Showing 63001 words to 66000 words out of 98220 words
Chapter 22 - YAR SARKI CE by Uwar batoolerh.txt
bathroom dis and that ETC.
Komai na ษakin blue color ne
A bakin gadon dake ษakin suka zauna duka yace masa "sannu bro, sannan ya ษaura da basa haquri akan abunda ya faru tsautsayi ne ya yafe sa".
Murmushi kawai yayi bai ce komi ba dama Daddyn Little yayi tsammanin haka
Mutumin bai fiye magana ba sai dai wani lokacin gwanda in Ameerah ce yakan amsa mata jefi-jefi
Bayan taga wucewan su itama cikin gidan tayi
mai gadi ne ya jido kayakin dake motorn duka ya biyota dashi sallama yayi ya jiye masu komi a palourn.
Tana shiga ษaki ta wuce direct dan ta watsa ruwa ganin yanayin garin ana zafi
Bayan Daddyn Little ya masa sallama wucewa yayi cikin palourn nasu ganin bata nan ya wuce ษaki dai dai ya samu Ameera ta gama shirin shiga wanka tana tsaye ษaure da towel sai kawai taji an rungumeta ta baya
Ajiyan zuciya ya sauqe ya lumshe ido yace "wiffeyh wankan zaki shiga ki qyaleni bayan kinsan na gaji ba iyayi da kaina zanyi ba" ya faษa da alaman shagwaษa.
murmushi tayi kai mutumin nan kai fa yanzu ka wuce wanka da yaron ka kuma ga wani ajiyan a ciki kaga ai sai dai awa yaran ka badai a maka ba
Sa hanu yayi zai kunce towel en au wato nine ma mutumi bama za kice husbyn ba ko
Bige hanunsa tayi kai fa ka tsufa yanzu Baban Little
kutt nine na tsufa a guje tayi banษakin tana addu'an shiga toilet
murmushi yayi! Allah ya barmun ke Ameerah ta Allah sa na rigaki mutuwa dan bana jin zan iya zama da kowacce mace bayan ke Allah maki albarka
Shima banษakin ya shiga, wankan suka yi tare suka fito fuskansu da murmushi daga gani kasan qaunan junansu suke sosai basa fatan abunda zai rabasu in ba mutuwa ba.
Shirya junansu suka yi, suka faษa gado tare Ameera tace "washhh baban su little na gaji" bakinta ya kaiwa cafka in baki daina ceman babansu ba sai na cire maki baki yarinya
Kissing junansu suka fara
Janye bakinta tayi tana murmushi kwantar da kanta tayi a qirjinsa tace
"Husby yanzu ya za'a yi da bawan Allahn nan? sa hanunsa yayi yana shafa kanta nima kaina abunda nake tunani kenan wiffey ban san ko zai yarda ya zauna damu har ya samu lafiya sosai ba, gashi bai son magana bare muji ko zai faษa mana ko kaษan ne dangane dashi.
Amma kasan me husby ni wallahi sai fuskansa kemun ษan yanayi da na Abba
Dariya Daddyn Little yasa amma dai wiffey bakisan kama ba to kina ga mutum kaman balarabe kice yana kama da Abba shikkenan kinga anyi 1-1 kema kin zama tsohuwan idonki bai gani har gwanda na amaryata akan ke
Hararan sa tayi a wasa ni dai ka dai na haษani da wancan stohuwan da ta gama zamanin ta
Hiransu suka cigaba dayi a haka har bacci mai daษi ya ษauke su .
A nasa ษangaren ma haka ya lallaษa ya shiga bayi yayi abunda zai yi ya fito ya kwanta dan ya huta wa zaman asibitin da yayi na kwanaki.
Abba sun isa airport inda suka shige jirgi suka kama hanyahn KD
Jirginsu ya isa lafiya, suka samu dakarun sojoji da motoci suna jiran isowan su dama
Shiga Motor suka yi shi da sojojin da aka qaro masa dan staron sa(escort) suka yi gida
Tun kan Motorn nasu ya iso qofan gida aka wangale masu gate sakamakon qaran jiniyan da ya sanar da sojojin dake cikin gidan dawowan mai gidan
Umma da Little ke mata daru wai shi sai dai akaisa wajan auntyn sa Maha, tana jin qaran motocin tace "yauwa Angon gilani oya miqe ga can aboki ya dawo kaje kace masa ya kaika" ta shuwa Little yayi yai hanyan waje
Umma ganin ya fita murmushi tayi tace "kaje can ku qarata da abokin naka dan anma yarona takwara da kai dai a kama a haษani da aikin renon ka"
miqewa tayi ta shige ษaki dan qara gyara jikin ta kamun mijin nata ya shigo.
