Showing 42001 words to 45000 words out of 98220 words
Sai can yamma lis kusan magrib Abba da Amjad suka kamo hanyan dawowa gida, suna tafiya suna hira har suka iso gida. Da farin cikin ganin mijin nata da tilon ɗan nata ta tarbesu tana masu sannu da gajiya, ledan hannun Amjad ta amsa ta shumfiɗa masu tabarma, ruwan sha ta kawo masu suka sha ta miqo masu wani ruwan a buta, alwala suka yi suka fita dan zuwa masallaci ita kuma Umma ta shumfiɗa darduma a kan tabarman ta tada Sallah, ba ita ta tashi ba sanda tayi har da magrib.
Ko da ta idar naɗe darduman tayi ta maida, jera masu kwanukan abinci da komi tayi a babban taburman da ta shumfiɗa ta zauna tana jan carbi tana jiran dawowan su masallaci.
Umma na zaune na jan carbi can sai ta jiyo sallaman su suna shigowa gidan, amsawa tayi ta miqe ta maida carbin da hijab ɗaki ta dawo ta samu har sun zauna Amjad ya zuba masu abincin, tuwon shinkafa Umma ta masu da miyan ɗanyen kifi wanda yasha haɗi gashi Umma expert ce a iya girki.
Bismillah suka yi suka fara cin abincin, Amjad loma ɗaya biyu yayi ya cire hannu, kallon sa Abba yayi "yau kuma rashin cin abincin ya mosta kenan" Abba ya faɗa yana cigaba da cin abincin sa.
Umma ce ta kallesa tace "wai har ka ɗanɗano girkin surkar tawa yafi nawa daɗi ko kaqi cin abinci gaba ɗaya yau, nayi favorite miyan ka kuma kaci sau biyu kace ka qoshi tabbas zan maka ɗure Jarumin Umma. Murmushi yayi ba haka bafa Umma ta, Tom Jarumin Umma in ba haka ba yaya ne? Kaqi cin abincin Ummanka meeyasa? Hannu yasa ya fara cin kifin dan dama yana daga cikin abinda yake so ɗanyen kifi barinma dahuwan Umman sa.
Sanda suka gama cin abincin duk suka wanke hannu ya taya Umman tasa tattare wajan, ya kai mata kwanukan kitchen.
Dawowa yayi suka kama fira da iyayen sa
Abba ne ya dube sa yace "yauwá jarumin Umma nasan itakam ka faɗa mata ya kuka yi da mai martaba saura ni a faɗamun. Umma ta ɗan dara wato dai anfaɗawa kishiyanka, Tom dai yana dawowa yace zashi wajan baban sa ko abun karyawa na ma baici ba, dan haka daga ni har kai muna sauran sa ya faɗa mana ya suka yi dan nikam ma Allah ya gani yaron nan ya ɗagan hankali yacce na gansa ɗazu, kuma gashi sai yaqi cin abun karyawa na.
Murmushin yayi ya sa hannun sa ya kama kunnen sa Ummata a yafemun na ɗaga maki hankali, komai lafiya Alhamdulillahi sai abinda baza'a rasa ba. Abba yace "to muna sauraran ka mene baza'a rasan ba". Nan take ya faɗa masu yacce suka yi da mai martaba da kuma baqin da ya haɗu dasu acan, da maganan kyauta da maganan aiki da suke son yayi dasu komai duk ya faɗa masu.
Abba ne ya nisa yace "yanzu yaya ake ciki jarumin Umma me mai martaban yace maka akan maganan nasu?"
Abba ba abinda yace fa sai kawai wai nazo nayi shawara da Iyaye na akan aikin. Umma tace "to jarumin Umma karatun da kayi ina fannin likitanci me? Mai ya haɗa likita da aikin soja?
Murmusawa yayi, Umma ta sun san da hakan duka, amma Dukansu huɗun shuwagabannin sojojin ƙasashen su ne, Kinga kenan hakan ba matsala bane.
