Showing 81001 words to 84000 words out of 231786 words

Chapter 28 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

"Allah Ya sauwake, Ya baka lafiya. Ya kamata ko chemist ka leka."


Ya jinjina kai yana mai sa hannu ya dauki Ummi dake faman mikomasa hannu tana ɓangala dariya.


***
ABU KAMARI just published "BABI NA ASHIRIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/ZRLvPBGxyab






🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Rahmanir Raheem.


25)


Abu kamar wasa, ƙaramar magana ta zama babba. Cutar amai da gudawa ta yiwa Aliyu kamun kazar kurkuku. Chemist ya je aka haɗa mishi magunguna.


Koyaushe yana gida, hankalin Ramlat ya tashi.


Abu ya wuce kwanaki ya koma sati, Aliyu ya bi ya ƙara ramewa ya yi duhu. Abin ya zamewa Ramlat goma da ashirin, ga ciki ga raino kuma ga kula da miji. Ganin abin ya ci tura ta tursasa mishi da taimakon Baban Nusaiba makwafcinsu, aka kaishi asibiti da motar Baban Nusaibar. Ta bar Ummi a makwafta.


"Madam, ba ka ji bane?"


Ta ɗan dawo hayyacinta ta kara duban inyamurin Likitan.


"Ka dauka ka je ka biya a yi."


Gyada kai kawai ta yi ta mike ta fito zuciyarta cike da tunani ga faduwar gaba. Tsoronta kar ta je Aliyu wani cutar ya shafo mai rikitarwa. Likita ya tabbatar gudawarsa bai da alaƙa da abinda yake tunani ke damun Aliyun, wannan ta sa har scanning sai da ya ce a yi.


"Ya ake ciki Maman Ummi?" Fadin Baban Nusaiba. Ta dubeshi idanunta duk sun faɗa sun yi ciki, ita kanta ta rame sai ƙaton ciki wanda sai ka rantse ya kai watanni takwas.


"Ba komai, bari na karasa na biya."


Ya gyada kai gami da amsawa da toh. Allah Ya taimaka ta taho da Atmcard dinta, ganin kudin hannunta ba zai isa bane ya sa ta fita ta zaro kuɗin. Komai ta biya aka yiwa Aliyu duk abinda ya dace. A nan ne Baban Nusaiba ya yi mata sallama kan zai koma. Godiya sosai ta yi mishi har ya fita sannan ta maido dubanta ga Aliyu wanda ya samu bacci.


Hawaye ta ji sun zubomata sakamakon tunanin da ya yi mata tsinke. Yanzu idan ya mutu me zai koma ya cewa UbangijinSa da Ya ba shi aron rai da kuma lafiya a rayuwa ya kasa tsayuwa ya kyautata rayuwarsa kuma ya godewa wannan ni'ima? Ba wannan ba ma, wace cuta ce da Aliyu? Idan wannan tambayar ta faɗomata a rai, numfashinta har tsayuwa yake cak tsabar firgici.


Tana wannan tunanin ta soma hamma kafin itama ta soma gyangyaɗi saman kujera don ɗakin ba su kaɗai bane, akwai majinyata har uku a bayansu.


Ƙarar wayarta ce ta katsemata baccin, ta yi firgigit ta ɗauka. Amrah ce. Miƙewa ta yi ta fita daga waje.


"Na ji shiru ba ki shigo makaranta ba, kuma nayi niyyar zuwa gidannaki ban san kwatance ba."


Ta haɗiyi miyau mai zafi.


"Muna asibiti, an kwantar da Baban Ummi bai da lafiya."


"Ya Rabb, meke damunsa?"


Ta gano rudewar da Amrah ta yi, ta kuma fahimci dalilin. Hakan ya ƙaramata rashin nutsuwa da tsoro.


"Wallahi ban dai sani ba Amrah, an mishi test."


"Toh Allah Ya sauwaƙe, Ya ba shi lafiya. Zan shigo ko zuwa gobe ne tunda yanzu kam na kama hanyar gida akwai tazara."


Nan suka yi sallama ta mata godiya.


Ganin dacewar ta kira ta sanar a gidan su Aliyu yasa ta dannawa Malam kira. Bayan sun gaisa ta fadamishi Aliyu ba lafiya suna Akth. Nan da nan ya ce gashinan zuwa suka yi sallama.


***
Bayan awanni biyu, tana zaune gefen Aliyu wanda ke shan kunun gyaɗa da Abulle ta kawomishi sai dai hankalinta ba ya tare da su, yana ga Malam da ƙanin Aliyu, Mudan. Suna wurin likita kai sakamakon Aliyun. Kirjinta dukan tara-tara yake yi. Fargaba kan ba'a magana.


