Showing 36001 words to 39000 words out of 98220 words
da son kuɗi har kashe rai ake akan dukiya, wannan yaro ya nuna bazai amshi dukiya ba ya yafe, inaji a jikina wannan yaro alkhairin ki ne kuma muma alkhaerin mu ne duka, bana buqatan ki da jayayya ko nuna wani hali daban, ke ƳAR SARKI CE amma inaso ki sani a wajan Allah ke ba kowa bace in dai bakya bin dokokin Allah da kuma son Manzon Allah SAW, shi wannan matsayi da kike da Allah ya baki ne dan kisamu lahiran ki dashi, kyautatawa talakawanki, mu'amala da jama'ar ki ba nuna haqidanci ko zalunci, acikin dokokin Allah har da Aure don sunna ne na mafi soyuwa acikin halittun sa Annabi Muhammadu SAW, hadisin Manzon Allah SAW yace, in zamu nemi Aure mu nemawa yaranmu Uba nagari/Uwa tagari, mai Addini, mai adalci, ba mai dukiya mara hali ba ko mai kyau mara kamala ba, Ako da yaushe ina yawan faɗa maki kibar ɗaukan wannan mastayi naki na Gimbiya ƴar Sarki abakin komi, ki duba Annabi Dawud (AS) irin dukiya nasa da matsayi nasa amma duk da haka yana mu'amalantar jama'a staftacciyan mu'amala, sannan ɗan sa Annabi Sulaiman (AS) wanda in dai mulki ne da ɗaukaka Allah ya bashi amma shima bai zamana mai amfani da wannan dama wajan cutar da jama'ar sa ba, duk wannan abubuwa da nake faɗa maki da misalai da nake kawo maki inaso ne kada ki taɓa cewa ke kaza ce shi kuma kaza ne kinfi qarfin Auran sa, ke kika saka wannan sharaɗin kuma an cika maki, karki ja da lamarin Ubangiji ko gorantawa ga wani dan bai da mulki Allah inyaso zai amshe mulkin a hannunki ya bawa wanda yaso (innallaha yuhlikil mulka liman yasha) dan haka ki amshi wannan zaɓin Ubangiji gare hannu bibbiyu kigode masa sai kiga ya qara maki, Allah Ubangiji ya maki albarka, Allah albarkaci rayuwanki da ta zuri'an ki" tari ne ya sarqe sa ya sa yayi shiru ya fara tarin.
Ruwa ta tashi ta ɗibo a cup ta miqa masa, amsa mai martaba yayi ya sha sanda tarin ya lafa kamun yace "inafatan kinji abun da nace da kyau?" Kanta a qasa tace "naji Papa Nagode kuma Insha Allahu akoda yaushe zan kasance mai aiki da maganan ka, Allah ja kwana ya baka tsawon rai, Allah qara lafiya" da Ameen mai martaba ya amsa yana murmushi! Daga kai yayi yaga agogon dake maqale a bangon palourn nasa yace "Allah maki albarka in yayi daga baya zamu sake magana ko yanzu baqin nan najira na ina tunanin sauran zasu tafi ta wuri gobe in Allah ya kaimu, kije ki kwanta ki huta gajiya ko sannan gobe ki shirya tarban baqonki" mai martaba ya faɗa yana miqewa. Inshà Allahu Papa Nagode Allah qara girma, ficewa mai martaba yayi a palourn ya nufi palourn da baqin nasa suke. Bayan fitan sa Gimbiya ajiyan zuciya ta sauqe ta dafe kai "Ni Maryam dama mai zance inba Alhamdulillahi ba" ta faɗa tana miqewa itama ta fice a palourn ta ja masa qofa ta fita a shashen mai martaba gaba ɗaya.
Sashen mahaifiyar ta ta nufa, da sallama ta shiga ɗakin, direct gadon da Ammaan ta take kwance ta nufa ta kwanta gefen ta tana ajiyan zuciya a haka har bacci ya ɗauke ta.
Da sallama mai martaba ya shiga palourn baqin nasa, amsa masa suka yi ya qarasa ya samu kujera ya zauna. Duk yunqurin sauqa qasa suka yi dan gaida sa mai martaba yayi saurin dakatar dasu "haba ku kuwa kuyi haquri mana ku zauna, bákomi wallahi" sarki ya faɗa da murmushi.
