Showing 228001 words to 231000 words out of 231786 words
Chapter 77 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
abinka da babba, sai ta ce mata lallai ta yi zamanta a ɓangarenta ta dinga hutawa tunda a sannan Dada ba ita kadai ba ce, wata dattijuwa kuma yar uwarta dake Mubi, Mariya ta dawo nan domin taya Dada zama. Mace ce da ba ta taɓa haihuwa ba ga kuma girma da ya ɗan kama ta babu mijin aure. Ita kanta tana jin dadin zama da Dada.
Kamar koyaushe, yau dinma tana kwana a falo, daga ita sai vest fara mara hannu da wando pencil da bai karasa ƙaurinta ba. Tun fitar Hussein take jin tashin zuciya, ta rasa meke mata dadi. Kamshin komai a gidan ma ji ta ke yana hawa kanta, karshe ma miƙewa ta yi kawai ta zura dogon hijabinta ta zagaya ɗan barandarsu da ake hango garden ta shimfida ƙatuwar dardumarta ta zauna. Ba laifi ta ɗan ji sauyi, ahankali kuma bacci ya yi awon gaba da ita.
Sallama ya yi har sau uku shiru, da mamaki ya karasa shigowa falon a karshe ya shiga leƙa kicin da dakuna. Bandaki ma wayam, yana shirin leƙawa sashinsa ya hango ƙofar fita ta hanyar kicin a bude don haka ya karasa. Sosai abin ya ba shi mamaki, ba ta taɓa yin haka ba, ga dai iskar fanka da komai a falon amma ta dawo nan ta kwanta, yanzu kam ya yarda ba ta da lafiya. Karasawa ya yi ya sa hannu saman goshinta. Zafin da ya ɗan ji ne ya sa shi shafa gefen fuskar.
"Ya Salam."
Jin hannunsa ta yi firgigit ta farka da salati. Ya kama hannunta.
"Sannu Heart, dama ba ki da lafiya? Tashi muje asibiti."
Ta mike zaune tana shafe fuskarta, sosai kam ta yi bacci don har yamma ta kawo kai, ta tuno ko sallah ba ta yi ba.
"Ban yi sallah ba."
Ya taimaka mata ta mike, yana rike da ƙugunta suka ƙarasa ciki, sai dai su na sanya kai a falon ƙamshin airfreshner da ta fesa ya hautsina mata ƴan hanji. Tana kokarin zama jikinsa daga natata hanyar amfani da hannun damanta ta dora saman kirjinsa za ta tureshi, shi kuwa ƙara riƙo ta yake a rude yana tambayar lafiya. Sai dai ina! Tuni ta soma sheƙa amai har yana ɓata jikin Hussein. Nan da nan ta zaro ido a rikice, ba ta mance sadda ta yiwa Aliyu amai a jiki ba ya ɗauketa da lafiyayyan mari yana ɗura ashariya.
"Ka yi haku.."
"Shii! Muje ki wanke jikinki." Ya ja ta suka nufi bangarenta, sai da ya cire rigarsa da ta ɓaci har da singilet, kafin itama ya ciremata nata dogon hijabin. Bandaki ya shiga ya hada ruwa. Wankan suka yi tare, duk wani abin ƙamshi da ya ɗauko za ta girgiza kai ta ce ita ba ta so, Hussein dai murmushi ya ke da fatan Allah Yasa abinda yake tunani ya tabbata. Sai da ya daukomata kaya sannan ya wuce sashinsa ɗaure da tawul a ƙugu. Ƙananun kaya ya sa kawai ya fesa turare. Aikuwa tana jin ƙamshin turarensa ta fada bandaki a guje ta shiga sheƙa wani aman, koda zai shigo ya dakatar da shi kamar ta yi kuka.
"Ni bana son kamshin turarenka."
"Toh fa." Ya tsinci kanshi da faɗi, turaren da a baya take masifar so kenan, Sorry kawai ya furta sannan ya fita daga dakin. Kaya ya je ya sauya sai dai wannan karon bai yi gangancin fesa turaren ba. Suka ɗunguma suka wuce asibiti, ta waya ya shaidawa Dada ya kai Ramlat asbiti. Dada murmushi kawai ta yi da addu'ar Allah Ya bata lafiya.
