Showing 192001 words to 195000 words out of 231786 words
Chapter 65 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
ta burgeshi kafin ya tantance abinda ya ke ji taƙamaiman a kanta, sai dai ya na da ja akan cewa akwai macen da za ta iya juyashi ba tare da asiri ba kamar dai Hajiya Zeenatu a baya. Amma zai jira ya ga irin juyawar ta Ramlatu. Kulawar ba zai nuna ba kamar yanda dan uwansa ya buƙata har sai bayan aurensu.
***
Tana tuƙi a hanyarta na zuwa Ofis bayan ta sauke yara a makaranta, tana tunanin zantukan Hajiyarta.
_*"Magidannaki fa ya bukaci ki bar aiki hakanan tunda can Adamawa za ki zauna. Ko ba don haka ba dama na fadamaki duk radda kika tashi aure idan mijin da za ki aura bai amince ba, to za ki bar aiki."*_
Sauke ajiyar zuciya ta yi. Kenan dai rabuwarta da yaranta ya zo, wani kewarsu ta ji ya kamata. Dama tasan aiki ko ba dade ko ba jima za ta bar shi kamar yanda suka yi da Hajiya a farko. Hon da aka cikamata kunne da shi yasa ta kara nutsuwa a tuƙinta, ganin ma ba wani tare hanya ta yi ba sai abin ya yi mata zafi, ta cikin gilashi ta ke duban motar, sam ba ta ganeta ba. Don haka ta yi gefe ta ba mai motar hanya. Ido suka hada ya yi mata murmushi ita kuwa dubansa ta shiga yi baki a sake sai kuma ta dara.
"Hilal?" Ta furta a bayyane, a hankali ta ga ya ja gefe ya yi parking, itama dolenta ta tsaya don su gaisa. Ba ta kai ga fitowa ba ya rigata isa wajenta.
"Ranki ya daɗe."
"Yaya Hilal? Saukar yaushe a garin?"
Ya yi ƴar dariya.
"Ko kwanaki uku ban yi ba da zuwa, shima daurin auren abokina ne ya kawoni, amma nan da jibi zan koma in sha Allah."
Ta yi murmushi.
"Allah Ya nunamana. Ya Fa'iza da Ɗiyarmu?"
"Suna nan kalau. Ai nake gidan Sis Bilki jiya, na ji kuma abin alheri. Allah Ya sanya albarka. Yasa zamu gani."
Ba ta yi mamakin yanda aka yi Bilkisun ta sani ba, tana da tabbacin daga bakin Mijinta ne. Amma faɗawa Hilal sai ta gani kamar da biyu ne. Cike da jin nauyinsa ta amsa.
"Amin. Ina godiya. Wato dai da ace ba mu haɗu ba anan sai dai mu ji labarin ka tafi ko?"
Dariya ya yi.
"Ni na isa na shigo garin nan ban je na ga Hajiyarmu ba? Aa sam. Wallahi yau nake cewa zan shiga zuwa yamma haka."
Ta jinjina kai.
"Allah Ya nunamana."
"Amin amin. Bari na bar ki kada na sa ki makara. Sai na shigo din."
Ta amsa da toh gami da yi mishi fatan alheri, ya rufemata murfin motar sannan ya wuce zuwa tashi motar. Ta ja numfashi ta furzar, Hilal kenan, mutumin da ya kaunaceta don Allah. Gaba daya ya sauya ya ajiye kumatu. Ga duk wanda ya gan shi zai fahimci yana cikin jin dadi da kwanciyar hankali. Wayarta ce ta yi ringing daidai sadda ta ke kokarin hawa titi. Ba tare da ta duba ba ta daga gami da karawa a kunnen da sallama.
"Ke da waye tsaye a titi?"
Tambayar da aka watsomata ba tare da an amsa sallama ba yasa ta gane ko waye. A hankali ta ɗaga kai ta dubi mirror, motarsa na nesa kaɗan da nata. Ta fi kyautata zaton daga wurin motsa jiki ya ke. Murmushi ta yi daidai sadda ta hau titi ta harba motarta.
"Ba ka da hurumin sanin da wanda nake magana. Kar ka manta ban kai ga zama matarka ba."
