Showing 30001 words to 33000 words out of 98220 words

yayi irin na masu zuwa yaqi, sosai dai shirin ya masa kyau ya amshe sa. Qaqqarfan namijine wanda kana ganin sa kaga jarumi na gaske, shi kaษ—ai ne zaune a gefen masu gwabzawan da dukkan alamu ษ—ayan bai iso ba tukunna.
Mai magana ne yake jawabi da kuma mawa manyan baqi Barka da halartar wannan taro dan wasu ba'a ma taษ“a tsammanin ganin su ba. Sarkin shela na tsaka da yin magana yaji wajan yayi shiru juyawan da zai yi wani kyakkyawan mutum kuma qaqqarfa ne yake shigowa cikin taron, shigowan nasa ne ya ษ—au hankalin jama'a har ya sanya kowa kusan barin zancen da yake .
Tafiya yake cikin taqama da kuma nuna stantsar Jarumta, wani bafade ne yai masa jagora har wajan zaman da yake aka tanada dan shi, zaman sa ne ya baiwa mutane daman gane cewa shine ษ—ayan abokin gwabzawan Gimbiya, nan take waje ya ษ—au surutu qasa qasa kowa da abinda yake cewa.
Sanye take da kaya mara hayaniya zaka ranste ba dashi za'a gwabza ba, (dan ko shirin sa na zuwa jeji yafi wannan) sai dai shigen nasa yayi bala'in masa kyau Kasancewan sa fari kuma dogo sannan qaqqarfan jarumin na miji.
Siririn tsaki yaja ganin yacce duk akabi aka zuba masa na mujiyoyi(idanuwa) sosai ya tsani yawan kallo ga qananun surutun dake tashi a wajan, wanda baya da ko shakka gulman sa mutane keyi, tsakin ya kuma ja yana magana a zuciyansa "Ni wallahi Umma ba don ke ba banayin wannan wasan yaran, yanzu gashi sai qareman kallo ake ana gulma na in aka cinye maki Ni shikkenan kin huta ai" stakin ya kuma ka yana qara murtuqe fuskan sa, dan karma a raina sa gashi wai zai yi gasa da mace qanwar bayan sa kayan reni "gaskiya Ni Umma baki kyauta mun ba" ya faษ—a yana tura baki kaman yana gaban Umman tasa..
Dayawan mutane a wajan kallonsu ya koma kan Amjad, sakamakon ba kowa ne ya san sa ba, ko karatu ba'a garin yayi ba in ba dai kana shiga kasuwa da Sa'a ba tom sannan ne zaka iya cewa ka taษ“a ganin sa, ฦดammatayen wajen duk sun masa quri da ido.
Duk abun da ake ciki Gimbiya bata da labari kuma bata sani ba dalilin ta faษ—a tunanin yacce zata damu ta kada su a agasan nan ko Papan ta zai bar batun auren ta yanzu, taษ“atan da jakadiya tayi shi ya dawo da ita daga tunanin da ta faษ—a, tana ษ—aga ido Carab sai a kan fuskan Amjad, qare masa kallo tayi kamun ta taษ“e baki "wannan mutum har mutum amma sakali sakalci da girman sa harda tura baki kaman mace a haka ya shiga gasan Gashi dai da zubin jarumai" bayan ta gama zancen ta a ranta taษ“e baki ta kuma yi.
Jakadiya dake gefen ta ne ta murmusa tace "Allah ja kwanan Gimbiyar mu ฦณAR SARKI KUMA JIKAN SARKI SANNAN DAI MATAN SARKI, wannan yarima namu na gobe yayi qoqari tunda har idon Gimbiyar mu ya sauqa a kansa." Girgiza kai Gimbiya tayi wanda hakan ya bawa jakadiya daman fahimtar Yaren uwargijiyan nata abinda take nufi.
Wasu ฦดammataye can gefe ke surutu "ke fa mastala na dake rahama rashin hankali wallahi, bar batun hassada da kike wa Gimbiya yanxu ace kece a matakin datake ga wannan kyakkyawan halittar na tabbata bazakice haka ba, nifa wallahi da ace nice wallahil Azeem da kaina zan buษ—e masa fuskan nawa, ai dai duk kyawun ta ba lallai ta kamosa ba" wacce aka qira da rahama ne tayi shewa hehehe! Lallai ma ita fa ฦณAR SARKI CE ina zaki haษ—a kyawun ta da namiji kede faษ—i gskyh yamaki shiyasa kikace haka, murmushi tayi "rahama kenan, Allah dai ya bawa mai rabo Sa'a namu kallo ne amma duk da haka nide inaso yayi nasara" da Ameen sauran qawayen nata suka amsa....

