Showing 39001 words to 42000 words out of 98220 words
kyauta na yabawa bajintan ka, nan mai martaba ya kwashe yacce suka yi da mutanen, abubuwan da suka faɗa da kuma daga inda suke duka ya faɗawa Amjad en, sannan ya faɗa masa amsan da ya basu, yanzu sun buqaci ganin ka dan amsa a bakin mai shi yafi daɗi, yanzu dai muna sauraran ka Muhammadu, mai martaba ya faɗa yana mai da kallon sa kan Amjad wanda kansa ke sunkuye.
Shirun da Amjad yayi shi ya qara burge Mai martaba dan ko ba komi tunanin babba da yaro ba ɗaya ba, yasan tabbas abun da ke ran Amjad bai wuce son shawartan iyayen sa ba. Mai martaba ya nisa yace "ya kayi shiru Muhammadu ?
Amjad Ya buɗe baki zai yi magana corp. Abeed ibn Zayd ya tari numfashin sa yace "ina ganin a barsa yayi shawara na, mu zamu tafi inyaso ko mai ya yanke daga baya a sanar damu mai martaba amma maganan kyautan goben nan Insha Allahu komi zai iso sa, hidiman biki kuma Allah nuna mana lokaci duk abin buqata za'a yi.
Mai martaba yace "shikkenan hakan za'a yi Allah mai daku lafiya, muna godiya sosai sosai". Amjad sai lokacin ya ɗago kan sa, godiya ya musu sosai da addu'oee.
Bayan sun kammala maganan Sallaman mai martaba suka yi duka suka miqe dan su samu su wuce akan lokaci, qara godiya Amjad yayi ya bisu da addu'an Allah stare hanya.
Bayan fitan su mai martaba yayi qiran wani dogari, da dogarin ya shigo ce masa yayi "a qiramun Gimbiya ta iso" amsawa dogarin yayi ya bi ɗayan qofan ya fice.
Ko da ya fita ya samu Gimbiya a main palourn sashen mai martaba a zaune don dama already mai martaba ya qira ta a waya jira take a mata izin isa ciki. Dogarin durqusawa yayi, yace "Allah ja kwanan Gimbiya Allah baki tsawon rai mai martaba na maki iso" gyaɗa kai kawai tayi ta miqe ta nufi palourn ko da ta isa bakin qofan janye abun da ta rufe fuskanta tayi ta kama handle en qofan ta murɗa ta shiga.
"Assalamualaikum" ta furta yayin da take shiga palourn, jin muryanta ya sanya shi ɗagowa, kallo ɗaya ya mata ya kau da kai. Amsa Sallaman suka yi shi da mai martaba, ganin sa a palourn ya sanya ta jin haushi buɗe fuskan ta da tayi, ba yacce ta iya haka ta qaraso ta zauna a wasa kusa da mahaifin nata, bata ko kalli inda Amjad yake ba tawa mahaifin nata Barka da hutawa ya amsa.
Mai martaba kallon su yayi duka biyun ya ga kowannen su gefe yake kallo kuma ba mai alaman yiwa ɗan uwan sa magana, girgiza kai yayi faɗi yake a ransa "duk zaku yi ku bari zaku dedeta kanku ba wanda ya sani".
Gyaran murya mai martaba yayi sannan ya fara magana kaman haka "inban manta ba dama nayi daku akwai sharaɗi na biyu dukanku ga duk wanda yaci wannan gasa, wanda wannan sharaɗin nace ba dole bane shi babban damuwan shine gasan, fatan kana tune da wannan magana Yarona"? Gyaɗa kai Amjad yayi yace "eh ranka shidaɗe ina tune da maganan ɗayan sharaɗin" to Allah maka albarka, maganan ɗayan sharaɗin zaku yisa da ita Gimbiya amma kamun nan inason sanin dalilinka na qin Karɓan dukiya da nace zan bawa wanda yaci gasan.
Cikin girmamawa Amjad ya fara magana "Ina mai neman afuwanka mai martaba akan wannan abu da na yanke ba tare da wani dalili ba. Jinjina kai mai martaba yayi yace "shikkenan Yarona Muhammadu Allah maku albarka duka, da Ameen ya amsa, Gimbiya kuwa tana sauraran su batace qala ba.
Mai martaba ne ya kalleta yace "Gimbiya maganan ɗayan sharadinki zaku yi tsakaninku, ni kuma na gama nawa maganan Aure nan da wata huɗu 4 in Allah ya yarda, sannan zai cigaba da zuwa wajan ki daganan har lokacin da al'ada ta ɗibar bazai ganki ba in anfara hidima. Kai kuma yaro na zaka iya zuwa cikin gidan nan a duk lokaci da kaga dama ba tare da sai anmaka iso ba ko jagora kaima ɗan gida ne nan gidanku ne.
