Showing 60001 words to 63000 words out of 98220 words
Chapter 21 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt
tayi gaba dan zuwa sashen mahaifiyar ta.
Umman Amjad da Abban sa kewan yaronsu suke sosai ba ษan kaษan ba Umma har da ษan ramewanta
Suna zaune akayi sallama, jin anfara shigowa gidan sai Abba yace a qariso.
Ahmad abokin Amjad ne ya shigo sannu da zuwa Umma ta masa ya durqusa har qasa ya gaida Abba da Umma duk suka amsa da fara'a, Umma Amjad yana nan ne?
Abba yace "Amjad dai? Baku haษu bane kan ya tafi ko bakasan zai yi tafiya ba?
Abba ban sani ba gaskiya jeji ya shiga ne ko Doha?
Murmushi Umma tayi yarona Ahmad wani jeji qasan gaba ษaya ya bari fa baka da labari kenan ya tafi wani qasa acan wai Nigeria aka ce mata nake ga.
Buษe baki kawai Ahmad yayi amma dai ba muyi hiran zai yi tafiya ba har na barin qasa ko da yake ma bamu cika haษuwa ba, yanzu dai Umma a taimaka mun da layin sa da kuke waya.
"Amadu Ni da Umman taku duka wayan jagwal ne sai a hankali kawai" Abba ya faษa yana murmushi,. Tom Abba amma mai yaje yi?
Umma tace "wannan yaron nawa sai a hankali wani irin abota kuke haka ni mairo wai bai faษa maka abinda ya faru bane?"
Umma bai faษamun wani abu ba gaskiya kinsan sa da rashin son magana bare dogon hira, taษa baki Umma tayi to Allah ya shiryamun shi, Nan ta kwashe labarin duk abinda ya faru ta faษa masa.
Kama taษa Ahmad yayi ya gyara zama "wato dai ranan abun da ya kaisa gidan sarki kenan shine bai faษamun ba shine har da kishi kar na rakasa" abinda ya gama faษa a zuciyan sa kenan kamun yace "to Umma Allah sanya alkhaeryh Allah basa Sa'a ya dawo dashi lafiya, dama zan koma ne inshร Allahu zan dawo nima in lokacin bikin yayi"
Ameen ya Rabbi yarona kaima Allah kaika lafiya Allah nuna mana lokacin da rai da lafiya
Miqewa yayi yace "Abba Umma sai wani lokacin" ya faษa yana yin hanyan fita, da addu'an Allah kiyaye hanya Umma da Abba suka bishi har ya fice.
Umma ta juyo ta kalli Abba murmushi tayi tace "wannan yaro naka Allah ya shirya sa wai dan ma abokin sa ne".
Sai bayan magrib Ameerah suka koma asibitin
Sun same sa a kan darduma, jikin sa da sauqi
likitan ne ya shigo yace "Insha Allah gobe zai sallamesu in yaso su qarisa jinyan qafan a gida ko nan da sati 1 zuwa 2 ne kamun ya warke sosai dan qafan ne kawai yanzu damuwa amma b abinda yake damun sa"
Godiya Daddyn Little yai wa abokin nasa yace "Allah kai mu goben frnd".
Da Ameen likitan ya amsa kamun ya fice a ษakin
Gaisawa suka yi duka da mara lafiyan suka masa ya jiki ya amsa da sauqi.
Har aka yi sallan isha'i suna can, sai da lokacin ya ษan tafi ganin dare nayi suka masa sallama
Suka kamo hanyan gida.
Sai da suka yi sallan isha'i kowa ya taษa hutu kamun suka tafi sashen kawun nasu wanda suke qira da baba qarami suka gaidashi da matan sa suka dawo kowa ya wuce dan ya kwanta don gajiyan bai tafi ba.
Soja ne yake ta laluษa wayan sa amma shiru babu wayan ba labarin waya, fitowa yayi yaje ya duba har cikin motor nan ma babu waya, abun da ya faru ษazu a hanya ne ya faษo masa a rai tabbas ba ko kokonto yarinyar nan ce ta ษau wayan nan.
Juyawa yayi ya koma ciki ransa a ษace yayi hanyan ษakin da yake na su Maha, da ya Abdoul ya haษu yana zaune a palourn Kakus yana danna waya
Ganin Soja sai ya Abdoul ya tsayar dashi yace "our able army sai ina haka? Ya Abdoul ษakin su Mahreen zan karษo wayana
Ya Abdoul yace okay plss a turomun Mahreen ษin tazo ina dinning area
Tom ya Abdoul.
Sallama yayi a qofan dakin nasu, Mahreen ce ta amsa ya Habeeby ka shigo
Shiga yayi ya bata saqon qiran da ya Abdoul ke mata, himar ta jawo ta saka ta wuce dan amsa kiran da ake mata.