Gimbiya wajan Ammaan ta taje dan yanzukam jikinta Alhmdlh
abunda har yanzu bata iya yi shine dai ta taka da qafafuwanta har waje kuma abunka da ciwo in ya kwan biyu ma sai a hankali bare ciwon da ya ษibi shekaru
suna aiki da rubutu da kuma magun gunan da Abba ke turo masu kullum
Sosai mutunci ya shiga tsakanin Mai martaba da kuma Abban ๐ผ๐๐
๐ผ๐ฟ.
Hira suke da Ammaan ta amma gaba ษaya tunaninta baya wajan Ammaan nata sosai take jin wani iri da kuma yawan kallon fuskansa a idanuwanta
Ajiyan zuciya ta sauqe, Ammaan ta dake kula da duk yanayin da take ciki murmusawa kawai tayi dan daga ganin ษiyar tata tasan matsalar ta
Kallonta tayi tace "tashi kije ki huta ko ibnateeyh"
Tura baki tayi tace "Ammaa a'a ni ban gaji da hira dake ba kuma ni banajin bacci
To ni kuma na gaji da hiran bacci nake son yi
Qara tura baki tayi idonta ko ya kawo kwallah Ammaan ni ษin? murmushi tayi tashi kije kiyi tunanin surkina da kyau amma adinga masa addu'a
Jin abinda mahaifiyar ta tace sai ta rufe fuskanta da hanunta ta tashi da gudu tabar ษakin tana dariya ya akayi Ammaan ta taramfo ta
Ganin ta fita da gudu har da rufe fuska sai abun ya bawa Sarauniya Dariya
Murmusawa kawai tayi tana Allah maki albarka ibnateeyh Allah nuna mana wannan rana alfarman Rasulullahi Sallallahu Alaihi Wasallam
Ko da t fita a wajan mahaifiyar ta maimakon ta wuce ษakinta sai ta stinci kan ta da son zuwa garden tuna ranan da suka yi sallama sai ta nufi wajan kaman zata same shi zaune yana jiran ta
Kuyangunta ne da suka biyota suka yi saurin mata shumfiษa Suna tambayanta Allah yaja kwanan Gimbiya mai za'a kawo maki ranki shidaษe?
Fuskanta a rufe kaman ko yaushe idonta ma a lumshe bata ko mosta ba bare tace uffan
Suna ganin haka sunsan me take nufi
abunda yaban mamaki banga an shiga ciki ba a nan garden ษin naga an taho mata da fruits ayanke kuma da alama a fridge aka cirosu, kayan itatuwan like kankana, abarba, ayaba, cucumber and apple etc.
Fav fruit nata ta ษauka kankana yanka 1 ta kai bakinta, mai ta tuna sai ta fasa ta ษau Apple ta tauna a hankali Lumshe ido tayi jin daษin Apple ษin ya ratsa mata har kai
she dont know why sosai take jin son ganin wannan kyakkyawan saurayin ko Apple ษin ma dan ta tuna fav fruit nasa ne Shiyasa taci sai kuma taji daษin sa daban yau....
Muje zuwaaโ๏ธ
๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐
๐ฟ๐ผ๐๐ผ ๐๐ผ๐๐๐ผ๐ ๐ผ๐๐๐ผ๐๐ผ๐๐๐
๐
๐๐ผ๐๐๐๐ผ๐๐๐๐ผ ๐๐๐ผ๐ ๐ฝ๐ผ๐๐๐๐๐
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
๐ฟ๐ค๐ข๐๐ฃ ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฉ๐ ๐๐๐๐๐ง๐ ๐ช, ๐ ๐ช ๐ฉ๐ช๐ฃ๐ฉ๐ช๐๐๐ฃ๐ ๐ ๐ฌ๐๐ฃ๐ฃ๐๐ฃ ๐ก๐๐ฎuka:-
08146292652
๐พ๐๐๐ฉ ๐ค๐ฃ๐ก๐ฎ.