"Hakane, ba ki kai ga zama ba. Amma kin manta cewa haramun ne nema cikin nema? Ke musulma ce."
Dariya ya ba ta jin yanda ya zaƙalƙale. Yanda ta ke tafiya a sannu, haka yake biye da ita da motarsa a sannun. Ta kauda kai kamar ba ta san da shi din ba.
"Babu wanda ba ya kuskure."
"Haka kika ce? To naga kin ƙara tsayuwa da wani ɗan iskan! Duk abinda na yi mishi, ke kika ja. Sannan lokacin da za ki ajiye yawon gantalin aikinnan ya yi! Ba zan lamunta ba."
"Wannan kuma ba ka da hurumi a ciki, ajiye aiki sai lokacin da naga dama. Ka bar tada jijiyoyin wuya tunda har yanzu aure bai tabbata ba tsakaninmu. Akwai sauran lokaci."
Tana kaiwa nan ta katse wayar ta taka motarta, sai dai ba ta je ko'ina ba ya zo ya gifta ta har yana kokarin buge wani ɗan sahu. Bai ko tsaya ba ya yi gaba. Ta bi shi da kallo tana dariyar farin ciki, ko ba komai ta san ta ba shi aiki. Wannan nishadin yasa ta ware waƙar Breaker na Jarumar Mata tana saurara har ta karasa wurin aiki.
Hussein bai kara kiranta ba kwata-kwata a wannan ranar.
***
Bisa umarnin Yayanta Munir, ta rubuta takardar barin aiki. A wannan satin Rafee'ah ke zuwa ta kai ta gidan mai gyaran jiki. Ya kasance Ramlat ba ta da lokacin kanta balle na yara, ɗawainiyarsu ta koma hannun Hajiya da direba mai safa da marwar kai su makaranta da daukowa. Waya ba ta kara shiga tsakaninta da Hussein ba sai dai kokari kawai ta ke yi itama don tana kewarsa. Ya aiko da wani leshi mai tsadar gaske da kuma atamfofi har kala uku suma masu tsada sai mayafai da jaka da takalma, sai kuwa tsarka kala biyu da abin hannu duk na fitar biki. Ba ɓata lokaci aka kai wurin dinki tare da wanda Munir ya siyamata.
"Wai ke angonnaki yana zuwa hira kuwa? "
Ta dakatar da shafa man da take yi a jiki ta dubi Amrah wacce ke zaune saman gado tana shayarwa. Taɓe baki ta yi.
"Mutumin da ko waya ba ya kirana."
Da mamaki Amrah ta ce.
"Bana son sharri Ramlat."
Harararta ta yi.
"Kawai sai na zauna na kantara maki karya saboda ina tsoronki ko?"
Murmushi Amrah ta yi. Nan ta kwashe duk yanda ake ciki ta faɗamata har maganarsu ta karshe.
"Kai amma kin fadi mai zafi da yawa Ramlat, to ko za ki rama ai kya bari ya zo hannu tukunna. Shima dai da alama yana da zafin kishi tunda ya kasa nemanki har yau. Amma kar ki kara tunanin wai ba ya sonki, wallahi Hussein na miki son da ba ki san adadinsa ba. Da kansa fa ya je ya fadawa Baba Dakta yana sonki da aure tun ma a lokacin Chairman. Abinda kawai na kula, kamar yanda ya faɗamaki, shi mutum ne da bai yarda da wata soyayya kafin aure ba. Ya fi imanin cewa soyayya ta gaske tana zuwa ne bayan an yi aure. Kuma kar ki yi mamaki, irin su Hussein sun iya tattali da nuna kauna ga mace. Ina goyon bayanki, idan ku ka yi aure ki nunamasa kefa mace ce, amma ba wai ina nufin kar ki masa biyayya ba, aa, ki dai ja ajinki yanda zai gane shayi ruwa ne. Ke ba yarinya ba ce, na tabbatar kin gane me nake nufi."
Suka yi dariya gami da cafkewa don tuni Ramlat ta taso ta dawo gefenta.
