Showing 48001 words to 51000 words out of 98220 words

da dawowa Umma" yauwรก jarumin Umma sannu da tashi kai ma.
Umma ashe kin fita na tashi inata nemanki ban ganki ba, Umma murmushi tayi tace "jinjirin Umman sa makwabta naje yin barkatu anyi haihuwa naga kana baccinka mai daษ—i shiyasa ban tada kai ba, sannun ka da tashi ko.
"Tom Ummata ya faษ—a" yana shigewa ษ—akin nasa dan ya shirya.
Bayan ya gama shirin sa fitowa yayi sanye da qananun kaya, Umma na ganin sa bakin ta yaqi rufuwa
"jarumin Umma irin wannan kyau haka, a lallai surkata zata ga wanka yaushe rabon da kasa qananan kaya? Maha Allah yaron Abba ko a kasuwan maqiya wannan kyawun dole a yabe sa bare a na masoya. Sosa qeya Amjad yayi yana murmushi dan shi kanshi yasan tabbas yayi kyau, kyau enma irin sai idonka ya gane makan nan, Amjad yace "Umma sai na dawo, washe baki Umma tayi tace "a gaidamun surka ta dan nasan wannan wankan ba dai kasuwa ba sai dai masarauta.
Allah tsaremun kai ya dawo da kai lafiya jarumin Ummansa.
Ummata surkanki zata ji gaisuwa, ya faษ—a yana dariya ya fice a gidan.
bayan sa Umma tabi da kallo sai kwalla a idon ta! Allah karemun kai ya tsaremun kai a ko ina Amjad.
Yana fita qofan gida, wani motor arsh color ya gani yana qoqarin parking a qofar gidan nasu, kallo ษ—aya yawa Motorn ya kauda kai ya nufi hanya, horn mai Motorn yayi Amjad bai ko juya ba yaci gaba da tafiyan sa.
Muryan da ya ke mararin ji ne ya jiyo sa anacewa "kai ษ—an air shugaban marassa mutunci ba kaji ina horn bane" juyowa yayi cikin hanzari mutumin da ya gani ne ya sanya shi cewa "whatttt"
mai muryan ne dai da yayi tsammani. Mai Motorn ne ya zo yayi hugging nasa ganin Amjad en yana tsaye ya kasa qarisowa.
Amjad yace "Ahmad kai nake gani ko mai kama da kai? Wanda ya qira da Ahmad en ne yayi dariya yace "yes ni kake gani Jaaad. Ashe rai kan ga rai?
kwana da yawa ba kai ba labarin ka shiru kawai ka manta da mutane.
Sosai qeya Ahmad en yayi da key na motor da yake hanun sa, yanzu dai ina ka nufa?
Ba wani waje mai nisa bane nan gidan Sarki zani. Amjad laifi kawa sarki ko me da rana tsakan nan i hope dai ba qasqantar da kanka kayi kana aiki a can ba?
Murmushi Amjad yayi yace "long story ne Man but to cut the long story in to short zance zani gidan Sarki.
Buษ—e baki Ahmad yayi sai kuma ya kwashe da dariya, duk Wannan kyau naka a gidan Sarki kuma ya staya Ina fatan dai ba hadima ba ko ฦดar aiki acan? Dafe kai Amjad yayi yace "You see mastalana dakai wallahi son dogon surutu and you know am having headache in long conversation.
Yanzu dai Jaaad baka yi missing na ba da kake cewa har zan sa maka ciwon kai, mu shiga na gaida Umma sai in yaso muje gidan Sarkin tare ko giftawan ฦณAR SARKI na gani, wani kallo Amjad ya ma Ahmad sanda ya haษ—iye sauran maganan bakin sa bai shirya ba.
Amjad yace "in zaka shiga ka gaida Umma ka je ka gaida ta ai zata gane ka, zuwa gidan Sarki kuma ina da qafa ban ce ka bini ba, tunda kasan hanya kaje da kanka. Ahmad jan baki yayi yai shiru bai ce komai ba, juyawa yayi zai shiga gidan yana cewa "Man you will never change, Allah taro ka zan je gidan Sarkin da kai na ai nasan hanya in ka dawo da dare zamu haษ—u.
Bayan Ahmad ya shiga gidan ษ—aga kafaษ—a Amjad yayi irin "i don't care" ennan yayi gaba abunsa.


