Showing 21001 words to 24000 words out of 98220 words

maqale jikin kakar tasa.
Qarfe 4:00pm na rana yai masu a ๐™†๐˜ผ๐˜ฟ๐™๐™‰๐˜ผ ๐™Ž๐™๐˜ผ๐™๐™€ ๐˜ผ๐™„๐™๐™‹๐™Š๐™๐™.
dai-dai lokacin jirgin su yai landing a Nigeria cikin babban birnin Kaduna.
Sauqo wa mutane ke yi daga jirgin da yayi landing ษ—in ษ—aya bayan ษ—aya
Leqa wa kawai Umma da Ameera keyi su ga ta inda ษ—an autan nata zai fito, ita kuwa tilon qanin ta wanda bata da kaman shi a duniyar nan.
Wowww!! Shi ne abun da na furta kawai, Wani kyakkyawan saurayi ne kyakkyawa ajin qarshe. Sanye yake da T-shirt na sojoji da kuma army green jeans. fari ne amman ba sosai har can ba, kyakkyawa ne na qin daษ—awa jikin sa ya nuna Jarumtan sa kana ganin sa kaga Soja don a dire jikinsa yake kana ganinsa za kai tsammanin ya kai shekara 30 aduniya(abunku da girman falo)
Ai kuwa Ameera na ษ—aura idon ta a kansa da gudu ta je ta rungume sa ayoyo bruh, murmushi yayi!! sisto ฦดammatan Daddyn Little ayoyo too, minstinin shi ta yi kaifa ka renani matsala na da kai. Turo baki yayi ya wuce wajan umma, Wayyoo ummana!!!! Dariya dukkan su suka saka "Allah shirya ka ๐™ƒ๐˜ผ๐˜ฝ๐™€๐™€๐˜ฝ" faษ—in Abba. Da Ameen ya amsa yana hugging Abban nasa da Daddyn Little en. Ya je ya faษ—a jikin Umman sa, ta ce "ah ah tashi ni kar ka karya ni a gaban nasii" Dariya yayi Umma kina so amun dariya ko? Amsan Little yayi a hanun ta yana "Umma ta bani yaro na, my Big broh ya akayi? Washe baki Little yayi unkui fafiya. Dariya yayi suka nufi motor dukan su driver ya ja suka yi gida.
Daษ—i a wajan waษ—an nan iyalin ba ya misaltu wa don ganin sojan nasu.....




Kar mu shagala fan's sunan littafin namu "๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€" daga Alqalamin Uwar Batoorl ๐Ÿ”ฅ


๐™ˆ๐™š ๐™ข๐™–๐™ž ๐™ข๐™–๐™ง๐™ฉ๐™–๐™—๐™– ๐™ ๐™š ๐™ฃ๐™ช๐™›๐™ž?
๐™†๐™ฎ๐™–๐™ช๐™ฉ๐™– ๐™ฏ๐™–๐™ž ๐™ฎ๐™ž ๐™™๐™– ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ๐™ˆ๐™š๐™๐™ฌ๐™ž๐™จ๐™ ๐™ ๐™ค ๐™ ๐™ช๐™ฌ๐™–?
๐™ˆ๐™š ๐˜ผ๐™ข๐™Ÿ๐™–๐™™ ๐™ฎ๐™–๐™ฎ๐™ž ๐™ž๐™™๐™ค ๐™—๐™ž๐™ฎ๐™ช ๐™™๐™– ๐™จ๐™๐™ž ๐™Ÿ๐™ช๐™ฎ๐™–๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™จ๐™–?
๐™๐™–๐™ง๐™ž๐™ฃ ๐™˜๐™ž๐™ ๐™ž๐™ฃ ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™–๐™๐™–๐™ก๐™ž ๐™ฃ๐™– ๐™œ๐™–๐™ฃ๐™ž๐™ฃ ๐™จ๐™ค๐™Ÿ๐™–๐™ฃ ๐™ฃ๐™–๐™จ๐™ช ๐™ข๐™–๐™ž ษ—๐™–๐™ช๐™ง๐™š ๐™ฌ๐™– ๐™ฃ๐™š ๐™ ๐™ช๐™ฌ๐™–?
๐˜ผ๐™ช๐™ง๐™š๐™ฃ ๐™œ๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™–๐™ฃ ๐™ฏ๐™š ๐™ฎ๐™ช๐™ฌ๐™ช ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™™๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฉ๐™– ๐™—๐™ž๐™ฎ๐™–๐™ง ๐™ ๐™ช๐™ฌ๐™–?
Muna da tambayoyi da yawa waษ—an da duka amsoshi su abun samu ne in muna bibiyan wannan labari


