Showing 96001 words to 98220 words out of 98220 words
Chapter 33 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt
liman sallama Abdoul yaja motor, malam liman yana ษaga masu hannu har Motorn nasu ya ษace a layin nasu gaba ษaya.
Juyawa malam liman yayi ya shige gida cike da kewan baqon nasa na kwana ษaya wanda kuma yana tunanin qara haษuwan su wataqil sai kuma a qiyama.
gaisawa Abdoul da Amjad suka yi wanda tun da Amjad ya shiga Motorn yake jin gabansa ya tsananta faษuwa, Abdoul kallon sa yayi sai yace "bros ina muka nufa?" Amjad yace "airport zaka kaini" Abdoul ya kuma kallon da ya kalli hanya yace "haba dai airport ba zaka je gida ka gaida Amarya ba? Am Amaryan ina nufin kakata gaskiya ya kamata kaje ka gaida ta inba dai kayi booking Flight na safe ba".
Amjad yace "nop banyi booking Flight ba yanzu dai in munje zanyi sai na jira, Amarya kuma inka koma kace wani jikanta na gaida ta sai wani lokacin zanzo". Murmushi Abdoul yayi ai tunda ba kayi booking jirgi ba gaskiya daganan sai gida ba wani airport da zamu ai in bankaika gida ba yau ba mai kwata na a hannun masifaffiyar stohuwar nan, kwashe yacce suka yi da Amarya yayi ya faษa wa Amjad yana dariya. Amjad sai da ya Murmusa jin rigiman stohuwar sai dai kuma har yanzun faษuwan gaban sa na yawaita, da Abdoul ya dage ba yacce zai yi qarshe yarda yayi ba dan yaso ba amma bai qudiri aniyan kwana ba yana zuwa ya gaida mutanen gidan su Abdoul ษin zai kawo sa airport ya samu ya shirya komi na tafiyan sa yau ษin nan.
Abdoul ne jin yayi shiru yace "bros ya kayi shiru? Maganan tafiya yau fa kabar sa dan anan kam ba lallai ka samu Flight direct to Qatar ba sai dai ko in zaka hau na Abuja daga can to sai ka samu na Qatar kaga kuma duka long process ne gashi yanzu rana ya fara ka bari kawai anjuma kayi booking anan sannan mijin Ameera ya maka na Qatar ษin in yaso d sassafe ka tafi ko in ansamu na dare sai kabi na Abuja da yamma da dare kuma ka hau na Qatar ษin" Amjad ba yacce ya iya haka ya aminta suka nufi GRA.
Amarya sashen baba qarami ta shiga tana bambami, kai jama'a Allah raba ษan mutum da wahala yo in ba wahala da tangaษi ba ace wai jikanka ya mai da kai birin wasa ai wannan ba ko kaffara uwar sa ke kista masa hmm! Shi uban kuma da yake maloho tangaษaษษe baya iya stawatar wa an mallakesa ni Mairo na shiga uku an raba ni da yara na. Baba qarami da ke zaune a palourn mama hafsatu yana aiki a system nasa kasancewar yau yayan sa na hanya shiyasa bai fita aiki ba, muryan mahaifiyarsu da ya jiyo ne ya sanya shi rufe system ษin ya miqe ya nufa hanyan babban palourn da yasan bazai wuce tana can ba.
Tarar da ita yayi tsaye tana share hawayen da babu shi da gefen hijab nata, baba qarami na isowa har qasa ya durqusa yace "Gwaggo ina kwana antashi lafiya?" Wani kallo Amarya ta masa sai kuma ta fece hanci tace "yanzu ba dan ubanka mijina bane kuma ya rasu bawan na kwance cikin rahamar Ubangiji yo da sai nace dan jakar ubanka, amadu ban kwana ba kuma in mutuwa nake na rashin lafiya ba to ba ruwanka,kullum faษi nake ka riqe azkar da salatin Annabi za ka fi qarfin duk wanni stubbace-stubbace amma dan tsabar lalacewa da tangaษewa yaron nan ba kayi, amadu baka neman albarka" baba qarami dake stungune a qasa ba abinda yake cewa sai "Gwaggo ayi haquri a yafeni".