09161720046
๐๐ค๐ช ๐๐๐ฃ ๐๐๐ก๐ก ๐๐๐จ ๐ค๐ฃ๐, ๐ญ๐๐ข๐ช ๐ข๐๐ ๐ช ๐ฉ๐๐ก๐ก๐๐ฃ๐ ๐ช ๐ ๐ง๐๐๐ช๐จ๐ ๐ข๐๐ ๐จ๐๐ช๐ฆ๐, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐
# ๐พ๐ค๐ข๐ข๐๐ฃ๐ฉ
# ๐๐๐ ๐ &
# ๐จ๐๐๐ง๐
๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ๐ฆ
๐๐ผ๐ ๐๐ผ๐๐๐ ๐พ๐๐
๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น๐น
๐๐ฉ๐ค๐ง๐ฎ ๐ผ๐ฃ๐ ๐๐ง๐๐ฉ๐ฉ๐๐ฃ
๐ฝ๐ฎ
๐๐๐ง๐๐ง๐ ๐จ๐๐ก๐๐๐ช ๐๐จ๐
(๐๐ฌ๐๐ง batoorl)
ุงูููู
ุตูู ู ุณูู
ุนูู ุณูุฏ ูุง ุฑุณูููู saw๐ค๐ค
_______________________________________________________________
๐ช๐ฎ๐ป๐ป๐ฎ๐ป ๐๐ต๐ฎ๐ณ๐ถ ๐๐ฎ๐ฑ๐ฎ๐๐ธ๐ฎ๐ฟ๐๐ฎ ๐ด๐ฎ๐ฟ๐ฒ๐ธ๐ถ ๐บ๐ฎ๐น๐ฎ๐บ๐ฎ ๐๐ฎ ๐ธ๐๐บ๐ฎ ๐บ๐ฎ๐๐ผ๐๐ถ๐๐ฎ ๐๐ฎ ๐พ๐ฎ๐๐ฎ ๐๐ฎ ๐ด๐ฎ๐ฟ๐ถ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐ต๐ฎ๐ฏ๐ถ๐ฏ๐๐ ๐ฎ๐บ
๐๐ถ๐๐ถ ๐๐ฎ๐ฐ๐ฐ๐ฒ ๐ธ๐ถ๐ธ๐ฒ ๐๐ผ ๐ฑ๐ฎ๐๐ต๐ถ ๐พ๐ฎ๐๐ฎ๐ฟ ๐ฎ๐บ๐ฎ๐ป๐ฎ ๐ผ๐ป๐ฒ ๐น๐ผ๐๐ฒ ๐ฑ๐ฎ๐ด๐ฎ ๐๐๐ฎ๐ฟ ๐ฏ๐ฎ๐๐ผ๐ผ๐ฟ๐น
๐ถ๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐ ๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ข๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐ฐ๐ ๐๐ฐ๐๐บ๐ธ ๐ฒ๐ด๐ด ๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ข๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐ ๐ข๐๐๐๐๐ ๐๐๐ฐ๐ ๐ฑ๐ฐ๐๐พ๐พ๐๐ป
๐ถ๐๐๐๐ข๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐ฒ๐ด๐พ ๐ป๐ฐ๐ต๐ฐ๐๐ธ ๐๐๐ธ๐๐๐ด๐๐ ๐ฐ๐๐๐พ๐ฒ๐ธ๐ฐ๐๐ธ๐พ๐ฝ (๐ฐ๐ฑ๐๐ฑ๐ฐ๐บ๐ฐ๐ ๐๐ฐ๐ณ๐ด๐ด๐) ๐ณ๐ฐ ๐ณ๐ฐ๐๐บ๐ฐ๐ฒ๐ธ๐ฝ ๐๐ฐ ๐๐๐ฐ ๐ฝ๐ฐ ๐ผ๐ด๐ผ๐ฑ๐พ๐ฑ๐ธ๐ฝ ๐๐ฐ๐ฝ๐ฝ๐ฐ๐ฝ ๐บ๐๐ฝ๐ถ๐ธ๐๐ฐ ๐ผ๐ฐ๐ธ ๐ฐ๐ป๐ฑ๐ฐ๐๐บ๐ฐ.