Godiya Amjad yayi wa mai martaba dake qoqarin miqewa, tashuwa mai martaba yayi yace tom "zan tafi fada Gimbiya zata kawo maka abun karyawa banyarda ka fita a gidan nan ba tare da ka karya ba, gyaɗa kai Amjad yayi Tom ranka shidaɗe, ke kuma Gimbiya ki sa a kawo masa abun karyawa ki tabbatar ya karya kamun ya tafi" mai martaba na gama magana ya buɗe qofan ya fice a palourn.
Mai martaba na fita ta tashi ta koma kan kujera ta zauna ta maida abun fuskanta ta rufe.
Murmushin gefen baki Amjad yayi ganin yacce take wani cika tana batsewa, kau da kai yayi kaman baison yin magana yace "Malama Gimbiya ki cire abunda kika sa a fuskan naki sai muyi magana ko"
A gadarance tace malami baza'a cire ba in ya dameka zaka iya zuwa ka cire bazan cire ba, kamun ta rufe baki taga mutun a gefenta( hhhh!!! aiki da cikawa)
Saurin matsawa tayi ta yaye abun fuskan nata ta harari gefe tana tura baki, cewa yayi "na zaci zaki tsaya na cire ne kinsan qaramin aiki nane acikin abubuwan da zan iya"
suna cikin haka jakadiya tayi sallama ta shigo ɗauke da qaton tire da aka cika da kayan abinci kala-kala da kuma kayan marmari da abubuwan sha, ganin Amjad kusa da Gimbiya sai tayi qasa da kanta. Tashuwa Amjad yayi ya koma ɗayan kujeran ya zauna ya dake kaman ba shi ba, qarasowa tayi ta ajiye tiren abincin a gaban Amjad, ta tashi ta juya zata fita Gimbiya tace "wa zai zuba masa abincin in kin tafi? Kallon Gimbiya Amjad yayi ya kalli jakadiya dake shirin dawowa dan zuba Abincin yace "karki damu baiwar Allah zaki iya tafiya" godiya jakadiyan tayi ta juya ta fice a Palourn.
Kauda kai Gimbiya tayi tace "da ka bari ta tafi kai zaka zubawa kanka abinci ko waye? Ya kalleta yace "Ke zaki zuba mun ba wata ba, sannan ina fatan kin iya feeding. Saurin kallonshi tayi ta buɗe qaramin bakinta ta murmusa! Subhanallahi Murmushin da ya kusa ɗauke wa Amjad numfashin sa da sauran jarumtar da yake da, tace "you most be joking indai MEHWISH ce kake nufin zata yi serving naka and kana magana akan feeding, girgiza kai tayi tace funny you".
Duk maganan da yake kaman an sashi dole yayi haka yake maganan, dogon magana in ba da Ummansa ba bayayi bai saba ba magana wahala yake basa wani bin har yayi ciwon kai in ya yawaita magana.
Ba tare da ya kalleta ba yace "can you come and serve me or I should come over there and make you serve me"? hararan gefen da yake zaune tayi taqi tasowa, kallon hararan yayi ta gefen ido ya ɗan yi Murmushi irin na nafiki iskancin nan, aransa kuwa cewa yake "zaki setu ne yarinya bari ki shiga hannu duk stiwan naki zan magance sa staff" a zahirin kuwa da ya murmusa baice qala ba, illa miqa hanu da yayi ya ɗau apple yana ci.
Ganin yana cin apple cewa tayi "better da ka taimaki kanka ka nemi abinci if not ba randa zan yi serving naka ni Mehwish" ta faɗa tana karkaɗa qafan da tayi Cross-leg tana danna wayan da ke hanun ta qirar iPhone 14 pro.
Kallon ta yayi, baice komi ba yaci gaba da taunan apple nasa kaman yana storon taunawa.
Jin bece komi ba takuma cewa "Yes gwanda kayi shiru dan ni ɗin ƳAR SARKI CE ko aurena kayi sai dai nasa amaka ba dai na maka ba, inkuma ka hana sai kayi da kanka faqat".
Ba tare da ya kalle ta ba yace "ke kikasan ke ƴar Sarki ce, for me I don't know this, all i know is that ke mata tace I will soon own you and make you deed whatever I want, so you should be minding your words dan karki bari nasa harda wanke bayi a ayyukan da xakiyi a gidana nan da wata huɗu.
Saurin kallonsa tayi tace "Au ashe har;na zama matarka, and kana lissafin zanyi ayyuka, murmushi kawai tayi tana kallonsa.