Umma na qoqarin hura wuta a kitchen ta jiyo sallama, amsawa Umma tayi ta fito tana waye ne? Ahmad na sunne kai yayi ya stugunna yace "Umma an wuni lafiya. Umma ta ce "lafiya Alhamdulillahi bawan Allah. Gaisawa suka yi Umma dai bata gane sa ba, bayani Ahmad ya mata, kamun Umma ta gane sa, wai wai wai Ahmad kana nan shiru-shiru ka manta da mutane kaman baka nan?
Umman ina nan sai a hankali ne da yake bana qasan gaba ษ—aya, Umma tace "gashi abokin naka ya fita yanzu wai zashi zance da rana staka baku haษ—u a hanya ba? Ahmad yace "Umma mun haษ—u, ni nace zan qaraso na gaidaki" ayya Allah ya maka albarka ya gida ya su maman naku? Suna lafiya Umma suna gaida ku. Masha Allah haka akeso, ruwa Umma ta kawo masa ya sha ya mata sallama zai tafi.
Umma tace "yaro na har zaka tafi ba zaka tsaya muci abincin rana ba kan abokin naka ya dawo? Murmushi Ahmad yayi yace "Umma zan dawo anjuma da dare Inshร  Allahu" Tom Tom ba komai Allah kaimu anjuman Allah maku albarka, "Ameen Umma" ya miqe ya mata sai anjuma ya fita, yana kan tunanin irin kallon da Amjad ya masa ษ—azu ya rasa mai kallon yake nufi dan baisan abun da yace ba in banda maganan Gimbiya da yayi.
Daga kafaษ—a yayi shima yace ohon maka in tayi tsami zanji..

Barka da jumaah masoya ayi haquri da wannan, happy friday garekuu daga uwar batoolerh takuu Ako da yaushe โœ๏ธ




ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ



๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa suka sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi!!!


# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š






๐™๐™’๐˜ผ๐™ ๐˜ฝ๐˜ผ๐™๐™Š๐™Š๐™๐™‡ ๐Ÿ”ฅโœ




๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ


๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–


(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorl)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค


_______________________________________________________________


๐Ÿ…ฟ๏ธ 37&38



๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹














Ahmad tada motorn sa yayi yaja ya tafi.
Umma ayyukan ta taci gaba da yi bayan ta kammala ta kwanta dan huta gajiya kamun mijin nata da yaron nata su dawo.




-----
Taxi da Amjad ya hau a iya inda baqin abun hawa ke tsaya wa in sun shigo cikin Masarautan anan aka stayar da shi.
sallaman mai taxi ษ—in yayi, ya kama hanyan shiga cikin Masarautan a qafa.
motoci ke shigowa haraban Masarautan, da alama wani babba ne yazo.
Acikin jerin motocin ne wani ruwan toka qiran Benz ya tsaya dai-dai gefen Amjad, dogarin da ke jan Motorn ne ya fito yana cewa
"Barka da shugowa ranka ya daษ—e, ka iso mu qarasa" ya faษ—a yana buษ—ewa Amjad qofa, ba musu ya shige motorn ya zauna.
Gimbiya yagani zaune a motorn, abun ya basa mamaki daga ina take da safen nan? Tun kallon da ya mata na farko ya kau da kai bai kuma kallonta ba.
hakan da yayi ya matuqar ษ“atawa Gimbiya rai dan taji daษ—in ganin sa amma taso ya fara mata magana.
kau da kai tayi tana tura baki, amma takan juyo ta saci kallon sa. Amjad tun da ya juya ko mosta kansa bai sake yi ba, yasan kallon sa take dan yana jin yawon idon ta a jikin sa.
Har bakin qofan shiga ainafin cikin gidan motorn ya kaisu, shi ya fara buษ—e qofan ya fita kamun Gimbiyar ta fito.
Dogarawan na kwasan gaisuwa, hanu kawai Gimbiya ta ษ—aga tayi gaba hadimominta suka bi bayanta.
ฦŠaga kafaษ—a Amjad yayi irin i don't care ennan ya ษ—auki hanyan da zai sadashi da babban palourn baqi.