Sarkin shela ne ya buqaci ganin Gimbiya da kuma ษ—aya daga cikin masu gwabzawa da ita, Sarkin shela bai gama rufe bakinsa ba, anwar ya miqe ya fito don baiso Amjad ya fara ballema yaci dan tun da ya ษ—aqa ido ya gansa yaji kishi ya rufe sa.
Bayan ya shiga Filin ya tsaya, Gimbiya ce ta shigo filin itama cikin takun ta mai ษ—aukan hankali, tun da ta tashi har ta shiga idon Amjad da Anwar na kanta haka ma ษ—okacin jama'an wannan fili duk kowa kallonta yake, Amjad ne ya kauda kai "yanxu in ba Umma ba wannan qaramar yarinya zan aura" stakin ya kuma ja ya kauda kai.
Anwar da Gimbiya Mehwish sun fara fafatawa, Faษ—a Anwar keyi da gaske cikin qwarewa da kuma burgewa, abunda ya sanya har Gimbiya ta murmusa ganin Anwar faษ—a yake bilhaqqi da gaske kaman ba wanda zai janye abun fuskan ta ba, duk ta inda ya juya in ya kawo sara tarewa take, ko halaman kai masa sara ba tayi ba kawai kare nasa harin take ba ta mai da martani ba. Tana yi tana kallon idon sa duk wani mostin sa da yanayin kai saran sa ta haddace,
Wasan da suke ya stuma jama'an wannan fili dan ba abinda kakeji sai ihu ana kiran sunan "GIMBIYA" da kuma "ANWAR" kaman ance ya kalli idon Gimbiyar karaf yasa idonsa cikin nata wanda hakan ya basu daman kallon juna sosai kallon da ya janyo wa Anwar shagala da kusan mancewa a filin gasa yake, Murmushin gefen baki Gimbiya tayi wanda rashin ganin fuskanta baze hanaka gane hakan ba ganin kwayar idonta kaษ—ai ya isa sanya mutum hasaso irin kyawun da murmushin ya mata!! lumshe ido tayi ta kuma buษ—ewa kaman mai jin bacci g kuma wannan haษ—aษ—ษ—en murmushi akan fuskan nata abun da bai wuce seconds ba ya gigita Anwar, yana ganin abun da tai da ido ya susuce be ankare ba ya jishi aqasa.(subhanallahi sannu!!)



๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– " ๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™–"๐™‚๐™ž๐™ข๐™—๐™ž๐™ฎ๐™– ba abun da kakeji yake tashi a wajan dai sunan GIMBIYA mutane na ihu suna qira.
Amjad dake zaune taษ“e baki yayi ya kau da kai. Runste ido Anwar yayi, yana jin kaman ya buษ—e qasa ya shiga dan kunyan da yaji ys lulluษ“e sa!


Amjad kau da kai yayi kaman bai san mai ake awajan ba, zaka ranste besan mai ke faruwa ba. Amma yafi kowa sanin mai yafaru yana kallon duk yacce tayi wa anwar har ta faษ—ar da shi, qaramin tsaki yaja "kai ka jawa kanka bansan mai ka tsaya kallo ba a wajan wannan qaramar yarinya."
Bayan Anwar ya fice a filin da kan sa aqasa bai ko tsaya ba yabar tsakiyar taron muqarraban sa suka bi bayansa.
Sarkin shela ne ya qira sunan Amjad dan ya shiga fili, Gimbiya kuwa tana tsaye a filin tana jiran shigowan sa. Amjad yaji anqira sa amma bai ko mosta ba, daga inda Umma ke zaune tare da Abba ta zubawa ษ—an nata ido, yana ษ—ago kai idon su ya haษ—e da na Umman tasa ba shiri ya miqe ya nufi cikin filin.
Tafiyarsa ma kaษ—ai abun kallo ne da burgewa gaba ษ—aya anzuba mashi ido kuma abinda ya stana kenan kallo!! Umma daga inda take zaune ta murmusa ganin yacce ษ—an nata ya haษ—a fuska kuma tasan idon da yaji yamasa yawa ajiki ne shiyasa cewa tayi "Allah ka shiryamun yaron nan" da Ameen Abba ya amsa, wannan yaron naki ai ko mace albarka yanzu fa kallon ne ya damesa haka muke fama kullum a kasuwa su kuma ฦดammatayen kaman me kallo kam, umma tace "Tom sunga ษ—an kyakkyawan saurayi ba dole ba, Allah dai ya basa Sa'a" da murmushi Abba yace Ameen.
Cikin tsakiyan filin ya tsaya fuskan nan a haษ—e kaman anmasa albishiri da mutuwa, ko alaman murmushi babu a fuskan sa wanda hakan bai ษ“oye kyau en sa ba.
Wallahi rahama wannan bawan Allah duniya ne dubi fa ya haษ—a rai ma kyau ya qara wayyo garin daษ—i na nesa inji hausawa inama nice Gimbiya, "Allah taroki bintalo" faษ—in rahama
Yana tsaye tana staye ko kallon inda take bai yi ba, fuskan sa a haษ—e (wai kace dan ma ฦณAR SARKI CE).
Suna staye shiru dukan su biyun ba wanda ya mosta kowa na kallon ikon Allah, a haka za'a yi gasan? Mai shela ne yayi magana "Allah ja kwanan GIMBIYA za'a iya fara wasa" Amjad yana jin abinda Sarkin shela ya faษ—a amma hakan bai sanya shi motsawa ba staye yake yana kallon duk wani mostin ta.
Ganin yayi shiru kaman mai tunani hakan ya bawa Gimbiya daman ษ—aga takobin ta dan kawo masa saran lokacin ษ—aya ta kadar dashi, sai dai kashhh tana kawowa........