"Ya kamata ki je gida ki huta."


Ta kalli Aliyu mai wannan batun cikin karfin hali. Girgiza kai ta yi.


"Um um."


"Nima abinda zan ce kenan, ki tafi gida tunda shi Mudan ne zai kwana, gobe kya shigo. Ai da gajiya, ke dai sannu Allah Ya saukeki lafiya."


Fadin Abulle cike da kulawa, kaunar Ramlatu sosai ke ratsata, tana lura da yanda take ba Zakinnata kulawa.


Shigowar Malam ne ya sanya hankalinsu komawa garesu, fuskar Malam ba za ka iya tantance yanayinta ba.


"Kun dawo? Me likitan ya ce?" Abulle ta nemi sani. Malam ya samu wuri ya zauna.


"Babu komai, sai dai likita ya tabbatar ciwon zuciya na barazanar kama yaron, ya kuma ce lallai ya bar shan duk abinda zai gusar da hankalinsa ko ya shaƙi iska marar dadi, idan kuwa ya ƙi komai ma zai iya faruwa. Shi gudawar sanadin me ma..?"


Ya maida akalar tambayar ga Mudan don shi ya mance ma tsabar damuwa.


Mudan ya dora.


"Bacterial infection ne wanda shan sigari ya haddasa masa, shi ya kawomasa gudawa. Amma ya ce in Sha Allah wannan mai sauki ne. Ya dai ce dole ya kula ya bar shaye-shaye saboda cutar dake masa barazana."


Salati kawai Abulle ke yi ta shiga yiwa Aliyu faɗan ya taimaka mata ya bari, tun tana yi har ta shiga kuka. Aliyu idanunsa suka kaɗa, ya kasa kallon kowa musamman ganin jama'ar ɗakin sun zubamusu idanu gami da baza kunne.


Cak ta mike tsaye.


"Zan wuce gida."


Abinda ta ce kenan. Suka dubeta.


"Toh Ramlatu, ki je da Mudan ya taho da kayan shi Alin. Ba sai kin yo girki ba, daga can gida sai a kawo. Allah Ya baki lafiya kema. Sai hakuri kin ji?"


Malam ke wannan jawabin cikin nutsuwa. Ta gyada kai, har lokacin danne hawayenta take yi, ba ta ko kara kallon Aliyun ba suka fice tare da Mudan. A hanya ma ba ta ce uffan ba duk kuwa da irin korafin da Mudan ke yi akan Aliyun da takaicin abin, suna isa ta haɗamasa abinda za'a buƙata, tare suka fito. Ita ta nufi makwafta ta dauko Ummi shi kuma ya miƙa titi.


Sai da ta zauna a falon tana duban Ummi dake wasanta, ta kara kai duba ga cikinta, kafin wasu zafafan hawaye su soma wanke mata fuska.


"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!" Ita ce kalmar da ta shiga ambata tana kara nanata wa.


Daga wannan sai wannan, komai na zuwarmata a daki-daki. Rayuwa kenan, kalar rayuwar da ta ke hangowa zasu yi da Aliyu a baya, ba irinta ta samu ba. Ta shanye dukkanin komai ta hakura, yanzu kuma ga wata sabuwa. Kukan ta shiga yi sosai, wayarta ta dauki ƙara ba ta yi ƙasa a gwuiwa ba wurin ɗauka ba tare da ta duba ko waye ba.


"Assalamu alaikum."


Ta fadi cikin muryar kuka.


"Waalaikumussalam. Ramlatu? Meke faruwa ne? Kukan me kike?"


Ta yi firgigit ta dawo nutsuwa da hayyacinta, ABBA ne. Da sauri ta saita kanta ta shiga ƴar dariyar yaƙe.


"Lah Abba ina wuni? Ba kuka nake ba, mura ce ta ke neman yimin kamu."


Shiru ya dan biyo baya can kuma Abba ya yi magana


"Kin tabbata Ramlatu?"


Ta gyada kai tana jin sabon kuka na tahomata.


"Eh Abba."


"Shikenan. Ya karatu? Ina fatan dai komai lafiya? Kar ki ga ina ta tambaya, mafarkinki nayi cikin wani irin yanayi shiyasa na damu."


So da kaunar Abbannata ya kara mamayeta. Ta shiga murmushi har cikin zuciyarta.


"Abba lafiyata kalau. Abba na gode na gode. Abba ka yafemin don Allah. Na yi maku laifuka masu tarin yawa, na so kaina.."