Gaggaisawa suka yi duka, mai martaba ya qara gode masu da masu ban gajiya.
Gabatar da kansu suka fara yi ga Sarkin.
Mutumin farko dake sanye da qananun kaya yace "sunana Peter James, wannan corporal abeed ibn Zayd, wannan major Ibrahim khadeer sai kuma marshal Abubakar Idris.
Murmusawa mai martaba yayi, gaskiya muna godiya sosai naji daɗin zuwanku kunga yanzu sanadi yasa ansan juna, sai dai bansan daga ina kuke ba.
Wannan mai qananun kayan shi ya kuma magana, yace "Ni daga Dubai nake nine shugaban sojojin Dubai, abeed ibn Zayd daga Bahrain yake, Ibrahim khadeer daga Nigeria sai kuma Abubakar Idris da ke nan qasan Qatar a yankin Doha." Mai martaba da murmushi yace " a'a wai Abubakar dai wanda na sani? Ya aka yi tom ban ganeka ba?"
Abubakar wanda ke sanye da jallabiya da hirami a kansa murmusawa yayi yai washe baki yace "Allah ja kwanan mai martaba aimana afuwa, ayyukan ne sai a hankali tun bayan appointment ɗin ban zauna ba sai this time, to Yanzu ma wani shungullan ake yi naji labarin wannan taro nace Tom insha Allahu zamu halarci wannan taro".
Mai martaba yace "Allah yayi jagora bákomi marshal Allah temaka sannun ku da qoqari gaskiya ina godiya"
Marshal Abubakar ne ya nisa yace "ranka shidaɗe mai martaba dama dai wani kyauta ne daga garemu kuma haɗe da roqo fatan za'a duba roqon namu". A'a Abubakar mai zai hana mu amsan kyautan naku tunda dai duka gida muke, karka damu muna godiya, menene roqon naku? Faɗin mai martaba. Allah qarama tsawon rai dama akan wannan bikin da za'a yi ne, kyautan mu shine Captain Peter yace yanaso yayi magana da wannan yaron da yaci gasan akan zai ɗauki nauyin komi da Yakamata yaron yayi zai masa shine kyautan sa, abeed ibn Zayd kuma ya basa kyautan motor, sai Ibrahim khadeer da yake roqon in ba mastala yanaso su ɗauki yaron aikin soja a can Nigeria, Tom maganan Ibrahim kam Ni da kaina nace a'a dan gida bata qoshi ba baza'a bawa waje ba muma in da dama muna buqata.
Numfasawa mai martaba yayi, yace "shukran shukran gaskiya ina godiya sosai, Allah saka da alheri abu yayi kyau sosai an gode. Maganan aikin soja kuma ni bazan ce komi ba amma dai da Nigeria da Doha duk gidane insha Allahu, sai dai kuma in munji daga bakin sa, muma nan shine yariman mu na gobe in Allah ya yarda.
Zantawa suka ci gaba dayi tsakaninsu cikin fara'a kaman waɗan da suka jima da sanin juna! Mai martaba ya qira waziri akan a maida su masauqin su ganin dare yayi lokaci ya ja sun ce zasu koma da wuri gobe, sunyi sallama da mai martaba suka bi wanda zai masu jagora har masauqin nasu.
Mai martaba ko da ya tashi ɗakin sa ya wuce, babban rigan jikin sa ya cire ya rage kayan jikin sa ya shiga banɗaki ya wasta ruwa. Shiryawa yayi cikin kaya mara nauyi ya ɗau alkyabban sa ya sanya, fitowa yayi ya nufi sashen matar tasa...
Umma da Abba sun nemi taxi ya kaisu har gida, da sallama suka shiga gidan nasu shiru ba'a amsa ba, qaran ruwan da suka jiyo a banɗaki shi ya tabbatar masu Amjad ya dawo.
Taburma Umma ta ɗauko ta shimfiɗa, ta wuce madafin su ta dauko kulolin abincin nasu ta jera, bayan ta gama ta shige ɗaki wajan Abba.