Tasan da yana jiranta amma sanda ta watsa ruwa ta kuma shiryawa cikin kayan da zamu iya qiransa na shan iska ta yafa alkyabban ta tayi hanyan palourn da tasan bazai wuce yana can ba.
Da sallama ษ—auke a bakinta ta shiga, amsawa yayi bai ko ษ—ago ba.
Waje ta samu ta zauna tana tura baki ganin har yanzu yaqi mata magana, daurewa tayi ta buษ—e baki tace "malam in baka da abun cewa nayi gaba ni inada abun yi" ta faษ—a tana juyar da kai gefe alaman dai da gaske take.
Murmushin iyaka leษ“e yayi yace "Allah kiyaye hanya kya iya yin gaba".
Hararan sa tayi kawai batace uffan ba.
"Daga ina kike?"
Kaman daga sama taji anjefo mata tambayan kallon sa tayi, hankalin sa na kan Apple da yake tauna a hankali kaman ba shi yayi tambayan ba.
"Mai kike kallo nayi tambaya baki ban amsata ba? Ya faษ—a yana kallon ta da idanuwan sa masu sanyata nistuwan dole, qarfin hali tayi tace
"Ai naga kaman ba dani kake maganan bane shiyasa" qara waro idonsa a kanta yayi, sai ta kau da kanta tace
"Daga ษ—aki na nake" kallonta yayi ya girgiza kai kawai baice komi ba yaci gaba da taunan Apple nasa.
Ta rasa meyasa amma bata iya ษ—auke idonta a kansa,
"Baiwar Allah kurwata tafi qarfinki irin wannan kallo haka" ya faษ—a yana miqewa jin ana qiran sallah.
Basarwa tayi ta miqe itama tace "inka dawo masallaci ina garden" ta faษ—a ta fice a palourn da kunyan kamata da yayi tana kallon sa.
Murmushi yayi yana binta da kallo har ta ษ“acewa ganin sa kamun ya fice shima ya nufi masallaci.
Sashen ta tawuce ta kuma gyara kwalliyan ta taษ—au wayanta a bedside drawer ta fito, jakadiya dake qoqarin shigowa ษ—akin nata suka kusa cin karo, kaucewa jakadiyan tayi tana fadin "amun afuwa ranki ya daษ—e ban kula bane" hanu ta ษ—aga mata tace "a gyara mun shumfiษ—a inada baqo sannan akai kayan marmari" ta faษ—a ta wuce.
Juyawa jakadiya tayi dan aiwatar da aikin da uwargijiyan nata ta umurce ta dashi.
Yana fitowa masallaci hanyan da zai sada shi da lambun ya nufa.
Zaune ya tarar da ita tana danna waya, sallama ya mata sannan ya zauna, kallon sa tayi ta amsa Sallaman fuskanta ษ—auke da murmushi.
Gyaran murya yayi kamun yace "nazo muyi sallama ne may be sai ranar Aure ki ganni" ษ—ago kai tayi tana wara idanuwan ta, "tafiya zuwa ina haka?" Ta faษ—a cike da son samun amsa.
Zanje wani qasa ne amma ba mai nisa sosai ba, though ban taษ“a zuwa ba bare nasan iya nisan nasa, akan batun maganin Ummanki and ba lallai na dawo yanxu ba so you should take care.
Ba zato ba tsammani yaji mutum a jikin sa, saurin janye jikinsa yayi a nata yana kallonta.
"Allah tsare hanya ya kaika lafiya Allah ya bada Sa'a Allah yasa a dace" ta faษ—a tana share hawayen dake bin kuncin ta!!
Da "Ameen" ya amsa yana miqewa, i have alot to do so saqon gaisuwa zuwa ga mai martaba da kuma Ummanki sai Allah yayi dawowa na kuma.
Ganin tanason masa yarinta sai kawai ya wuce bai ko tsaya sauraran mai zata ce ba.
Miqewa tayi jiki a sanyaye ta nufi part na mahaifiyar ta.


