Showing 99001 words to 102000 words out of 231786 words
Chapter 34 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
30)
Wannan abu da ya faru, sai ya ƙara ragewa Ramlat walwalarta a Ofis. Tambayar duniya ƴan ofis din sun yi amma ta nunamusu ba komai. Tsakaninta da Halima gaisuwa kawai, daga nan ba ta kara bari wani abin ya shiga tsakaninsu. Ga Halimar hakan ba karamin dadi ya yi mata ba, ko ba komai ta samu wani makami wanda yake ganin a koyaushe za ta iya rushe Ramlat din da shi. Wannan girma da ƙimarta da ake gani a daina.
***
Bayan sati daya da auren A'isha, ranar Lahadi misalin karfe uku na rana, Ramlat ta shirya cikin riga da skirt na leshinta ja, ya yi mata kyau sosai, fuskarnan banda hoda ba abinda ta shafamata, sai gidan A'isha. Nan ma sai da A'ishar ta yi ta roƙonta akan ta zo. Abin ita har mamaki ya ba ta, yarinyar da basu fiye ɗasawa ba, raini ya shiga tsakaninsu, yau ita ke nemanta? Murmushi ta yi, aure ba karamin gyarawa mutum zama yake ba. Kodayake me akai da maza ma?
Ɗan sahu ta hau zuwa gidan A'isha, su Ummi tun safe Muhibbat ta zo ta ɗaukesu don halartar taronsu na Zuri'a.
***
Kai tsaye ta shiga cikin falon da sallamarta, A'isha ta amsa tana mai fitowa daga kicin cike da zumuɗi da jin dadi.
"Kai Maman Affan, wai sai yanzu? Wallahi kamata ya yi ki zo tun safe ki wuni."
Harara ta ɗan watsamata tana murmushi.
"Ko? Ga babbar kobo, to ban iya wannan katoɓarar ba."
Dariya A'isha ta yi, ita kuwa Ramlat sai bibiyarta take da kallo yanda ta yi fresh ta yi ɓulɓul abinta tsaf.
"Toh don Allah ku din ne ba wanda na ƙara gani a gidannan, nasan shirye-shiryen auren Yaya ma zai iya ɓoyeku amma ai ba hujja ba ce."
Taɓe baki Ramlat ta yi tana mai ajiye jakarta.
"Ke ni rabani, ba wani shiri da nake yiwa bikinnan. Inace dai mijinki ba ya nan?"
Ta tambaya sadda ta dakata da yaye mayafinta da take shirin yi. Girgiza kai A'isha ta yi.
"Ya fita amma ba jimawa zai dawo, abokinsa ne zai zo shi ne ya fita yin cefane. Ni wallahi naji dadin zuwanki, ko ba komai za ki taimaka mu shirya daddaɗan abinci."
Ramlat ta ji inama ba ta zo ba. Ba taya girkin ne matsalarta ba, ba ta so Hisham din yana gida ba ne. Dakyar A'isha ta samu ta lallaɓata ta zauna. Ba jimawa kuwa sai ga Hisham. Shi kansa ya ji dadin ganin Ramlat, mutum ne mai barkwanci don ko kadan bai tsaya wani kunya ko ƙumbiya-ƙumbiya ba. Itama ganin haka ta ɗan saki jikinta, daki ya shige su kuwa suka nufi kicin suka shiga aiki, Ramlat na mitar inama ba ta zo ba. Ita dai A'isha ba ta iya magana ba don tasan yanzun sai ta fadi abinda zai sa ta bar gidan ba shiri. Sai da suka yi la'asar suka faɗa kicin.
Fried rice suka yi wanda ya sha hanta. Suka yi chicken pepper sai hadin salad da lemun Mango. Komai suka jera saman tebur, A'isha ta shige don yin wanka. Ita kuwa dakin da ke falon ta shige ta hau shirin tafiya gida.
"Gaskiya Antinmu ba inda za ki je, ki yi hakuri mu ci abincin gaba daya. Na rantse har gida zan kaiki." Hisham ke maganar cikin alamun roƙo. Duk yanda ta so ta ƙi hakan ya gagara, magiya irin na Hisham sai da ya ci galaba a kanta, ta kara duban su da zummar magana, wayar Hisham ta yi ƙara. Ya dubesu kafin ya ce
"Inaga ma ya ƙaraso. Bari na fita."
Daga nan ya fice, dole Ramlat ta koma ta zauna A'isha na mata dariya.