Samun Abba tayi yana rage kayan jikin sa, sanda ta taya sa kamun ta fito a ɗakin dai-dai Amjad ya fito banɗakin. Ayoyo Umma ya sannu da dawowa, sannun ka jarumin Ummansa je ka shirya kazo ba baka abinci nasan ka gaji ga kuma yunwa, amsawa yayi "Tom Ummata" ya wuce ɗakin sa. Umma ruwan wanka ta kaiwa Abba banɗakin, ta dawo ɗakin nata, Abban jarumin Umma nakai ruwan wankan aje a wasta .
Fitowa a ɗakin Abba yayi yana zolayan Umma "bazaki zo ki mawa mijin ki wanka ya gaji". Murmusawa Umma tayi tace "umm Abban yarona kai da ka girma nan da kwanaki zaka ji anfara ce maka kaka" Abba murmushi yayi yace "wai dai yanzu kice kishi kike tun da an kusa haifamun Amarya sabuwa gal. Umma murmushi tayi batace komai ba, Abba ya shiga wanka ya wasta ruwan ya fito ya shirya, Amjad ma ya fito a shirye, tabarman da Umma ta shimfiɗa masu Abba da Amjad suka zauna suna fira Abba na zoyalan sa.
Umma wasta ruwa tayi ta shirya cikin kaya marassa nauyi, zuwa tayi ta zauna a tabarman gefen ɗan nata. Abinci ta zuba masu duka, kallon Abba tayi tace bismillahi Abban Yarona. Da hanun ta take ɗibo abinci tana bawa yaron nata a baki, Abba zuba masu ido yayi yace "wato dai a gidan nan kullum sai an nuna banbanci, yanzu mutumin da nan da shekara zai haifoman jika shine ake bawa abinci a baki"
Amjad murmushi yayi! Abba yanxu dai jinjiri dani kake wannan magana? Umma ce tasa masu baki a maganan nasu, ba kyau surutu in ana cin abinci.
Shiru suka yi Abba yaci gaba da cin abincin sa, Umma ta ciyar da ɗan ta sanda ya qoshi kamun ta sawa cikin ta. Bayan sun gama cin abincin tattare kwanukan Umma tayi ta ajiye gefe suka kama hira, sallahn magrib da aka qira shi ya tada su duka suka yi alwala Amjad suka yi masallaci dan yin Sallah Umma kuma ta tada nata a gida.
Da sallama mai martaba ya shiga ɗakin matar tasa, akwance ya same ta kaman yadda ya tsammani, Gimbiya ta rungume ta tana baccin itama a gefen ta .
Kallon su yayi sai ƴar tasa ta basa tausayi, shi ciwon rashin uwa bai da daɗi! Ita kuma nata qaddaran ga uwan amma bata da lafiyan da ma zatayi hira da ita bare ta bata shawara ko ta mata faɗa, Allah baki lafiya Meerah. Hawaye ne ya cika idon mai martaba wanda ke nuni da cewa abu ya tuna, banɗakin ɗakin ya wuce yayi alwala yazo ya tada sallah, nafilfulu yayi ya ɗaga hanun sa sama yana addu'a hawaye na bin fuskan sa.
Ya ɗau stawon lokaci yana addu'an kamun ya miqe ya naɗe darduman, ganin ƴar tasa na kwance gefen mahaifiyar ta bai yi gigin tashin ta ba, addu'a ya masu ya shafa masu ya ja masu qofan ɗakin ya fita ya nufi sashen sa.
Rage kayan jikin sa yayi ya kashe wutan dakin ya kwanta, amma bacci ya kasa ɗaukan mai martaba sai juyi yake, daga qarshe alwalan ya qara ɗauro wa yazo ya tada sallah kuma.
Bayan dawowan su masallaci suna zaune duka Amjad, Abba da Umma sai aka masu sallama a qofan gida, da mamaki Umma ta kalli qofan sai Abba ya yunqura zai tashi, Amjad yace "Abba ka zauna zanje na duba waye ne" ya tashi ya nufi qofan gidan.