"Ai ko yanzu ya ganki ya san kin sauya. Kin kara kyau gyaran jikin ya karɓeki. Duk inda kika gifta kamshi kawai kike kamar mai wanka da turare. Nidai akwai tsarabar da zan maki na kananun kaya, saura ki ƙi sanyawa."
Murmushi Ramlat ta yi, sai kuma ta ji zuciyarta na neman karyewa.
"Allah Ya jaddada rahma ga Aliyu."
Ta furta a fili, Amrah ta amsa da amin. Nan kuma suka shiga tuna baya, sai da Amrah ta ga dagasken Ramlat kukan take son yi don idanun sun cicciko da kwalla, sai ta share gami da sanyo wata hirar.
"Zan so naga yanda waccan bakar munafukar za ta yi idan ta ji labarin aurennan."
"Ni kuma kinga tsoron ranar da za ta sani nake yi. Sai kuma mamakin dalilin Hussein na ƙin ɗaukar mataki a kanta. Idan na yi tunanin ko yana sonta dagaske, ba ki san ya nake ji ba."
"Gaskiya da mamaki ace yana sonta, nidai jikina sai ya bani kamar so yake sai ya nunamata ita din ba komai ba ce kafin ya dauki mataki. Ai ko don yanda ta dinga kai maki hari, ya cancanta dama Hussein ya aureki mu ga ta tsiya."
Ramlat dai dariya kawai ta yi.
"Kin sanar da Muhibbat?"
"Eh na fadamata, ta ce za ta shigo ranar daurin auren tunda dai wunin ma duk rana daya ce."
"Allah Ya nunamana."
Ramlat ta amsa da amin gami da lumshe ido.
A daren bayan ta yo wa Amrah rakiya kofar gida don Dahiru ya zo daukarta, sai ganin Hussein ta yi. Suka dubi juna da Amrah da mamaki. Amrah ta murmusa.
"Kinga ɗan halak, ashe dai yana tafe."
Ita dai Ramlat mamaki ma ya hanata cewa uffan. Suka karasa daidai sadda ya fito daga mota suna gaisawa da Dahiru, daga nan ya amsa gaisuwar Amrah har da karɓar Baby ya yi mata wasa sannan ya yi musu sallama ya shige ciki ko inda Mutuniyartasa ta ke bai kalla ba. Ita ma ta dauke kai ba ta damu ta gaidashi ba.
"Wai ke ba Angonnamu kenan ba? Shi ne ko gaisuwa."
Dahiru ya fadi cike da zolaya. Ta harareshi don dama sun saba.
"Ban ga damar gaidashi din ba."
Ya daga kafada.
"Ai shikenan. Mu dai maza ba'a ja mana aji."
"Ko?" Cewar Amrah cikin son a tuna baya. Ya yi dariya kawai ya bude motarsa ya shiga.
"Allah Ya bamu alheri Amarsu. Sai da safe kafin wannan Madam din ta ɓallomin ruwa."
Dariyar suka yi kawai, ta bude gidan baya ta ajiyewa Amrah ledarta. Ba ta juya ba har sai da ta ga sun ja mota, ta koma ciki tana son ganin yanda za su kwashe da Gogannata.
A hankali ta ke takawa tamkar mai tafiya akan ƙaya, murmushi kawai ta ke zabgawa tana duban sararin samaniya wanda taurari da kuma watan na Rajab da bai fi kwanaki shida da bayyana ba. Hakan na nunk da kusantowar da wata azumin Ramadan ke ƙara yi. A hankali kuma ta maida kanta ƙasa ta ci gaba da tafiya har ta kusa barandar da za ta sada ta da falonnasu. Yanda ta ganshi a tsaye hakan ya dauremata kai, ta yi zaton yana ciki su na gaisawa da Hajiya, ko kuwa dai ya shiga ne ya fito? Oho. Ba ta da tabbaci, ganin kallonta kawai ya ke yi sai ta sunkui wa kai, koda ta karasa har za ta gifta sai kuma ta ga rashin kyautuwar hakan, don haka sai ta tsaya ta gaishe shi.