*manxon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam, yace duk wanda ze kwanta bayan adduan baccinsa ya liximci
"Hasbiyallahu la ilah ha illah huwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbul arshil azeem"
Qafa bakwai, Allah zai karesa daga dukkan wani sharri acikin wannan daren, Na mutum ko aljan, ko da jifane asirine Allah zae karemu.
*'Wallahu ahlamu'*


Yin alwala kamun bacci nada matuqar muhimmanci, komin yaya mu daure mu dinga yi walau kinada tsarki walau bakida ( inkina al'adanki)


Allah datar damu yabamu ikon bin dai dai.


Muje zuwa...
ฦณAR SARKI CE daga dausayin Alqalamin uwar batoorl
Justice Hareeyh๐Ÿ•Š๏ธ



๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


๐˜ฟ๐™ค๐™ข๐™ž๐™ฃ ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฉ๐™– ๐™๐™–๐™Ÿ๐™–๐™ง๐™ ๐™ช, ๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™ช๐™ฃ๐™ฉ๐™ช๐™—๐™š๐™ฃ๐™ž ๐™– ๐™ฌ๐™–๐™ฃ๐™ฃ๐™–๐™ฃ ๐™ก๐™–๐™ฎuka:-
08146292652
๐˜พ๐™๐™–๐™ฉ ๐™ค๐™ฃ๐™ก๐™ฎ.
09161720046
๐™”๐™ค๐™ช ๐™˜๐™–๐™ฃ ๐™˜๐™–๐™ก๐™ก ๐™™๐™ž๐™จ ๐™ค๐™ฃ๐™š, ๐™ญ๐™–๐™ข๐™ช ๐™ข๐™–๐™ ๐™ช ๐™ฉ๐™–๐™ก๐™ก๐™–๐™ฃ๐™ ๐™ช ๐™– ๐™ง๐™–๐™๐™ช๐™จ๐™– ๐™ข๐™–๐™ž ๐™จ๐™–๐™ช๐™ฆ๐™ž, wai hausawa sukace sai an gwada akan san na qwarai. Ni Hareeyh ina maraba da ku masoya, har da alakoron talla inayi๐Ÿ˜!!!


# ๐˜พ๐™ค๐™ข๐™ข๐™š๐™ฃ๐™ฉ
# ๐™‡๐™ž๐™ ๐™š &
# ๐™จ๐™๐™–๐™ง๐™š








๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ๐Ÿ’ฆ


๐™”๐˜ผ๐™ ๐™Ž๐˜ผ๐™๐™†๐™„ ๐˜พ๐™€๐™€


๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน๐ŸŒน

๐™Ž๐™ฉ๐™ค๐™ง๐™ฎ ๐˜ผ๐™ฃ๐™™ ๐™’๐™ง๐™ž๐™ฉ๐™ฉ๐™š๐™ฃ

๐˜ฝ๐™ฎ


๐™ƒ๐™–๐™ง๐™ž๐™ง๐™– ๐™จ๐™–๐™ก๐™ž๐™๐™ช ๐™ž๐™จ๐™–


(๐™๐™ฌ๐™–๐™ง batoorl)

