Showing 45001 words to 48000 words out of 98220 words
Chapter 16 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt
kuwa shima a haka ya kusan raba dare ya juya haka da qyar dai ษarawon bacci ya sace shi.
Gimbiya bata san mai yasa ba amma har cikin ranta tana cike da kewan ganin sa yau gaba ษaya baizo ba, kuma mai martaba yace mata zai ke zuwa.
Sai dai abu ษaya da ke kwantar mata da hankali shine ta yarda da cewan Insha Allahu zai cika alqawarin da ya ษauka, kusan yau wuni tayi masa addu'an dacewa da Sa'an samowa mahaifiyar tata magani.
Bayan ta idar da Sallahn isha'i a ษakin mahaifiyar ta, tana kan darduma kaman ance ta juya, sai hanun Amman nata ta gani yana motsi kaman tana son ษaga hannun.
Da saurin gaske tayi wajan gadon, Bayan kusan sati gashi yau Ammaan nata halaman sauqin dai ya qara nuna wa jikin zai lafa, dan dama takan yi sati bata ko mosti, in jikin ya lafa kuma tashuwa ne da kuma cin abu bata iya wa amma zata yi magana har ta ษan jingina da kanta, sai dai komai sai anmata duk da haka
Ta sameta ta buษe ido amma bata iya magana, sai mosta bakin ta take alaman tana son yin magana amma ta kasa, Gimbiya tace "Ammaa Sannu" gyaษa kai kawai tayi da murmushi a fuskan ta, sai kuma ta mai da idon ta ta rufe.
Ko ba komai taji daษin farkawan mahaifiyar tata gashi har ta mata wannan murmushin nata da ke yaye mata damuwan xuciyan ta, "Allah baki lafiya mai ษorewa Ammaah ta" shine abinda ta furta tana mai zama gefen maman nata tana ษan daddana mata jikin ta kaman massage.
Har Mai martaba ya shigo ya samesu a haka, ganin ษiyar tasa cikin farin ciki ya sanar dashi me ke faruwa ko bai tambaya ba, tabbas shima yana jin tausayin tilon ฦดar tasu dan kwata-kwata batadan daษin uwa ba, a maimakon uwa tayi hidima da ita, ita take hidima da uwar tata tunda tayi wayo.
Mai martaba yace "Ibnateey me aka bata? Tace "Papa ba komai fa. Masha Allah, Allah ya bata lafiya mai ษorewa Alfarman Rasulullahi SAW. Da Ameen ta amsa
Zama yayi a gefen gadon ita kuwa Gimbiya ta sauqa qasa, mai martaba yace mata "ya kuka yi da Muhammadun? Nan Gimbiya ta kwashe yacce suka yi duka ta faษa masa har da alqawarin da yace ya ษauka, kuma Papa inaji a jikina Inshร Allahu za'a dace, Allah dai ya temaka. Mai martaba yace "Ameen ya Allah, Allah ya sa a dacen.
Nan ya qara da ce mata "in dai abun da ta faษa da gasken shi take nema kan ga Auri mutum tom tabbas wannan ne mijin da take nufi akoda yaushe dan wannan ya haษa fun yacce take so ma, Allah ya tabbatar maki da alkhaeri Ibnateeyh, da "Ameen, ta amsa tana tuno maganan su da jakadiya.
Mai martaba ne ya sauqe ajiyan zuciya yace "Amma akwai abun da yake damuna". Gimbiya ta kalli Papan nata cikin damuwa tace "menene Papa?
Murmusawa yayi ba komi karki damu kanki Ibnateeyh kai na ke ษaure wa kawai, tabbas yana mun akwai mai irin fuskan sa da na sani amma abun da jimawa na kasa tunawa.
Ayya Papa ai dama haka ne yawanci ance ko wanne ษan adam da masu kama dashi guda bakwai 7 a duniya, Tom may be shiyasa kake ganin hakan.
Haka dai hiran nata ita da mahaifin nata har dare yayi, ta tashi ta wa mahaifin nata sai da safe, ta wuce dan tafiya sashen ta tasamu ta kwanta.
Sai dai muce safiyar alkhairi jama'a.........
๐พ๐๐๐ ๐ฌ๐๐ ๐๐ฎ๐ ๐จ๐ช๐ฃ๐๐ฃ ๐ฌ๐๐ฃ๐ ๐๐๐ก๐ข..