Kyakkyawan albishir din da ya yi fata kuwa shi ya samu, wato dai ciki ne da ita. Yanda ya dinga tarairayarta tun daga asibitin har gida, ita abin ma kunya ya dinga ba ta.
Tun daga ranar kuwa kulawar da Hussein ke ba ta na musamman ne, tausayi sosai ta ke ba shi ganin yanda ta ke laulayi mai wahalarwa. Ita kanta abin tsoro ya dinga ba ta, gani take kamar wannan haihuwar farko ne za ta yi don komai sabo ta ke ganinsa.
Kafin watannin haihuwar su cika gaba daya ta sauya, ta rame, sai ƙaton ciki wanda scanning ya nuna ɗa ɗaya ne kawai. Kowa kallon mai haihuwar biyu yake mata, duk yanda ta so ya bari ta je Kano ta haihu ya ƙi, itama don kanta ta hakura da batun zuwa don ko nawa za'a ba ta a yanda take ji, ba za ta iya bin hanyar Kano ba.
***
Bacci ya ke sosai, yayinda ita kuwa baiwar Allah ta zubawa silin din ɗakin idanu wanda hasken farin wata ya haska, mararta da bayanta babu inda ba ya ciwo, a hankali ta miƙe zaune tana cije baki, ta rasa ma ina za ta sa ranta, wani irin murɗawa da ya yi ba ta san sadda ta ɗakawa Hussein duka ba. Ya mike kuwa firgigit don a farko bai dauka mutum ne ya dakeshi ba, hannu yasa ya kunna fitilsr bedside yana kallonta gami da ruƙo ta.
Ta matse hannunsa ƙam!
"Mutuwa zan yi wallahi!"
"No! Naƙudar ce? Bari muje asibiti."
Haka ya mike tsaye yana gyara zaman pyjamas dinsa. Dakyar ya samu nutsuwar ganin mukullin motar, ficewa ya soma yi da ita, Buzu Maigadi da fitowarsa daga bandaki kenan, ya ajiye butar ya karaso da sauri ya taimaka ya karbi mukullin motar ya budemishi yana kwaranyo addu'ar Allah Ya bata lafiya. Lokacin wuraren ukun dare ne. Sai da Hussein ya zaunar da ita kafin ya koma a guje ya dauko akwatin da tun shigar cikin wata tara ta haɗa abinta.
Su Dada basu sani ba sai ƙarar buɗe kyaure da rufewa suka ji. Ba shiri ta fito ita da Baba Mariya a ruɗe, nan Buzu ke fadamusu Madam ce ba lafiya. Nan da nan a rude suka kira wayar Hussein, amma ina tana ta ringing bai ɗaga. A dole suka koma ciki don ba direban da zai kai su. Nafiloli suka shiga yi da addu'ar Allah Ya sauketa lafiya don sun sani loda sun je, ba abinda za su iya yi mata sai addu'ar.
***
Ramlat suna zuwa ko awa ɗaya cikakka ba ta yi ba ta haifo ɗanta namiji, sai dai kafin Nos ta yi wani yunƙurin, wata naƙudar ta kara zuwar ma Ramlatu, da mamaki Metron da Nos suka ƙara yin kan Ramlat, wannan karon sai da aka haɗamata da ruwan naƙuda, ba karamin galabaita ta yi ba, Hussein kamar kansa zai tarwatse yana daga waje, ga kukan jariri yana ji kuma ana fadin ai ba ta kammala ba. Ga murna ga kuma tashin hankali da tausayin matarsa. Kalmar mutuwar da ta ambata har yanzu ba ta sakeshi ba, fargaba sosai ya ke ciki duk kuwa da ya sani mutuwar ba a baki ta ke ba.
Kukan jaririn da ya kara ji, sai ya rude, ya rasa na farkon ne ko na biyun, kawai sai ya cusa kai ba tare da neman izni ba. Aikuwa wata jaririyar ce aka kara cirowa Ramlat. Ita kuwa ta lumshe ido sai faman sauke ajiyar zuciya ta ke yi.
Dole ya fita yana murna, kafin a kammala gyarasu ya shiga laluben waya don ya sanarwa Dada da ɗan uwansa sai dai wayam. Hakanan ya hakura ya dinga murna da farin cikinsa shi ɗaya. Gaba daya jariran aka kawomasa, Metron na fadin sai fa ya ba ta goron albishir, dariya ya yi yana ɗaukarsu.