***
Hussein ke tuƙin, Hajiya Zeenatu tun washegarin rikicinsu ta yi tafiya zuwa Abuja wurin Aminiyarta a yanda ta sanarmishi sai dai a zahirin gaskiyar Nijar suka wuce. Wannan karon wajen wani buzu za ta je don samarwa kanta mafita. Dama an dade ana ba ta labarinsa.
Waya yake cikin nutsuwa, sai ka nutsu za ka san me yake fadi. Magana yake fitarwa kamar ba ya so, a zahiri haka muryarsa ta ke. Motsa bakin yake kamar ba ya motsawa.
Ya yi parking a wani madaidaicin gida, ya sa hannu ya bude murfi ya fito. Hisham dake tsaye ya ƙaraso suka cafke suna dariya. Ya haɗe cikin shaddarsa blue. Ya dora hula mai adon fari da ruwan blue. Sai yatsunsa biyu na dama da basu rabo da zoben azurfa guda biyu, sai agogo ruwan silver da ya ɗora.
A Gym suka soma haɗuwa da Hisham, har yawan haduwartasu ya sanya shakuwa mai ƙarfi ya shiga tsakaninsu. Hatta da Hussein ya yi mamaki don bai zaci zai sakarwa kowane mutum fuska ba har su zama abokan juna. To sai ya kasance Hisham mutum ne wanda nan da nan za'a iya sabo da shi, yana da barkwanci sosai. Duk da irin abotarsu, sai ya kasance a waje. Koda wasa bai taɓa gayyatarsa gidansa ba balle ya fadamishi wani abu da ya dangance shi. Shi ɗin dai ya gayyaceshi sun gaisa da iyayensa ba sau daya ba kuma ba biyu ba.
"Kamar ni a yi bikina a ƙare shi ne ko ƙeyarka ban gani ba ko? Daidai kenan?"
Taɓe baki Hussein ya yi.
"Kana da mita. Hakurin ne ba za ka iya ba? Ba abin tada jijiyar wuya a abinda ya wuce."
Hisham ya yi ƙwafa, shi kuwa murmushi kawai ya yi, har suka karasa ciki suna ɗan hirarsu.
***
A'isha ta mike ta fito daga ɗakin ta bar Ramlat kwance saman katifa. Sun gaisa da Hussein kafin Hisham ya dubeta.
"Ki cewa Yayarmu ta fito don Allah."
Ta amsa da toh tana murmushi sanin halin ƴar uwarta, ba lallai din ta yarda ta fito ba. Aikuwa kamar yanda ta zata hakan ne, cewa ta yi ba ta ga dalilin fitar ba tunda ba ita ce matar gidan ba.
Yanda ta faɗa haka A'isha ta kai saƙon ba surki, abin sai ya Hisham dariya shi kuwa gogan kamar bai san ana yi ba. Wayarsa yake amsawa da Hajiya Zeenatu wacce ta tafi kamar ba ta tafi ba, bini-bini za ta kira ta ji a inda ya ke. A karshe ma cewa ta yi za ta gaisa da Hisham din. Ya cire wayar a kunne ya miƙa wa Hisham.
"Madam."
Hakan da ya faɗa ya ankarar da Hisham ko wace, suka gaisa sai dai ya ɗan yi turus jin muryar kamar ta babbar mace amma bai nunamishi ba. A karshe ya mikawa A'isha wayar kamar yanda ta buƙata. Ita kanta ta yi mamakin jin muryar mace kamar Hajiyarta. Abinda ta kawo, matar ƙatuwar murya gareta ne kawai, banda wannan ba wani abu.
Sai da ta kawowa Hussein ruwa da lemu kafin ta koma wurin Ramlat.
***
"Kai kin ganshi? Wallahi kamar wani buzu."
"Astagfirullah, ke fa matar aure ce." Ramlat ta katseta da sauri. Anan itama ta ankara da katoɓarar da ta yi, ta ja istigfari kafin ta yi dariya.
"Allah kuwa ban faɗa don wani abu ba, kawai dai na ganshi ɗan gayu. Da ace ba ki taɓa aure ba kuma ke fara ce, ba karamin matching za ku yi ba."
Daure fuska ta yi, ta ɗan ji takaicin kalaman A'isha, sai ya ɗan yi mata fami da irin cin zarafin da Halima ta yi mata a ofis. Ganin yanda fuskarta ta sauya ne yasa A'isha gyara zancenta.
