Showing 132001 words to 135000 words out of 231786 words
Chapter 45 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
wata dariya ta kufcemasa. Rigar bacci ce a jikinta shara-shara kuma marar tsawo don duka tsawon iyakarsa gwuiwa. Ƙaton tumbinta da ruguza-ruguzan mamanta wadanda suka zube sun kwanta luf sun bayyana cikin rigar. Damtsenta kuwa a cike sosai sai dai ba ka misalta shi da na karfafan maza ba. Akwai bambanci.
Duba sosai ya ke mata, riga dai gatanan mai ɗan karen kyau da daukar ido. Lumshe idanunsa ya yi yayinda wani tunani ya bijiromasa.
'Za ta yi kyau sosai.' Ya furta ƙasa ransa, ankara da kuskuren kalaminsa ne yasa shi jan istigfari. Sai kuma lokacin ya tuna da bai yi sallar Isha'i ba ya ke shirin kwanciya. Abin yana damunsa, ya rasa me ke shagaltar da shi daga bautar UbangijinSa, ma'ana gabatar da sallah akan lokaci. Abin yana mishi ciwo, sai dai mafi yawan lokaci ji yake kamar wanda aka mantar. Sau tari ma wani bacci ke zuwa ya rufe idanunsa da zarar an soma kiraye-kirayen sallah.
Ganin ya mike yasa Hajiya Zeenatu tunkaroshi, hannayenta biyu ta sanya saman kugunsa.
Ya yi mata murmushi mai kama da yaƙe. Duk yanda ya so nunamata tsana ko wani abun, sai ya ji ya kasa.
"My Zeenat, kin yi kyau sosai."
Wani sanyin dadi ya mamayeta, ta sumbaci leɓɓansa.
"Nagode Sweetheart."
Ganin tana kokarin wuce gona da iri yasa shi janye jiki.
"Bari nayi sallah."
"Sallah, wace sallar?"
Yanda ta fadi a mamakince shima sai ta jefashi cikin mamakin kalamanta. Ya zubamata idanunsa mai adon fari ƙal da baƙin kwayar idanu siɗik.
"Me kike nufi? Wace Sallah muke yi matsayinmu na musulmai?"
Gaban Hajiya Zeenatu ya bada dam!
_*"Kiyi duk yanda za ki yi, ki dinga shagaltar da shi daga ibada, zamu turamasa arnen aljan wanda zai tayaki yaƙi. Ina kara gargadinki! Kar ki kusa ki bari ya dinga sallah akan lokutanta!!!"*_
Wannan yana daga cikin farkon abinda Gora ya fadi mata sadda suka soma zuwa wurinsa a karon farko game da lamuran Hussein.
Ganin ta tsaya tana kallonsa yasa shi giftawa ya fice zuwa banɗaki. Ta bi ƙofar da kallo.
'Ke me zai dameki? Ba yanzu za ki yi aikin da za ki samu ciki ba? Idan kika samu komai zai zo karshe!'
Wani ɓangare na zuciyarta ya tunatar da ita. Ta sauke ajiyar zuciya tana wani irin murmushi kafin ta zauna gefen gadon. Tana kallonsa ya yi sallah a tsanake, ya yi addu'a kafin ya naɗe dardumar ya mike.
Mintuna talatin da suka biyo baya, komai ya kammalu kamar yanda ta ke so, murmushi kawai take kamar koyaushe cike da gamsuwa idan ka ɗauke Hussein wanda ransa sam ba dadi. Kusan hakan ce ta saba faruwa da su, zai iya cewa wahalar da shi kawai ta ke yi a kowace tafiya don ba wani gamsuwa yake ba. Ganin ta soma jan munshari yasa shi miƙewa ya faɗa banɗaki. Can ya fito ya sauya kaya, yunwar ɗazun ce ta dawo mishi. Matsawa ya yi ya tasheta. Cikin magagin bacci ta dubeshi.
"Lafiya?"
"Muje ki ɗan ɗumaman abinci, nasan yanzu John ya sanya a fridge."
Yamutse fuska ta yi.
"Wallahi na gaji, ko nan da can ba zan iya motsawa ba. Ka je kawai ka tasheshi ya yi maka."
Daga haka ta juya ta cigaba da bacci, girgiza kai ya yi gami da gyaramata abun rufa. Wayoyinsa ya dauka ya fita daga dakin cike da damuwa. Kamar akwai abinda ya rasa, kamar yana da wata damuwa amma ya kasa gane kan zaren.
