Showing 78001 words to 81000 words out of 98220 words
Chapter 27 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt
jawo mata qofan ษakin ta rufe ta wuce kitchen Dan haษa mata abinci me sauqi da kanta (me aikinsu tayi tafiya).
AMISCO BEAUTY AND SALOON KD
Mahreen zaune ana wanke mata kai, Mahar kuma qafa ake wanke mata
Mahreen tace "Kinsan me ? Ta faษa tana kai dubanta kan Maha".
nop sai kin faษa
Wallahi haka kawai yau nake jin farinciki and I don't know why?
Taษe baki Maha tayi, yo waya sani ko ya abydoul ne kuka yi waya ko yake son maki surprise.
Murmushi Mahreen tayi, ke dai ba'a yin abin arziiqi dake, waya da ya Abdoul kam ai tun kan mu fito nayi so bana tunanin dalilinshi ne, duk da dai bansan ko surprise en yake son mun ba ni kaman ma nace aiman qunshi wallahi may be ma zuwa zai yi.
Kutt ai Addah kina cewa ai maki qunshi sai dai ki koma ke ษaya nima ni ษaya kowa ya kama hanyansa haka kawai na zauna zaman jira har ayi har ya bushe har a cire caษ ba dai Maha ba.
Hararanta Mahreen tayi tace "to inna uwasu maida wuqar nima bance zanyi ba kaman inyi nace ai"
Dede lokacin aka gamawa Maha wankin qafa, ciro waya tayi a jakan Mahreen, kallonta tayi tace "back to business a ci-gaba d karatu lafiya".
Murmushi tayi, Adda ba zaki fahimci daษin littafin nan ba se kin fara karantawa wallahi dan ya haษu.
Karatunta taci gaba dayi, har aka gamawa Mahreen gyaran kai.
Mai wanke kanne ta kalli Maha tace "Hajiya kizo a wanke maki naki kema mun gama na sisternki" shiru bata jita ba.
Mahreen tace sister ina zataji ki hankalinta na kan novel, Mahreen ta minstineta du Allah je ki a wanke maki kai mu samu muyi gida yunwa nake ji, turo baki Maha tayi Allah zai saka mun banmaki komi ba.
Zaunawa tayi me wanke kan tana dariya qasa-qasa sister plss kamun ku tafi kituramun novel ษin dan nasan zeyi daษi yacce hankalinki duka yake kansa ษinnan, murmushi Maha tayi to zan tura maki.
Amma na littafin wacce marubuciya ce plss?
Maha tace "Kinsan uwar batoorlerh?
No ban gane ta ba gaskiya, amma kaman naji labarin wani book nata MAFARKI NAH ko?
Yauwa dai kekam ashe kin gane ta ita dai sunan littafin nata na yanzu JAHILCI KO AL'ADA?
Mai wanke kan tace "Wowww daga ji littafin zai haษu plss zan baki WhatsApp number na in yayi ki bada a sani a group nata dan a wani group na novels naji ana labarin haษuwan littafin nata na MAFARKI NAH"
Shikkenan karki damu sai mun gama sai ki bani ke kuma ki turamun MAFARKI NAH ษin dan Allah ban qarisa ba.
A haka suna hira tana wanke mata qafan har suka gama, me wanke kan nata yabon gashinta gaskiya sister kuna da kyau ke da sistern ki gashinku yamun kyau kaman larabawa.
Murmushi Maha tayi bata ce komai ba, dan ita aduniya tana son taji ana yabonta ( abunda ke saurin haษata da Soja cewa da yake bata da ko kyau)
Tura mata book en tayi kaman yacce ta buqata suka yi exchanging number, Suka yi mata sallama bayan sun mata transfern kuษinta,kasancewan sanja kuษin da akayi ba a cika samun cash ba, fita suka yi suka shige motor driver ya jasu.
Maha ce tace "driver ka kaimu Rufaidah plaza"
Ok ma'am
Rufaidah plaza ya kaisu, suka shiga suka jido rufaidah ice-cream, rufaidah-bread, rufaidah-chocolate, rufaidah-yoghurt etc.
