Showing 24001 words to 27000 words out of 98220 words

Chapter 9 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt

yana tafiya bisa dokin sa a wannan dokan daji da baka jin komi sai kukan stunstaye. Mamaki ne cike da ransa na abubuwan da ke faruwa tsakanin shi da wannan dattijon. yanzu ma shi ai a iya sanin sa cikin farinciki yake zaune tare da iyayensa. Amma dai koma me zai yi yacce stohon ya umurce sa da kuma yacce iyayensa zasu umurcesa. Sunyi nisa sosai da tafiya ba abinda yake sai karatun Qur'ani a zuciyar sa tunda stohon can ya masa faɗa ya daina ɗaga murya Insha Allahu...




Umma da Abba ne zau ne suna hira.
Sallaman Amjad suka jiyo tashuwa Umma tayi ayoyo yaron kirki sannu da dawowa ɗan albarka, da murmushi kaman ko yaushe me nuna stantsar qaunan da yake wa Umman da ya qarisa cikin gidan zuwa rumfan da yake ma'ajiyar dokin nasa ya ɗaure ta. Zuwa yayi ya ɗan ranqwafa ya rungume Umman sa uwata Barka da gida nayi kewanki!! Shafa kansa Umma tayi zata yi magana Abba yai Carab yace "ai kullum kai dai cikin kewan matar mutum kake ka kasa yin matar ka tom na kusa shiga tsakanin ka da kewan matata"" dariya Umma ta saka shi kuwa Amjad tura baki yayi. "Abba ya kuma cewa dubesa gardi da shi yana shagwaɓa". Umma ce tace ta isheka fa Abban jarumin Umma daga dawowan sa ko hutawa bai yi ba. Kama hanunsa tayi muje ka watsa ruwa kaji yaro na. Bayan ya watsa ruwa alwala yayi bai tsaya cin abinci ba suka fice dan tafiya masallaci tare da Abban sa.
Suna fita umma ta ɗauro alwala itama tayi sallah ta shimfiɗa masu wajan zaman cin abincin su ta zauna jiran dawowan su.
ayahn sun idar da sallah suka tashi suka yo gida suna tafiya suna hira.
Da sallama suka shigo gidan, amsa masu umma tayi tana masu sannu da dawowa. Sun samu umma ta haɗa komai su kawai take jira.
Dukan su zama suka yi a shumfiɗin da tayi, Amjad ne ya zubawa kowa nasa shima ya zuba nasa, da bismillahi duka suka fara cin abincin. Shiru ba wanda yace komai har san da suka gama ci kusan lokaci ɗaya suka cire hannu Dukansu ukun.
Amjad ne ya tashi ya tattare kwanukan da suka ci abincin Yana "Ummata tun da ɗan ki ya dawo ki huta ba na gyara wajan". Murmushi tayi!! Allah maka albarka jarumin Umma duk macen da ta auri ɗana ta huta duniya da lahira Allah baka ta gari. "Ameen" Abba ya faɗa yana murmusawa!!
Da ya gama tattarawa ya kai madafi dawo wa yayi ya zauna washhh Ummata na gaji. Murmushi tayi sannu Autan Umma, Abba ne yace "ina Auta anan ya zo ya hana sauran zuwa Allah yaye maka lalaci Amjad"
Umma ta kalli Abba suka yi magana da ido, ya jinjina kai, lumshe ido tayi itama ta Jinjina kai en ka mun ta buɗe baki tace " jarumin umma" ya amsa na'am Ummata!!
Murmushi tayi! "yauwa wani Alfarma nake so kamun ko nace wani abu nake so kayi dan Allah kar kace a'a tunda dama nasan kai mai biyayya ne da jin magana Umman sa."
Lumshe ido yayi!! Yacce suka yi da stohon can ne kawai ya faɗo masa a rai. Ummata ko me kike so a duniyan nan inyi in dae raina zse iya yi zan yi Insha Allahu in har bai saɓa wa Allah ba.
Murmushi tayi!! na sani jarumin Umma ba zaka qi ba, Allah maka albarka, wannan kuma ba saɓon Allah ba ne saide ma Allah yaji daɗin abunda zaka yin.
Tom Umma ta ina sauraren ki.
Nan take ta kwashe labarin komai ta basa komin yacce akayi tun ranan farko har jiya yau da aka kammala da kuma abinda ake ciki, ta kuma faɗa masa abinda take so yayi.
A ransa kuwa ba don ya riga da yace wa Umman sa komai zai yi ba da gaskiya zai bata haquri!! Kuma sai yanzu ya fara gane maganan da tsohon can keyi yake kuma nufi.
Kalllon Umman tasa yayi.
Umma ayya dai, yanxu mai za'a cewa wannan abun? auren jari ko auren me?
Umma nifa banson auran wacce zata rena mun iyaye ko ni. dan ba 𝙮𝙖𝙧 𝙨𝙖𝙧𝙠𝙞 take ba ko wace ce zan saɓa mata akan ku.
Murmushi Umma tayi ta qara masa bayani da basa baki, kaga ga yacce Sarki yace kai da kake ɗan gari kuma cikakken jarumi, ko so kake wani daga wata duniyar ko aljani yazo ya karɓe mana gari?
Ni dai ka amince kawai kaji Jarumin Umman sa Sadaukin Umma.
Yace "shikkenan Ummata in hakan zai saku farinciki ke da Abba na amince insha Allahu zan yi kuma zan ci.
Dariya Abba yasa, yana kai masa bugu, Wallahi yaron kin nan ya renamu, yana so yana kaiwa kasuwa fa, dan ma baiga Gimbiya ba har wani batun aure yake tun bai lashe ba halamu dai kafaɗa kogin qaunar Gimbiya, ka kusa yin mata nima tawa matar ta huta da maganan kewan ka ka dinga yin na matar ka.
Turo baki yayi!! Abba zafa kasa na fasa kuma ba wacce ta isa ta haɗa kanta da Umma ta kewan Ummata sai na mutu zan daina ina qaunanki Umma ta!!
Umma ce ta murmusa tace a'a jarumin Umma kar ka fasa ka ji kayi haquri koh jarumin Ummansa.
Abban sa kai kuma ka fita a maganan mu ba ruwan ka da yarona.
Murmushi Abba yayi!! da alama dai shima yaji daɗin amince wan da yaron nasu yayi.
( sun riga sun tattauna kuma basu da shakkah a jarumtan yaronsu da kuma abunda zai iya yi)