Bayan fitan ta in da Mahreen ke kwance tayi ษaษษaya ya nufa, yana zuwa wajan ba jinkiri kawai ya jawo ta qasa ji kake timmmmm!
Kaman a mafarki ta ji an buga ta da qasa ihu ta saka 'Wayyo Mutum ko Aljan na shigesu za'a karya"
Cewa yayi "qanin ubanki ne zaki tashi ne ko sai nayi ball dake? wai ke ina wasa dake ne kam da har zaki ษauki wayana? Kin tashi kin ban wayana ne ko sai na harbe ki idiot kawai
Jin muryan sa kuma tasan halin sa tashuwa tayi a hankali tana hawaye dan tabbas ta bugu
ฦauko wayan tayi ta basa tana Allah ya isa kuma sai Allah ya saka mun.
Sarai yaji me tace amma sai ya basar heษe ransa yayi yace "ke me kika ce?
Tura baki tayi ni ba abinda nace
Qwafa yayi ya duba wayan yaga chajin shi bai ko sauqa ba alaman bata yi komi dashi ba kawai neman magana ne, tsaki yaja "Ni na rasa mai yasa bansa security a wayan nan ba" da ya gama seta mata zama yai hanyan waje dan ya koma ษakin sa.
Bayahn fitowan Mahreen wajan zama ya abdoul ya nuna mata ya mata umurni da ta zauna dan samun su tattauna
Bayani yake ta koro mata daki-daki na yacce yai kewansu sun jima basu zo Bauchi ba
Sai da ya tabbatar ta sake dashi suna hiran kamun ya numfasa a yanayi na muhimmin magana ya dube ta yace "qanwata ki aramun duka hankalinki anan zamu yi magana mai muhimmanci kinji"
kallon sa tayi da murmushi tace "yayana in da qarin hankalin ma duka na ara maka ina sauraranka"
Nan ya kwashe duk abinda ke xuciyan sa abinda yake ji game da ita tun da ya ganta ya faษa mata(hausawa suka ce abari ya huce shi ke kawo rabon wani).
Qanwa ta ina sonki so kuma na gaske son Aure wanda in son samu ne ayi bikin nan cikin wata 1 kai yamun nisa ma irin dai week hakan nan
Tun da ya Abdoul ya fara jawabi tayi qasa da kanta ta ษoye fuska a hijab da ya kai aya ya buqaci da ta ษago ta basa amsa taqi ganin ya masta ko takan wayan ta dake hannun sa bata bi ba tayi hanyan ษaki har da ษan gudun ta
Dede tana shigowa ษakin shi kuma Soja zai fice a ษakin kenan suka kusa yin karo
Ransa a ษace amma ganin Mahreen tsayawa yayi ya dara yace "yarinya ta kamu kenan taga handsome yayana*
Wucewa tayi tana rufe fuska bata ce komi ba.
Duk abunda ke faruwa kuwa Hajiya kakus ta fito ษaukan abun gurza goronta data bari a palourn sai ta tarar da draman da ake yi
Ganin duka jikokin nata na son junansu abun ba qaramin daษi ya mata ba( a tunanin ta Soja ma hira yaje) haka taje ta kwanta da farinciki.
Ya Abdoul ganin ta gudu sai abun ya burge sa ya kuma qara masa qaunan ta "tabbas inason mace mai kunya" abun da ya faษa ya miqe yana murmushi
Soja yace "yayana Allah kaimu musha biki"
Ya Abdoul da farinciki Yace "Ameeรฑ our able army"
Dariya soja ya kuma yi ya wuce wajan baccinsa, shima ya Abdoul fice wa yayi ya nufi nasa wajan baccin a sashin su, wanda yake dama da soja ne amma yace a sashen kakus zai kwana.
Ya Abdoul ko da ya koma ษakin sa haka ya kwanta yana ta juye-juye shi dai har ga Allah yake son qanwar tasa kuma bai qi a ษaura masu aure ko yanzu ba.
(haba malam abdu daga uhmn sai ehem ko a hand kake ne?
Kunga inko a hand yake ya hwaษan nice ourmman batoolerh mai wuqa da nama sai nasa a aura masa ita yanzu)
ko ba haka ba FAN'S ?
Mahreen na shiga ษaki ta samu Maha na sharar kwalla sai tace "menene ya sameki ko wani abun ya habeeby ya maki?