ุงู„ู„ู‡ู… ุตู„ู‰ ูˆ ุณู„ู… ุนู„ู‰ ุณูŠุฏ ู†ุง ุฑุณูˆู„ู„ู‡ saw๐Ÿ–ค๐Ÿค


_______________________________________________________________




๐Ÿ…ฟ๏ธ 31&32

๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ ุงู…ู‰ ุจุชูˆู„ุฉ๐Ÿ’‹


















Tana kawo masa sara abinda ya bata mamaki amaimakon ya tare sai kaucewa yayi saran yabi iska, daganan taci gaba dayin duk yacce zata yi ta kadar dashi.
Tayi qoqarin ya kalli idon ta amma bai ko kalla fuskan ta ba ma balle idon ta duk wani mostin da take yi yake kallo kawai (hhhh!!wato dai idon ta makamin ta)
Faษ—a suke sosai( gwani da gwanaye, qwararriya da qwararre anhaษ—e). Ba abunda kake ji sai qaran takobin su da ke bugun juna duk abun da take bai yi yunkurin kai nasa takobin ba sai dai ya tare ko ya kauce ya juya haka ta juya haka faษ—a dai daษ—in kallooo.
Faษ—an ya qayatar da mutane, acikin mutanen waษ—anda suka san sunan shi sai ihu suke suna
"A๐™ข๐™Ÿ๐™–๐™™๐™™" "A๐™ข๐™Ÿ๐™–๐™™๐™™" "A๐™ข๐™Ÿ๐™–๐™™๐™™"
suna ihu suna qiran sunan sa barin ma ฦดammatan wajan
Waษ—annan ฦดammatayen ke ihu suma suna qiran sunan, bintalo ce tace "dan Allah lubcy ji sunan sa ma kaษ—ai abun burgewa dubi yacce yake nasa salon faษ—an" ai kam dai bintalo wannan crush nakin daga gani ya dama Gimbiya a iya faษ—a ya shanye ku ne da nasara da alama, rahama ce tayi caraษ“ tace
"kar dai kuyi saurin yanke hukunci Kun manta wacece GIMBIYA d aalama da kuma iya faษ—an t yaran sarakuna nawa ta gagaresu bare wannan ba ษ—an kowa ba"
dariya bintalo da lubcy suka sanya harda tafawa, wai wa ya gaya maki abun daga kai ษ—an wane ne? Abun baiwa ne rahama staya kisha kallo...