Mama hafsatu da ke qarasowa palourn ne tace "Alhaji ai ba haquri zaka bada ba tambayan me kayi zaka yi" Amarya kallonta tayi sai tayi qwafa za tayi magana sai baba qarami ya riga ta "ke Hafsa banson rashin hankali".
Amarya tace "a'a karka sona amadu ba laifinta bane ai komai tace kai ka nuna masu ba dai baka neman albarka ba?"
Mama saratu ta qaraso palourn itama tace "Gwaggo Barka da shigowa ki zauna mana". Kallonta itama Amarya tayi sai kawai ta sa kuka "yanzu amadu fistaran da kuke shuka mun kai da matanka har ya kai haka? Wai ni da gidan Yaro na sai ance na zauna da uban wani ya gina masa gidan to banson shishishigi shigilitu, amadu kai dai Allah staremun kai amma mata sun mallake mun kai ai daษi na da Haruna kenan bawan Allah gashi dai mace ษaya gare sa kaman mahaifin sa amma yafi qarfin gidan sa yanzu dan stabar ba mai ganin girmana a gidan nan ace yaranku ma kun hure masu kunne sun fistare qafafunsu sun ษauko baqin halin ku" baba qarami jin haka to yasan tabbas wani abun Abdoul ya mata dan in hayra ce ba mai jin tsakanin su suyi faษan su su shirya acan ba mai ji amma in ta shigo tana faษa tom indai yara ne Abdoul ne ya mata abu ko kuma Autan ta Jamila.
Ajiyan zuciya baba qarami ya sauqe yace Gwaggo kiyi haquri Insha Allah zan ษau mataki kiyi haquri ki zauna, Amarya kujera ta samu ta zauna har da ษaura miqe qafa tace "tunda kana neman albarka har da haษa ni da Allah tom na zauna Allah maka albarka amadu na Allah yasa ka gama da duniya lafiya yanzu dai amadu kaji storon Allah kaji storon haษuwa da shi wai ace ba za ka yiwa yaranka faษa ba ka nuna masu nice uwarka nice na haifeka sai sun kyautata mun nasa maka albarka kamun suma zasu samu kasa musu albarka su gama da duniya lafiya" ayi haquri Gwaggo Insha Allahu za'a gyara.
Ai nasan zaka gyara amadu wai ni zancewa Abdu ya jira ni na ษauko lufaya muje aikin ladan tare amma wannan yaro da farantin goshinsa kaman na uwar sa tunda shina dai kaman hariran matar ubansu tana hure masu kunne tunda ita bata haifa ba ita ta mallake ku duka da kai da uwarsu da su ษin dan kar kuyi albarka, yaron nan ya ja akwalan motar sa ya tafi ya barni tsaye riqe da lufaya kaman mata mai takaba yo Allah na tuba tun ba'a auri uwarsa ba na gama takaba na ja'irin yaro zai dawo ya same ni, du Allah miqo mun ruwa na jiqa maqoshi na duk yaro ya sani surutu maqoshi na kaman zai tsage bani ruwa na yayyafa masa".
Mama hafsatu da ke kusa da fridge miqewa tayi ai Amarya da sauri tace "haramun ni Mairo ban aike ki ษibamun ruwa ba Saratu ฦดar albarka tashi kiban"
Mama Saratu tashuwa tayi ta ษauko ruwan ta bawa baba qarami yasa a cup ya miqawa Amarya ita kuma ta amsa ta kai baki da mugun sauri ta tufar da ruwa ta ษaura hannu a kai tace "amma dai Saratu Allah shiryaki shi kawai zance maki kashe ni za kiyi wannan sanyin ruwan ai kurษa ษaya sai lahira, kinga Hansatu ษiyata ฦดar albarka bani ruwa nasha" mama Hafsatu ta miqo mata ta amsa tasha tayi hamdala.