"Zancennan ba ya wucewa ne Ramlatu? Ban hanaki tayarwa ba? Sau nawa za'a ce maki ya wuce?"


"To na daina. Ya jikinka?"


Ya yi murmushi mai sauti.


"Jiki da sauki Ramlatu, ba abinda ke damuna yanzun."


Ta tsinci zuciyarta da yin sanyi, dadi ya rufeta.


"Allah Ya karamaka lafiya Abbana."


Ya amsa da amin, ya tambayi Ummi. Nan ta hadashi da ita tana mishi jagwalgwalon hausarta ya yi ta dariya. A karshe Ramlat ta maida wayar kunne.


"Wai ita ƴar nan ba za'a bani aronta ba?"


Ta kasa gaskata kunnuwanta, ba ta taɓa zaton Abban zai nemi Ummin a gidansa ba. Da wani irin farin ciki da ya mantar da ita bakin cikin Aliyu ta amsa.


"Abba ko yau ka aiko a daukarmaka ita."


Dariya Abba ya yi.


"Yanzu yamma ta yi Ramlatu, gobe zan turo Autar Hajiya ta daukarmin ita amma ki nemi iznin mahaifinta."


Sai sannan ta tuna Aliyu, ta ji kamar ta fadawa Abban rashin lafiyarsa amma ta ɓoye gudun kar Abban ya shiga damuwa.


Suka yi sallama, shigowar saƙo ya sa ta dauka. Aliyu ne. Ta bude ta shiga karantawa.


_*"Na cuci kaina Baby, na cutar da mu. Kaicon rayuwar da na zaɓarwa kaina. Ki yi hakuri ki yafemin. Ki tayani addu'a, da yardar Allah zan daina. Na daina din ma Baby. Abin ne ya ke zamemin kamar karamin hauka idan ban yi. Ciwon kai da damuwa su tararmin."*_


Ta ɗan yamutse fuska kawai ta share batun. Dakyar ta iya miƙewa ta shiga wanka ƙofa a bude saboda Ummi.


Babu komai a kicin din sai wani guntun Doya da Aliyu ya siyo. Kusan kwana uku kenan da ƙarewar abincinsu sai maneji.
Dafa doyar ta yi, Allah Ya taimaka tana da sauran yaji ta ci da shi.


A daren ta yiwa Aliyu text na zuwan Ummi gidansu, bai hana ba sai fatan alheri.


***
Washegari kuwa tun safe Mudan ya kirata akan kar ta zo za'a basu sallama zuwa anjima, hakan na yi fiyemata don bata kaunar shiga asibitin a yi mata kallon matar mashayi. Abin da kunya.


Wuraren karfe sha daya na safe sai ga Amrah, ba jimawa sai ga A'isha ta zo ɗaukar Ummi. A tsaitsaye ko zama ba ta yi ba har Ramlat ta mike ta shiga dakin dauko jakar Ummi da ta haɗa kayanta.


"Ke kam Auta ko zama fa ba ki yi ba." Fadin Amrah tana kallon A'isha dake tsaye tana dan yiwa Ummin wasa. Ko ba komai yarinyar ta shiga ransu sosai. Taɓe baki ta yi.


"Wallahi Anti Amrah sauri nake, kinsan yau za'a soma bikin Yaya Hilal. Zamu je tare da Anti Bilkisu, tana can tana jirana."


Daidai sadda Ramlat ta fito, karaf maganar ya shiga kunnenta. Ji ta yi gabanta ya fadi, Hilal zai yi aure? Ko ya ya dama tasan sai ta ji wani iri. Hilal mutumin da ya yi mata so da kaunar da wani ɗa namiji bai mata makamancinsa ba. Ya mata so a sadda ya kamata ace ya fi kowa gudunta adalilin wulaƙanci da cin mutuncin da take mishi, sai dai madadin hakan cewa yake "Bana miki son da zan iya barinsa a lokaci guda."


Ta sauke ajiyar zuciya gami da share fuskarta da gyarawa gudun kada su gane. Karasowa ta yi sadda A'isha ke koɗa matar Hilal.


"Ba ki ganta ba wallahi kyakkyawa da ita ga kirki. Har waya suna yi da Hajiya."


Jakar ta miƙamata.


"Gashinan."


A'isha ta karɓa tana kallonta kadan don so take ta ƙular da ita. Amrah da bata gane ba ta yi murmushi.


"Aikuwa na yi mishi murna wallahi. Allah Ya basu zaman lafiya."


"Amin. Na wuce."


Suka yi mata fatan alheri ta fita.


Shiru ya biyo baya kafin Amrah ta dubeta.