***
๐
ฟ๏ธ 47&48
๐๐ ุงู
ู ุจุชููุฉ๐
Asuban farko Mahreen ta tashi ta gabatar da nafilan ta sannan ta tashi Maha
Ana qiran sallah suka bi masallaci tare da Maha, bayan sun idar da salla kowa azkar nasa yayi da lazumin safe suna shafa addu'a Mahreen ta miqe ta fice a ษakin, Maha kuwa komawa kan gado tayi ta gyara kwanciya dan har yanzu buguwan da tayi jiya yana damun ta
Ko da Mahreen ta fita Gyaran palourn ta soma ta gyara dinning
Sanda ta tabbatar ta gyara ko ina tass ta kunna burner da ta gani
sannan ta wuce kitchen ta ษaura ruwan abun kari
Wanke wanke ta haษa na ฦดan stiraran kwanukan da ba'a wanke su jiya ba dan ta wanke sai ga hayra ta shigo kitchen en da sallama
Amsawa Mahreen tayi suka gaisa hayra tace "sister irin wannan aiki haka da sanyin asuba gaskiya duk wanda ya aure ki ya huta na taya sa murna, ni fa duk jaraban tsohuwar nan da sanyin asuban nan ba fita zan ba atou"
Murmushi Mahreen tayi kai de sissy
Me a cikin aikin asuban yafa fi daษi gaskiya nikam ma banjin sanyinn da kuke faษa a nan Ji nake ma garinsu Umma yafi nan sanyi
Haka dai kika ce sister amma bauchi yafi kaduna sanyi ina ma za'a haษa chaษษ
( to to kuzo ku raba mana musu yan kd da bauchi ina ne yafi sanyi)
Karษan wanke wanken hayra tayi amma da qyar Mahreen ta bar mata sai ta koma kan girkin
A haka suka cigaba da aikinsu suna yi suna hira su bibbiyun su har suka kammala komi
Mahreen tace "tom sissy ni dai ba naje na duba wancan malalaciyar ko ta tashi ko kuma baccin ta koma, Na barki da aikin jerawa a dinning afuwan".
Caษ sister jerawa shine aiki? Ai aikin kam ya qare dan kin riga da kin gama yau delicious naki zamu ci
Murmushi tayi ta fice a kitchen ษin ta nufi ษakin su
tana shiga da sallama kallon ta takai kan gado kaman yacce tayi tsammani kuwa hakan ta tarar a kwance ta samu Maha tayi ษaษษaya tana sharar baccinta kaman bata yi na dare ba
Girgiza kai kawai tayi tace "dede dake ai sai yaya habeeby ษin Allah Ubangiji yasa ya Aure ki ko zai saita mana ke"
Har zata shige bayi sai ta tuna yanxu ba safiya bane a jiddah qaramin wayanta ta jawo tayi dialing layin Ummeyn ta
Yana ringing ษaya Ummeyh ta ษauka tana "Assalamu'alaiki beenty"
Amsa Sallaman tayi "wa'alaikissalam Na'am Ummeyh na antashi lafiya?
Lafiya Alhmdlh ฦดar Ummeyh ya ummata?
Uhmn Ummanki ki ko rigima Ummeyh daga gani ma halin tsohuwar nan Maha ta ษauko wallahi
Eyye Ummeyh kama haษa tayi kaman ฦดar tata na gaban ta nace gidanku Mahreen dan dai kin renani ki dubi idona kice uwata rigima mun fara wasan reni ko?
Uhmn ni dai bance ba Ummeyh, ya Abeeyh?
Igiyan ajiyansa da kika ban ya tsinke ya gudu,
Ki fita idona Mahreen uwata ba sa'an wasan ku ba
Turo baki tayi Allah ya baki haquri Ummeyh
In ya bani haqurin ki qwace da kanki a wajan
Ayya dai Ummeyh na kiyi haquri Allah baki haquri
Ameen to ke kuma Allah ya maki albarka Mahreen ษin Ummeyh da Abbeyh
Murmushi tayi tace "Ummeyh yaushe zakizo? Muna missing naki"
Very soon beenty Insha Allah
Yanzu dai ina Auta? banji mostinta ba
Gata nan kwance kaman kayan wanki Ummeyh tana bacci, Allah ba ษiyarkin nan bata ji ko kaษan Ummeyh ni so nake ma wataran ya soja ya taimaka ya jibge ta ko zata nistu shi kuma baya dukanta kaman me storon ya ko me ta masa sai dai surutu
Ummeyh murmushi tayi tace "duka wannan dogon bayanin akan ฦดar jinjirata Autan Abbeyh tom ta Allah ba taki ba za kiji dashi ne ba mai taษa mun jinjira bawa Auta ta waya nikam naji muryan ta
Daka mata mari a acinya Mahreen tayi "tom sarkin masu baccin safe tashi Ummeyh na magana" ta faษa tana miqa mata wayan.
