Showing 135001 words to 138000 words out of 231786 words
Chapter 46 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
bai hakura ba ya ƙaraso ya zauna gefensa.
"Kai mutumin, na fa gama gane bakin zaren. Ka dai yi gamo."
Guntun tsaki Hussein ya ja.
"Kai maganar ma da ba ta kamata ba yinta ka ke yi. So kuma? Ban da lokacin shirmennan."
Murmushi kawai Hisham ya yi. Kamar ya ce wani abu sai dai bai ce ba.
Wayar Hisham din ce ta dauki ƙara, ganin sunan da ke jiki ya sanya shi satar kallon Hussein yana murmushi. Shi kam bai ma san yana yi ba, wai harara a duhu.
"Ranki ya daɗe Antinmu."
Fadin hakan yasa Hussein satar kallonsa, ya basar kamar bai gani ba, can ya ce.
"Af, wayarta ba chaji ne toh inaga don ba ta saba kashewar ba."
Can ya ƙara faɗin.
"Toh Allah Ya kaimu goben, amma dai a tahomin da yaranmu."
Hussein ya gaji da satar kallon ya juyo gaba dayansa yana mai tsuramasa idanu.
Dariya Hisham ya yi, ba don bayanin Ramlat din ya ba shi dariya ba sai dai yanayin amininnasa.
"Ayya toh Allah Ya maidomana su lafiya. Allah Ya kaimu goben. In Sha Allah idan na koma zan sanarmata."
Daga haka ya kashe wayar. Yana dariya ciki-ciki ya ce.
"Kai kuma wannan mayun idanun da ka tsuramin fa? Toh wallahi kurwata kurrr!"
Duka Hussein ya kai mishi a kafaɗa, ya yi dariya. Shi kuwa ya mike ya dauki jakarsa ya yi gaba zuwa hanyar banɗaki. Yana jin Hisham na fadin.
"Oho dai, na gane komai!"
Har ya kammala shiri yana maimaita kalmar na gane komai din da Hisham ya furta.
Sai da ya kimtsa sosai ya fito, wannan karon dogon wando ja ne ya sa da t-shirt bodyhug fara ƙal.
"Sai ka taho."
Hisham ya bude baki.
"Au haka za ka yimin? Toh ai shikenan. Nidai gobe kam ba zan zo ba, inada baƙuwa ta musamman a gidana."
Taɓe baki Hussein ya yi.
"Matsalarka." Daga haka ya yi gaba bayan ya yi sallama da ƙalilan da suke a dakin motsa jikin. Hisham ya bishi da kallo yana dariya.
***
WASHEGARI...
Cikin shirinta tsaf na riga doguwa ta shadda kalar sea green ya sha adon stones. Mayafi ƙarami ta ɗora samansa. Tuƙi take hankalinta kwance, kaso na damuwarta
Sati daya kenan da ta nemi sauyin wurin aiki, ta samu takardar sauyi daga ma'aikatarta zuwa ma'aikatar ilimi. Wani farin ciki na musamman take ji, ko ba komai za ta rabu da alaƙaƙai. A gefe guda kuma ta gama fahimtar yanda ta yi nisa a son HUSSEIN. Soyayyar da idan ta tuna shi ma dadi take ji, murmushi take yi
Ta bude hirarsu ya fi a ƙirga, ta tuna zantukansu ya fi sau dari a satinnan. Ji take inama yanda take jinsa shima haka take a wajensa. Har ta ƙaraso gidan A'isha ba ta bar tunaninsa ba.
"Assalamu alaikum."
Ta furta sadda ta isa ƙofar falon, ƴar aikin A'isha mai suna Bingel, ta amsamata sallamar. Laulayi da ta soma ne yasa dole Hajiya nemarmata ƴar aiki wata dattijuwa. Suka gaisa ta karasa cikin falon daidai da fitowar A'ishar daga ɗaki. Baki Ramlat ta saki tana kallon yanda duk ta zabge ta rame. Ta ƙaraso ta zauna.
"Kai Auta, duk laulayin ne?"
Yamutse fuska A'isha ta yi kamar ta yi kuka. Cike da shagwaɓa ta amsa.
"Wallahi Maman Affan ni duk cikin ma ya isheni. Allah kuwa ji nake kamar a .."
"Astagfirullah! Kar ki karasa Princess. Ina rabaki."
Suka dubeshi, Hisham ne wanda ya fito daga dakin sanye da jallabiya. Dariya ma suka ba Ramlat. Ta dara kadan, ya ƙaraso yana hararar A'isha. Daga bisani suka gaisa da Ramlat.