Daganan kasuwa ya nufa wajan Abba, suka gama tsara komai na tafiyan nasa wanda zai yi gobe insha Allah, sune basu dawo gida ba sai magrib.
Da sallama duka abakin su suka shigo gidan Umma suka tarda tana sallah, buta Amjad ya kawo wa Abban sa shima ya ษ—au nasa suka yi alwala, Abba yaja su jam'i suka gabatar da sallahn magrib. Sun idar bada jimawa ba isha'i ya shiga suka kuma miqewa tare da Umma suka gabatar.
Bayan sun idar da sallolin nasu Umma ta qara masu sannu sannan ta gabatar masu da tuwon daren nasu, tare suka ci kaman ko yaushe har suka kammala ta tattara komai ta kai kitchen.
Abba ne yace "tunda kana da tafiyan sassafe gobe in Allah ya yarda ga kamata duk muje ku kwanta dan kar ka makara, ko Amjad" maganan da Abba yayi sanda ya sanya wa Umma faษ—uwan gaba amma ta daure! Murmushin qarfin hali tayi tace "gaskiya ya kamata kam Jarumin Umma ka samu ka dawo da wuri insha Allahu, Allah dai ya bada Sa'a Allah sa a dace.
Da "Ameen" duk suka amsa suka miqe dan kowa ya wuce makwancin sa, abinda ya damu Amjad bayan shigansa ษ—aki ษ—aya ne ganin yau iyayen nasa basu masa yacce suka saba ba amma sai yabar hakan akan kewansa da zai damesu yayi alwala yai addu'an ya kwanta dan samun yayi sammako.
Abba na shiga ษ—akin ya kalli umma kawai y girgiza kai ya wuce ya ษ—auro alwala ya kwanta. Tashuwa umm tayi daga tagumin da ta zuba taje ta ษ—auro alwala ta tada sallah.
Sanda ta raba dare tana sallah kamun ta stagaita ta daga hannu sama tana hawaye tana addu'a, sai dai abinda tafe furta wa ne ya cika ni da mamaki....