^^^Gimbiya tasha bacci ta tashi in da tayi mafarkin, daya mata daɗi amma ta shiga ruɗani. wani murya ke ce mata, ki dai na damuwa insha Allahu mahaifiyar ki ta kusa warkewa, tana gab da samun sauqi bayan dogon jinya na kusan shekaru fun 15
Duk da mafarkin ya ruɗa ta amma taji daɗin mafarkin addu'a tayi ta tashi ta ɗauro alwala a dakin tayi sallah.
Tana zaune a sallaya mai martaba ya shigo ɗakin da sallama, amsawa tayi kanta a qasa ta gaida sa ya amsa fuskan sa a sake. Ibnateeyh kinji hukuncin da na yanke?
Tace eh naji Papa Allah ya san ya haka ne alkhaeryh.
Yace Ameen Allah ya maki albarka,
Kaman yacce kika tsara tun farko, nima nace wanda yayi nasaran buɗe fuskan ki kaman yacce kika buqata, ko akwai wani sharaɗin?
Sauqe kai qasa tayi Papa... Uhmm Daga baya za'ayi. Mai martaba yace menene?
Tace dama Papa tun da, dai ba cutan da baida magani ina so, ya zamana wannan wanda zai lashe gasar ya nemowa Ammaah ta magani kamun bikin. Kanta a qasa tai maganan.
Mai martaba bai ce komi ba, can ya nisa yace "na amince Amma kisani tabbas aurenki nan da wata 5 duk wanda ya buɗe fuskanki ya nemo ko bai nemo ba. Kuma ba ƴaƴan sarakuna bane wannan karon kowa da kowa ɗan talaka, ɗan gari, ba ɗan gari ba duka. Ina maki fatan dacewa da miji na gari Allah maki albarka. Da Ameen ta amsa kan ya a qasa dan bata da tacewa sai abinda Allah yayi da ita.
A haka suka ɗan taɓa hira, can da dare ya ja ta tashi tawa Papan nata sallama ta fice a sashen tayi ɗakin ta.