"Kin ganta nan, girki ma yanzu ba ta fiye yi ba yayi dadi. Wataran gishiri ya yi yawa, ko maggi ya yi yawa. Wai dama haka ake laulayin da shegen tsawo da kuma wuya?"
Murmushi sosai Ramlat ta yi.
"Irin naku kenan sai hakuri."
Nan dai ya yi ta caccakar A'isha ita kuwa sai cika take da batsewa. Dariya kawai Ramlat ke yi, ganin dagasken fita yake son yi siyo abinci ta mike tsaye.
"Haba dai, wallahi ka barshi bari na girka tunda na zo."
Ya kuwa shiga godiya, ya ja hannun A'isha wai ta zo ta kwanta ta huta ya mata tausa. Kunya ya kama Ramlat, ta yi saurin faɗa wa kicin tana murmushi. A can ƙasan ranta ƙara godewa Allah ta yi da baiwar da ya yiwa ƴan uwanta na mazaje nagartattu masu sonsu. Tunanin Aliyu ya faɗomata da yanda aka sha fama akan aurenta da shi da kuma Hilal. Idanunta suka ciko da kwalla. Ta haɗiyesu sakamakon Bingel da take tare da ita a kicin din.
Shinkafa da miya kawai ta girka, ganin suna da kayan ganye sai ta yanka kabeji da su karas ta haɗa coleslow.
Ta shirya komai saman tebur kafin ta dawo falon ta zauna tana danna waya. Muhibbat ta kira suka gaisa ganin kwana biyu ba su yi magana ba. A karshe ta nemi Amrah a waya suka hau hira. Har zuwa sadda A'isha ta fito.
Zama ta yi tana hamma, dagasken dai bacci ta yi don idanunta da fuska sun nuna.
"Ya kike ji yanzun?"
Gyada kai ta yi.
"Da sauki sosai. Sai dai yunwa."
Murmushi Ramlat ta yi.
"Daukomin hijab sai ki je ga abincin can saman tebur."
Miƙewa Aishah ta yi ta koma daki, ca ta fito rike da Hijab da darduma. Ramlat ta shimfida ta tayar da sallah, tana cikin sallar Hisham ya fito yana amsa waya.
"Dagaske kake ko wasa?"
Can kuma ya ce.
"Ok ganinan zuwa."
A'isha ta dubeshi tana kokarin zuba abinci a plate. Kafin ma ta tambaya ya amsa da dariya yana satar kallon Ramlat.
"Wai kinsan kuwa Hussein ne ya zo yana waje? Bari na shigo da shi."
Daga haka ya fita, har suka shigo tare ba ta idar ba. Jin sallamarsa sai da gabanta ya fadi kafin ta yi istigfari a zuciya ta maida hankali ga sallarta. Sai da ta idar ta shiga addu'a hannun har yana rawa. Ya na zaune kujerar da ke fuskantarta. Gaisawa suke da A'isha amma kusan hankalin yana kanta. A'isha ta saci kallon Hisham ya kashemata ido daya. Ta girgiza kai, ta san dama shi ya haɗa hakan.
Ramlat ta kasa cire hijabin, ta mike ta ninke dardumar.
"Ina wuni." Ta gaidashi, ya amsa a hankali. Rabonsu da juna tun wayar a suka yi kwanaki, ko a WhatsApp bai ƙara kulata ba.
"Ku muje mu ci abinci, don wallahi Princess yunwa take ji."
Fadin Hisham yana mai miƙewa.
"Na ƙoshi." Daga Hussein har Ramlat kusan a tare suka furta, abin sai ya ba Hisham da A'isha dariya. Suka saci kallon juna, kunya ta kama Ramlat ta kauda kai. Shi kuwa Hussein murmushi ya yi.
"Toh duk sai kun ci wallahi."
Fadin Hisham.
A dole suka bi bayansa, Ramlat ta dage a falon za ta ci.
"Kai Sis." Fadin A'isha kamar ta yi kuka. Hussein ya ja kujera ya zauna bai ce musu uffan ba. Wayarsa ta yi ƙara ya mike cak ya fita gami da fadin.
"Ina zuwa."
Hajiya Zeenat ce, tambayar inda yake ta hau yi, ya dafe goshi.
"Ina gidan Hisham, wani abu?"
"Shi ne ba za ka fadamin ba? Na dawo gida ban ganka ba."
Ransa ya ɗan sosu.
"Da za ki fita yawon biki kin fadamin?"
"Ni kake faɗawa haka?" Fadin Hajiya Zeenatu cike da wani irin firgici.
Ya lumshe idanu ya bude.
"Sai na dawo."