"Kiyi hakuri, wallahi ba wai ina nufin wani abu ba, kawai ganin irin yanda ya haɗu ne sai nake ga kamar bai dace ma ya auri wacce ta taɓa aure ba ball.."
"A'isha! Ya isa haka don Allah ki rabu da ni. Wai ni sa'arki ce?"
Ɗan taɓe baki A'isha ta yi tana murmushi.
"Allah Ya ba ki hakuri babbar Yaya, na yi shiru."
Ramlat ba ta ƙara magana ba don tasan ban hakurin ma irin na ƙannen zamani ne. Karshe ma miƙewa ta yi ta soma gyara mayafinta.
"Tafiya zan yi, tunda har na miki mai wuyar ai shikenan."
Anan ne kuma A'isha ta marairaice.
"Wallahi ba zan iya cin abinci da baƙon nan a wurin ba. Don girman Allah ki yi hakuri ki zauna. Ya ce fa har gida zai kaiki."
Gaba daya ta koma kalar tausayi tana roƙonta. Wayar Ramlat ta yi ringing, ganin Hajiya ce yasa ta nunawa A'isha
"Kin gani dai da idonki ko? Uwata nemana ta ke yi."
Daga haka ta ɗaga wayar, aikuwa tambayar da ta soma jefomata shi ne me ya tsayar da ita?
Da sauri A'isha ta karɓi wayar ta yiwa Hajiyar bayani gami da roƙon alfarmar Ramlat ta jira har baƙon ya tafi sannan Hisham ya maidota. Dakyar Hajiya ta amince don ta ce ba hannunta idan Munir ya tambaya.
Suka kammala wayar ta mikawa Ramlat, bayan gama jin bayanin Hajiya ta amsa da toh kawai kafin ta wurgamata harara. Dariya A'isha ta yi tana kara nema afuwa.
***
Sai da suka idar da Magriba sannan suka hau saman dining table. Sai a sannan ne da Hisham ya matsa, Ramlat ta fito.
Bayansa kawai take hangowa don ya ba ƙofar ɗakin baya, ko kadan ba ta gane ko waye ba har ta ƙaraso da sallama.
"Haba ko kefa Antinmu, amma ace tun ɗazu sai kiranki ake kina togewa."
Murmushi kawai ta yi jin kalaman Hisham, shi kuwa Hussein jin an ce Anti yasa ya tsammaci wata babba ce don haka ya ɗago ya dubeta da zummar gaisuwa. Yanda bakinta ya tsaya a bude haka na shi ya dakata, mamaki ne a saman fuskar kowannensu.
'Wannan matar ko dagasken dai mayya ce?' Fadin Hussein a zuciyarsa cikin son gasƙata abinda matarsa ta hasaso a kan Ramlat. Mamakin yawan haɗuwartasu yake. Ta kai har ya ganeta, kamanninta sun yi zaman dirshan a ƙwaƙwalwarsa.
Toh haka itama Ramlat, haduwarsu na ba ta mamaki. Da kuma ace ta san shi ne baƙon, da har ya fita ba za ta yarda ta fito ba.
"Kun sa juna ne?" Tambayar Hisham ya katse kallon ƙurillar da suka tafi yiwa juna, kusan a tare suka kauda kai, ta ƙaraso ta maze ta zauna kujerar dake kallonsa. A'isha da Hisham dai abin mamaki ya basu, yanayin sauyawar kowannensu.
"Ina wuni, an zo lafiya?"
Ta gaisheshi cikin dakiya da kuma son kauda zargi daga zuƙatan ma'auratan da suka zubamusu ido.
Shima ya amsa a tausashe.
"Lafiya."
"Wai ba za ku amsamin ba, kun san juna ne dama?"
Hisham mai naci, ya ƙara neman ba'asi. Hussein ya dubeshi da dara-daran idanunsa yana dan murmushi.
"No, yau ne ma farkon ganin da na yi mata."
Ta dubeshi da sauri, itama ita din ya kalla har lokacin murmushinsa bai gushe ba. Me yake nufi da yau ya soma ganinta? Ta dubi Hisham ta yi murmushin yaƙe kawai.
"Uhm, idan ma ta yi wari ai ma ji, ko ya kika ce Princess?" Ya fadi yana duban A'isha mai kokarin zubawa Hussein abinci.
Dariya kawai ta yi don ita kam kanta ya daure, ta kuma sani Hussein ya fi ƙarfin Yayarta. Da kamar wuya abinda Hisham ke nufi ya tabbata.