Maimakon ya kira John da ya wuce Boysquarters, sai ya ɓige da dafa ruwan shayi, ya zaɓi shan tea da bread kawai. Sai da ya kammala ya dawo falon, wayarsa ya fiddo ya kunna Data. Kwanaki biyu kenan rabonsa da hawa online, wannan tasa saƙonni suka shiga faɗowa, da na mutanen da ya sani da baƙin lamba kamar koyaushe. Ya kuma riga da yasan baƙin lambobin bai wuce na mata, idan da sabo ya ci ace ya saba.
Saƙonta ya ɗauki hankalinsa, ya kuma yi mamakin ganinta online, ya kara duban lokaci. Ƙarfe goma daidai na dare. Murmushi ya yi ganin amsar da ta ba shi a wancan lokacin, maimakon mayar da martaninsa sai ya ɓige da wata tsokanar.
"Ba ki yi bacci ba? Da wa kike hira toh?"
Yana aika hakan sai ya maida kai ya ci gaba da shan shayinsa. Tausayinta ya ji ya mamaye zuciyarsa, shakka babu sam bai kyauta ba.
***
A ɓangaren Ramlat, tana kwance ne tana kallon Status, duk duniyarta ba dadi. Ga lamarin Chairman ga kuma Hussein da ya yi fushi da ita. Tana shirin sauka ganin uban hamman da ta ke dokawa, sai ta nemi baccin ta fasa ganin saƙon da ya shigo. Da wani irin ɗoki ta buɗe ta karanta. Murmushi sosai take yi haɗe da dariya ciki-ciki. Ko ba komai hankalinta ya kwanta.
"Kai nake jira, hakuri nake so na ƙara ba ka."
Abinda ta aikamasa kenan.
***
Yana kammala shan shayin, ya dauki wayar, ganin abinda ta ce yasa shi jin wani daam, lumshe idanu ya yi kafin ya buɗesu. Sai kawai ya zaɓi kiranta. Kai tsaye ya dokamata kira, sai da ya kusan katsewa sannan ta ɗaga.
***
"Kira war haka? Ina Madam dinka? Ka rufan asiri."
Abinda ta ce kenan bayan ɗaga wayar.
"Ni kenan na tonawa kaina asiri ko? So kike yi a gane damuwar da ke kwance saman fuskata na jefaki a damuwa?"
Maganarsa sai ta yi mata nauyi, ta rasa amsar bayarwa, can ta daure.
"A'a, ni ce mai laifi, ni na zaƙe da yawa. Ka.."
"Kika ƙara bani hakuri ina miki rantsuwa da Allah za ki ganni a gidanku yanzu."
Yanda ya yi maganar daga ji ka san ba wai faɗa ya yi ne kawai ba. Kirjinta ya soma bugu da ƙarfi, ta ji kanta na neman tarwatsewa. Ta kasa gane a maudu'in da za ta jefa kalamansa. Ta rasa abinda ya haɗa kalmar hakuri da batun ziyartarta a wannan lokaci don haka sai ta kasa cewa uffan. Shiru ya biyo baya na ƴan sakanni sai numfashin junansu da kowanne ke jin fitarsa.
"Ɗazun na ce kinsan me? Ba ki bari na ƙarasa ba, yanzun ki bani damar na ƙarasa maganata."
Ta kasa ce mishi uffan. Har ya kara magana.
"Na baka." Ta furta a hankali.
"Ke ce mace ta farko bayan Zeenat, da lambarta ya shiga cikin wayata har nayi saving. Ke ce mace ta farko da ƙafata ya taka har gidansu, ke ce mace ta farko da na zauna muka yi hira da ita har na tsawon mintoci ba tare da naji hirar ta ishe ni ba. Kawai dai idan so ki sani, kina da babban matsayi a rayuwata da ba zan ce gashinan ba. I want you to keep staying in my life, ina jinki kamar wata ƴar uwata mai bani ƙwarin gwuiwa. Kamar dai kina ban ƙarfin ci gaba da rayuwa, na daina tunanin inama Allah Ya dauki raina, na bar tunanin bani da kowa a duniya. Please Ramlat, kar ki gujeni ko me zai faru, ko me zan miki. Kiyi hakuri, nayi maki laifi a ɗazun da ni kaina ba haka na so ba. I just can't do otherwise idan aka zo irin wannan lamarin. Ban kuma san dalili ba."