Sauran jama'an kuwa sai cewa suke "GIMBIYA" "GIMBIYA" "GIMBIYA" "GIMBIYA"
Sunansa da aka qira ya qara ษ“atawa Gimbiya rai, sara ta kawo masa ta yacce ko taji masa ciwo ba ruwanta damuwan ta kawai ta kaisa qasa, fusatan da tayi hakan ya masa daษ—i dan tana kawo sara da dukkan qarfinta ya shammace ta ya kauce, kamun ta farga sai jinta tayi a jikin mutum, yana qoqarin kai hanunsa ya kama abun fuskanta dan ya warware..
Wani zabura tayi tabar jikinsa zuciyanta na qara zafi, "har shi wa zai taษ“a jikina? Waye shi da zai yi qoqarin kai hanunsa fuskana, lallai sai na nuna masa bai da wannan jarumtar kuma sai na masa hukuncin taษ“a jikina" tagama saqa maganan ta a zuciyan ta, sai ta ษ—ago ta kalli idonsa, shima kallon ta yake idon su na haษ—uwa ya sakar mata murmushi mai cike da ma'anoni da yawa wanda ko ita kanta bata iya fassara wa ba, kau da kai tayi ( Amma daga gani dai murmushin na mugunta ne).
Ihu jama'ar wannan wajan suka sanya , Sarki har da Murmusawa yayi ko ba komi yasan wataqil wannan ne mijin tilon ฦดar tasa.
Umma ba abinda take sai murmushi cewa take "tabbas ina alfahari da kasancewa ta uwa ga wannan bawan Allah, Allah yai maka albarka jarumin Umma" Abba dake gefen ta shima murmushin yayi yace "Ameen maman Amjad"
Runguman nan fa ya sanyawa gimbiya jin wani iri ta stinci kanta a yanayin da bata san mai yake nufi ba, haka gogan naku ma. Duk wannan abinda suke ji bai hana su cigaba da fafatawa ba, fafatawan da yafi na farko armashi kasancewar Gimbiya na fusace shima Amjad da abun da ya taษ“a masa rai, kai masa wani bugu tayi wanda garin ya kauce saura kaษ—an ya fadi har dai sanda ya sa takobinsa ya tare shi yahanasa kai wa qasa, harta fara jin daษ—in ta kai sa qasa sai kuma murna ya koma ciki ganin ya dawo ya tsaya da qafafunsa cak. Stiririn staki taja wanda dagani sai ita muka ji sa!
Ganin yana kallonta, hakan yasanya ta lumshe ido tabuษ—e su akansa, sai idon nata yayi kaman mai jin bacci, kallon wannan idon da yanayin da ta sarrafa sa in bakada qarfin imani zaka mance ko hanyan garinku, takuwa ci nasara dan tabbas hakan ya haifar masa da qaruwan yanayin da yake ji wanda wannan yanayin haushin sa yake, wannan qaramar yarinya bata isa sashi jin wani abu ba.
Yi yayi kaman ya biye mata yacce take so, tana shammatan sa ta kawo sara, yayi caraษ“ ya buge takobin nata da nasa wanda ya sanya duka tokubban nasu faษ—uwa, ษ—ayan hanun sa ne ya fara warware abun fuskan nata
( ษ—azu daya rungumeta bakin abun da tayi rolling a fuskan ya nemo) abun na fara warware wa ta ษ—auke wuta gaba ษ—aya, dai dai abun ya ciru duka tayi Suman wucen gadi, wanda hakan ya sanya qafanta ya kasa ษ—aukan ta tayi baya luuuuuu zata faษ—i. Hanun da ya sanya a bayanta dan taro ta kar ta faษ—i, kaman wanda aka jonawa shocking haka tayi qasa shima ya bita, a samanta ya faษ—o, fuskansu ya haษ—e.
Wani qara da ihun da aka sanya da shewa ne ya fargar dashi mai yake shirin faruwa (jarumin umma ya mance da ummansa awajan, wani abu sae mace).
Gimbiya Mehwish gaba ษ—aya ta qarisa sumewa,
Sarki da sauran jama'a kowa kallo kawai yake yayin da gefen Umma inbanda murmushi ba abunda take yi, mai martaba gaba ษ—aya yafi kowa jin farinciki a zuciyansa ganin dai wanda yake kyautatawa zaton ya lashe gasar.
Har zai yunqura ya miqe sai kuma kaman an sanya shi ya rasa meya jashi Kawai ya sumbaci qaramin bakinta mai ษ—auke da pink lips nata da tunda ya janye abun fuskan nata bakin kawai yake kallo.
Sumbatan da ya mata ne yayi nasaran farfaษ—o da ita daga wannan suman da tayi, tana buษ—e idonta sai ya haษ—e da nasa, tashuwa yayi ba tareda neman shawaranta ba ya kama hanunta ya tayar da ita. Haushin da take ciki qaruwa yayi ya linku Ji take kaman ta sare masa kai ta huta, Mutuwan jikin da ya same ta kuma ya tafi.
Duk ษ—auka cin jama'an dake wannan fili kuwa sai faman kulle ido suke suna qara buษ—ewa dan tabbatar da wannan mutum ce agabansu ba aljana ba. Hatta mai martaba sai yake ganin kaman ansauya masa ita.
Umma da ke zaune miqewa tayi tana kabbara da hamdala faษ—i take "Allahu Akbar Allah Alhamdulillahi Allah yasa kyawun ki har halinki haka yake Alhmdlh"
Shima Amjad kaman kar yabar kallonta yake ji, amma sai ya basar ya fita a filin lokacin ne nasamu daman kallon fuskan GIMBIYA MEHWISH..
Fara ce irin fari mai ษ—aukan idon nan bazaka ce yellow ba bazaka ce ja ba, tana da dogon hanci siriri fiye da hasashe dogon hancinta da madedecin bakinta waษ—anda suka yi dai-dai da round face nata, idanuwanta manya ne dara-dara, farin idon ta tsabar farin sa har kaman kwantaccen hawaye blue blue a ciki sai qwayan idon nata wanda yake blue blue shima ba har can ba, a maimakon yawanci na wasu da ya kasance baqi, kyakkyawa ce ta ajin qarshe zayyano kyau da haษ—uwa irin na wannan Gimbiya zamu kammala labari a zayyano kyawun ta kawai.


"๐™ˆ๐™–๐™จ๐™๐™–

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login