Kallon baba qarami tayi tace "Amadu kai da matanka ni Mairo ba abinda zance muku sai Allah ya maku albarka Allah yasa kuma yaranku su kula da ku su muku biyayya Allah sa ku gama da duniya lafiya, amma ke Hansatu ki dena mun fistara in ba haka ba kwashe maki albarka zan yi ba naje na jira ja'irin yaron naku da kuka hure wa kunne yau sai ya faษa mun sadakin uwar sa tunda ni zai ษauka birin wasan sa ya tafi ya barni kaman stinkakken silifas" qarisa maganan tayi tana miqewa, baba qarami haquri ya qara bata Mama Hafsatu da Mama Saratu duka suma haqurin suka bata, tayi gaba suka bi bayanta suka nufi hanyan waje dukansu.
Amjad bayan zuciyansa dake stinke wa yanzu kuma da yaga sun shiga anguwan sai yana jin wani irin zafin wuta na bugun sa kaman yana tunkaran wajan da aka hura gunguman wuta haka yake ji, ga faษuwan gaba ga kuma wannan zafin da yake ji yana tunkara.
Abdoul ne ya juya ganin yanayin sa sai yace "brother lafiya kuwa?" Lafiya lau amma Please in bamu kusa iso gidan ba mu juya.
Kallonsa Abdoul ya kuma yi mu juya kuma? Ga gidan nan fa banda waษan can gate ษin da kake gani wancan na gaban shine gidan. Amjad suna qara tunkaran gidan tururin wutan da yake ji na qara daษuwa suna iso qofan gidan kuma kaman an kama masa maqoshi sannan ji yake kaman tsakaninshi da wutan da zafin sa ke damun sa bai wuce taku ษaya ba.
Qofan fitan baba qarami ya buษe ma Amarya ta fito shima ya fito mama Saratu ne ta fito itama Mama Hafsatu kuwa da ke staye a bakin qofan haka kawai sai taki kaman ana juya mata gidan jiri lokaci ษaya ya kamata ha wani kukan jarirai da take ji ya cika mata kunne, dafa qofan sashen nasu tayi ta jefo qafan ta waje. Amarya da ke zuba surutu har yanzu kaman zata ari baki sun iso tsakiyan haraban gidan kenan mai gadi ya wangale gate sakamakon horn na motorn Abdoul da yaji.
Suna shiga cikin gidan tun bai qarisa parking ba Amjad da ya sanya hannunsa a wuyan sa sanadin jin shaqan da aka masa yayi yawa kuma kaman an jefa sa acikin wutan wani wawan qara ya saka wanda ya kusa da Abdoul sakin staring motorn, yana sakin qaran hannun sa a wuyan sa sai ya faษo jikin Abdoul a matacce ba numfashi Ba shiri Abdoul yayi parking.
Wannan qaran ya razana duk wani halitta dake cikin gidan, Amarya da Mama Saratu san da suka kusa sakin fistari a staye duk suka rikice, baba qarami nufan Motorn yayi sai kuma suka kuma jin wani qaran a bayan su da kuma sautin faษuwan mutun, waye za kuma su gani? Mama Hafsatu ce yashe a qasa. Amarya zama tayi dirsham a qasa gaba ษaya ta rikice Mama Saratu kuwa ba'a magana, baba qarami qara juyawa yayi sai ya kuma jin....
Jirgin su Abba yayi landing a tafawa ษalewa airport dake garin Bauchi, Abba waya ya ษaga yayi qira shiru ba'a ษauka ba, ganin haka sai ya tare taxi ya juya dan mawa su Ummey magana suzo su shiga sai kawai yaga Umma ta yanke jiki ta faษi.....
TIRQASHI TASHIN HANKALIN DA BA'A SAKA MASA RANA KENAN!
CAKWAKIYA, SARQAQIYA GAMI DA ฦAUREWAR KAI.