Lumshe ido yayi, bai ce komai ba, gaba ɗaya kallonta da irin kallon da take masa da wannan killer smile natan na haddasa masa shiga yanayin da bai son kusantan sa bare ya shiga, stiririn tsaki yaja kaman a kasalance yace "can you please stop looking at me with dis ur tiny eye's"
haɗe fuska tayi alaman taji haushin abinda yace, cewa tayi "Ko makaho ya ganni ya san idanuna ba qanana bane bare mai ido. taci gaba da cewa "am abu na gaba da yake sharaɗin qarshe wanda zai tabbatar mun zaka iya aurena ko ba zaka iyaba shine, mahaifiyata bata da lafiya kuma a sharaɗina dole wanda zan aura sai ya nema mata magani, mai martaba yace maka wannan sharaɗin bai zama dole ba amma ina so na sanar maka wannan ne babban sharaɗi na.
Yana jinta har ta gama magana bai ce ko qala ba, ko ci kanki baice ba. Tashuwa tayi tace" inka gama zaka iya biyo ni muje ka ganta" tana gama faɗan haka ba tare da ta staya ba tayi gaba abunta.
Tashuwa yayi ya bi bayanta, ba ta ainafin cikin gidan suka bi ba ta cikin sashen mai martaba suka bi hanyan da zai sada su da shashen Sarauniyar. duk inda suka wuce bayin wajan gaida su suke har qasa da shi da ita duka.
Sun iso qofan ɗakin ta buɗe qofan t masa iso, da sallama dukansu abakinsu suka shiga ɗakin, a kwance Amman nata take sai dai da alama mai martaba ya goge mata jiki ya sauya mata kaya (dama ko shi ko Gimbiya suke wannan aikin).
Tace masa "ga Ammaa na, a take kuma sai kwallah ya cika idonta, tun da ya ɗaura idon sa akan matar yaji tausayin ta da na iyalanta duka ya rasta jikin sa, sai ya raya da ace ke wannan ciwo ya zaiji, a take ya ji mugun tausayin Gimbiya ya shigesa lokaci ɗaya.
Zuwa kusa da Ammaan nata yayi ya durqusa a gefen gadon, addu'oee masu yawan gaske yayi mata na karya sihiri da kuma kariya da neman sauqi, ya kuwa minti talatin a durqushe, da ya idar da addu'an ya kama kanta ya tofa ya shafa mata. Miqewa yayi ya masta kusa da ita yace "karki sa damuwa a ranki Insha Allahu Ammaa zata samu lafiya bada jimawa ba kuma Ni Muhammad Amjad na maki alqawarin sai randa na samowa mahaifiyar ki magani tukunna za'a yi aure na dake, inafatan hakan ya maki?
Ba tare da ta kalle sa ba ta share hawayen ta ta ɗaga kai.
Daga haka ya miqe zai fice bayan sa tabi har suka fita a sashen mahaifiyar tata, ba wanda yace da ɗan uwansa qala kowa da abinda yake tunani a ransa, rakasa tayi ta juyo ɗakin ta ta wuce direct, tana cike da alhinin Maganan ciwon Ammaa nata, ga shi maganan da yayi harda alqawari ya baya mamaki dan tasan mai martaba bazai taɓa fasa maganan auren nan da wata huɗu ba.
Sai dai har a ranta ta yarda da shi tana ji a jikinta Insha Allahu za'a dace.
Maganan da basu qarasa ba kenan shima ya fito, dogari ne yazo da motor ya staya gefen sa ƴallaɓoi ka shigo mai martaba yace a kaika gida, ba musu ya buɗe murfin baya ya shiga dogarin yaja motor suka nufi gidan su Amjad..
Dogarin har qofan gida ya kawo sa, sauqa yayi ya masa sallama ya tura qofan gidan nasu ya shige. Abban sa ya tafi kasuwa Umma ce kawai a gida ya sameta.
Ummansa na kallonsa ta yi guɗa tana murmushi tace "Kaga Angon Gimbiya Jarumin Umma ɗan gidan Abba" Amjad murmushi kawai yayi wa Umman tasa amma bai ce komi ba.
Ganin yanayin sa sai jikin Umman sa yayi sanyi, amma batayi yunqurin tambayan sa me yake faruwa ba. Ruwan wanka ta kai masa yaje yayi wanka. Bayan ya fito Umma tace masa "jarumin Umma zo ka karya" Umma ta a qoshe nake na karya a can. Ko ba komi taji daɗin da har ya karya a can ɗin hakan na nufin Insha Allahu komai lafiya, sai ta ci gaba da ayyukan ta, shi kuma ya shirya ya fito ya ma Umman tasa sallama ya bi Abban sa kasuwa.
Ko da ya isa kasuwan Abban sa yayi farincikin ganin sa, ya so tambayan sa ya suka yi a gidan Sarkin amma ganin suna kasuwa sai ya bari sai sun koma gida zai tambayesa.
nan suka zauna suna kasuwan su tare sannan Amjad ya kan yiwa Abban sa tambayoyi akan wasu ciwuka Abban sa na qara masa bayani, duk da dai shi irin sana'ar nan baiwa ce kawai ta Ubangiji...