๐๐ช๐ฃ๐ ๐๐๐ฃ๐๐ฃ ๐ฉ๐ช๐ฃ๐๐ฃ๐๐ฃ ๐ผ๐ข๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐ข๐๐๐ฎ๐ ๐ฉ๐ ๐๐๐ง๐ ๐จ๐ค๐ฎ๐๐ฎ๐ฎ๐ ๐๐ ๐ ๐ค ๐ฌ๐๐ฃ๐ ๐๐๐ช ๐๐๐๐๐ฃ?
๐๐๐ช๐จ๐๐ฎ๐๐ฃ ๐๐๐ข๐๐๐ฎ๐๐ ๐๐ ๐ผ๐ข๐๐๐ ๐ฎ๐ ๐๐๐ง๐ ๐๐ ๐ฏ๐๐ ๐๐ฎ๐ ๐๐ช๐ฎ๐๐ฌ๐ ๐ฏ๐ช๐ฌ๐ ๐จ๐ค๐ฎ๐๐ฎ๐ฎ๐ ๐ ๐ช๐ฌ๐?
๐๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ฉ๐๐๐๐ฎ๐ ๐ฏ๐'๐ ๐ฎ๐ ๐จ๐๐ ๐ ๐ช๐ฌ๐?
๐๐๐ฃ๐๐ฃ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐จ๐ฉ๐ค๐๐ค๐ฃ?
๐๐๐จ๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ข๐๐๐ฎ๐ค๐ฎ๐๐ฃ ๐ข๐ช ๐๐ ๐๐๐ช๐ฃ๐๐ ๐ฏ๐ช๐๐๐ฎ๐๐ง๐ข๐ช ๐ฏ๐๐ฉ๐ ๐ ๐ ๐จ๐๐ฆ๐ ๐ข๐๐ฃ๐ ๐๐ ๐ฎ๐๐ฌ๐....
ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐๏ธ
Nace ba jama'a muje zuwa, labari fa yanzu aka fara โ๏ธ
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
๐ฟ๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ ๐ช, ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ก๐๐ฎuka:-
08146292652
๐พ๐๐๐ฉ ๐ค๐ฃ๐ก๐ฎ.
09161720046
๐๐ค๐ช ๐๐๐ฃ ๐๐๐ก๐ก ๐๐๐จ ๐ค๐ฃ๐, ๐ญ๐๐ข๐ช ๐ข๐๐ ๐ช ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ง๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐, wai hausawa suka sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi!!!
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐๐ฉ๐ค๐ง๐ฎ ๐ผ๐ฃ๐ ๐๐ง๐๐ฉ๐ฉ๐๐ฃ
๐ฝ๐ฎ
๐๐๐ง๐๐ง๐ ๐จ๐๐ก๐๐๐ช ๐๐จ๐
(๐๐ฌ๐๐ง batoorl)
ุงูููู
ุตูู ู ุณูู
ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู saw๐ค๐ค
_______________________________________________________________
๐
ฟ๏ธ 35&36
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
WASHE GARI..
Qiran farko na asuba, Umma ta farka a ษan razane har jikin ta na sassafo da zufa, salati tayi tana dafe qirji! Wannan salatin da tayin shi yayi nasaran tada Abba a bacci.
Miqewa Abba yayi ya laluษi hasken ษakin ya kunna, kallon ta yayi yace "Lafiya kuwa maryama? Ko dai kinyi mugun mafarki ne?
Umma ta kasa cewa qala sai kawai jingina da tayi da kan gadon ta rufe ido tana mai da numfashi!
Miqewa Abba yayi ya fice yaje dan ya tashi Amjad amma ya samu har ya tashi, magana Abba ya masa "kayi alwala mu tafi masallaci ko" amjad dake miqa a kan madedecin gadon sa yace "Tom Abba na, yau fa ina Umma ta Bata zo tashi na ba" ya faษa yana miqewa. Umman ka na can tana fama da rigima ta kusa yin jika bata san ta girma ba har yanzu. Dariya Amjad ya sanya! Yanzu dai Abba wannan abu da kake faษa cin fuska ne, uwattawa ce ke rigima? ฦata fuska Amjad yayi! Daga kafaษa Abba yayi ya fice a ษakin yana "da kai da Umman taka duk Allah ya taroku" ษakin su ya wuce.