Bayan Maha ta gama jidan abunda suke buqata ta juya kenan wani bawan Allah ya buge ta, saura kaydan abubuwan hanunta su faษi.
Salati tayi, na shigesu da wani makahon na haษu ni Maha kai jama'a gaskiyan takwaran mutane suna tafiya dai suna layi, qan-qance ido tayi zata yi tijara, sanin halinta Mahreen dake kallon duk abinda ya faru tana qumshe dariyan ta tayi saurin cewa "bawan Allah kayi haquri bata gani bane" ta faษa tana qara riqe dariyan ta.
Murmushi yayi be ce komai ba idonsa na kan Maha dake aika masa da harara tayi qwafa ta juya kan Mahreen tace "Yanzu sabida Allah da Manzon sa Adda ya kama ya bankaษe ni kaman makaho ne shi yayi abu kuma ki basa haquri gaskiya ni ki dinga tafiyar ki daban nayi tawa daban haka kurum" ta faษa tana qara haษe fuska ganin irin kallon da yake mata ji take kaman ta shaqesa.
Wucewa tayi qarshe Mahreen ce ta kai kayan wajan accounter(payment table) suka tsaya aka lissafa komi Mahreen tayi masu transfern kuษin, kasancewan Abba already yasa masu enough kuษi a account nata.
Sa musu akayi a ledan dake ษauke da tambarin plazan, ษaya daga cikin ma'aikatan ya ษauka yace "madam's we can go".
Murmushi Maha tayi, wato dai su anan in ka saya abunsu har motor ake kai maka, abun ya matuqar birgeta ( ita dai har ranta taso girma)
Duk abun nan dake faruwa wannan matashin na kallo ba abinda yake yi sai murmushi dan stiwan yarinyar ya mugun burgesa.
Bayan sun fice an sa masu ledodin su a motor ma'aikacin ya juya ya koma ciki abinsa.
Mahreen har ta shige motor, Maha ta ybude motor zata shige kenan taga wannan saurayin a staye a bayan ta, haษe fuska tayi a ranta tace "wannan mara ganin kuma uban ne yake nema dani ne"
Yawaltaccen Murmushi ne a kwance a kyakkyawan fuskansa, sallama yayi mata yace "ฦณammata in ba laifi ki taimakamun da numbern"
Shigewa Motorn tayi bata ko kallesa ba ta banko murfin tana jan staki.
Mahreen ta sauqe glass en gefen ta tace masa "brother ga numbern nata zan baka" da murmushi ya za gaya site nata basa numbern tayi yace "thank you sister nagode Allah tsare hanya agaida gida"
"Ameen" tace
Maha da haushi ya cika ta kaman ta fashe tace "hey you wa kake da suna will you drive the car or i should come and drive us?"
Da sauri drivern yace sorry ma'am yaja sukai hanyan gida
Mahreen ce ta kalleta tace Allah ya shiryeki Maha wato dai wulaqanci kika sawa kanki ke ba ฦดar kowa ba in baki kula samari ba zama za Kiyi ba Aure? Dubi fa yacce bawan Allahn nan ya haษu ga kuษi ga kyau.
Maha ta tura baki tana hararan gefe "Oho ina ruwanki kuma a kunnen ya Abdoul kin bawa wani gardi layin ki.
" hmmn" Mahreen tace kawai bata qara cewa komai ba har suka isa gida yamma liss.
Suna sauqa a motor soja na fitowa daga cikin gida, Kallonsu yayi bai ce komai ba ya kau da kai, Maha ta taษe baki tace a ranta "kai ka jiyo me baqin hali kawai ko ance ma dole in zamu fita sai mun faษa maka tunda gaka ubanmu oho dai".
Mahreen ce tayi qarfin halin cewa "ya habeeby sorry mun je wanke kai ne fa bayan fitan ka kuma Abba ya sani"
Bai ce komai ba ya wuce yayi waje, su kuma cikin gidan suka shige da sallama dukan su.