Maha kaman zata rufe addan nata da duka tace "Idon matambayi ne ya sameni, ba habeeby ba habibu mutum sai son jin gulma"
Kallonta Mahreen tayi tai murmushi ita dai tana farinciki bata da time na surutu da Maha
"Allah shiryaki" shine abinda tace tayi kwanciyan ta tana ta murmushi ita dai tana ji kaman ta jita a jikin yayan nata.
Mutumiyar kuwa Allah ya isa take jawa soja yafi cikin girgi.
Autan Umma yana komawa ษaki kwanciya kawai yayi ko ta kan wayan bai bi ba ransa fess ya fara maganin renin yarinyar nan.....
Masha Allah jama'a sahiyar alkhaery
Mu dai mun riga mun tashi๐ฏ sai kuma inda qarfi ya qareโ๏ธ
Muje zuwa
Masoyan ๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐
๐ฟ๐ผ๐๐ผ ๐๐ผ๐๐๐ผ๐ ๐ผ๐๐๐ผ๐๐ผ๐๐๐
๐
๐๐ผ๐๐๐๐ผ๐๐๐๐ผ ๐๐๐ผ๐ ๐ฝ๐ผ๐๐๐๐๐
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
๐ฟ๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ ๐ช, ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ก๐๐ฎuka:-
08146292652
๐พ๐๐๐ฉ ๐ค๐ฃ๐ก๐ฎ.
09161720046
๐๐ค๐ช ๐๐๐ฃ ๐๐๐ก๐ก ๐๐๐จ ๐ค๐ฃ๐, ๐ญ๐๐ข๐ช ๐ข๐๐ ๐ช ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ง๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐๐ฉ๐ค๐ง๐ฎ ๐ผ๐ฃ๐ ๐๐ง๐๐ฉ๐ฉ๐๐ฃ
๐ฝ๐ฎ
๐๐๐ง๐๐ง๐ ๐จ๐๐ก๐๐๐ช ๐๐จ๐
(๐๐ฌ๐๐ง batoorl)
ุงูููู
ุตูู ู ุณูู
ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู saw๐ค๐ค
_______________________________________________________________
๐
ฟ๏ธ 45&46
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
Kasancewan yau Sunday ba aiki da sassafe Ameerah ya haษa kayan karyawa suka shirya suka nufi asibiti.
Isan su asibitin direct wajan abokin nasa ya nufa ita kuma Ameera tayi ษakin da mara lafiyan nasu yake
Da sallama ta shiga ษakin ya amsa mata
Wajan gadon taje ta zauna kamun ta gaida shi
Yaya na fatan ka tashi lafiya ya qarfin jiki?
Lafiya Alhmdlh jiki da sauqi sosai
Masha Allah haka muke so yayana Allah qara afuwa
Ya amsa da Ameen daga haka bai qara cewa komi ba Ganin haka itama bata ce uffan ba
Suna zaune shiru Daddyn Little yayi sallama ya shigo
Amsawa suka yi a tare ita da mara lafiyan
Gaisawa suka yi da Daddyn Little ya masa ya jiki? Yace "da sauqi sosai"
Ameerah ce tace "husby har ka karษo mana Sallaman?
A'a wiffey ban same shi ba kinsan yau Sunday ba lallai yazo da wuri ba ga kuma munyi sammako
Tace "Tom shikkenan sai kazo nasa maku abun karyawa"
Sauqa tayi ta shumfiษa masu babban darduma ta jawo kondon kayan karin ta zuba masu peppe chicken da chip's sai soyayyen kwai ta haษa masu tea kowa da cup na sa.
Yayana ka sauqo ku karya ko
Ba musu ya sauqo a gadon suka zauna tare shi da Daddyn Little kowa ya ษau spoon
Chips en yaci kaษan sai kuma peppe chicken, a jiye cokali yayi ya ษau cup na tea yana kurษa
Daddyn Little ne yaci abinci sosai da ya gama ya ษau tea shima
Suna gamawa ta masto ta tattara wajan sannan ta koma ta zauna
Bayan wasu lokuta Daddyn Little barin danna wayansa yayi ya maida aljihu, miqewa yayi yace "ba na koma wajan likitan nan ko ya zo" Ameera ta amsa adawo lafiya to
Office na likitan ya nufa cikin sa'a kuwa dai-dai isan sa qofan office ษin lokacin likitan ke isowa shima, da murmushi suka kalli juna Daddyn Little yace "kai man wanne irin likita ne kai haka ka tsaya soyayya kabar mu a asibiti tun qiran asuban farko".