"Ki biyoni bashi."
Itama dariyar ta yi ta miƙa masa tana fatan Allah Ya rayamasa.
Kammanin Dada sak ko kuma yace kamanninsa yake hangowa a fuskar yaran wadanda suma ke cike a kansu a saman fuskarsu.
Sumbatar kowannensu ya yi yana mai jin taruwar kwalla a idanunsa, ashe dai wataran mafarkinsa zai tabbata, zai ga gudan jininsa? Ya soma yiwa namijin huɗuba a kunne kafin ya juya ga macen.
Daga nan kuma ya yi zamansa yana ƙaremusu kallo, haka har aka soma kiraye-kirayen Assalatu. Aka ba shi umarnin ganin Ramlat, ya shiga ciki. Ta zubamusu do tana kallonsu cike da kauna, yana karasowa ta yi murmushi.
"Alhamdulillah." Ta furta, ya ajiye yaran a gefe kusa da ita ya sumbaci goshinta shima ya na hamdalar. Dakyar ya samu ya wuce masallaci. Ana idar da sallah ba jimawa sai ga AlHassan tare da su Dada.
Kowa ya ga ƴan biyunnan sai ya hau murna. Dada har da hawayenta tunawa da ta yi da Yayanta kuma ɗan uwanta Aminu.
Ranar dai Ramlatu ta sha baƙi dakyar aka fice aka bar ta ita kadai ta samu bacci mai nauyi ya fisgeta. Jariran kuwa su na hannu, wannan ya dauka wannan ya dauka har sai da Hussein ya yi ta maza ya ce ya isa hakanan su ma a bar su su huta. Duk shaƙiyancin da ake mishi ko a jikinsa. Ya shimfidesu a kusa da uwar ya tsaya ya kuramusu idanu yana kallo. Ya kalli Ramlatun ya kallesu. Tausayinta ya kamashi, ba karamar wuya ta ci ba. A karshe dai ya fice ya bar su. Sai da Dada ta lallaɓashi kafin ya koma gida ya yi wanka ya sanya suturar arziki ya kuma biya shago ya siyo kayan jarirai na mace don kusan rabin siyayyar duk na namiji suka yi jin abinda scanning ya bayar.
Kwanan Ramlatu biyu aka sallameta, sashin Dada ta koma inda Baba Mariya ke wanketa tas ita kuwa Dada ke wanke jarirai.
Hussein ko yana ofis ba ya rabo da waya. Ranar suna aka sanyawa yara suna Amina da Aminu, farin cikin Dada ba ya misaltuwa. Daidai da iyalan Kawu sai da suka zo suna wannan karon har da Umma matar Baba Dakta, Hajiya ma ta so zuwa sai dai makarantar yara ta sanya dole ta hakura amma itama kam zuwa lokacin kewar diyarta take ji. Abinda ya yiwa Ramlatu dadi bai wuce na zuwan Muhibbat ba. Sosai ta yaba da wannan karar da ta yi mata, abin mamaki kuma har saƙo ta samu na kayan jarirai daga iyayen Hilal, matar Hilal ta kira ta mata barka ta kuma yi mata fatan alheri. Koda ta ke ba su Rafee'ah da suka zo suna labarin wayar, dariya suka yi.
"Ai ke yanzu wacce da kika sani a baya yanzu ba ita ba ce, ko ma dai mene ai yanzu dole ta sauko tunda aure zai ƙara kuma yanzu ko ba komai ta ga kin auri wanda ya shanye mijinta a komai da komai na rayuwa.
Jinjina kai kawai ta yi tana murmushi a ƙasan ranta tana mai hamdala da Ubangiji.
***
Rayuwa sosai ta ke yiwa Ramlat da mijinta dadi, zuwa lokacin gininsa da yake ya kammala sai fenti da ake yi da kuma zuba furnitures da ya yi saura. A wannan lokacin ne kuma ba zato ya yi mata albishir da kai ziyara Kano. Dama tun sadda ta yi kwanaki arba'in ta ke saka rai da hakan, ya nuna ba yanzun ba. Har faɗa suka yi ta gama fushin ta haƙura ta sauko. Haka ta dinga shirya tsaraba, Dada ma ta haɗamata da nata.