Ramlat ji ta yi kamar ta ɗaga farantin tangaran din ta kwaɗawa Hisham a kai tsabar haushin da ya ba ta, shi kuwa Hussein shanyewa ya yi kamar bai gane inda zantukan Hisham din ya dosa ba.
Tunda ta ɗora kai saman farantin da A'isha ta yi serving dinta, ba ta kara ɗagowa ba balle idanunsu su yi katarin haɗuwa.
'Dan uwansa ya fi shi kirki, sam bai da kirki wannan.'
Ta fadi hakan a ƙasan ranta, a fili kuwa guntun tsaki ta ja wanda karaf ya shiga kunnensa. Ya ɗago a hankali ya dubeta, ƙaramin bakin ya kalla da mamakin ma yanda tsaki ya fito daga cikinsa. Koma mene ya san da shi ta ke. Murmushi kawai ya yi ya ci gaba da cin abincinsa a nutse.
Ita kuwa Ramlat gyara ƙafafunta da za ta yi, ta ji ta taka wata lallausar ƙafa kamar carpet. Alokaci guda ta yi aiki biyu, ta janye ƙafar a razane gami da dubanshi idanu a waje, kallon da ya jefamata ne ya yi sanadin ƙwarewarta. Ta shiga tari ba ƙaƙƙautawa su A'isha na mata sannu gami da zubamata ruwa a kofi. Shi kuwa ci gaba ya yi da kai lomarsa irin ko a jikinsa. Sai da ta sha ta samu nutsuwa kafin ta mike tsaye.
"Ina za ki kuma?"
Ta dubi A'ishar.
"Na ƙoshi, gida ma nake son tafiya yanzu."
"A'a ki jira, kinga ma Allah Ya so ni da rahmarSa. Tunda ga Hussein sai ya kaiki har gida tun da Madam dinsa ba ta nan, kuma ni sai na zauna na kula da tawa Madam din."
Da wani irin sauri ta juyo ta kalli Hisham. Shi kuwa ransa fari ƙal, ya shinshino wani abin tsakaninsu. Koda ba soyayya ba, toh shakka babu akwai wata a ƙasa, bai yarda da cewar basu san juna ba.
"A'a, zan tafi kar ka damu."
Daga haka ta faɗa ɗaki ta dauki jakarta da mayafi, jikinta har wani rawa yake tsabar kaɗuwa ta fito.
"Ai fa na rantse sai dai ki jira abokina ya saukeki."
Ji take inama Hisham din ba sa'anta bane yanda za ta ji dadin gasamishi baƙar magana. Dole ba yanda ta iya ganin A'isha na nanata mata ba haka suka yi da Hajiya ba, zama ta yi ta daure fuska kamar kunun tsamiya.
Har ya kammala cin abincinsa bai ce musu uffan ba, sarai ya ji shirin Hisham din, ya kuma san da biyu ya yi. Shi dariya ma ya ba shi amma bai yi ta a fili ba, wato dai dagasken Hisham gani yake kamar wata alaƙar ce ta soyayya tsakaninsa da wannan baiwar Allahn.
"Alhamdulillah. Abinci ya yi dadi. Nagode."
Abinda ya ce kenan yana goge baki da tissue, ya zura hannu ya ciro kudin da bai san adadinsu ba, ya ajiye saman tebur.
"Ga tukuici ka ba Amarya."
Hisham ya yi dariya sosai yana kallon falon inda A'isha ke zaune tare da Ramlat.
"Ai ba ita daya ta girka ba, kusan ma ƙarfin aikin Antinmu ce ko ince Yayarmu."
Hussein ya ɗan ɗaga kafaɗa da sunan ko a jikinsa gami da miƙewa.
"Nidai na bayar, girki kuma ya yi dadi."
Murmushi Hisham ya yi sanin hali. Kudin ya dauka ya je ya dire saman cinyar A'isha.
"Ga tukuicinku na girki, Abokina ya yaba."
Ramlat ba ta ce uffan ba, A'isha ta shiga godiya bai ko amsa ba sai murmushi da ya yi mata.
"Toh Madam, ni zan wuce. Allah Ya bar zumunci."
A'isha ta mike tana ƙara yin godiya. Ya yi waje. Hisham ya dubi Ramlat.
"Antinmu don Allah ki yi hakuri ki taso ku tafi."
"Wai shi ya ce maka zai kai ni? Ni da ka bar ni na hau adaidaita."