Daga haka ya katse kiran. Ya koma ciki.
Madadin ya ganta a tsakar falon, sai ya ganta zaune kujerar gefen da ya tashi, ya karasa ya zauna.
"Hala Madam din ce ko sabuwar kamun da muka yi?"
Fadin Hisham yana ƴar dariya da satar kallon Ramlat.
Kirjin Ramlat ya buga, wani irin kishi ya turniƙeta. Ba ta san Hisham na da zancen da hankali ba zai dauka ba, zance marar kan gado ba, sai yanzun. Wani haushi ya bata, abincin ma ya daina yi mata dadi, dama tun zaman Hussein ƙamshin turarensa ya mamaye ilahirin jikinta ya haifarmata da kasala. Yanzun jikinta ya idasa mutuwa.
"An fadamaka kowa irinka ne kenan."
Abinda Hussein ya ce kenan bai ƙara uffan ba ya bar Hisham da dariya.
Tunda ya soma cin abincin wani dadi ke ratsa kunnuwansa. Ya kasa ɗagowa har sai da ya yi nisa da soma ci, can dai ya dubi Hisham.
"Nikam Princess dinka hala ta yi makarantar koyon girki ne."
Haba! Ai daga Hisham din har A'isha da uwar gayyar Ramlat, dariya suka ya basu. Ya dubesu yana dan yarfa hannu, ya tsaida kallon kan Ramlat.
"Mene abin dariyar?" Ta sunkuyar da kai tana murmushi.
"Antinmu kinga karo na biyu wannan bawan Allahn na buga santi akan girkinki. Gaskiya yau goron da zai ba da kamata ya yi ya fi na rannan."
Ita dai ba ta ce komai ba, ta kasa ci gaba da kai lomar, karshe ma miƙewa ta yi.
"Na ƙoshi."
Daga nan ta yi gaba da sauri ta koma cikin falon ta zauna ta basu baya tana sauke ajiyar zuciya. Shima gogan bai ƙara magana ba har ya kammala ci ya mike ya bar Hisham da A'isha ma ƙusƙus.
Wuri ya samu ya zauna yana danne waya, sai dai rabin hankalinsa a kanta yake. Tun yana satar kallo har ya koma kallon sosai. Karshe ya maida hankali saman wayar, whatsapp ya shiga. Ganinta online ya taɓota.
"Thank you."
Ta bude saƙon kafin ta saci kallonsa, murmushi yake amma idanunsa na saman waya.
"Kallon fa? Kar ki mata kwace."
Jin bing na shigowar saƙo ta maida hankali ga wayar. Abinda ta gani kenan, ta turo baki kadan ta kashe data gami da jefa wayar cikin jaka.
Miƙewa ta yi ta dauki mayafinta ta nufi dakin baƙi. Hijab din jikinta ta cire ga gyara zaman mayafin ta fito. Lokacin su Hisham sun dawo falon.
"Ba dai tafiya ba?"
Fadin A'isha.
"Tafiya zan yi, Hajiya ta ce kar nayi dare."
"Kai kamar wata karamar yarinya. Ko hira fa bamu yi ba. Prince ka yi mata magana."
Fadin A'isha a shagwaɓance. Sakin baki Ramlat ta yi don ita abin ma na A'isha da Hisham mamaki yake bata. Soyayyar dai kamar ana ƙaramata zuma.
"Ji, toh banda uzurin gabana da zan ƙare a gidanku?"
"A'a amma don Allah ki zauna, kinga fa yanzu shida, ga hadari a gari..."
"Shiyasa ai zan tafi, kinsan ban fiye tuƙi idan ana ruwa ba."
A'isha kuma ta rasa abin faɗi. Hisham dama bai ce ba, so yake abokinsa ya ce!
Jakarta ta dauka cikin lallashi ta ce.
"Haba Autar Hajiya, In sha Allah za ki ganni kwanannan, ai yanzun sai ana leƙowa ana dubaki. Yauwa Maman Twins ma sun ce na fadamaki suna nan zuwa."
Jin haka yasa A'isha sakin ranta kaɗan.
"Toh ai shikenan. Allah Ya kaimu."
Ramlat ta amsa da amin tana murmushi.
Hussein ya mike yana duba agogo.
"Nima zan gudu."
"Kamar hadin baki?" Fadin Hisham.
Girgiza kai Hussein ya yi.
"Yamma ta yi ga hadari."
Gyada kai Hisham ya yi.
"Ai shikenan, don ma dai kai din baki da hanci ne. Ba nisa sosai."
Hussein bai amsa ba ya bi bayan Ramlat da tuni ta fice.