Cikin lallami Abba ya fara magana "Mero ta kina son saka ษan naki cikin damuwa ko? Kinga ganin ni naje tashin sa ba ke ba har yana tambayan ko baki da lafiya ne, in dai bakyason zuwan ษan naki can qasar shikkenan ki faษa masa nasan shi kuma in dai bakyso bazai je ba. Amma inason ki sani Alqawari ya ษauka masu sannan kuma kece kika fara yarje masa maganan wannan gasa dan girman Allah da Manzon sa Maryam ki lallashi zuciyanki" ganin da alama har ran Abba ya fara ษaci sai Umma ta sauqo a gadon faษawa jikin Abba tayi, Abban jarumin Umma kayafeni amma kayi haquri wallahi Nima banson saka damuwa a rai na abunne ya kasa bari na, Mafarki nayi fa akan yaro na.
Umma ta buษe baki da niyan labarta wa Abba mafarkin sai Abba ya ษaura yastan sa akan bakin ta yace "shiiiii, ya isa ba sai kin faษa mun ba yanzu sallah zaki yi, ki sanar da Ubangijinki sannan kiyi wa ษan ki addu'an nasara da ta kariya, kuma kada ki manta wani lokacin akwai sharrin shaiษan, da yawa mafarki kan zama gaskiya amma wani mafarkin sharrin shaiษan ne. Wani lokacin mukan kwanta a tunanin abu a ranmu Tom ba shakka wannan abun ya damemu har a mafarkin mu ya zo mana.
Akwai kissar wani bawan Allah da yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass(RA) yace masa "ance in kana yawai ta salatin Manzon Allah SAW Tom tabbas zaka gansa, me yasa kullum ina yi amma ban taษa kallon sa ba? Sai Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Annabi kake so ka kalla? Wannan bawan Allah yace "eh" Sheikh Ibrahim inyass yace masa "Tom yau in zaka kwanta inaso kaci abinci kawai kar kasha ruwa, ka kwanta haka ko mai ka gani a mafarkin ka kazo kaban labari. Wannan bawan Allah ya tashi ya tafi da yaje gidan sa dare yayi ya ci tuwo bai sha ruwa ba ya kwanta, washe gari asuban fari yaje wajan Sheikh Ibrahim inyass (RA). Sheikh Ibrahim inyass ya ce masa "bawan Allah labarta mun abun da ka gani a mafarkin naka. Bawan Allah yace "malam nayi yacce kace amma da na kwanta mai makon naga Annabi sai kuma nayi mafarkin inata shan ruwa kawai har dai na farka, murmusawa Sheikh Ibrahim inyass yayi yace masa "Tom in zaka kwanta da qauna da kuma begen son ganin Annabi SAW kaman yacce kaman ka kwanta da qishin ruwan nan Tom tabbas in kana qishin ganin Annabi wataran Manzon Allah SAW zai baka ruwan kashe qishin qaunan ganinsa".
Tom inaso ki sani tabbas akwai mafarkin da suke gaskiya kaman labarin dake cikin (MAFARKI NAH littafin Uwar Batoorl) da kuma ( A MAFARKI NA littafin A'isha Mika'il) akwai kuma waษan da suke ba gaskiya ba.
Dogon ajiyan zuciya Umma ta sauqe tana mai jin nistuwa ya shige ta sosai, hamdala tayi ga Allah sannan ta ce "kar Jarumin Umma ya jira ka sosai Abban sa a samu a tafi masallaci" kallon ta Abba yayi yana murmushi yayi hanyan fita a ษakin yana cewa "inma ya gaji jira ya zai yi ba uwar sa ce ke mun rigima ba ta tsayar dani, mutum har ya kusa yin jika ya girmi yin rigima amma yaqi dai nawa, dole ma na hana Amjad maki takwara dan rigiman masu suna Maryam in ya haษamun ku har biyu zaku qarisa ni, ya qarasa faษa ya bar ษakin dan yin alwala ganin an kusa shiga salla.
Murmushi kawai Umma tayi, tabi bayan mijin nata dan ita ma tayi alwalan ta samu jam'i.