"Wai meke samun Aliyun?"


Ta haɗiyi miyau mai daci, nan ta kwashe dukkan abinda ke faruwa ta fadamata. Salati kawai Amrah ke yi, hakan ya kara raunana zuciyar Ramlat ta fashe da kuka.


"Kinga sakamakon abinda na aikata ko? Duk abinda kika ce ya faru a kaina. Na wulakanta kaina kafin kowa ya wulakantani. Na fita zakka a cikin ƴan uwana. Amrah rayuwata ta ƙare, na kashe kaina da hannuna. Ban taɓa riskar farin ciki mai daurewa a aurena da Aliyu ba banda bakin ciki da takaici. Me zan ce ga yarana a sadda suka dubeni suka tuhumeni da zaɓamusu mahaifi irin .."


Hannun Amrah ta ji a saman bakinta, ta shiga girgiza mata kai tana fidda hawaye.


"Ya isa, ya isa don Allah Ramlat. Ki gaggauta istigfari, kin fita hayyacinki har kin soma kalaman saɓawa mahaliccinki. Kar ki manta, Allah Ya riga Ya rubuta zuwan yaranki duniya ta jikin Aliyu. Ki yi hakuri ki yi ta istigfari da nemawa mijinki shiriya. Addu'ar mace ga mijinta ba ya faɗuwa. Komai ta roƙamasa, Allah zai amsa."


Gyada kai Ramlat ta shiga yi tana sauke numfashi. Haka suka wuni da Amrah, tana cike da jin kunya ganin Amrar ce ta fita ta yi musu cefane da kudinta ta dawo suka girka dafadukan taliya suka ci.


"Kina da labarin yajin aikin da aka soma kuwa?"


Fadin Amrah, ta zaro ido.


"A'a, ki ce sun tafi?"


Taɓe baki Amrah ta yi.


"Asuu ai basu yi ba, ina ta so na fadamaki na manta. Zaman gidan ya ganmu. Karatu a ƙasarnan ya zama abinda ya zama."


Ramlat ta numfasa.


"Allah Ya kyauta."


Suka amsa da amin.


Amrah na nan Aliyu ya dawo, gaisawa kawai suka yi sannan ta wuce.


***
BAYAN SATI DAYA.


Jikin Aliyu sosai ya yi sauki don har ya ci gaba da fita kasuwa. Sabon yaron shagonsa Sama'ila, ya je ya tarar ya tafiyar da komai duk kuwa da irin ɓarnar da ya mishi na karya wasu cikin farashin kayayyakinsa. Shi a nasa tunanin ya yi dabarar da kayan zasu siyu.
Kayan abinci ya soma kaiwa gidansa, duk abinda yasan za'a buƙata. Hakan da ya yi ya yiwa Ramlat dadi, ba ta fita ko'ina iyakacinta makwaftansu sai fita awo asibiti. Zaman gida sosai ya kamata musamman sanadin yajin aikin da ake wanda ba ta ga ranar kammalawa ba.


***


Ummi ta zama ƴar Hajiya, koyaushe idan Abba na gida suna tare. Wannan ne silar da yasa Munir dauke ƙafa daga gidan. Ba ya kaunar ganin yarinyar tare da su. Akwai sadda ya gaji ya yi magana


"Yanzu Hajiya ba za ku maida yarinyar nan ba?"


Ta daure fuska.


"Ai dama ina kula da kai, na lura da take-takenka Muniru. Ka fita idona, ko ba komai ai hannunka bai ruɓewa ka yanke ka yarr. Duk lalacewar Ramlatu kanwarka.."


"Shikenan, shikenan Hajiya. Allah Ya huci zuciyarki. Da yardar Allah ba zan ƙara magana a kai ba."
Ta yi kwafa.


"Ka ma ƙara mana Muniru. Ka ma ƙara tunda kai zuciyarka ba ta san afuwa da mantuwa ba. Mu da muka haifeta mun yi hakuri sai kai ko? To ka ci gaba."


Shi dai ya yi shiru ya lallaɓa ya bar gidan.


***
"Yaron nan da yake auren Ramlatu fa naji kamar jama'a na raɗe-raɗin yana da cutar ƙanjamau, shiyasa nace gwara na faɗa maka."


Abba ya ji gabansa ya fadi, ya tsurawa manajansa Audu ido.


"Wa ya fadamaka wannan zancen? A ina ka ji?"


Audu ya gyara zama don dama maganar na cinsa, kwana hudu kenan da ya ji daga bakin ƙaninsa Lamin wanda yake abokin kasuwancin Aliyun a kasuwa.