Hisham na dariyar mugunta ya yiwa A'isha raɗa a kunne ya bi bayansu.
"Innalillahi, garin yaya?" Fadin Ramlat a hankali tana jin kamar ta yi kuka. Hussein ya juyo yana dubanta, iska na faman ɗaga mayafin nata da ja mata rigar. Tayarta ya gani a sace.
"Ya Salam, Antinmu garin yaya hakan ta faru?"
Fadin Hisham sadda ya karasa yana kyafkyafta idanu ganin iska na neman yi mishi lahani. Kamar ta yi kuka ta dubi Hisham.
"Wallahi nima bansani ba."
Ta furta cike da takaici.
A'isha ta danne dariyarta, game din dadi yake mata sosai. Tuni Hussein ya bude motarsa ya shige ya ba ta wuta.
"Shigo na kaiki." Abinda ya ce kenan. Ta dubeshi ta maida duba ga su Hisham.
"Je ki don wallahi hadarinnan yanda ya haɗe ba zan iya fita ba. Sai dai ko ki kwana zuwa safe."
Ta haɗa daga shi har A'ishar ta watsawa harara.
"Gobe na ƙara zuwa gidanku."
Nan kuma suka hau aikin ban hakuri, ta karasa ta bude gidan gaba ta zauna. Hussein ya dubi abokinsa.
"Sai mun yi waya."
Daga haka ya fice bayan Maigadi ya budemusu ƙyaure.
***
Tunda suka kama hanya yake murmushi, ya san ko mene aikin Hisham ne. Amma hakan ba karamin dadi ya yi mishi ba, ya juya ya kalleta. Ta takure kanta wuri guda, ta wani rungumi jaka. Basu yi mintuna biyar da soma tafiya ba aka soma ruwa dagasken gaske. Ganin irin karfin ruwan yasa dole ya taka burki ya sauka ya gangara gefe. Wayarta ta yi ringing ta duba, Hajiya ce.
Hakuri ta bayar gami da bata tabbacin ta taho. Hajiya na faɗa akan ba ta ji dadin hakan ba suka yi sallama. Tasan a zatonta ita ke jan motar, ba zata fadamata ga abinda akai ba.
"A dalilinki na zo gidan Hisham."
Ya fadi kansa tsaye yana kallon yanda ake zuba walkiya da ruwa kamar da bakin ƙwarya. Ta dubeshi da mamaki, maimakon murmushi, wani kwantaccen damuwa ta gani shimfide saman fuskarsa. Ya karkato yana dubanta, ta kauda kai saboda nauyin da kwayar idanunsa suka yi cikinnata.
I just published "BABI NA ARBA'IN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/GhWrzYe49bb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
41)
*Assalamu Alaikum yan uwana. Fatan Alheri ga dukkanku. Ina matukar farin ciki da irin addu'o'inku gareni. Allah Ya bar zumunci. Ameen.*
*Ban kammala Exams ba, amma aski ya zo gaban goshi. Nagode sosai.*
"Kar fa ki fassara kalamaina."
Ta yamutse fuska kadan.
"Fassara ta me?"
Ya yi murmushi yana dubanta sannan ya maida kai ga tuƙinsa.
"Akwai hoton da nake da buƙata a wurinki."
Ta saci kallonsa. Ba ta tanka ba ya ɗora.
"Wata little angel da na gani kwanakin baya kin ɗora hotonku tare. Ita ba ƙatuwa ba kuma ba siririya ba. Fara ƙal."
Da gaskiyar Bature da yace Blood is thicker than water. Fati yake nufi.
Murmushin da ba ta san ta iya shi ba ta shiga yi kafin ta saita kanta da tunaninta.
"Ka santa ne?"
Taɓe baki ya yi gami da girgiza kai.
"Ko daya, kawai dai yarinyar ta burgeni sannan ina jinta kamar ƴar da ta fito daga jikina."
"Alhamdulillah." Tsabar ruɗu yasa ta furtawa a fili har ya kai dubansa gareta.
"For?"
Ya nemi ba'asi. Murmushi kawai ta ke yi.
"Murmushin fa?
"Ba murmushi nake ba." Ya dubeta sai kuma ya yi dariya. "Toh kuka kike yi." Ta shafi bakinta sai kuma ta sunkuyar da kai tsabar kunya.
Ya sanya hannu ya kunna music. Wannan karon ma dai muryar Nancy Ajram ke tashi. Abinda Ramlat ta fahimta, Hussein ma'abocin jin waƙoƙin larabawa ne.