Maha na wayyo! Ummata ina kike na gaji washh!
Saurin haษiye sauran maganan dake bakin ta tayi tana zaro ido itama Mahreen zaro idon tayi tana kwalla qara ta mirza ido
Wayyooooo!!!!...
Wannan kenan โ๏ธ
Muhadu a next page fan's
๐๐๐๐๐๐ค๐ค๐ @ justice Hayratou saleehou eyserh
๐๐๐๐ฉ๐จ๐ผ๐ฅ๐ฅ@ 08146292652
๐๐๐๐ฉ๐ฉ๐ฅ๐๐๐ @ourmmahnbatoolerh
๐๐๐ก๐๐๐ง๐๐ข@ 08146292652
๐๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐จ๐๐๐๐ช๐ ๐, ๐๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ ๐๐ง๐๐ฃ๐ฉ๐ ๐ก๐๐ฉ๐ฉ๐๐ฉ๐๐๐๐๐ฃ๐
๐๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐ค๐๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐จ๐๐๐๐ช๐ ๐
Akan ๐๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐ ๐
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐๐ฉ๐ค๐ง๐ฎ ๐ผ๐ฃ๐ ๐๐ง๐๐ฉ๐ฉ๐๐ฃ
๐ฝ๐ฎ
๐๐๐ง๐๐ง๐ ๐จ๐๐ก๐๐๐ช ๐๐จ๐
(๐๐ฌ๐๐ง batoorl)
ุงูููู
ุตูู ู ุณูู
ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู saw๐ค๐ค
_______________________________________________________________
๐
ฟ๏ธ 57&58
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
Dukansu yada ledodin hanunsu suka yi da ihu suna ayoyoooo Ummeyhn mu, da gudu suka je suka faษa jikinta dukansu.
"Wayyoo! Ummeyh na nayi kewan ki" Maha ta faษa idonta na kawo kwallah
Ummeyh ce ta haษe fuska kinga Umman yara kice su tashi mun a jiki bansan su ba kar su karyawa mijina Ni.
Qara qanqameta Maha tayi, Ummeyh Allah ba inda zanje muce munyi kewanki kice mu sake ki, sai ga hawaye sharr-sharrr a idon ta Ummeyh ba kiso kallon mu bama wato, Itama Mahreen idonta ne ya kawo kwalla.
Umman yara kina kallonsu ko baza ki masu magana ba zasu karyani, nikam miqoman wayata na qira habeeby yazo ya ษaga mun wannan shugabar marassa ji ษin.
Me Maha zata yi in ba kuka ba, har da bubbuga qafa tana ta tura baki, Umma ce ta kalleta tace "haba Gwaggon yara ki dubi girman Allah da Manzonsa ki kulamun ษiyata dan ma anyi kewanki"
Murmushi Ummeyh tayi ta buษe hanun ta zo maman abunki Ummeyhn ta, da sauri Maha ta matsa kusa da ita ta shige jikinta sai dukansu ita da Mahreen suka sa kuka Ummeyh sai yau za kizo?
Jan kumatun su tayi farin cikin Ummeyhn su ba dai ganinan ษin nazo ba kuma lafiya har naga ababen qaunata.
Mahreen tace "Ummeyh yaushe kika zo amma?" Ummeyh ta bata amsa ai tun lokacin da kuka fita yawon ku nazo gashi sai yanzu kuke dawowa tun safe har yamma.
Turo baki Maha tayi tace "Ummeyh bafa yawo bane munje wanke kai ne" ta faษa tana cire rolling en da tayi da mayafin abayan da yake jikinta tana nunawa Ummeyh kan ta, dede soja ya shigo palourn yana waya, gashin nata da yasha gyara ya zuba ma ido, shi baima san yayi hakan ba.
Ummeyh na kingani yayi kyau ko?
Murmushi Ummeyh tayi ta sumbaci gomshin ta ,wowww! ibnateeyh o boษi masin.