"Laminu ƙanina, ai kasan kasuwarsu daya. Kwanakin baya a asibiti ma ya kwanta, yanzu haka dai ya koma kasuwa kowa na takatsantsan da shi."


"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun! Ka tabbatar da wannan zancen Audu?"


Audu ya gyada kai cike da karfin gwuiwa.


"Kwarai kuwa Alhaji, wannan magana haka take."


Abba ya mike tsaye da sauri.


"Alhaji."


Abba ya daga mishi hannunsa wanda har rawa yake.


"Tafiya zan yi Audu, ka kula da komai."


Cike da ladabi Audu ya gyada kai da kara russunawa har Abban ya fita. Wani a shagon da suke kira Garzali ya ƙaraso wurinsa.


"Amma ba ka kyauta ba Maigida, sai da nace kar ka fadawa Alhaji wannan zancen amman ka ƙi."


Audu ya harareshi.


"Kai waye da za ka fadamin abinda ya dace da wanda bai dace ba Garzali? Kar ka manta a ƙasana kake, idan na ga dama sai na yi maka sanadin barin shagonnan."


Garzali ya daga hannu alamun saranda ya wuce ya na mai ba shi hakuri.


***
Shi kuwa Abba yana fita, Idi na ganinsa ya taso da sauri, wasu a gefe na gaida Abba bai ma tsaya amsawa ba.


"Muje."


Ya fadi hana kama hannun ƙofar motar, da sauri Idi ya bude da muƙulli ya budemasa ya shiga. Shima ya shiga ya ja suka wuce.


Idi na lura da yanda Abban ya yi shiru yana fidda numfashi, ya kasa hakuri ya cez


"Ranka ya dade ko asibiti zamu wuce?"


Abba ya yi murmushin takaici ya girgiza kai yana ci gaba da jin wani zafi a kirjinsa.


"Aa idi, kai ni cikin iyalina. Ba komai."


Idi ya amsa ba don ya so ba suka nufi gidan.


Abba kuwa tunanin da ya soma zuwa kansa shi ne Ramlatu ta kamu da cutar ƙanjamau.


'Shikenan ya cuci ɗiyata,ya kashemin rayuwarta. Innalillahi wa inna ilaihir raajiun.'


Abba ke nanata wa a ransa. Ya zama dole ya je ya dauko ɗiyarsa.


***
"Please Zaki ka bar bibiyata. Haba! Wai dole ne na kulaka?"


Aliyu baki sake yake duban G Baba wanda ke kokarin shigewa wata haɗaɗɗiyar Jeep sabuwa dal. Koda dai dama, mahaifinsa mai kudi ne, yanzun kuma ya samu aiki ya bar yawon shashanci aure ma zai yi.


"G Baba, ni kake cewa na daina binka? Don ubanka ka manta waye ni a wurinka ko?"


Aliyu ya ƙarashe da ƴar zolaya, so yake ya samu ko rance ne yana son yin odar abayoyin mata daga Dubai.


G Baba ya kalleshi kallon raini kafin ya ja guntun tsaki.


"And so? Wai don Allah ka yi zaton ban san cutar da ke damunka bane? Kana yawo da HIV shi ne kake so na ci gaba da yawo da kai sunana ya ɓaci a hanani auren Teemah? Haba Zaki, kai kanka kana iya tunawa iyakarmu bariki, ko gidanmu ka ga na taɓa kuskuren kai dayanku? No! So please ka fita daga rayuwata ka bar bibiyata. Ni wallahi daga yau abotar tamu ma na datseta da ƙaton almakashi. Ban sanka ba, kai ma ka saka a rai ba ka sanni ba. Ka je can ka ji da lafiyarka. Mtsw."


Daga haka ya shige motarsa ya bar filin parking din na kwari. Dama kasuwar ya shigo ganin wani abokin Dad dinsa wanda zai hadomishi lefe daga Dubai. Aliyu ya bishi da kallo har ya fice. Ranar iyakar wuya ya kai, wato kowa ma kallon mai cutar ƙanjamau yake mishi shiyasa kowa ya juyamasa baya a kasuwar.


Dawowarsa kenan daga wani gidan abinci ya hango G Baba zai tsallaka ya biyo bayanshi don dama yana ta kiransa a waya bai daga ba, shi ne ya mishi wannan cin kashin.


Haka ya koma kasuwar ransa na suya, karshe ma kasa zama ya yi ya mike ya tafi gida don dama lokacin tashi ta kusa.


Ramlat na zaune tana karatun Alkur'ani bayan ta gama girki sai ganinsa ta yi, ya zube saman kujera ransa a ɓace. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login