Amsa Sallaman yayi ganin dogari ne daga fada sai ya masa iso cikin gidan amma sai dogarin yace "a'a ranka ya daɗe nanma yayi, saqon qira ne daga mai martaba, yana buqatan ganin ka gobe da sassafe bayan sallahn asuba" Amjad yace "tom shikkenan Insha Allahu zanzo da safen" godiya Amjad ya masa suka yi sallama dogarin ga juya ya shiga motor ya kama hanyan komawa fada.
Ko da ɗan aiken ya tafi kulle qofan gidan Amjad yayi ya dawo ya zauna gefen Umman sa, Abba ne yace "waye ne yayi sallaman? Amjad ya ce "dogari ne ya zo wai mai martaba ya turo sa, nan ya kwashe duk yacce suka yi da dogarin ya faɗawa wa iyayen nasa". Umma ce ta nisa tace "Allah gwada mana goben da rai da lafiya, Allah shige lamarin ka Allah maka albarka ya dafa maka Jarumin Ummansa. Da Ameen suka amsa shi da Abban nasa.
Umma ce tayi gyaran murya tace "Jarumin Umma mai yasa ɗazu ka maida hanun kyauta baya ? Meyasa kayi jayayya da maganan babba?
Sunkuyar da kansa Amjad yayi ya buɗi baki yace "Umma ta kiyi haquri ki yafemun, kece kika haifeni na kuma kika mun tarbiyya na tabbata kinfi kowa sanin waye ni, in wasu zasu gane ma da su tambayen dalilin qin amsan wannan dukiya ke ya kamata su tambaya dan kece mahaifiya ta, ko mai nayi cikin tarbiyan ki ne. Umma ba jayayya nayi da mai martaba ba face nema wa kaina da iyayena dama ita kanta Gimbiyar mutunci a idon duniya, sannan maganan kyauta kuma Umma yacce muke rayuwanmu haka yafi burgeni, nasan tunda mai martaba yasan daga gidan da nake kuma ya yarje na shiga jerin masu hasa hakan ya tabbatar ya aminta ƴar sa tayi irin rayuwan da muke saboda baiga qazanta a ciki ba, Umma ina mai neman afuwanku ku yafemun na yanke hukunci ba tare da yin shawara daku ba, juyawa yayi wajan Abba , Abba ku gafarce Ni in nayi ba daidai ba.
Murmushi Abba yayi ya sauqe hannun ɗan nasa da ya haɗa alaman roqon afuwan su yace "Allah maka albarka baba na Allah dafa maka a rayuwanka gabanka da bayanka hukunci da ka yanke da dalilin hukuncin duka sunyi sai dai muyi fatan Allah ara mana stawon rai muga bikin nan har da ƴan jikokin mu. Umma ma da murmushi tace "Ameen Angon Amare masu zuwa, Jarumin Umma Allah maka albarka, akoda yaushe ina kasancewa cikin Godiyan Allah da ya bani kai a matsayin ɗa na tabbas akace ɗaya mai albarka yafi dubu taron yuyuyu, Allah maka albarka Allah tabbatar maka da dukkan alkhaeran rayuwanka".
Hira suka ɗan taɓa akan abin da ya gudana yau a cikin garin nasu,. Bayan wasu a wanni tashuwa suka yi duka, raka Amjad ɗakin sa suka yi, Umma ta masa addu'a suka ja masa qofan ɗaki suka nufi nasu ɗakin.
_________
Ameera da Daddyn Little mutan Abuja jirgin su yayi landing lafiya, taxi ne ya kwashesu sai gidan su dake anguwan Asoo road a cikin garin Abuja. Sun yi isan yamma wanda hakan ya sanya bata yi girki ba bayan sun huta suka tafi eatery suka ci abinci suka dawo, da wuri suka kwanta dan gobe Daddyn Little na da morning meeting a wajan aiki kuma ya kwana biyu bayanan.
Yana aiki a 𝘾𝘽𝙉 (𝙘𝙚𝙣𝙩𝙧𝙖𝙡 𝙗𝙖𝙣𝙠 𝙤𝙛 𝙣𝙞𝙜𝙚𝙧𝙞𝙖).
𝙒𝘼𝙎𝙃𝙀 𝙂𝘼𝙍𝙄.....