^^bayan sun gama hira dare ya ja, kaman ko da yaushe haka iyayen nasa suka masa, har ɗakin sa suka raka da Umma tayi mai addu'a, Suka yi sai da safe suka jan masa qofa. Suka tafi nasu wajan baccin.




AFTER 1 WEEK
^^^ a haka rayuwan ke tafiya in da yanxu har anci sati a cikin watan ɗaya da aka ɗiba za'ayi wannan gasan da mai martaba yace.
Kwata-kwata mutane 2 ne suka fito akan zasu yi gasan, kowa ya sare da ganin lamarin ƴaƴan Sarakunan yacce suka yi da Gimbiya.
Mutum na farko, Yaron wani Attajiri ne a masarautan, wanda yake ji da jarumta da kuma dukiya, kuma yake ji da kansa. Kasancewar yana practicing na faɗan hakan ya sanya ya qware sosai. Sunan sa 𝘼𝙉𝙒𝘼𝙍 kuma dama already yana cikin masu son Gimbiya Mehwish.
Sai kuma mutum na biyu shine 𝘼𝙈𝙅𝘼𝘿 shi kuma ya fito ba don yana son komi akan abunda aka saba sai dan kawai ya farantawa mahaifan sa da kuma son karya ji-ji da kan yarinyar na ganin da take tafi qarfin a buɗe fuskanta common fuska
Sunyi zama da mai martaba dukansu biyun, inda yace masu akwai wani sharaɗin bayan wannan Amma wancan ba dole bane. Buɗe fuskan Gimbiyar shi yafi muhimmanci.
Muddin ɗayan su yaci na farkon yayi alqawarin yin abunda yace kuma nan da wata biyar aure tsakanin sa da Gimbiya Mehwish ya qara da cewa "ko bayan raina ni Sarki Qaseem wannan alqawari na ne. Nan da wata biyar auren MEHWISH da duk wanda ga lashe gasan.
Akwai wani mai magana a cikin ku? Ko wanda yake da abun cewa? ba suce komi ba dukan su biyun, wanda hakan ke nuni da kowa ya aminta da batun sarki
Haka zaman nasu yazo qarshe kowa ya kama hanyarsa bayan mai martaba ya sallame su.
Awannan satin ukun da suka rage kullum cikin practicing Anwar yake dan shi lallai sai yayi nasara saboda yana son ta(hhhh Reader's a tafawa Anwar).


Shi kuwa gogan naku Amjad ko a jikin sa lamuransa yaci gaba dayi kaman ba zeyi abunba har ma mantawa yake da batun gasan.
Yau ma da yake saura kwana uku ya shiga jeji kuma bazai koma gida ba sai ana gobe gasar. Sakamakon magun gunan da yaje ɗebowa Abban nasa, duk da dai sun hanasa zuwa amma ya basu haquri ya tafi.


Sun qara haɗuwa da wannan stohon
Yace "yarona allah maka albarka naji dadin daka wa iyayenka biyayya, sannan in anyi duniya dan Manzon Allah SAW wannan gasar Insha Allahu kai ne zaka lashe.
Sannan abu na biyu da akace ma kai ne zaka ci. Dan dama kai ne, ake jiran zuwanka, kai ne kake da abunda ake nema, dalilin shigarka gasan kenan dan yana cikin kundin qaddaran ka kuma hanyan yayewan wani hijabi a rayuwar ka. Insha Allahu qofofin ainafin rayuwanka da sanin wanene kai asalinka na gab da buɗewa. Ina mai maka fatan alkhaeri da nasara a ko da yaushe. suka yi sallama yana masa fataan alkhaeryhn.
Ya dai ci gaba da abunda zai yi a dajin,. Amma duk da haka sau da yawa maganganun wannan dattijon na masa yawo a kwakwalwar sa. Ya dae share yaci gaba da abunda yakamata.
Bayan yayi kwana biyu a dajin ya samu abun da yaje nema yau ne zai koma kuma gobe ne gasan da za'ayi insha Allahu.