Shiru ya biyo baya har suka kai ƙofar gidan su Ramlat. Kirjinta ne ya bada dam ganin Yayanta Munir tsaye a jikin motarsa yana amsa waya. Tunda motar ta tsaya ya ƙuramata idanu yana son ya shaida waye.
Hussein ya dubeshi sadda ya ke ƙoƙarin cire Seat Belt din da ya sanya. Kamanninsa da Ramlat kawai ya gani da kuma irin firgicin da ke saman fuakar Ramlat din, ya fahimci ko waye. Bai cewa Ramlat komai ba ya fita, itama ganin haka ta fito kirjinta na lugude. Yaya Munir da ganin Ramlat ya ba shi mamaki, dakyar ya iya miƙawa Hussein hannu suka gaisa. Ita kuwa Ramlat tana gaidashi wuf ta faɗa cikin gida.
"Ke kuma lafiyarki?" Tambayar da Hajiya ta watsomata kenan ganin shigowar da ta yi a hargitse. Girgiza kai ta yi ta zauna kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki.
"Ba komai."
"Hala kin haɗu da yayannaki a waje?"
Ta gyaɗa kai, ba ta kai ga bata amsa ba sai ga Munir din. Abinda ta ke gudu ne ya kasance, faɗa sosai ya shiga yi akan don me za ta shiga motar abokin Hisham. Hajiya dai mamaki ƙarara don ba ta da labarin hakan.
"Ku yi hakuri, wallahi tayar ce ta sace. Ga Auta ba lafiya shiyasa dole Hussein din ne zai kawoni. Kunsan yanayin unguwarsu ba'a samun abin hawa cikin sauƙi."
Ta faɗi jiki a sanyaye. Harara Yaya Munir ya danƙara mata. Hajiya kuwa jin Hussein ne yasa ba ta ƙara uffan ba.
Dakyar dai ta lallaɓashi ya tafi. Bayan fitarsa ta miƙe ta yi ɗaki, sai bayan sallar isha'i sannan ta fito, ta ƙara wanka ta sanya doguwar rigar bacci da ƴar hula.
"Gidan gaba ɗaya sai ya yi ba daɗi wallahi."
"Uhm, ni zan faɗi haka ba ke ba Ramlatu, nayi kewar yarannan kamar na kira waya a maidomin su."
Murmushi Ramlat ta yi ta zauna.
"Hajiya kinsan wani ikon Allah? Yau da kansa ya tambayeni hotin Fatima. Wai haka kawai yarinyar ta burgeshi, na aikomasa hotunanta."
Hajiya ta ɗan yi shiru alamar nazari.
"Fatima wacce?"
"Ɗiyar baƙonmu na Adamawa."
"Ikon Allah, jini ba wasa ba. Allah Sarki."
"Ni kaina nayi mamaki."
"Allah Ya ci gaba da taimakonmu, in sha Allah za'a dace. Wataran komai zai zama labari."
Cikin gamsuwa Ramlat ta jinjina kai tana murmushi, fuskar Hussein na yawo cikin ƙwayoyin idanunta.
"In sha Allah." Ta maimaita.
***
Ranar litinin da tana kammala shiri ta fito, a gaggauce ta karya ganin tana dab da makara. Haka ta fito titi don har sannan Hisham bai ga damar maidomata motarta ba, ba kuma ta ƙara kiransa ba tunda ta ji yana kiran shi ba shi da kuɗin gyaran taya toh ta san da biyu ya ke yi.
Ta yi tafiya kaɗan kafin ta fito bakin titi ta samu abin hawa. Zamanta keda wuya cikin Napep, wayarta ta ɗauki ƙara. Halima ce. Kamar ba za ta ɗaga ba sai kuma ta ɗauka.
"Ke kuwa Ramlat ba faɗa me ya kawo gaba? Shikenan don kin bar Revenue an rabu?"
Yaƙe ta ɗan yi kamar a gabanta.
"Ayya Halima ba haka bane. Allah Ya huci zuciyarki. Fatan kuna lafiya, Ya sauran mutanenmu?"
"Uhm, lafiya kalau, sai dai kin tafi kin bar baya da ƙura."
Da mamaki ta ce.
"Ban fahimta ba. Wani abu aka yi?"
"Eh, yanzu ba wanda bai san cewa Chairman yana sonki ba. Idan ma kina tunanin bamu sani ba gwara ki san cewa ƙwai ya fashe."
Wani ɓacin rai ya zo wa Ramlat wuya, ta danne komai.
"Shi ne me? Don yana sona mene a ciki Halima?"
"Aa ba komai bane, Allah Ya ba ki hakuri. Yanzun sai na faɗi zancen da