Fitowan Umma Abba kaษai ta gani ya fara alwala, wucewa ษakin Amjad tayi dan tasan halin sa sarai zai iya komawa ya kwanta. Tana shiga ษakin nasa ta hango sa kan sallaya yana addu'a, tsayawa tayi har ya shafa kamun tace "kar dai jarumin nan yace mum har yayi Sallah? Tashuwa yayi yana murmusawa a'a fa Umma ta nafila nayi kamun Abba ya fito mu wuce. Umma ta buษe baki zata yi magana Abba da ke tsakiyan gida yace "jarumin Umma ka fito mu tafi kar mu rasa jam'i.
Bayan fitan su alwala Umma tayi dai-dai ana shiga sallah a masallaci, jam'i ta tasamu ta bi da aka idar lazumin ta tayi da addu'oeen ta kamun ta shafa, tashuwa tayi ta shiga aikin gida dan tasan in ษan nata ya dawo ya samu tana yi zai ce zai taya ta.
Umma tayi sharan ta da wanke-wanke san da ta ษaura abincin karyawa kamun ta shiga ta gyara wa ษan nata ษaki ta sanya masa turaren wuta mai daษin gaske. Cikin qanqani lokaci gidan gaba ษaya yayi staff baka jin komai dai qamshin turaren wutan da tasa a ษakin ta da kuma ษakin yaron nata, sai kuma qamshin ruwan shayin da take dafawa.
San da gari yayi haske tarr kamun Abba da Amjad suka dawo gida, sun shigo gidan lokacin Umma na banษaki tana wanka.
Abba ษaki yayi, shima Amjad ษakin sa ya wuce direct ya kwanta dan mai da baccin da bai yi ishashshe jiya ba. yana kwanciya ya rufe idon sa da zummar yin bacci, kyakkyawar fuskan Gimbiya da wannan murmushin ta mai mantar dashi ko sunan sa ke masa gizo, buษe ido yayi ya kuma kullewa ita ษin yake qara gani, laษษan ta da yafi ษaukan hankalinsa da kuma kalan qwayan idon ta su suka hana sa sukuni, duk ya juya haka ya juya haka amma yana rufe ido ita ษin yake gani tana masa gizo.
Tashuwa yayi ya zauna a stakiyan gadon nass magana yake shi ษaya "wannan kwailar yarinyan mai take nufi dani ne? Guntun tsaki ya ja! Fasa baccin yayi ya tashi ya fita a ษakin.
Umma da ke qoqarin shigowa ษakin nasa da qiran sa ya karya tukun yayi bacci, ya kusa yin karo da ita, ja baya Umma tayi tana kallon sa tace "lafiya kake surutu kai kaษai har ka kusa ya da ni? ina son nazo na ganki ne Umma ta. kallon sa Umma tayi da murmushi tace "kadai faษa gaskiya ko Gimbiyar zuciyar taka kake tunani? ฦago kan sa yayi da zumman kallon Umman tasa da mamakin ya aka yi ta gane abun da yake tunani, ganin yan da idon Ummansa ya kumbura sannan yayi ja kaman mai ciwon ido san da yaji gaban sa ya faษi!
Umma ganin ษan nata ya zuba mata ido, nan take ta tuno da yacce idon ta ya kumbura tai saurin juyawa dan kar ya fahimci wani abu ya sawa kansa damuwa, sanin halin ษan nata.
Jarumin Umma biyo ni ka karya sai ka koma baccin ko kaje wajan Gimbiyar taka in kuma yau zaka tafi tom.
Bin bayan Umman tasa yayi yana qara nazarin yacce ya kalli idon Ummansa mai ya same ta? Mai ya hana ta zuwa tada shi da asuba kaman ko yaushe? Zama yayi a gefen Abban sa a kan tabarman ta yacce zai ke kallon Umman tasa da kyau.
Kunun tsamiyan da ya gani a kofi ya ษeba ya fara sha, kallon sa Abba yayi yace "yau kuma kunu za'a sha kenan rogimammen Umman sa" Umma ta murmusa ta ce "a qyale mun yaro komai ma yake so in dai akwai tom yasha, Jarumin Umman sa sha abunka dama wa kai nai wa kunun.