WAI ME KUKE TUNANI?
ME KE FARUWA?
DUK ME YA JAWO WANNAN TASHIN HANKALIN?
ME YAKE FARUWA DA AMJAD?
MENENE YA SAMU MAMA HAFSATU LOKACI ฦAYA?
ME KUMA KE FARUWA DA UMMA?
DUK MENENE HAฦIN WANNAN TASHIN HANKALI DA YA SAME SU LOKACI ฦAYA?
INA LABARIN UMMAN AMJAD?
INA LABARIN GIMBIYA DA MAGANAN AUREN SU DA AMJAD?
ANYA WANNAN NE DALILIN FAฦUWAN GABAN DA KE DAMUN AMJAD?
IN BA WANNAN BA ME ZAI FARU GABA KENAN DALILIN FAฦUWAN GABAN SA?
ANYA MA KUWA AMJAD NA DA RAI?
TAMBAYOYI BARKATAI DAI
SANNAN ANAN NA KAWO QARSHEN FREE PAGE'S DOMIN SAMUN AMSOSHIN WANNAN TAMBAYOYI DA SUKE RANMU DA KUMA KUNCEWAR WAฦANNAN RIKITATTUN AL'AMARIN KUYI HANZARI KU BIYA NAIRA โฆ300 KACAL DAN ACI GABA DA LABARI DA KU.
NORMAL PAYMENT GA WAฦANDA KE GROUP ALREADY โฆ300
GA WAฦANDA BASA GROUP โฆ400
GA MASU BUQATAN COMPLETE PAGE'S โฆ500
V.I.P COMPLETE DOCUMENT โฆ500 ONLY
TA WANNAN ACCOUNT
๐
2220553988
HARIRA SALIHU ISAH
UBA BANK ๐ฆ
KO KATIN WAYA TA WANNAN LAYIN
09161720046 MTN
07015870735 AIRTEL
SANNAN ZAKU TURO SHEDAR BIYA TA WANNAN LAYI A WHATSAPP 09161720046
Ina mai qara baku haquri waษanda tun farkon littafi suka biya sannan ina da babban garaษasa gareku a next book namu da kuma baku zaษi akan labarin da kuke so mu fara.
ฦณan uwa abokan arziqi masu daraja gaisuwa gare ku Ako da yaushe kuma ako ina kuke a faษin duniyan nan daga taku har kullum mai nishaษantar daku HARIRA SALIHU ISAH (UWAR BATOORL)
MARUBUCIYAR ๐ฅ ๐๐๐
๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐ฅ
YANZU KUMA ๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐ ๐
Sannan da labarai daษaษa da na tanadar domin ku da nishaษin ku.
Kar ku manta sunan labarin da muke ciki ๐ฦณAR SARKI CE ๐ DAGA DAUSAYIN ALQALAMIN UWAR BATOORL ๐ฅ
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
๐ฟ๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ ๐ช, ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ก๐๐ฎuka:-
09161720046
๐พ๐๐๐ฉ ๐ค๐ฃ๐ก๐ฎ.
07015870735
๐๐ค๐ช ๐๐๐ฃ ๐๐๐ก๐ก ๐๐๐จ ๐ค๐ฃ๐, ๐ญ๐๐ข๐ช ๐ข๐๐ ๐ช ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ง๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐
NOTED : karku nemeni a wannan layi 08146292652 domin yanzu baya aiki both whatsapp and call.
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐
ALHAMDULILLAHI ALA KULLI HALIN
Anan na kawo qarshen BOOK 1 Wand yake a FREE BOOK
Masu buqatan ci-gaba BOOK 2 ๐'YAR SARKI CE๐
Sai subi process da nayi magana ko su mun magana via WhatsApp number na
09161720046
Masu comments wasu bana samun yin reply afuwan abubuwan sai a hankali
Fatan alkairi a gare ku daga uwar batoorl taku
Sai mun haษu da ku a book 2 fan's