Muje zuwa fan's


Ku nishaษ—antu, ku faษ—akantu, ku wa'azantu, sannan ku dara๐Ÿคฃ daga alqalamin uwar batoorl takuuuuuuu ako da yaushe
Fatan alheri agare ku masoya alqalamin uwar batoorl a ko ina kuke a faษ—in duniyar nan....




๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎ๐™ช๐™ ๐™–:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž,


# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š


๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ
๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€
๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ


๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–


(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorlโœ๐Ÿ”ฅ)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค


_______________________________________________________________






๐Ÿ…ฟ๏ธ 27&28




๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹












Mai martaba ne ya tashi ya fara jawabi kamar
"Da farko ina mai bawa ษ—auka cin jama'a haquri da abinda ya kasance. Sannan baqin mu yaran Sarakuna na nesa da na kusa ina mai baku haquri, da abubuwan da suka faru. Nima banji daษ—in yacce abubuwan suka kasance ba amma ina matuqar baku haquri da kuma maku fatan alkhaeri, Allah sanya hakan ne alkhaeri a gareku duka. Daman ita matar mutum kabarinsa, kuma kowa rabon sa yake aura. Insha Allahu zaku samu rabon ku na alkhaery wa ษ—anda suka fi Mehwish!! Ina mai maku fatan komawa Masarautan ku lafiya kaman yacce kuka zo lafiya. Sannan ina mai baku haquri akan duk abinda aka muku a Masarauta ba dai-dai ba. Kuma ina mai qara gayyatan ku auren Gimbiya Mehwish wanda za'a yi nan da wata biyar 5 masu zuwa Insha Allah. In dai hakan bai zama ba dai-dai a gareku ba! Nagode sosai sosai ma'assalam".
Mai shela ne ya amsa abun magana ya qara bawa yaran sarakuna haquri sannan kuma da ban gajiya, ya nawa ษ—auka cin jama'ar gari ma ban gajiya, "Allah ja kwanan mai martaba zai gaya mana yacce gasan mu na gaba zai kasance" ya faษ—a ya qara bawa sarki Miche ษ—in.
Amsa sarki yayi yace "Ni Sarki ๐™Œ๐˜ผ๐™Ž๐™€๐™€๐™ˆ na saka gasa kuma gara ษ“asa ga duk wanda ya lashe gasan. Insha Allahu shi ne mijin Gimbiya nan da wata 5!! In dai zaka iya kar kayi tunanin ko kai wani abun daban ne, kawai ko ma waye zai iya shiga gasan nan ina ma kowa da kowa fatan alkhaeri.
Gasan bai sanja ba sai dai abun da ya qaru na abinda mutum zai samu in ya lashe gasan. Duk wanda yayi nasaran buษ—e fuskan Gimbiya Mehwish a karo na biyu, auren su da ita nan da wata biyar kuma zan basa dukiya mai tarin yawa, Sannan zaka faษ—i duk abinda kake so Masarauta kuma zata maka Insha Allahu in bai fi qarfin mu ba. Koma waye kai, a qasar nan kake, a garin nan kake, ko kuwa ba'a garin nan kake ba duka ba damuwa Masarauta na maraba da kai.
Sannan Ina son gasan ya kasance nan da wata 1 mai zuwa da yardan Allah, duk wanda zai iya qofa a buษ—e yake".
Bayan Mai martaba ya gama jawabin nasa ya tashi, shi da jama'an fada suka hau dawakai Sarki da waziri da sauran jama'an fadan sarki aka nufi fada, yayin da sauran kuma manya manyan ฦดan kasuwa da saura masu abun hawa suka hau kowa ya kama hanyan sa.
Nan dai taron ya watse da ihu!! ya wanci da sunan Gimbiya a bakin su suka tafi, don kuwa ta nuna Jarumta maza manya jarumai har sha biyu 12 ba wasa ba.
Yayin da a gefe ษ—aya kuwa wasun su duk yawanci jikin su yayi sanyi, wanda abun da ya haddasa wannan sanyin da jikin nasu yayi ba komai bane face jin abun da mai martaba Sarki Qaseem yace na kuma yin wani gasan. gasan da sun san ba lallai bane ya faru, ko inma ya faru ba lallai wani ya cinye gasan ba. Dan suna ganin tun da waษ—an nan jaruman yaran Sarakunan ba wanda yaci gasa a cikin su bare Kuma wani daban a gefe.
Gasan ne suke tunanin ba mai ci amma tabbas sun san Mai martaba Sarki-Qaseem zai bada fiye da abun da ya faษ—a. domin kuwa shi ษ—in adalin shugaba ne wanda babu irin shi ba iya nahiyar su ba har ma wasu nahiyoyin.
Sarki Qaseem mutum ne wanda baya ษ—aukan kan sa shi Sarki ne, yace dan haka yana daban da sauran talakawan sa. Yacce yake haka yake ganin kowa ma yake, Sarki ne mai qaunar talakawan sa da kuma ษ—aukacin jama'ar garin nasa, adalin shugaba wanda samun irin sa a yanzu akwai matuqar wahala, duk da kasancewan ฦดa ษ—aya tilo Allah ya basa amma bai zama mai fifita ta akan cewa ita ษ—aya ba, shi uba na gari ne kuma shugaba na gari, shi a wajansa sarauta ta Ubangiji ne ba amfanin zaluntar wani dan mulki ma tabbata zaiyi ba..
Duk abunda ake yi daga Umman Amjad har Abbansa suna cikin masu kallo a wajan taron, sannan duk abinda akayi sun gani. Sai dai su suna ษ“angaren masu yabawa bajinta irin na Gimbiya Mehwish.
Waste wa ake a wannan taron kowa da abunda yake furtawa albarkacin bakinsa. Kowa ya kama hanyan komawa gidansa.
Umma da Abba ke tafiya suna fira, Umma ce tace "Abban jarumin Umma kasan me?" A'a Maryama ta sai kin faษ—a. Umma tace "wallahi wannan yarinyar MEHWISH burgeni take yi sosai sosai inason mutum haka". Murmushi Abba yayi! Yace "ai dai kam abar burgewa ce ita dan kuwa tana da qoqari sosai fa Allah dai yamata albarka ya bata miji na gari". Da Ameen Umma ta amsa. Suka ci gaba da tafiyan su suna hiran su....