"A'a. Wallahi na san Hussein daidai gwargwado, yana da kirki. Ina tabbatarmaki har ƙofar gida zai kaiki."
Ta sauke ajiyar zuciya, dolenta ta taso suka fito, Hisham da kansa ya budemata mazaunin kusa da direba ta shiga. A'isha na gefe tsaye tana kallonsu. Wanna dacewar da ta ke kira ba zasu yi ba, sai ta ga sun yi fiye da dukkanin zatonta. Murmushi take, wani irin murmushi mai haɗe da zumuɗi da kuma fatan alheri.
Har Hisham ya zagaya suka yi sallama da Hussein da ke tsaye jikin motar ya riƙe murfin motar, ba ta daina kallonsu ba. Suka yi sallama ya kara yi mishi godiya sannan ya shiga motar.
A nutse ya soma tafiya har ya bar layin, wani shiru ne kawai ke gudana tsakaninsu. Kowanne da abinda yake saƙawa a ransa. A ɓangaren Hussein murmushi ya yi, tunaninsa kawai Hajiyartasa, da za ta ga yarinyar a gaban motarsa yau kam hauka ne kawai ba za ta yi ba.
"Kin hau motata ba ki sanar da ni inda zan kaiki ba."
Wani kululun baƙin ciki ya tokaremata ƙahon zuci. Yana magana kamar ma ita ce ta ce za ta hau ya manta cewa bisa tilas take zaune a ciki.
"Wace unguwa?"
Ya tambaya kai tsaye ba tare da ya dubeta ba, kuma bai tsaida motar ba.
"Sharaɗa." Ta furta a ciki-ciki, sai a sannan ya juya ya kalleta, fuskarta na kallon waje. Ya maida kai ga tuƙinsa, gudu kawai yake ita kam ko a jikinta.
"Alaƙarku fa?"
Ta ji muryarsa cikin kunnuwanta, sai a lokacin ta dubeshi. Cikin rashin fahimta ta ce.
"Me ka ce?"
Fuskarsa a sake ya dubeta kaɗan, ta kauda kai shima ya kawar.
"Alaƙarki da Hisham."
Kamar ta ce ba matsalarta ba ce, sai ta ji ta kasa. Ta ɗan ja sakanni kaɗan kafin ta amsa.
"Mijin ƙanwata ne."
Ya gyada kai daidai sadda ya sha kwanar da za ta sadashi da titin sharaɗa.
"Sai ina?"
Ta dubeshi, ita wannan magana guntu-guntun takaici yake ba ta, ganin ba ta gane ba ya ce.
"Ina zamu yi?"
Ta yi mishi kwatance har lokacin muryarta ba daidai ba, ta rasa dalili.
Gyada kai kawai yake yana sauraronta da dukkan hankalinsa, har ta gama ya rasa dalilin da yasa bai so ta tsaya din ba. Ya numfasa ya shiga bin kwatancen har suka iso layin da take fadi.
"Ya isa, zan sauka a nan."
Ya dubi wurin, akwai jama'a ba laifi, gidajen unguwar ya kalla, ba laifi suna da kyan gani.
"Kofar gidanku fa?"
Girgiza kai ta yi.
"A'a ba sai mun ƙarasa ba. Nagode."
Gyada kai ya yi. Ta murɗa kofar ta ji ta gam!
"Kiyi hakuri. Ina mai ba ki hakuri on behalf of my wife na abinda ta yi maki kwanaki."
Ta ɗan tsuke fuska.
"Wa kenan? Ai ban sanka ba balle har wani abu ya haɗani da matarka. Ni dai Ramlat kake nufi?"
Wani murmushi ya yi da har haƙoransa suka bayyana, irin murmushin da Hajiya Zeenatu kadai ke da ikon gani. Ta ɗan kauda kai daga kallon da ya ke jifanta da shi, murmushin ya kara kashemata gangar jiki da ruhi.
"Ramuwar gayya kenan fa?"
Ta yi shiru ba ta amsa ba amma ta ɗan murmusa itama ganin ya ɗagota.
"Shikenan. A gaida su Mama."
Daga haka ta ji ƙarar cire lock. Ta dubeshi kafin ta fita ta leƙo ta window.
"Nagode, zasu ji. Nima a gaidamin Hajiya."
Kusan ta faɗa da biyu hakan yasa shi dubanta, lokaci guda suka yiwa juna murmushi, daga nan ta soma tafiya babu ko waige. Har