Ajiyan zuciya Umma ta sauqe tayi shiru ta rasa mai ma zata ce, Abba ne yace yanzu Tom kai ya kake gani maganan kyautan kuma mai Sarki yace?
Abba maganan kyauta za'a karɓa abinda nake faɗa maku yanzu haka insha Allahu gobe anbamu komi sai hidiman kuma sai biki yazo. Tunda dai duka kuma kun rasa abun cewa shikkenan Abba karku damu kanku daganan har zuwa randa muka yanke shawara sunce suna maraba da Ni. Sai kuma abinda ba za'a rasa ba nan ya kuma kwashe yacce suka yi da Gimbiya da yanayin jikin Sarauniyan da kuma alqawarin da ya ɗauka mata. Sai hawaye kawai Umma ta fara ta kasa cewa komi dan tabbas taji tausayin matar sannan ta tausaya wa Gimbiya. Abba ma bai ce komai ba, wanda hakan ke masa nuni da iyayen nasa na goyon bayan abun da ya yanke.
Umma tace "Allah bada Sa'a jarumin, Umma, Allah sa a dace, tabbas zan so haka kuma zanyi alfahari da hakan in har sanadinka Allah ya bawa Sarauniya lafiya, wannan na tabbata zai sa Gimbiya ta soka da ga mutuncinka fiye da tunaninka a rayuwa, ina maka fatan nasara akoda yaushe Jarumin Umma.
Abba ma kusan abun da Umma ya faɗa hakan ya faɗa, dan tabbas ya jima da jin labarin rashin lafiyar Sarauniyar sai dai bai ɗauka har yanzu jikin nata ba, "Allah bada Sa'a jarumin Umma, In yayi akwai rubutun da zan yi da kuma wani maganin anan zaka kai masu su fara aiki dashi kamun ka shiga jeji ka dubo maganin tunda kaga yanayin jikin fatan mu dai Allah yasa adace"
Da Ameen suka amsa shi da Umman sa. Nan dai hiran nasu bai yi tsayi ba ya tashi yace zai je ya kwanta dan yana son ya sammaka a zuwa kai masu maganin gobe sai ya shige jeji. Rakasa ɗakin nasa suka yi kaman koda yaushe Umman sa ta masa addu'a suka ja masa qofa suka fita.
(wolleh iyayen sannan na mugun qaunar sa da sonsa).
_____________
Mahreen da Maha suna gidan Umma hankalin su kwance, sai kuma shirye shiryen zuwa Bauchi da suke yi, ranan saturday soja zai kaisu suje su gano Kakus. Adamawa Kuma sai Ummeyhn su tazo zasu je, dukda Maha ba qaunan maganan zuwa Adamawa take ba.
Zaune suke da Umma a palourn, suna kallo a TV, Maha ce tace "Umma nikam gaskiya in Ummeyh tazo kice bazan bisu Adamawa ba" ta faɗa tana shagwaɓe fuska. Umma ta kalle ta tace ko meeyasa bakyason zuwa doter? Allah Umma kekam nasan kina sona zaki fahim ce ni, Kinga Arɗo wlh zalina yake ci, duk in naje sai ya zaneni ko ya kwaɗa man sandan sa, kuma ranan inaji kamun Abeeyh yayi tafiya da yace masa zamu je Adamawan yace wai kar mu yarda mu je ba tare da miji ba in ba haka ba zai bada kyautan mu a can qauyen.
Haba doter karki damu kinji kekam kina da mijinki ba mai yin kyauta da ke, kuma Arɗo bazai taɓa ki ba yanzu ai kin girma. Kallon Umma tayi tace "Umma Nifa banda saurayi bare miji kuma bakisan halin Arɗo bane shiyasa Umma" ta faɗa kaman zata yi kuka.
Murmushin manya Umma tayi! Doter ai Arɗon in ya takura maki Tom kice shine mijin naki ya baki sadaki kuyi Aure, shikkenan ba?