Bayan shigan ta ɗakin ta, kwanciya tayi a kan qayataccen gadon ta da yasha shumfuɗi, a kwancen ta rage kayakin jikin ta a haka har bacci yayi awon gaba da ita.
Itace bata farka ba sai daf ana qiran Sallahn azahar, jin kanta na ciwo sakamakon kukan da tayi ɗazu sai ta nemi magani tasha taje ta wasta ruwa ta ɗauro alwala ta tada Sallah.
Ta idar da sallah ta shirya cikin riga da skirt ruwan kwai, irin kayan ƴan India. Bata sa ko ɗan kwali ba ta ɗau alkyabban ta ta sanya ta fice a ɗakin, a palourn ta tarar da Laure na goge goge, goggoji da ke jera abinci a dining en dake sashen ta takalla tace "ina jakadiya? Goggoji ta juyo har ta durqusa dan bata amsa sai ga jakadiya ta shigo, tana magana a waya. Ganin Gimbiya tsaye ba tare da ta kammala wayan ba ta kashe, durqusawa tayi Allah ja kwanan uwar ɗakina mai kike buqata? Gimbiya batace qala ba ta nufi hanyan qofan baya daga nan sashen ta wanda zai sada ta da lambun dake gidan sarautan nasu.
Ganin haka jakadiya ta yi sauri tabi bayanta, kamun Gimbiya ta isa har jakadiyan ta shumfiɗa mata darduman da zata zauna ta wuce cikin part en Gimbiyan da sauri. Gimbiya zama tayi ta yaye alkyabban ta dan tasha iskan dake kaɗawa a lambun mai daɗin gaske, jakadiyan ce ta kuma dawowa ɗauke da tray dake a shaqe da kayan marmari ta zo ta ajiye a gaban Gimbiya, kanta aqasa tace "Allah baki tsawon rai uwar ɗakina, shikkenan ko da wani abun da kike buqata? Sai yanzu Gimbiya ta buɗe baki tayi magana.
Shikkenan maimuna kina yin abu ne a cikin gidan?
Saurin girgiza kai jakadiya tayi a'a bana komi ranki shidaɗe uwar ɗaki na, okay kije ki gyara mun ɗaki sai kizo and bayan ke banson kowa ya shiganmun ɗaki bare har yace zai gyara mun toilet nasha faɗa maki amma inaga kina barin sauran yaran na shiga mun ɗaki. Ki gafarceni uwar ɗaki na, ban sanya kowa gyaran ɗakin ki ba sai dai jiya da dare da naje ɓangaren su Umma dan dubo jikin ta bansan ko akwai wanda ya shiga ba.
Gimbiya tace yayi kyau amma dai a kula dan banason qazanta, and ya jikin Umman? Fatan da sauqi?
Da murmushi Gimbiya tace eh uwar ɗaki na jikin da sauqi sosai ma, Insha Allahu zuwa wani sati inaji zata dawo bakin aikin ta ma. Allah kaimu ya qara sauqi ko Umma ta dawo, zata kula da sauran ɓangarorin da masu ayyukan gida amma sashe na ke zaki cigaba da kula dashi. Inshà Allahu uwar ɗakina Allah ja kwana, ta tashi ta juya dan komawa ciki ta gyarawa Gimbiya ɗakin nata.
Gimbiya wayan ta tajawo ta kunna data dan duba class da suke yi a online, tana yin master's a ɓangaren Islamic, Amma online master's. Tana dudduba class en tana shan kankana, sanda suka yi almost 1 hour suna class kamun aka gama, ganin ya qare class en yastine baki tayi ta kashe datan tayi jifa da wayan tana miqa, idon ta na sauqa akan apple da ke cikin bowl en kayan fruit en sai shi ya faɗo mata a rai, tun da ya tafi basu yi magana ba koya ya isa gida bata sani ba. Lumshe ido tayi ta sa hannu ta ɗau apple en tana ci a hankali, Sallaman jakadiya ne ya dawo da ita hayyacin ta.
Amsa Sallaman tayi, jakadiyan ta durqusa ɗan gefen ta kaɗan, nuni ta mata da kan darduman da nufin ta zauna, ba musu jakadiyan ta masto ta zauna tana "Barka da hutawa Uwar ɗakina" gyaɗa kai kawai Gimbiya tayi batace komai ba sanda ta ɗan ci kusan rabin apple en kamun ta ajiye ta juyo tana fuskantar jakadiyan, magana nakeso muyi dake shawara nakeso zaki ban, jakadiya tace "ina sauraranki uwar ɗaki na , nan dai suka tattauna......