Maimakon ya amsa kawai sai ya kuramata idanu, idan ya ce ba ta sauyamasa ba, to ya yi karya. Ta wani cicciko ta yi haske, kamshi ke tashi kawai a jikinta. Ramlat ta ji shirun ya yi yawa don haka ta ɗan ɗago kai. Nan da nan ya daure fuska ya hadiye murmushin da ya yi niyyar suɓucemasa. Ya wayance da ɗan jan karan hancinsa da jan hancin kamar mai mura.
"Am...Meyasa ki ke giftawa cikin maza da uban ƙamshinnan? Koda ace babu maganar auren wani a kanki, kina sane da cewa haramun ne ko?"
Kanta a kasa ta yi murmushi a kasan ranta ta ce.
'Ka ji da masifaffen kishinka.'
"Ni ko fita ba na yi yanzu."
"Ko? Meyasa na ganki a waje? Idan mijin Amrah ne, mijinki ne?"
Ta ɗago ta dubeshi sai ma ya ba ta ƴar dariya. Maimakon ta ba shi haushi sai ta burgeshi, kawai sai ya jingina kai jikin gini yana kallonta. Ganin haka ta hadiye dariyar.
"Allah Ya huci zuciyarka."
Lumshe ido kawai ya yi ya bude.
"Matso, magana za mu yi."
Ba musu ta dawo ta tsaya daga gefensa. Kamar ta ce masa su nemi wurin zama amma kawai sai ta share.
"Kamar yanda na san cewa kin sani, yana da kyau na kara faɗamaki da bakina. Bayan aurenmu Adamawa zan kaiki. Kano sai dai mu zo ziyara. Abu na biyu babu batun aiki, ko a Kanon ko a Adamawa. Ba zan jure ganin ina fita nema, matata na fita ba. Kar ki ce za ki haɗa kanki da Zeenatu, wannan daban take hakanan tsarin rayuwarta daban da taki. Ina fatan kin fahimta?"
Ramlat da ta kasa haɗiye kishin Hajiya Zeenatu, ta gyada kai, ciki-ciki ta amsa.
"Na ji."
Jin yanayin sauyawar muryarta ya sanya shi ɗan matso da kai kaɗan yana murmushi, cikin rada-rada ya ce.
"Mece ce damuwarki? Hajiya Zeenatu ko kuma maganar aiki?"
Ta juyo da zummar harararsa, sai dai ganin irin kusancin ya kai har fuskarsu na dab da haɗewa yasa ta saurin ja baya tana maida numfashi. Shi kansa sai da ya ji wani yarr tun daga yatsar ƙafafunsa zuwa kwakwalwa. Ya sauke ajiyar zuciya.
"Ina iya tafiya?" Ta nemi sani a gaggauce.
"Kin gaji da ganina? Sati nawa ba ki ganni ba?"
Baki sake ta dubeshi. To ma duka-duka yaushe suka hadu a titi ya cashe mata? Sai kuma ta juya kanta kawai tana duban yatsun kafafunta.
"Shikenan, zan kiraki a waya. Kina iya tafiya."
Ta amsa da toh sannan ta nufi ciki.
"Ba ki ji ba."
Ya katse ta, ta ciji lebban bakinta don ita kam ba ta son kallonnasa, ta daure ta juya. Murmushi kawai ya yi mata. Sai aikin kallo, ta gaji da rashin maganar ta juya abinta zuwa ciki.
Yau kam duk juyinta tunanin Mijinnata ne, ta yi mamakin sauyinsa amma ta fi kyautata zaton kawai kewarta da ya yi ne ya chanja shi. Koda ta kammala shirin kwanciya, ta ji bai kira ba sai ta yi zaton ya yi bacci. Da Asuba bayan ta idar da sallah, ta zare wayar a chaji. Ga mamakinta missedcalls har biyar duk na Hussein sai saƙon da ya turo. Ta bude.