Wani sabon yanayi ke shigarta game da HUSSEIN, wani abu take ji na yawo tun daga tsakar kanta har yatsun ƙafafu. Zuciyarta gaba daya ta cika da tausayinsa. Ganin kamar tana neman wuce gona da iri yasa ta saurin magana.
"In sha Allah hakan ba za ta faru ba. Allah ne Ya haɗa mu, ban isa na kawo karshen zumuntarmu ba. Ina rokon Allah Ya yayemaka dukkan damuwarka. Sai dai don Allah ina roƙonka akan ka dage da kai kukanka gareSa. Kamar yanda ka bani shawara a ɗazun, kaima yanzu ina so ka yi amfani da hakan."
Murmushi ya yi mai sauti yana ƙara gyara mazaunin wayar, ƙafafunsa a saman kujera.
"Kina shiga haƙƙin Madam ɗita fa."
Harara ta bugamishi kamar yana kallonta, wani abu ta ji kamar ya soke ta a ƙahon zuci mai kama da KISHI.
"Ai ba ni na kiraka ba, sai da safe."
Tana ji yana dariya sadda ta datse kiran. Ita kuwa kwanciya ta yi ta shiga duniyar tunani. Murmushi sosai ta ke yi, wani sabon yanayi take ji game da Hussein wanda a yanzu ta kasa ƙaryatawa. Tunaninta ya tsaya cak! A gefe guda kuma tausayin kanta ya mamayeta. Wato dai ta gama fahimtar ta faɗa SON MASO WANI.
Miƙewa ta yi ta faɗa banɗaki ta dauro alwala, nafila ta shiga yi kafin ta yiwa Hussein addu'a ta musamman.
***
Washegari ta tashi ranta fari ƙal, kaso mai yawa na damuwarta ya yaye. Ta yarda ta kuma aminta, ta rasa dabara ko wani makami da za ta kare kanta na cewar ta faɗa tarkon SO.
Tana kai yara makaranta ta wuce kai tsaye Head of service inda ta kai takardar neman transfer da ta rubuta. Kusan sun yi waya da Zulaihat da Rafee'ah, duk sun goyi bayanta don a cewarsu mutunci ya fi komai.
Kai tsaye ofishinsa ta nufa ganin da ta yi ya iso. Kwankwasawa ta yi gami da sallama, jin muryarta da gaggawa ya bata umarnin shigowa. Ta shiga fuska a haɗe. Kallonta yake har da ɗan miƙewa duk ya rikice. Ya san da cewa ya mata laifi amma ba yanda ya iya, gani ya yi idan ya biyemata to fa za ta kai shi ta baro ne. Ba tare da ta damu ta gaidashi ba ta fiddo ƙaramar envelope waanda ta sanya dukkan kuɗaɗen da ya bata.
"Idan har wannan ce damar da ka samu na zuwa tambayar aurena a gidan iyayena, to ka sani daga yau na rusata. Kuma kar ka manta, ni ba yarinya ba ce ballantana ka yi tunanin za'a tursasani ko a yimin dole akan aurenka."
Ta zazzage kudin saman tebur.
"Ka ƙirga ka gani, idan da su kake taƙama har ka yimin wannan aika-aikar, ko sisi ban taɓa a cikinsu ba. Ina fatan daga yau komai zai wuce. Kar kuma ka kara tunanin cewa zuwa wurin Kawu Bello zai ba ka dukkan wata dama a kaina."
Daga haka ta juya da zummar tafiya ya dakatar da ita ta hanyar kiran sunanta. Ta juyo tana dubansa fuska a daure. Gaba daya ya sauya fuska.
"Haba Ramlat, saboda na bi hanyar da addini ya tsara na neman iznin aurenki gurin magabata shi ne za ki watsan ƙasa a ido? Wannan wace irin kiyayya kike nunamin? Ina da kudi, ina da gidaje da dukkan matsayin da na cancanci ki so ni dominsu, amma ke wannan duk bai sa kin saduda ba. Idan don matana ne, wallahi wallahi ba zan haɗaki gida ɗaya da su ba. Kin ji rantsuwar ɗan musulmi. Ya kike nema ki yimin wannan kwalelan?"
Ta dubeshi duba na raini, ita dariya ma ya soma bata.