Dariya ya saka wato dai freind sammako kuka yi gaskiya sannu da qoqari Nikam inacan manne da matata sai yanzu aka barni na fito
"ฦan iska Zaka ji dashi ai Nikam buษe mana qofa mu shige" Daddyn Little ya faษa yana dariya
Tare suka shiga office ษin da sallama, likita ya zauna a wajan zaman sa shi kuma ya nema wajan zama ya zauna
Gaisawa suka yi suka ษan taษa hira kamun Daddyn Little yace "kaga frnd sallame ni nasan zaka je duba Patience's naka so kar na ษata maka lokaci a sallamemu mukam.
sallama ya rubuta masu sannan da sauran magungunan da ake buqata na game da qafan nasa
bayani ya masa yacce za'a sha da na shafawa duka sannan ya kamata ya kai sati a gida kamun ace ya fara fita sai dai yana da kyau ya dinga mosta qafan yana ษan takawa dan zai fi saurin warke wa ko bai cika sati cif ba
Daddyn little yace "bakomi doctor Insha Allah za'a kiyaye fitansa yanzun fatan mu dai Allah sa ya warke da wurin
Musabaha suka yi ya kuma yiwa abokin nasa godiya yai masa sallama ya fice a office ษin
Wucewa pharmacy dake cikin asibitin yayi dan ya sayo maganin da aka rubuta a hanya ya haษu da Abba ya shigo qara duba marar lafiya kamun ya wuce don jiya bai samu komawa ba.
Tare suka je pharmacyn aka basu maganin duka da suka je wajan cashier Abbane ya biyan kuษin duka yace Daddyn Little ya bari
Suna gama biya suka koma ciki wajan su Ameerah
Gaishe da Abba yayi suna tafiyan sannan ya masa godiya Allah qara arziqi Abba l
Ameera ganin Abba sai taji daษi sunkuyawa tayi ta gaida Abban nata ya amsa da fara'a yace "sannunku da qoqari mamana"
Gaisawa suka yi da mara lafiyan
Ya masa ya jiki? amsawa yayi da sauqi Alhaji
Umma ya qira bayan sun gaisa sai ya bawa Ameerah wayan
Karษa tayi ta gaisa da Umman, tambayanta mai jiki tayi tace "da sauqi sosai har an sallamemu"
Umma tace ta basa wayan su gaisa
miqa masa tayi "yaya na ga Umma ku gaisa"
Amsan wayan yayi ya kara a kunnen sa, lumshe ido yayi bayan Jin sallaman Umman Ameera
Bai san meyasa ba jin muryan wannan baiwar Allahn na rage masa kewan Umman sa.
Gaisawa suka yi tace masa "yanzu ya jikin naka yaro na?
ya amsa da sauqi Alhamdulillahi
Addu'oee tai masa sosai wanda yasa shi Jin daษi fin tunani gaba ษaya sai yake jin kamar Ummansa ce.
"Ameen ya Hayyu ya Qayyum Nagode sosai Umma Allah saka da alheri"
Suka yi sallama ya miqawa Ameerah wayan
Sallama itama suka yi tace" ga shinan Umma ba na miqa masa"
Daddyn Little ta miqawa wayan tayi amsa yayi suka gaisa da surkar tasa
yace "Umma bakomi Allah qara girma mungode sosai"
Ya miqawa Abba wayan bayan sunyi sallama
Abba kara wayan yayi a kunne ya fita a ษakin.
Ameera tattara komi da suka zo dashi asibitin tayi Daddyn Little na taya ta yana kwashewa ya kai masu motor
Bayan sun kai komai motor Taimaka wa mara lafiyan yayi yana ษingisawa har suka isa in da motorn nasu yake Parke, suna isa yabuษe masa murfin back seat ya shiga ya zauna.
Sallama suka yi da Abba, escorts nasa suka tada motor sae filin jirgin dake garin Abuja
Gaba Ameerah ta shiga Daddyn Little ya shige mazaunin driver ya jasu sai gida
Hira suke sama-sama a motorn suna sako sa shi kuwa yayi nisa a tunaninsa baya amsawa hiran nasu ma (dama shiba ma'abocin surutu bane).
Driving yake a hankali
Juyowa yayi ya tambayesa bro akwai abunda kake buqata mu tsaya mu saya kamun mu wuce gida?
Girgiza kai kawai yayi bai ce komi ba
Ameerah ce tace "husby ka tsaya musai koda fruits ne to"
Tsayawa suka yi suka saya da yawa kaman masu sari, aka sa masu a boot en motorn suka biya suka qarisa gida
Suna isa mai gadi ya buษe masu qofan yana ranka ya daษe sannunku da dawowa amsa masa yayi
Parking space ya isa yai parking motorn
ฦakin da suka shirya already don shi a balconyn gidan Daddyn little ya temaka masa ya kaisa har ษakin
ฦakine madedeci mai ษauke da duk wani abunda mutum zai buqata a ษaki
Gado,walldrop,resting chair,mirrow,