^^^ Gimbiya Mehwish ko isansu fada, shigan ta gida ษ—akin ta tayi direct ko takan kuyangun ta bata bi ba. Tana shiga haษ—aษ—ษ—en ษ—akin nata kan faffaษ—an gadon ta taiwa kanta masauqi. Rub da ciki ta kwanta. tunani take "menene ke shirin faruwa da Ni haka? kaman wanda ake xuga mai martaba akai naa mai nayi haka? Papa kyauta zai yi dani ko me?"
Lumshe ido tayi!! Tabbas wannan karon komi zai iya faruwa. Ga shi bata san wa mai martaba zai haษ—ata dashi ba kuma bata san mai sharaษ—in nasa ba.
Amma nufinsa tasan tabbas tayi aure ne ba komai ba.
Sanda ta gama juyin ta akan gadon nata ta tashi ta shige bathroom. Wasta ruwa tayi ta futo, duk da yanayin da ake na zafi hakan bai hanata shiryawa tsaff cikin dogon riganta. ( masha allah!! hurul eyn)
Ko abakin alqalami faษ—an irin kyawun da Allah yaiwa Gimbiya Mehwish ba mae yiwuwa bane. qoqartawa nike nake tara jarumta ran da muka ga fuskanta mu faษ—i ko kaso 2 ne acikin 100 na kyawun wannan halittar kudai ku qirata "hurul eyn"

Wajan mahaifiyarta ta nufa bayan ta fito ษ—akin nata, da kuyangun ta har ta isa qofar sashen kamun ta shiga su kuma suka juya.
Da sallama ta shiga ษ—akin da Ammaahn nata take, ba'a amsa mata sallaman ba sakamakon jikin mahaifiyar tata da har yanxu sai a hankali kawai!! Kwantawa tayi gefen ta ko zata samu nistuwa dan sosai take jin wani iri a zuciyar ta ga halin da mahaifiyar ta ke ciki ga abubuwan da suka mata yawa a kai, bata da wanda zata faษ—awa damuwan ta! Ko kukan ta!! Ammaaahn ta kaษ—ai gare ta kuma bata da ko lafiyan amsa mata sallama barai tayi lafiyan rarrashin ta!! a haka bacci yayi gaba da ita.