Turo Baki tayi nifa Ummeyh banson yaren nan gwan da kimun da Hausa ko larabci zan fi ganewa, Ummeyh tace "ai kuwa dan gidanku dole kiso dan kuwa yaren ki ne tunda ubanki gaba da baya bafulatani ne, Turo baki ta kuma yi.
Ummace tace "Auta ta kanki yayi kyau sosai koh ki qyale Ummeyh". Murmushi tayi ta koma jikin Umma tace "yauwรก Umma ta ina sonkiiii.
Stoki kaษan yaja, Ummeyh da ta jiyo stakin ne ta ษaga kai habeeby kaikuma kai da wa? ฦan haษe fuska yayi Ummeyh issuen tafiya turkeyn nanne, tom habeebyn Ummeyh if possible kaje mana cuz you don't have to worry ur self pray for all blessings in the mission, Ummeyh I don't think there's something good there but I will keep on praying kuma ku tayani da addu'a da ni gaskiya ma banson zuwa dan banason qara yin nisa da gida.
Mahreen ce tace "ya habeeby niko da kaban Aron matsayinkan nan dan mugun son zuwa turkeyn nan nake naje naga ko duka garin tolo-tolo suke da kawai" ta faษa tana dariya.
Caษ rabani da ya Abdoul reeyh(Mahreen) me ya kaini?
Zaro ido tayi ta kallesa ta kalli Umma ta kuma kallon Ummeyh da ita kanma bata fahimci abinda suke nufi ba, Tura baki tayi ts tashi tayi ษaki da sauri.
Ummace ta murmusa nasu na manya
Allah ya shiryeka gashi katayar mun da yarinya kai kuma ba'a isa a fada naka ba, sosa kai yayi, Ummeyh tace "ban gane ba kumun bayani"
Ummah tana dariya tace "bakomi fa Gwaggon yara" taษe baki tayi in tayi tsami zanji ai".
Harara soja ya jefawa Maha da tun ษazu hankalinta yake kansa, taษe baki tayi ta ษauke idonta akan sa ,tana magana qasa qasa danma kasamu ana kallonka, Qwafa yayi zamu hadu ne yarinya
"Ummeyh tsarabafa" Maha ta faษa tana kallon mahaifiyar ta, Ikon Allah ikon gaske ni Jamilatu tsaraba tun yanzu? Tom ban kawo ba kuma kona kawo bazan bada ba kiqwata na qarfi ne tunda tun ban huta ba kike tambayan staraba.
"Ayyade Ummeyh nikam in wani abun nayi ki faษamun in baki haquri kaman anshiga tsakaninmu Ummey" ta faษa tana kallon gefen da soja yake
Dariya Umma ta saka dan tana kallon su duka, a ranta cewa take "Allah dai ya shiryamun ku yaran nan ya nuna mun bikinku"
Ba wanda yashiga tsakaninmu sai rashin jinki, kina fara ji zamu shirya
Yanzu dai Ummeyh na gane wato qarya da gaskiya aka kista maki kika yarda wai bana ji, shikkenan Allah zai sakaman ta faษa tana yin hanyan ษakinsu.
Murmushi Ummeyh da Umma suka yi duka suka bita da kallo, Kaikuna kwashe ledodinnan kasa kayakin a fredge kan Abban ku yazo ya gani
Yanzu umma dan Allah dan kawai yarinyar nan ta qara renani ni zan mata aiki, "Zaka tashi ne ko ni natashi na kwashe" Umma ta faษa tana yunqurawa.
Tashuwa yayi yana tura baki gaskiya Umma nikam ki dena sawa ana renani, Ummeyh de tana kallon sa yacce yake tura baki, Umman yara duka yaranki shgwaษaษษu habeeby ma dakansa yana tura baki kaman mace
Dariya Umma tas aka danma ษan ki ne ni babu ruwa na, Tashuwa yayi ya kwashe abubuwan da suka kawo duka yasa a fredge harda bread en.
Dede Maha tashigo ษakin wayan Mahreen ya ษau qaran neman agaji(qira).