"Ni kudi bai isa ya siyeni ba, hakanan ba kuɗi ake nema a zamantakewar aure ba. Yarda, biyayya, kauna, so, mutunci, daraja da ƙima dama sauransu, su ake neman a aure. Babu ko daya da ka samu a idona. Ina kara neman alfarma akan ka rabu da ni ka fita daga rayuwata. Ba zan iya aurenka ba."
"Idan kudi na siyan soyayya! Wallahi Ramlatu sai kin aureni koda ba kya so! Mu zuba ni da ke!!"
Ya fadi a tsawance, kalaman sun faɗarmata da gaba, ta dake ta yi murmushi.
"Allah Zai tsayamin."
Daga haka ta sa kai ta fice dama ba da niyyar zama ta zo ba. Maimakon ta yi gida sai ta nufi gidan Amrah da aka sallama, ƙara duba jikinta.
Ta sameta kamar ba ita ba don Magajiya har ta koma gida. Tun a asibitin suka sauya shawara, da ace ta dawo gida gwara Magajiyar ta biyota gidanta su kwana tare.
"Ya na ganki wata iri? Ke kullum dai da damuwa kike zuwarmin." Amrah ta ƙarashe cike da zolaya. Harara ta samu daga Ramlat. Sai kuma ta ja tsaki.
"Ke kinsan dalilin wai da yasa Kawu ke nemana?"
Amrah ta girgiza kai. Nan ta labartamata komai da komai har haduwarta da Hussein da yanda ta kaya tsakaninta da Chairman yanzun a Ofis.
"Kai jama'a! Wai shi wannan mutumin da me yake taƙama ne? Ai sai ki yiwa kanki kiyamullaili, ba zama za ki yi ki zuba ido ba. Wallahi ki yi kokarin fito da miji ki yi aure abinki ya fiyemaki alheri, ke kanki kinsan tunda ya furta ba kyaleki zai yi ba."
Ramlat idanunta suka cicciko, batun fito da miji sai ya yi mata famin rashin Aliyu. Banda kaddarar mutuwa da ke kan kowa, yanzun da ba tana cikin inuwar aure ba? Waye zai ganta har ya ce yana sonta ko kuma ita ta ji son mutumin da ya yi mata nisa?
"Ni wallahi da ace wannan Hussein din ba shi da mata, wallahi zan so ki aureshi. Mutum ne iya mutum. Ke ko shi ko dan uwansa Hassan."
Kalaman Amrah suka sa ta fiddo idanu tana dubanta, Amrah ta yi dariya.
"Meye toh? Allah kuwa ni na fi so ma ki yi auren nesa. Kinsan mutane magulmata ne. Abinda ya riga ya wuce ma sai su ɗagoshi. Kuma fa ni sai naga kamar Hussein dinnan sonki yake."
Guntun tsaki Ramlat ta ja. Gabanta na faduwa, yanzun ko sunansa aka ambata sai ta ji sauyi a zuciya da kwanjinta😜
"Malama mu bar maganarnan, ba ta da fa'ida."
Dariya sosai Amrah ta yi, ta fuskanci inda Ramlatun ta sa gaba kawai dai ta yi shiru ta ga gudun ruwanta. Matar da ko labarin Hussein ta ke bada wa sai yanayinta ya sauya.
"Uhum, a juri zuwa rafi." Fadin Amrah kafin ta kai mangwaron da ta kammala yankamusu bakinta. Harara ta kuma samu daga Ramlat.
***
ADAMAWA..
I just published "BABI NA ARBA'IN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/dlZmI7H2Cbb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
*_Rufaida Umar_*
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
40)
*Assalamu alaikum. Masu karanta Karfen Kafa ku yi hakuri. Na fadamaku exams zan soma gobe In Sha Allah. Daga wannan post din kuma sai sadda ku ka ji ni. Nagode sosai sosai.*
ADAMAWA..
Ɗaure fuska ya yi kamar bai taɓa dariya ba yana duban Dada, cikin harshen fulatanci ya yi magana.
"Akan me zai sauka a gidannan? Me hakan ke nufi?"
Dada ta harareshi.
"Taheer ɗan uwanku ne, don ya zaɓi gidannan matsayin wurin kwanansa ba laifi bane. Kar ka manta ɗan ɗan uwana ne."
AlHassan ya ɗan dafe goshi, sam bai ji dadin wannan hukunci ba. Sallamar direba rike da ƙaton akwati yasa AlHassan miƙewa.
"Ni zan wuce Dada, akwai inda zan je."