Dariyar Maha ta sanya yauwa Ummata kin iya kawo dabara. Little dake kwance a cinyan Maha yace "ancii cice unkui ne mijin ci ba aiyo ba(Arɗo ba).
Mahreen da ke danna waya ne ta sa dariya tace "indai mu bazamu faɗa maki gaskiya ki yarda ba Tom ɗan ki ya faɗa maki ki auri uncle nasa shikkenan dama kune iyayen sa" qarasa magann tayi tana dariyan. Maha tura baki tayi ta harari Mahreen tace "Umma kinji yaya Mahreen ko" Umma ta murmusa tace "qyaleta doter zan saɓa mata kinji" ɗaga kai tayi ta koma kan Little tace "my son kana so mu ɓata? Gyaɗa kai little yayi alamun a'a tace "okay karka qara faɗan wannan maganan ko" sai ya ɗaga ka tace "that's my good boy. Dariya litttle ya san ya yaji an yabeshi!
Qira ne ya shigo wayan Mahreen, ganin Abeeyhn su ya sa ta ɗau da wuri tana murmushi!
"Assalamualaikum Abeey masahul khair" shiru tayi na ɗan wani lokaci kamun ta kuma cewa "duk muna lafiya Abeey ga Mahan nan. Miqawa Maha wayan tayi, amsa Maha tayi suka gaisa da Abeeyhn nasu, da suka gama tace "ga Umman nan a kusa Abee ba na bata" miqawa Umma wayan tayi.
Sanda suka gaisa sosai da Umma cikin girmamawa da fara'a ya tambayi Abba da su Ameera da soja, Umma tace "yayan ku yana lafiya, baban yara Ameera kuma jiya suka koma da mijin ta duk suna lafiya, soja ma yana lafiya ya fita, Inshà Allahu duk zasuji gaisuwa baban yara" faɗin Umma. Miqawa Mahreen wayan tayi nan suka fara larabci da mahaifin nata....
--------
Washe gari da sassafe bayan idar da Sallahn asuba sama-sama ya karya ya kama hanyan shiga jeji.
Shine bai isa inda zashi ba san da gari yagama haske, har fa inda baya isa duk yau ya isa a jejin yasha yawo yasha yawo, amma kwata-kwata bai ga halaman wannan bishiya da yake nema a jejin ba, tun safe har yamma. Ganin lokaci na qure wa ba lallai ya samu ba sai kawai ya karya kan dokin sa dan ya juya ya dawo gida, ganin ko yace ya kwana ko ya qara gaba wahala zai sha, sai dai in ya koma gida gobe in Allah ya yarda ya kuma tafi wata gefen in ta kama ko garin ya bari indai zai samo wannan maganin.
Har ya juyo da dokin sa ya kama hanya dan ya komo gida kar dare yayi, kaman daga sama aka jefo mutumin sai kawai ganin sa yayi a gaban sa, ko kaɗan bai razana ba dan inda sabo ya saba da zuwan da wannan stoho yake masa ako da yaushe, bai storata ba sai ma hamdala da yayi dan dama ya kwaɗaitu da ya haɗu da stohon ko Allah zai sa ya taimaka masa da wani abun. Har zai sauqa a dokin nasa dan gaida stohon, wannan stohon ya dakatar dashi ta hanyar cewa "a'a yaro na ba sai ka sauqo ba" gaisar da stohon yayi.
Da murmushi a fuskansa ya amsa gaisuwan, yarona nayi nisa ne shiyasa baka ganni da wuri ba amma naji zuwan ka, shidai har ransa yana mamakin abunda stohon kecewa wataran kaman ya tambaye sa amma bakin sa sai ya masa nauyi.