Har zata wuce ta cire kayan jikinta da ta tuna kuma tana banษaki ne sai ta ษau wayan ganin ba layin ya Abdoul bane sanda ta bari ya kusa tsinkewa ta ษauka
Tace "Hello tana sallah"
Assalamualaikum ya ke kyakkyawa ma'abociya nistuwa da kuma tarin hankali fatan kin koma gida lafiya?
Cire wayan tayi a kunnenta ikon Allah kaga mutum kaman kurma ance masa tana bayi ya dage sae zuba yake kaman kurna, can tace "Malam ance maka tana sallah ba ita bace qanwarta ce haba" ta faษa tana hararan wayan kaman mai qiran na ganinta.
Murmushi akayi a ษayan ษangaren ta yacce sautin murmushin bai ษuya ba dan sanda taji sound ษin, yace "dama ba ita na qira ba ai Malama ta malam kece nake nema"
Tom wrong number don banyi da kowa ze nemen ba malam kashe waya, Dariya ya ษanyi ya tsaya,s hankali cikin zazzaqar muryansa da kaman ba na miji bane yace "everything about you is special I like the whole you beauty"
Turo Baki tayi kaman tana gaban sa, sai kuma kaman ya sani yace "afuwan lemme explain my self ko Hajiya, Sunana ๐จ๐บ๐ฌ๐ฌ๐ญ ๐ด๐ผ๐ฏ๐จ๐ด๐ด๐จ๐ซ ๐จ๐ฏ๐ด๐จ๐ซ, asalin ษan kano ne ni so aiki ya kawo ni Kaduna da rabon Allah zai haษani da future wife na, nine wanda kika kusa yasarwa a plaza.
Shiru tayi bata ce komai ba, jin tayi shiru sai ya qara murmusawa yace "Am apologizing for what I deed to you cutie, ya kamata na baki haquri beauty cuz is my fault"
Ai jin yace beauty bata san randa tayi murmushi ba shiri ba tace "Bakomi ya wuce handsome makaho"
Ta basa dariya jin yacce ta kuma cewa makaho amma dai yace "Ooh! so that mean you already looked me up and down, though I know am not handsome you are just kidding"
Maha fuskanta da murmushi tace "No I mean it keep joke a side you're handsome"
Murmushi yayi, dan har ransa yaji sunan ya burgesa, to ko zan iya jin sunan malama beauty?
Sunana ๐๐๐๐๐๐ ๐จ๐ฉ๐ผ๐ฉ๐จ๐ฒ๐จ๐น ๐จ๐น๐ซ๐ถ amma ana qirana da ๐๐๐๐.
Wow! very nice name sunanki yayi daษi kaman yacce kike da kyau duk masu suna Maryam daban ne a cikin mata so ke acikin masu suna Maryam ษin ma you're the best, special and unique, ban taษa jin irin nickname na sunanki ba kaman sunan larabawa gaskiya yamun daษi.
Murmushi tayi tace "mu ba larabawa ba amma dai a jiddah muke zaune da parent na, nan Kaduna munzo gidan uncle namu ne.
Wow! kaman fa yacce nace da farko ke ษin ta daban ce, Yanzu dai hope za'a ke ษaukan call na? kuma za'a bani dama nake zuwa kallon wannan kyakkyawan halittar sarauniyar kyawawa?
Lumshe ido tayi, ba damuwa Insha Allah, kamun dai mu koma dan very soon zamu bar maku Nigerian ku.
Dariya taso basa jin wai Nigerian ku sai yace "Noo ai ko kin koma jiddahnku nima zan biki har can, kinsan ance garin masoyi baya nisa, hope am not late ba'a rigani ba?
Rufe idonta tayi da hanunta tana dariya, late like how?
Gyara zaman sa yayi ya qara riqe wayan dan sosai yarinyar ta shiga ransa sai yace "late like I said, kinsan kyakkyawa irin ki ba lallai ace har War haka wani bai sace zuciyan ta ba"
Imahreen ta fito bayi ta