Amjad bayan sunyi Sallahn asuba sallama ya wa Abban sa, daga masallacin bai koma gida ba hanyan gidan Sarki ya kama dan amsa qiran mai martaba, tafiya ne mai ratan gaske tsakanin su da gidan sarautan, dan gari ne guda Masarautan nasu.
Masarautan qubaish cikin jihar Al-khawr a qasan Qatar.
Gimbiya ba itace ta farka ba sai qiran farko na asuba, janye jikinta a na mahaifiyar ta tayi taje ta ɗauro alwala ta tada sallah.
Mai martaba ne ya shigo ɗakin da zummar tada su Gimbiya suyi Sallah, bakin sa ɗauke da sallama ya shigo tarar da Gimbiya yayi akan sallaya tana nafila, ganin haka sai ya juya da niyan fita a ɗakin, mai ya tuna sai kuma ya dawo zama yayi bakin gadon ya jira ƴar tasa ta idar da raka'atainil fijir. Ko da ta idar durqusawa tayi ta gaida sa, sabahul khair papa, mai martaba yace "sabahul Noor ibnateey, khaifa antee khaifa Amma ki? Nahnu bi Khair papa, khaifal umur? Ibnateey umur sai shukran Lillah... Bayan sun gama gaisawa mai martaba yace "inkin idar da sallah anjuma inason ganinki kamun gari ya gama waye wa" ya faɗa yana miqewa dan fita zuwa masallaci. Tom Papa Allah kaimu adawo lafiya Allah amshi ibadunmu, da Ameen mai martaba ya amsa ya fice a ɗakin. Gimbiya carbi ta jawo ta fara lazumin ta kamun a shiga sallah.
Amjad ya iso gidan sarautan lokacin gari yayi haske, yana isowa qofan fada dogarayen dake wajan suka miqe suna gaida sa, fuska a sake ya ɗaga hannu ya amsa. Wani a cikin dogarayen ne ya masa jaroga har zuwa qofan shiga palourn baqi na mai martaba, suna zuwa qofan dogarin yace "ranka ya daɗe za'a maka iso ni iya nan ne mastaya ta, afito lafiya" yana gama faɗa ya juya ya bar Amjad tsaye a wajan. Yana tsaye wani dogari yazo ya masa iso har cikin palourn baqin, palourn mai girma ne yana ɗauke da set na kujeru 2 sai TV dake maqale a bangon palourn sai fridge babba a gefe, akwai toilet guda biyu a palourn da dai sauran su, palourn ko a Saudi albarka kenan.
Wani qofa dogarin ya nuna masa, yace "ranka ya daɗe wannan qofan zaka shiga mai martaba na ciki, afito lafiya ya masa" ya juya ya fita a wannan palourn. Kallon ɗayan qofan yayi ya tunkare sa, sallama yayi a bakin qofan sanda aka amsa masa kamun ya tura qofan ya shiga palourn.
Mai martaba ne a kishingiɗe sai wasu mutane guda huɗu a palourn, girman wannan palourn ya ninka wanda ya wuce domin kuwa wannan set na kujeru uku 3 ne aciki, sannan ga kumbo a jere a qasa set huɗu 4. Mai martaba na kishingiɗe a shumfiɗeɗɗen carpet da aka jera kumbon akai riqe da carbin sa, sauran mutane huɗun suna zaune a qasa da alama tattauna wa suke.
Zaunawa yayi a qasa shima ya sunkuyar da kai ya gaida mai martaba cikin girmamawa mai martaba da murmushi a fuskan sa ya amsa yana "ka saki jikin ka yarona Muhammadu" qara yin qasa da kai Amjad yayi ya kuma gaida waɗannan mutane suna cikin girmamawa, duk suka amsa da fara'a.
Mai martaba ne yayi gyaran murya kamun ya fara magana "Yarona Muhammadu waɗan nan da kake gani baqi ne da suka samu halartan wannan gasa da kuka yi jiya, sunji daɗin irin salonka kuma sun yaba da kwarjinin ka da jarumtar ka, wanda hakan har ya kwaɗaita masu neman wata alfarma a wajanka da kuma qarin