Muje zuwa......


𝘿𝙤𝙢𝙞𝙣 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙩𝙖 𝙝𝙖𝙟𝙖𝙧𝙠𝙪, 𝙠𝙪 𝙩𝙪𝙣𝙩𝙪𝙗𝙚𝙣𝙞 𝙖 𝙬𝙖𝙣𝙣𝙖𝙣 𝙡𝙖𝙮uka:-
08146292652
𝘾𝙝𝙖𝙩 𝙤𝙣𝙡𝙮.
09161720046
𝙔𝙤𝙪 𝙘𝙖𝙣 𝙘𝙖𝙡𝙡 𝙙𝙞𝙨 𝙤𝙣𝙚, 𝙭𝙖𝙢𝙪 𝙢𝙖𝙠𝙪 𝙩𝙖𝙡𝙡𝙖𝙣𝙠𝙪 𝙖 𝙧𝙖𝙝𝙪𝙨𝙖 𝙢𝙖𝙞 𝙨𝙖𝙪𝙦𝙞,


# 𝘾𝙤𝙢𝙢𝙚𝙣𝙩
# 𝙇𝙞𝙠𝙚 &
# 𝙨𝙝𝙖𝙧𝙚
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•
*_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️
───────────────────────
```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.```


```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️
____________(✪)______________


https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980
•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·•


💦💦💦💦💦💦💦💦


𝙔𝘼𝙍 𝙎𝘼𝙍𝙆𝙄 𝘾𝙀𝙀


🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹

𝙎𝙩𝙤𝙧𝙮 𝘼𝙣𝙙 𝙒𝙧𝙞𝙩𝙩𝙚𝙣

𝘽𝙮


𝙃𝙖𝙧𝙞𝙧𝙖 𝙨𝙖𝙡𝙞𝙝𝙪 𝙞𝙨𝙖


(𝙐𝙬𝙖𝙧 batoorl)