Bude baki Amjad yayi da niyan zai faɗa wa stohon yacce ake ciki komai da komai, sai kuma stohon ya tari numfashin sa Yace "karka damu ko kaɗan yarona nasan komai yacce ake ciki, Inshà Allahu za'a yi Auren ku nan da wata huɗu sannan mahaifiyar ta zata samu sauqi sai dai akwai abinda zai faru wanda bana iya hangowa kuma bana ganewa sai dai nace maka ka dage da addu'a da kuma neman stari, Allah na tare da kai Inshà Allahu komai ya kusa zuwa qarshe, sannan ka kusa daina ganina, randa zamu yi haɗuwan qarshe a ranan zan sanar dakai haɗina da kai da komi, ina maka fatan nasara a rayuwan ka, ka riqe Umman ka da Abban ka da kyau, ko da kasamu wasu masu mastayin su nan gaba, wannan iyayen naka sune alkhaeryhn ka su suka maida ka mutum a lokacin da kake gaf da barin duniya.
Sannan ganyen da kake nema da iccen suna makarin ciwon jikinta insha Allahu, Allah qara maka baiwa da basira.
Amma sai dai akwai ɗan mastala ɗaya, mastalan shine ba zaka same su anan ba. Nayi qoqari tun kan kazo da maganan maganin ace na samo maka ko na aika an kawo maka, Amma bazai yuwu ba dole zaka shiga waccan qasan da nace maka NIGERIA, a garin Bauchi akwai wani jeji YANKARI a wannan jejin ne Inshà Allahu zaka samo duka maganin har kayo guzurin wasu.
Jinjina kai yayi yace "Nagode sosai baba nagode Allah saka da alkhaery. In ka samu tafiya Allah stare hanya Allah kai ka lafiya ya dawo da kai lafiya, Allah yasa adace, suka yi sallama ya kamo hanyan dawowa gida abun da ba tare da ya ko waiwaya ba.
Shine bai isa gida ba sai bayan sallahn isha'i.
Ya zuwa direct wanka ya shiga yayi, ya ɗaura alwala anan gida yayi sallolin da wanda bai yi ba.
Rasa yanza zai yi ya faɗa wa Umman sa wannan magana yayi suna hira yana jinsu yayi shiru yana tunani, ya rasa ta ina zai fara yana storon kar Umman nasa ta hana sa.
Abba ne ya kalle sa yace "Jarumin Umma andace kuwa? Sosa qeya yayi Tom Alhamdulillahi dai kawai Abba, Umma na kallon sa tace "akwai Magana abakin ka na sani, menene ya faru Angon Gimbiya? Ganin Umman tasa ta ramfo sa qarshe dai ba yacce ya iya haka ya faɗa masu gashi-gashi sai dai bai basu labarin wannan stohon ba kuma bai ce masu shi ya faɗa masa ba, ɓoye masu yayi yace "wani bawan Allah ne maharbi kuma shima mai bada magani ya faɗa masa hakan" ya faɗa yana kallon Abban sa dan yasan tabbas yayi qasa da kai Umma zata gane ya ɓoye wani abun ko in ya kalleta zata gane.
Ba tare da Abba ya damu ba yace "Allah yasa hakan ne alkhaeri Allah sa kayi tafiyan a Sa'a Allah yasa adace" Umma ta amsa da Ameen, Sannan dan Allah inaso ka kula sosai Jarumin Umma kaga baka taɓa zuwa wannan qasan ba ka kula sosai, yanzu in ka tafi ta yaya zanke jinka?
Murmushi yayi ya sauqe boyayyen ajiyan zuciya dan bai tsammani Umman tasa zata amince da wuri haka ba, ya ɗau sai sunsha wahalan bata baki da fahimtar da ita shi da Abba, cewa yayi "Umma ai bazan daɗe ba Inshà Allahu bazan wuce sati ba" Tom Allah ya yarda jarumin Umma Allah baka Sa'a.
Duka suka yi Ameen
Yanzu yaushe ne tafiyan naka? Inshà Allahu Umma ta gobe ko jibi dai, Tom Allah nuna mana.
Ɗakin sa suka raka sa Umma tai masa addu'a da ahuta gajiya suka ja masa qofa suka yi nasu ɗakin.