(Allah sarki uwa da ฦดa, wani abu se soyayyyan uwa da ฦดarta
Allah ka sakawa iyayenmu da aljannah
Allah kabamu yara masu albarka dason mu da tausayin mu Alfarman Annabi SAW ).




KADUNA


^^^ Tafiya suke a motorn suna hira, Ameera na zolayan Soja jefi jefi Umma da Abba na sa musu baki. Little kuwa yana maqale jikin soja tunda ya ษ—auke sa yaqi yarda sauqa jikin sa. Wani wawan birki drivern nasu ya ja ji kake qiiiiiiiiiiiiiiii!!! Ameera ce ta sanya salati "innalillahi wa inna ilaihirraji'un!! Dan Allah bamu shirya mutuwa ba kabi a hankali." Soja ne yace "wai wani driver ne Abba kuka ษ—auka kam? So kake ka kashemu? Can't you drive good? Mtswwwww!!" Qara qanqame sa Little yayi dan shima ya razana! Abba ne yayi gyaran murya, duk sai suka yi shiru. Ka kula da hanya ku kuma banson surutu okay. Drivern ne yace sorry sir mai mashine ษ—in ne ya shigo bai duba hanun sa ba. Okay just becareful with what ur'e doing, okay Sir. Motorn sai yayi shiru har suka isa anguwan GRA horn drivern yayi, mai gadi ya buษ—e suka shige. Bayan yayi parking duk suka sauqa sukayi cikin gida.
Suna shiga side nasa yayi da already yake a gyare, har yanzu Little na maqale da shi. Ajiye sa yayi a kan kujeran da ke cikin ษ—akin yace "my boy let me take shower an coming" ok unkui.
Shiga yayi ya wasta ruwa ya fito ya shirya ya ษ—au yaron nasa sukayi palourn. Ya same su duka suna jiran sa cin abinci, da murmushi ya qarisa wajan!! "Umma ni fa abaki zaki bani dan nayi missing en feeding na da kike yi" ya faษ—a yana zauna wa gefen Umman tasa. Unkui in granny ta baka food a mouth nima you wiy gim me a baci (you will give me a baki). Duka wajan dariya suka sa da turancin nasa da ko nuna maganan bai yi ba bare turancin, har Abba sanda ya murmusa!!! Abincin suka soma ci wajan yayi shiru baka jin qaran komi sai na spoon's da kuma taunan abinci, soja na ci yana bawa yaron nasa a baki..

After kaman 1 hour na dawo palourn
Zaune suke sun gama cin abincin hira suke cikin nishaษ—i da farin ciki!! Ameera ce tace "habeebyn Ummeyh wai yaushe zaka Bauchi ne? Kakus fa tana neman ka" caษ“ gashi Ni kuwa ban shirya zuwa Bauchi ba. Umma ce tace "Aikuwa sai kaje dan nice nan zan kora ka" tura baki yayi Umma bakison ganina ko? Carab Ameera ta amsa "ai kuwa Umma ke son ganinka kai dai asirin ka a rufe ka kama hanyan Bauchi state gobe. Harara ya doka wa Ameera ko ba gobe ba kam sai ta ganni. "Haba bros angon Kakus so kake Amarya ta buga mu a court in bata ganka ba" Daddyn Little ya faษ—a yana dariya. Tura baki soja yayi ya kalli Umma!! Murmusawa tayi tace "ku fita idon Auta na ko na saษ“a maku son kai da Ameeran, sunkuyar da kai Daddyn Little yayi yana "Allah huci zuciyan Umman mu mun daina.
Dariya Soja ya saka!!! Yace "sistor kinsan mai na tuna kuwa?" Girgiza kai Ameera tayi a'a ban sani ba sai ka faษ—a. Dariyan ya kuma sanya wa amma dai gaskiya storon ki yayi yawa sistor wai ษ—axu kin ganki kuwa, Kinga azara'ilu kawai abinki. Harara ta masa ta haษ—a fuska!! Daddyn Little ne yace "karfa kaga kai soja kasan dai mun girme ka kuma zamu iya maka bulala kabar taษ“a Adda Babba. Umma ce ta murmusa in ga mai taษ“a mun Auta inaji dai ba sharri ya mata ba. Haka suka ci gaba da hiransu tsakanin su suna darawa!! Kowa farin cikin ganin soja ne tattare da shi.
Abba kuwa kaman yafi kowa jin daษ—in ganin ษ—an nasa barin ma da ya gajesa a dai-dai lokacin da yake kusa da yin retire a aikin nasa. kasancewan shekaru sun ja kuma gashi babba sosai a cikin sojojin. Farin ciki yake sosai na ganin iyalan nasa kuma cikin farin ciki, yana kuma gode wa Allah da addu'an wanzuwar farinciki na har abada a gare su. Sai dai gefe guda na zuciyar sa, yaron sa yake tunani yana jin inama ace dashi duka a zaune anan wata qila da shima har da iyalan sa.