اللهم صلى و سلم على سيد نا رسولله saw🖤🤍




_______________________________________________________________




🅿️ 29&30



💋💋 امى بتولة💋
















QASAR JIDDAH


Wani haɗaɗɗen gida na kutsa kai ciki.
Fatabarakhallahu Ahsanul Khaleeq! shine abinda baki na ya furta.
Wasu kyawawan ƴammatan larabawa na gani su biyu tsaye a harabar gidan, wanda a shekaru ɗayar bazata wuce 17/18 ba, ɗayar kuma bazata haura 20 ba. Sanye suke da dogayen riguna komi iri ɗaya, sai dai color da ya ban-ban ta. Na babbar da ya kasance peach colour, na qaramar kuma white colour. Farare ne su duka, fuskan su mai ɗauke da dara-daran idanuwan su ga siririn hanci kaman su suka wa kansu, sai dai qaramar tafi babbar qaramin baki. Babbar da alama tasa ribbom akan ta, ganin yacce tayi rolling da ɗan kwalin rigan nata. Ita kuwa qaramar xubo da gashin nata tayi a bayan ta sai ta yafa ɗan kwalin rigan kaman veil. Masha Allah!! Gashi kam har gadon baya ga tsayi ga baqi. Dukan su biyun cikakkun ƴammataye ne, dan kuwa ko wanni qira na budurci ya gama bayyana a jikin su. inka gansu kaman ƴan biyu saboda kaman su bazaka ce ga wacce tafi kyau ba cikin su. Babbar ce tace "MAHA please dubo mana Ummeyh, tun ɗazu fa bata fito ba, kuma nafiso muje da wuri". Wacce aka qira da Maha ce ta tura baki "uhmm nifa yaya MAHREEN ba son komawa ciki nake ba na riga na fito inkoma ciki nabar Sa'a ta caɓ, mu jirata kawai ko kuwa ke ki koma ki dubo ta Ni dai ba inda zani, sai kace Ummeyhn kwana zata yi a cikin gidan". kama haɓa wacce aka qira da yaya Mahreen tayi tace "Lallai Maha Ni kike cewa ba zaki qira ta ba ko? Good ya miki kyau" ta faɗa tana qwafa.
Wata dattijuwa ce ta fito harabar gidan, wacce girman ta bai ɓoye kyawun ta ba. sanye take da dogon rigan zani ta yafa mayafi hanunta riqe da jaka da kuma key wanda da alama na motor ne. Wajan da ƴammata biyun nan suke tsaye ta nufa tana cewa "yaran Ummeyh na tsayar da ku ko kuyi haquri". Qaramar ce ta tura baki "Ummeyh kin kama kin daɗe kinaso muyi late ba". Wai kekam Maha bakyaji ko harda Ummeyhn a rashin kunyan naki? "Qyaleta Mahreen Allah ya shirya ta ai zata haɗu da habeeby inshà Allahu zai yi maganin rashin jinta." faɗin Ummeyh tana bankawa Maha harara. Maha tace "yanzu Ummeyh dan kawai nace zaki fito ai mujiraki shine rashin kunya kaman ana jirana?". Maha ubanki ne ke jiranki, inbaki rufe baki ba zakisa afasa tafiyan nan dake. Allah na gode maka ni Jamila yara kaman masu ganin hanjin junansu, Allah ka shiryamun su ka masu albarka, Kuwuce ku shige motor mu tafi marassa ji kawai. Buɗe gidan gaba Maha tayi zata shiga, kallon da Ummeyh ta jefa mata ya sanya ba shiri ta juya ta buɗe baya ta shige tana tura baki. Gefen mazaunin driver Ummeyh ta buɗe ta shige ta zauna batare da tace komi ba. Ganin haka ba tare da ko tari ba Mahreen ta buɗe mazaunin driver ta shiga kallon Ummeyhn nasu tayi, ba tare da Ummeyhn tasu ta ko ɗago ba ta ajiye mata key en ta ciro waya tana picking call wanda da alama baban yaran nata ne. Idon Mahreen ya kawo kwalla bata tada motorn ba tayi shiru, "zaki tada motorn muje ne ko kuwa kun fasa tafiyan ku koma ciki inada abun yi" Faɗin Ummeyh. Mahreen tace "Ummeyh afuwan kiyafe mana bazamu sake ba karkiyi fushi dan Allah Ummeyhl khair" naji banyi fushi ba tada motorn muje Allah maki albarka. Key tawa motorn mai gadi ya buɗe masu gate, ficewa sukayi a gidan yana masu Allah tsare hanya. Tafiya suke tana driving a hankali ba high speed ba, cikin motorn shiru bakajin muryan kowa sai Ummeyhn su da ke waya. Wayan ne a kare a kunnen ta tana magana "Abeeyhn su yanzu muka fito gidan muna hanya" shiru tayi alaman tana sauraran na ɗayan bangaren, can ta kuma cewa "a'a Abeeyhn su ban qira sa ba, sai mun isa airport en zanqira sa inshà Allahu, Okay tom shikkenan Allah dawo da kai lafiya gasunan duk zasuji gaisuwa, sallama suka yi ta kashe wayan. Abbeynku wai Allah kaiku lafiya hope Mahreen kin ɗau card en ciran kuɗin ki? Eh Ummeyh na ɗauka. Maha ce tace "Ummeyh haka zan tafi ba waya? baki sauya mun ba fa tunda ya ɓaci" rashin jinki ya sauya maki faɗin Ummeyhn tasu. Jan baki Maha tayi tai shiru, dukansu shiru a motorn har suka isa airport en wajan parking suka yi parking.
Fitowa suka yi duka a motorn sunzo dai-dai jirgin da sukayi booking ya kusa tashi, kayan su dake Boot Mahreen ta fitar masu ta kulle Boot en, miqawa Ummeyhn tasu key tayi "Ummeyh ga key en nan" amsa Ummeyhn tasu tayi ta jefa a jaka. Maha ce tayi magana "Ummeyh bakice komi ba maganan wayata, Ummeyh kiyi haquri". Maha bakyaji ko kaɗan Ni zaku ta sawa surutu,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login