Umma na shiga ɗakin ta zauna bakin gado tayi tagumi, Abba da ke bayan ta Murmushi yayi dan yasan tabbas za'a yi haka, ko shi yaji mamakin amincewar ta lokaci ɗaya amma yasan hakan baya rasa nasaba da tausayin Gimbiya da take ji.
Abba Zuwa yayi kusa da ita a bakin gadon ya zauna, jawo ta yayi ya haɗata da jikin sa yana bubbuga bayan ta alaman rarrashi "haba MARYAMA ta sarauniyar mata uwar Muhammadu matar Ibrahim, so kike kisa ɗan naki yayi qasa a guiwa? Kefa kikace ɗan ki jarumi ne ko kinason ki zama raunin jarumtar sa ke da kanki? Girgiza kai Umma tayi hawaye nabin idanuwan ta! Abban yaro na bazaka gane ba ko kaɗan ya nake jin wannan yaron namu a rai na, kullum addu'a ta ɗaya Allah yasa na mutu kamun ace yau ba yarona kusa dani, qaunar da nake wa yaron nan kusan kullum cikin zullumi nake inya fita zai dawo yace yasan gaskiya, kullum cikin mafarkin an rabani dashi nake, kullum cikin addu'a nake kamun wannan rana Allah ya ɗauki rai na! Kuka ta fashe dashi Abban yaro na inason yayi tafiyan nan dan tabbas inajin tausayin wannan mata da kuma yarinyar da marabin ta da Maraya mara uwa kaɗan ne. Abban yaro na kasani haka kawai zuciyata bata kwanta da tafiyar nan ba kuma inaji a jiki na kaman wani abun zai faru ko kuwa sanadin rabuwana da Amjad kenan, kuma kasan bszan iya ɗaukan haka ba daga randa akace an rabani da Amjad daga ranan nayi bankwana da farinciki har mutuwa na wataqila ma sanadin mutuwa na kenan!
Ajiyan zuciya Abba ya sauqe! Tabbas acikin magana Maryam ba qarya ko ɗaya ko kowa bazaiyi shaidan son da take wa Amjad ba shi zai yi shaida tun daga randa ta ɗaga idon ta ta ɗaura akan yaron nata tabbas yasan qauna ce na ɗa da uwa Allah ya sanya tsakanin su dan Amjad ma sonda yake wa Umman sa ako ina baya ɓoyewa.
Abba yace "MARYAMA ta inaso ki ɗago ki kalle ni, ɗagowa Umma tayi fuskan ta duk hawaye!
Abba yace ki kalli idona Maryam, kallon Abba tayi, Abba yace mata "Maryam wa ya baki Amjad? Umma tana sheshsheqa tace "Allah" Abba ya qara cewa "wa zai ɗauki ranki ko na Amjad ya rabaku? Umma ya qara cewa "Allah".
Jinjina kai Abba yayi yace Alhamdulillahi, Maryam nasan ke musulma ce kuma kin yarda da Allah sannan akwai samu akwai rashi akwai mutuwa akwai rayuwa, kuma duk kinsan mai qaddara wannan abubuwa Tom dan Allah kar maganan mu yayi nisa, kar Amjad yaji wani magana yasa kokonto a ransa ko kinason hakan ya faru? Da sauri Umma ta girgiza kai tace a'a. Tom Masha Allah inaso akoda yaushe kidinga binsa da addu'a, Allah ya ga son da kike masa kuma yaga sonda shima yake maki, Allah ne ya baki shi Inshà Allahu ba mai rabamu da Amjad sai mutuwa. Kici gaba da sa masa albarka kinji. Umma ta ɗaga kai, da qyar da qyar Abba ya lallashe Umma har suka yi alwala suka yi nafila, tilon ɗan nasu suka wa addu'an kariya da Sa'a sannan suka qara da godiya ga Allah da suka idar suka kwanta anan Abba yaci gaba da lallaɓa matan sa lallaɓa irin na masoyan gaske wanda soyayyan su bata stufa....
A ɓangaren Amjad