasan me yaranka suka yi
A'a sai kin faษ—a maman yarana
Kwashe yacce suka yi da Ameerah tayi ta faษ—a masa
Subhanallahi yanzu shi mijin nata biyewa shirmenta yayi? To shikenan Insha Allah zan qira mijin nata ya turoman numbern yaron in yaso sai na turawa Abdul ya kaisa gida ko ina fatan hakan yayi maki Hajiya ta
Allah qara girma yallaษ“oi hakan yayi sosai ma, Allah shirya mana su sukuma Allah barmun kai
"Ameen hajiyata" Abba ya faษ—a yana murmushi
ฦŠan hiransu suka yi na masoya
Insha Allahu nima nan da kwan 2 zan dawo hajiyata dan nayi kewanki
Amma mai za'a ajiyemun haka aka damu na dawo?
"Kaima dai yallaษ“oi ka sani dolema a tanadar maka abu mai daษ—i koda kaman ruwan roba ne( faro)" Umma ta faษ—a tana dariya
haba dai hajiyata wannan kam kice nai zamana nasha anan kawai sai dai ko acemun yar buduwar matata ta ajeman kanta
Zaka sani jin kunya yallaษ“oi har da jikanne nake budurwa?
a'a nikam a wajena matata ฦดar shawal-shawal take kaman ฦดar 18 years
Dariya tayi yallaษ“oi banda zugi fa kar kasa kai na ya fashe ba jini
Dariya suka sa duka sukai ta hiransu gwanin sha'awa har suka yi sallama.
Itama Umma hawan gadon tayi takwanta gefen Maha da ta jima da yin bacci...










Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login