Ta bishi da a dawo lafiya, a kofar suka yi kiciɓus da Taheer. Dauke kai ya yi kamar bai ganshi ba zai wuce, da sauri Taheer ya karasa ya mika masa hannu da sallama. Akan dole ya bude nashi hannun suka gaisa daga nan bai ƙara cewa uffan ba ya yi gaba.
Taheer ya bishi da harara, dama ca ya tsaneshi saboda girman kai. Shi kuwa ya zo kuma sai ya cimma manufarsa, idan ana so dole sai Hafsat ta so shi ta kaunceshi. Sai ya aureta.
Dada ta tarbeshi a mutunce, aka mika kayansa dakin su AlHassan na baya.
Hafsat dake makaranta tana dawowa ta yi kiciɓus da shi a falo yana cin abinci suna hira da Dada kamar dama can sun wani saba. Turus ta yi tana kallonsa ranta na wani irin zafi, Dada ce ta lura da ita.
"Mene na tsayawa haka kamar kin ga Dodo?" Dada ta furta cikin harshen Fulatanci sanin da ta yi Taheer din kusan ba abinda aka koyamusu, manyan yara Modibbon ne kaɗai masu jin fulatanci. Su kam saura sai Hausa da turanci.
Maganar Dada ya kai hankalin Taheer ɗin ga Hafsat, ƙuramata idanu ya yi, ta watsamasa harara ta kauda kai gami da karasowa ciki. Maimakon ta ba shi haushi sai ta ba shi dariya. Ya yi murmushi.
"Welcome my dearest."
Ya faɗi sanin da ya yi shi ɗin ma Dada ba ji ta ke ba. Ciki-ciki ta gaidashi saboda hararar da Dada ke watsamata. Ya amsa a sake. Ta mike ta faɗa ɗakinta har wani kwalla ta ji sun cikamata idanu tsabar ɓacin ran ganinsa. Ta rantse ba za ta ƙara kwana a gidannan ba, gidan AlHassan za ta wuce.
Tana soma haɗa kaya kenan sai ga Dada. Nan ta yi mata kaca-kaca ta kuma rantse muddin ta ce za ta bar gidan sai ta saɓamata.
"Ku kenan haka ku ke son na mutu da bakin cikin ban shirya da ƴan uwana ba? Yayana ya mutu ya bar ni zuciyarsa cike da burin ganin watarana su Hamma Modibbo sun riƙemu matsayin jininsu kuma ƴan uwa, bai samu ya ga hakan ba, sai yanzun da Allah Ya soma amsa addu'a ta har gashinan wani a gidan Modibbo ya yi sha'awar zuwa gidannan ku ke neman ku sanyamin ciwon kai? Toh sa ƙafa ki fita daga gidannan mu zuba ni da ku!"
Dada na kaiwa nan ta fice ranta na suya. Hafsat ta yi cilli da atamfar da ke hannunta ta fashe da kuka. Dada ba ta san manufar Taheer na shigowa gidannan ba. Ita kuwa ta rantse nan duniya ba wanda zai sa ta aurensa. Sai dai ko me zai faru ya faru.
***.
_*So ne baƙin duhu zallah, a faƙaice zai yi ma illah, ciwon so ba ya biɗar sassaƙe...*_
*Hamisu Breaker.*
KANO.
Karfe biyar da mintuna na yammacin Asabar, tsaye yake jan abin motsa jikin na (Treadmill), daga shi sai riga da gajeran wando. Ya sanya tawul a saman wuyansa, a hankali yake tafiya ba kamar Hisham dake gefe yana zabga uban gudu ba.
Kacokan kusan hankalinsa ba'a jikinsa yake ba, Hisham ya kalleshi ya fi a ƙirga, karshe ya tsayar ya sauka yana maida numfashi, kai tsaye water bottle ya dauka dake gefen jakunkunansu ya shiga kurɓa can ya ƙaraso ya tsaya gami da dafe ƙarfen da Hussain ke kai, ya ƙuramasa ido.
"Lafiya?"
Ya fadi yana maida numfashin gajiya.
Hussein ya dubeshi. Sai a sannan ya yi amfani da ƙaramin tawul din ya goge gumin da ke zirarowa daga goshinsa har yana ɗiga daga karan hancinsa zuwa baki.
"Me ka gani?"
Gira Hisham ya ɗaga yana murmushi.
"Sai wani tunani kake kamar wanda ya faɗa tarkon so."
Kallonsa Hussein ya yi a karo na biyu kafin ya sauka ya zauna saman kujera.
Hisham