Umma ke stokanan Autan nata. "Wai yaushe zaka je ษ—auko mun yarana en tunda ka dawo gida" ษ“ata fuska yayi! Umma nifa in yarinyar nan Maha tazo gidan nan Tom barinsa zanyi ah to don tamun fitsaran ta bubbuge ta zan yi.
Dariya suka saka duka! har da Daddyn Little dan Abba ya tashi ya shige ciki shikam
"Shikkenan kuwa na huta sai ka tattara ka koma Bauchi ko Barack" inji Umma. Wato haka za kice Umma, tom ba inda zan je itace dai ba zata zo ba tayi zaman ta inma zuwan dole ne tom Mahreen tazo dan ta fita hankali. Daddyn Little yace "a'a bros karfa kazo gaba kana cewa na taya ka bata haquri ta yarda ta aure ka". Haษ—a fuska yayi!! Umma dai dariya take yi ษ—an dama tasan kwanan zance in dai zance ne akan Mahar.
Little dake maqale jikin uncle en nasa yace "gilani cibal mawa unkul daliya a'aco..



๐ŸŒผ DAJII๐ŸŒผ
Yana hayewa saman dokin suka juya da niyan tafiya. Ido biyu yayi da wannan stohon da suka haษ—u ranan (wanda ya basa maganin da yake nema) ba tare da yaji alaman tafiyan zuwan sa ba ko wani alama kawai juyowan da yayi ya gansa. Yaji mamakin ganinsa amma yaboye mamakin!!
Murmushi stohon yayi! yace "yarona sai gida ne?" Gaida shi Amjad yayi tukun na bayan ya amsa, sai yace "eh baba gida zan koma naa samu abun da na fito neman.
Stohon Yace "tom yarona hakan yayi kyau ko Ina fatan dai baka storita da gani na ba? Duk da nasan dama kai ษ—in jarumin duniya ne ba mai tsoro ba." Murmusawa Amjad yayi ba komi baba namaji daษ—in ganin ka
Stohon ne yayi murmushi! Bakin sa wanda kaman ba haqora ya washe yace "yauwa yarona. In kaje gida yau iyayen ka zasu maka wani magana inaso in iyayenka sun umurceka da yin abunda zasu faษ—an maka yau ka amsa kaji.
Yace "tom baba duk da dama ban kasance mae masu musu ba, komi Ummata tace ina yi in bai saษ“a Addini ba! stohon Yace "haka ake son yaron kirki dama ina mai maka fatan alkhaeri Muhammadu, sannan ka rage yawan karatun Qur'ani da qarfi acikin dokan jejin nan Allah tsare ka ya kare ka akoma gida lafiya."
Godiya ya masa, ,zai wuce yace sannan ko daa me wannan abun dake tunkarar ka yazo maka karka damu Yarona. Allah na tare da kai kuma ina tare dakai sannan kai ษ—in mai Sa'a ne mai kawo dai-dai to ga al'umma. Ka amshi koma menene, domin hanya ce ta buษ—in haske da farin ciki a rayuwarka ina mai maka fatan nasara. suka yi sallama ya juya ya kama hanyan gida dan tabbas yayi kewan Umman sa!!
Ya kama hanyan gida

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login