Hajiya ba karamin farin ciki ta yi ba, abincin da Ramlatun ta fi kauna shi ta girka mata, hakanan Umma itama ta aikomata girki. Su Ummi kamar su haɗiye ƴan biyu wadanda suka dauko hasken mahaifinsu kamar ka latsa jini ya fito. Duk ganin da Ramlat ke yiwa Ummi tana da gashi sadda tana ƙarama ashe ba komai bane idan aka haɗa da na Meena. Kamar yanda suke kiran Amina don Dada sam ta hana a ɓoye suna.
Hisham kuwa koda ya ga amininsa sai ya hau dariya da zolayarsa ganin yanda ya ajiye naman wuya ya ƙara zama wani fresh. Har gidan su Hisham din ya je ya gaida mahaifiyarsa kafin ya koma masauki.
Washegari ya juya Adamawa ya bar Ramlat, sati biyu kawai ya ba ta hakanan ta hakura don a son ranta ne ta yi wata guda cif. Ai kuwa a sati biyun ta zage yan uwa da abokan arziki, koda ta je gidan Yaya Munir ta kara shan mamakin zamantakewar matansa wadanda tuni ya haɗe su gida daya. Salma kanwar Bilkisu ita kanta ta sauya ta yi sanyi. Anan suka hadu ta dinga ba ta hakurin abinda ya faru a baya, banda murmushi ba ahinda Ramlatun ta yi don har ga Allah ita kam yanzu dukkan kunci ko bakin cikin da ta shaƙa a baya ta bar sanya damuwarsa a rai sai dai ta tuno ta auna da yanzu ta godewa Allah.
Ana jibi zasu tafi ne ta fita tare da Amrah, daga gidan Muhibbat suke kafin su karasa wani katafaren shago don nemawa Kausar wani man jiki da ta addabeta a kansa. Dama daga Kano ake aikamata, wacce kuma ta ke siya wajenta, nata ya ƙare.
Sai da suka fito Amrah na kara yi mata bayanin wani maganin mata da ta ba ta, ba zato ta ji an kirayi sunanta. Juyawa suka yi a tare ita da Amrah, mamaki ya kama su ganin Chairman da wasu ƴan matan yara da zasu kai shekaru goma sha biyu zuwa goma, bayan yaran sun gaishesu ya basu umarnin shiga shagon kafin ya zo. Ya juyo ga su Ramlat, suka gaidashi fuska ba walwala. Sai da ya soma da neman gafarar Ramlatun kafin ya dora.
"Kina da labarin rasuwar Hajiya Zeenatu ko?"
Kusan a firgice ita da Amrah suka ce.
"Hajiya Zeenatu?!"
Ya jinjina kai da mamakin rashin saninsu.
"Ta rasu yau wata hudu kenan, tun dai iftila'in gobara da ya afkawa shagonta ta samu matsalar shanyewar ɓarin jiki. Haka dai a sanadin jinya komai nata ya ƙare. Sau ɗaya naje duba ta na kuma bada tallafin kuɗi domin a yi mata abinda ya dace. Na isketa cikin mawuyacin halin da har babu wani ko wata da ke tsaye a kanta domin jinya. Nima saƙo ta bayar ta hanyar Ƙawarta Hajiya Batool akan a faɗamin. Ta bar min wasiyya akan duk sadda na haɗu da ke ko Hussein na nemamata gafararku. Ita kanta yanzu Hajiya Batool din kokawa take da tata lafiyar, ciwon Kansar Gaba take fama da shi. Abin dai babu dadi don yanzu haka ɗanta ma ba ya ƙasar, ya juya da iyalinsa ƙasar waje."
Chairman na kaiwa nan ya girgiza kai, kansa a ƙasa kafin ya ɗago ya dubi su Ramlat wadanda tsoron Allah ya kuma mamayesu. Wai Hajiya Zeenatu ta mutu. Lallai Allah abin tsoro.
"Ki yafemin nima Ramlatu, ko aurenki da na je nema banda soyayya har da sa hannun Hajiya Zeenatu."
Ya basu labarin komai, take Ramlat ta ce ta yafemishi, aka rabu suka wuce shi kuma ya shige ciki.
"Allah Kenan! Kin ji yanda jikina ya yi sani Ramlat?"
Amrah ke zancen tana matsar kwallar tunanin rayuwa, shakka babu DAN ADAM ba a bakin komai yake ba. Ramlat ta sa hannu ta share nata hawayen.