Hararan Mahreen tayi ta amshi waya sai kuma ta fashe da kuka
ni dai Ummeyh ko kizo mu koma ko na biyo ki tunda nazo ya habeebu duka na yake haka yaya Mahreen ma duk se cin zalina suke ba mai sona sai Umma da Abba da ya Abdoul da yarona
Murmushi Ummeyh tayi tom ai naga masu sonki sun fi masu dukanki yawa kiyi haquri uwata ta kaina duk wanda ya qara taษa ki sai ki haษa shi da Umman ki ko ki faษawa takwaranki kinji
Insha Allah very soon nima zan zo nan da week in Allah yaso ya yarda in dai har ayyuka suka yi dama-dama kinji
Tom Ummeyh naji
Yauwรก to share hawayenki Auntan Ummeyh
turo baki tayi ni dama kuka na ba hawaye
Dariya duka suka yi ita da Ummeyhn nata to Allah ya shiryaki uwata
Maza a tashi aje a gaida Ummata nasan ko gaisuwa ba kiyi ba
Uhmn kawai tace suka yi sallama ta bawa Mahreen wayarta
Sallama suka yi itama ta katse call en, ajiye wayan tayi ta shige bathroom
Maha tashi tayi ta gyara ษakin tsaff kaman ba i taba ta kunna turaren wuta.
Mahreen ta fito wanka da mamaki taga har Maha ta gyaran ษakin kuma tsaff har qamshi yake
Taษe baki tayi dama haka kike kekam kaman me aljanu
Batace ma Maha uffan ba ta wuce dan ta shirya ta fita ta gaida kakus
Maha ma toilet en ta shiga sanda ta wankesa tass sannan tayi wanka itama ta fito
Kusan a tare suka gama shirya wa
Tabarakhallah Masha Allah kyau suka yi sosai kaman masu zuwa gasan kyau
Abaya suka sa ita Mahreen ta saka peach ita kuma Maha ta saka maroon gashi dukansu farare
Kar kuso kuga kyan da suka yi kyau har yana ษiga.
Fita suka yi a ษakin sun samu hayra itama ta gama shirya komi har tayo wanka abunta, dukan su suka yi ษakin Kakus dan gaishe ta
sallama suka yi ta amsa tana ษaurin ษankwali
juyowa tayi tana kallonsu tana murmushi Masha Allah kaga larabawan jikoki na Allah dai ya rayamun ku ya maku albarka
Gaisawa suka yi duka tana qara sa musu albarka
Hayra ce ta shigo tace "Amarya kizo mu karya"
danqwalon hayra tayi dan fatarin kakarki amma ba niba uwaki ce Amarya ba ni ba dan jakan ubanki dama tare dani kike karyawa ko neman magana
Maha da bata iya yin shiru tace "ke dai stohuwar nan ba'a maki gwaninta ko kaษan"
Takwara ke kuma ki fita a idona kamun na taso banson aikin masu tangaษi da sanyin safiyar nan bazaki sani sinqin surutu kaman mai layiii ba
Ita dai Mahreen murmusawa take, tashuwa suka yi suka fice duka suka bar kakus dake qoqarin fitowa itama
Bayan duk sun fito sun zauna a dinning ษin
Maha ce ta kalli hayra tace "yanzu yaya hayra dan jaraban tsohuwan nan itama a dinning take cin abinci mutum na tafiya kaman me tete"
Dariya suka sa duka na rabaki da surutun safe na kakus Maha, kinga dai ke takwaranta ko tom wallahi ba rage maki zata yi ba jaraban masifan ta na safe yafi na ko yaushe
Maha tace "yo to ni ina ruwana tamun na mata kalass"
Kakus ne ta iso wajan tace "ke hariratu ubanki Muhammadu ne mai jaraban masifa, ke kuma mai sunan aljanu ubanki kika rena dan jakar ubanki, tangaษaษษun yara kawai masu sinqin reni".
ja mata kujera hayra tayi ta zauna
Tace "to ina su sojan mijina?
Kai amma dai yaran nan baku da kirki harda ke indo da nake wa kallon mai hankali cikin carbi, yanzu dan sikitin sinqin rashin mutunci shine har za kusa abinci a gaba baku nemo ฦดan uwanku ba sufa sune maza suke nemowa ku ba abinda kuka iya sai ci bari kuji tom inga ษan kwal uban dazai ci abinci anan su soja basu zoba ingwada masa nawa tagaษin yafi nasa"
Maha ce ke qunquni, yauwa kin fara ai kenan da wannan zagin da bansan a ina kika koyo saba
Kallonta kakus en tayi, juyar dakai tayi nide ba inda zani atou
Hayra ce ta tashi taje sashensu ta qira ya Abdoul ta kuma dawowa ta qira ya habeeby
Ta samu ya Abdoul ya gama shiryawa fitowa yayi yayo dinning ษin, shima ya soja dinning en yayo