๐™’๐˜ผ๐™Ž๐™ƒ๐™€ ๐™‚๐˜ผ๐™๐™„
Qiran sallah na farko a kunnen Umma dake kwance kan sallaya, miqewa tayi ta fita dan hura wuta tunda yau sammako tilon ษ—an nata zai yi. Ana kiran sallah ta tada mijin nata shikuma ษ—an nata da kansa ya fito suka yi alwala suka nufi masallaci dan samun jam'i, itama alwala tayi ta wuce dan gabatar da nata Sallahn.
Kamun gari ace ya waye ta kammala komai ta shirya komai wa yaron nata, har kayan d ya haษ—a na tafiyan ta qara gyara masa, dawowan Amjad da Abban sa suka samu har ta ta fitowa da Amjad jakan tafiyan nasa.
Bayan sun karya a gurguje yaje yai wanka ya shirya ya fito dan tafiya, Umma ce ta kalle sa murmushi ta sanya sai kuma ga hawaye ya biyo idanuwan ta da sauri ta goge su dan kar ษ—an nata ya kalla.
Har qofan gida Umma da Abba suka rako sa, ba zato ba tsammani motor suka tarar a qofan gidan, dogari ne ya fito ya durqusa yana kwasan gaiusuwa, amsawa Amjad yayi yana masa kallon neman bayani.
Dogarin yace "ranka ya daษ—e Gimbiya ce ta aiko mu a kaika airport" lumshe ido Amjad yayi yace okay ina zuwa ga kayan kasa a motor. Umma ta murmusa a ranta albarka kawai take sawa surkar tata da ษ—an nata, bankwana yayi da iyayennasa suna masa addu'an adawo lafiya da kuma fatan nasara, durqusawa ya ษ—an yi Umma ta shafa kansa "Allah maka albarka ka kula sosai" tana gama faษ—in haka ta juya tayi cikin gida tana share hawaye. Kallon Abba yayi zai yi magana, saurin taran numfashinsa Abba yayi yace "jeka kawai karka damu ka kula sosai".
Juyawa yayi ya shiga Motorn yanawa Abban nasa murmushi har motor nasu ya ษ“ace suka ษ—au hanyan ๐™Œ๐˜ผ๐™๐˜ผ๐™ ๐˜ผ๐™„๐™๐™‹๐™Š๐™๐™ dake babban birnin ๐˜ฟ๐™Š๐™ƒ๐˜ผ.
Sun ษ—au awanni shida suna tafiya kasancewan Masarautar Qubaish babban gari ne sosai sannan kuma Doha akwai nisa tsakani. Sun isa ya samu tuntuni Mai martaba ya sa an kammala masa komai na issuen tafiya sai dai kawai ya jira washe gari jirginsu ya ษ—aga, har ษ—akin da zai kwana dogarin ya masa jagora ya kaisa a wani babban hotel na masu hannu da shuni kusa da airport ษ—in, sallama suka yi da dogarin ya masa fatan dawowa lafiya ya juya dan komawa Masarauta.

Tafiyansu sai washe gari 7am dan haka ganin kwai sauran lokaci wayan sa ya jawo dan dudduba abubuwan da Ya kamata ya sani game da qasan da zashi, bayan wasu lokuta tashuwa yayi yai sallah sannan yaci abincin da aka shigo masa dashi ba jimawa y wasta ruwa ya bi lafiyan gado ya kwanta sai dai ya kasa bacci sai juyi kawai yake, kewan ummansa ya fara tun yanxu ( niko nace faษ—a gaskiya Umma ko Gimbiya? ) Lol.


bayan tafiyan sa Abba da kansa ya haษ—a maganin da kuma rubutun da yace zai yi ya tura gidan sarki kaman yacce ya faษ—awa yaron nasa zae tura musu, ko da ษ—an saqon yaje hannu bibbiyu sarki ya amshe sa sannn ya haษ—a masa da tukuici.






WASHE GARI wanda yayi dai-dai da ranan juma'a qarfe 7am jirgin su ya ษ—aga sai qasar NIGERIA (qasarmu ta gado).๐Ÿ›ซ
Lokacin sa na farko kenan da yahau jirgi amma ba mai kallonsa yace hakan, idanuwan sa a lumshe suke yanajin wani nistuwa na ziyartan sa wanda baisan dalilin sa ba. Bayan wasu awanni Jirgin su ya sauqa Lafiya a airport ษ—in dake babban birnin ABUJA NIGERIA.



Hamdala yayi ganin kansa a qasan da bai taษ“a mafarkin zuwa ba, da bismillah ษ—auke a bakin sa gami da addu'oee yayi stepping qafan sa dan fita a jirgin yana kallon ko ina da kyau, yanayin yacce mutane kowa ke harkan gaban sa a wajen sai yaji qasan ya burge sa. Wayan sa ya jawo ya duba ganin da sauran tafiya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login