"Bari kawai Amrah, duniya abin tsoro. Allah Ya gafartamata. Ni dama ban riƙe ta ba, wadanda ta yiwa su ne abin ji."
Amrah ta gyada kai.
"Allah Ya basu ikon yafemata."
Ramlat ta amsa da amin. Haka suka dinga maganar su na kara roƙon Ubangiji akan cikawa da imani.
Washegari kuwa duk yanda ta so Hussein ya amincemata da ziyarta Halima a gidan yari kamar yanda ta ƙudurta, sai dai ina! Hussein ya ce bai lamunta ba. Dakyar da siɗin goshi ta shawo kansa ya amince akan ta nemi Yusufa ƙanin Halima ta isar da saƙo ta hannunsa. Hakan ba yanda ta iya kuwa, ta aikata. Yusufa ya zo har gidansu Ramlatun, bayan sun gaisa ta ke tambayarsa batun Halima.
"Yaya Halima tana nan, wallahi wacce kika sani a baya yanzu ba ita bace Anti. Ina nufin sauyi a ɓangaren ɗabi'u da halayya, ta samu sake litattafai da dama na addininta. Koyaushe idan na kai mata ziyara sai ta tambayeni ko ina da labarinki. Amma in sha Allahu yanzu kam ina da labarai kwando-kwando da zan kai mata har da na twins."
Ya fadi yana kara sumbayar goshin yaran, Ramlat ta yi dariya. Basu rabu ba sai da ta ba shi kudi da nashi, da kuma na siyayyar abin bukata da ta ce ya yiwa Halima. Ta kara da fadin.
"Ka isarmata da saƙon gaisuwata sosai."
Yusufa da farin ciki ya sa kwalla taramasa, ya yi ta yiwa Ramlat godiya, ita dai ta karbi yaranta ta yi cikin gida.
***
Koda suka koma Adamawa, ba ta ɓoyewa Hussein komai ba, har faɗa ya dinga yi akan don me ta tsaya kula wani ƙaton a waje. Dakyar ta lallaɓashi ta nemi gafara ya hakura ya sauko. A karshe kuma ya ce bai son batun Hajiya Zeenatu. Hakanan ta kyale zancen sai dai ta ci ɗamarar ƙara yinta ko nan gaba ne. Ɓangaren Dada kuwa koda ta ji murmushi ta yi.
"Babu sauran tabon matarnan a zuciyata, ni tuni na mance da ita. Na kuma yafemata, Allah Ya gafartamata."
Ramlat ta amsa da amin cike da jin dadi. Hakanan bangaren AlHassan shi dama mai sauki ne.
Satinsu biyu da dawowa Adamawa suka tattara suka tare a sabon ginin gidansu. Gida ƙerarre flathouse mai shegen kyau. Tsayawa fasaltawa ma ɓata lokaci ne. An ɗan yi liyafa ƙarami wanda yan uwa da abokan arziki suka zo, daman kafin nan sai da aka yi saukar Alkur'ani a gidan. Kowa ya yaba ya kuma sanya albarka. Daga bisani aka watse aka bar Hussein da iyalinsa.
***
BAYAN SHEKARA ƊAYA
Rayuwa mai tsari da kuma daɗi su ke gudanarwa, ƴan biyu sun yi wayo sun yi ɓulɓul abinsu. Duk inda ka gansu sau sun burgeka, Amina ta fi Aminunta ƙiba sosai, sai dai duk ƙibarta idan rikici ya haɗasu yanzun zai kirɓeta. Ita kuwa ta wangale baki da kuka, idan kuwa ka ce za ka ɗau mataki akan Aminun, yanzun za ta hau taremishi tana dukan wanda ke kokarin dukansa. Shiyasa iyayen basu shiga rikicinsu.
Yau ma Ramlatu na zaune jiki duk babu kuzari, gaba daya damuwa ta bayyana karara saman fuskarta, tun safe ta yi test na ciki da pt-strip sakamako ya bata positive, tana jin Aminu na kukan cizon da Amina ta narka mishi a gadon baya, ya kuwa bi ta a guje ya shiga bugu, aikuwa da Ramlat ta fusata ta yi kansu duka biyun ta zane tas. Suka haɗa kai su na kuka ita kuwa ta shige ɗaki don takaicinsu. A haka uban ya shigo ya iskesu.