"Ummata tafiyan nawa ne har ya sanya idonki kumbura da ja haka? tambayan da Amjad ya jefowa Umman sa wanda bata yi tsammanin ji ba, Abba da ke shan ruwa zafi ajiye kofin yayi a take ya kalli Umma ya kalli Amjad, kamun Umma tayi magana Abba yayi saurin cewa "jarumin Ummansa idon Ummanka ke ciwo".
"Abba ciwon ido dai? tun yaushe haka? Abba ka kalli idon Ummata fa yacce ya kumbura yayi ja kaman wanda yayi kuka, Abba akwai dai abun da Ummata ke ษoyemun ko kuke ษoyemun duka, ko dai Umma bata son tafiyan ne na haqura? Ya faษa fuskan sa na nuna da gasken yake zai haqura.
Umma tace "jarumin Umma idona kawai ke ciwo, ka karya ma kasamu kaje ka gano surkar ta in ya so sai kayi shirin tafiya. Shiru Amjad yayi bai ce komi ba, ba don ya yarda idon Umman tasa ke ciwo ba kawai yasan dai wani abu ne suka ษoye masa, ya san Umman sa duk in yace zai yi tafiya na kwana biyu in dai ba jeji ba Tom hankalinta baya kwanciya har sai ya dawo, ya rasa mai yasa haka? Kuma bare wannan karon da zai je qasa ne wanda bai sani ba bai taษa zuwa ba, iyayen nasa ma basu taษa zuwa ba yasan dole bazai wuce hakan bane ya tada mata hankali! Ajiyan zuciya ya sauqe ya aje kofin dake hannun sa. "Umma ta Allah baki lafiya" ya faษa yana miqewa.
Kallon sa Abba yayi yace sai kuma ina Jarumin Umman sa? Abba bacci nake ji, yau baza'a raka Abba kasuwa ba kenan? Miqa Amjad yayi yace "Abba zan biyo ka in na tashi baccin, Umma tace "jeka abunka kayi baccin ka ษan albarka Jarumin Umman sa. Murmushi yayi yace "tom Umma ta, Abba Allah kai ka lafiya sai nazo" Abba yace "kace dai sai na dawo dan baka yi alaman biyo ni kasuwa ba yau, Amjad dariya yayi bai ce komai ba ya wuce ษakin sa. Yana shiga ษakin nasa ya kwanta, a take bacci ya ษauke sa.
Amjad na barin wajan Abba ya juyo ya kalli Umma, Maryam Kinga ko, kema kinsan irin qaunan tsakaninki da ษan kin nan ko bai ga idon ki ba tsaff kaman mai Aljanun Umman sa zai san mai ke faruwa, kidinga koyan haquri da ษoye wani abun kinji meron ibro maman amadu. Umma dariya ta sanya, yanzu dai ka ษata sunan kowa ban da na yarona, sunan sa Muhammad ba amadu ba.
Tashuwa Abba yayi yana dariya ya shiga bayi dan wasta ruwa ya shirya zuwa kasuwa, Umma kuwa tashuwa tayi ta kama gyaran inda suka karya ta haษa kwanukan wanke wanken ta kamun ษan nata ya tashi ya gani yace zai yi.
Abba shiryawa yayi cikin manyan kaya ya kafa hulan sa, har bakin qoga Umma ta raka sa tana masa adawo lafiya.
Bayan tafiyan Abba Umma ta kammala komai nata, ta gyra gidan ta qara yin wanka, ganin har qarfe sha ษaya 11am yayi kuma ta leqa Amjad haryanzu bai tashi ba, Hijab ta sanya ta fita a gidan.
Amjad wajajan qarfe sha ษaya da rabi ya tashi 11:30am, mafarkin da yayi ya tuna shi ya sanya shi jan guntun tsaki, magana yake a zuciyansa "ni dai wannan qwailar yarinya bata kai ta sanya ni wanka ba" fita yayi a ษakin yana qiran sunan Umman sa, jin ya qira shiru bata amsa ba kuma bai ji qaran ruwa a bayi ba.
ษakin ta ya leqa ko tana ciki nan ma bata ciki, haqura yayi da neman ta ya ษiba ruwa ya shiga wanka.
Sai da ya yi kusan minti talatin a bayin kamun ya fito, shiga ษaki yayi dan ya shirya sai ya jiyo sallaman Umman sa, fasa shiga ษakin yayi ta tsaya.
Amsa Sallaman yayi yace "sannu