_*Kin kyauta kenan?*_
Ta yi murmushi, Hussein rigima kenan. Ita shaf ba ta tsammaci zai kira ba tunda har goma ta wuce ga kuma bacci na cin idanunta don kwanakinnan ba ta fiye samun yi sakamakon sammakon zuwa wurin gyaran jiki da ta ke yi. Madadin ta ba shi amsa sai kawai ta share ta jefa wayar gefen gado sannan ta fita gaida Hajiya. Koda ta dawo, biyawa ta yi ta tashi Ummi da Ansar su yi sallah. Ba ta ci wuya ba suka tashi domin sun riga sun saba. Kamar yanda ta yiwa Hajiyar, hakanan su ma suka shiga suka gaisheta.
Ƙarfe takwas a gidan Hajiya Bingel Sudan ta yi mata, ta yarda sosai da gyaran matar don ta san ta kan gyara. Duka-duka ba a sani jima da farawa ba amma gaba daya ta sauya, sai dai ba laifi Yayyunnata mata sun kashe kudi.
Koda ta koma gida ta iske kaya jibgi a falo, ashe kasuwa su Maman twins suka je. Tarkacen kayan kicin ne kala-kala da Munir ya bada a siya. Babu laifi kullum kudinsa daɗa albarka ya ke yi. A bakin Rafee'ah ta ke jin zancen furnitures, wai Baba Dakta ya ce komai da ya danganci wannan a barshi a hannunsa. Ta kara jinjina riƙon zumunci da kuma abota na Baba Dakta wanda bai taɓa bari sun koka da rashin Abba ba.
"Kai wannan Jug din ya yi kyau. Ga azumi ya taho, har na hango bakin Hussein yana kwankwaɗar lemu."
Rafee'ah ke maganar tana dariya, gaba daya suka sa dariyar har Ramlatu.
"Ke dai Rafee'ah ban san sadda za ki girma ba. Yara uku amma har yanzu da sauranki."
Rafee'ah na dariyar furucin Hajiya, Maman Twins ta ce.
"Ai da alama sai Baban Abba ya rangaɗomata kishiya."
"Shi ya isa? Taɓdi! Ai shiyasa ko magana ya dauko nake katseshi da cewa ko gidanmu daya tal na tashi na gani. Soyayya tun na yarinta har girma don haka kada ma ya fara."
Daƙuwa Hajiya ta mata.
"Ungo nan! Kin isa ki ja da ikon Allah? Yau Isma'il ya so aure ai kuwa baki isa ki hana ba. Ba gwara kishiyar ciki ba da a yi maki ta waje ba?"
Nan fa aka shiga hirar kishiya, Maman Twins na fadin ita kam tana ma ji a jikinta Baban Twins aure yake son yi tunda ginin da ya fara na bangare biyu ne. Ita dai Ramlatu ta yi shiru kawai tana duba kaya, idan abin ya ba ta dariya ta dara. Can kuma maganar ta dawo kanta.
"Kedai me kishiya irin Zeenaru take ko wa? Wallahi sai kin tashi tsaye da addu'a. Azkar safe da yamma kar ki bari ya wuceki. Ni na ji dadi ma tunda ba wuri daya zai haɗaku ba."
Ta dubi Maman Twins.
"A ina kika ji?"
"Ni ya fadawa. Na fi zaton akwai dai abinda ya ke nufi a kan matar, amma bari mu zubawa sarautar Allah ido. Ke dai kamar yanda Uwanin ta fada, ki zage damtse da addu'a. Ya sanar da ni ma zuwan matar Hassan da wasu cikin yan uwansu, amma ba gidansa za su sauka, masauki zai kama musu. Ba yanda ban yi ba da shi akan ya bari su zo nan yace babu komai."
Hajiya ke zancen ita dai ba ta da labari ma sai lokacin. Sai kuma suka koma batun rakiyar Adamawa, su na tantance wadanda ya kamata su je.
"Bilkisu fa? Ke an fadamaki Bilkisu za ta shiga sabgar Ramlat?"
Rafee'ah ta tambaya da mamaki jin Maman twins na batun Bilkisu.
"Toh aikuwa za ki sha mamaki tunda Munirun da kansa ya sanarmin cewa za ta je. Kuma ita ta amsa da hakan."
Hajiya ta fadi. Nan dai Maman twins aka hau rantsuwar gulma ce kawai za ta kai ta. Haka suka yi ta tattaunawarsu abin gwanin sha'awa. Aisha ciki ya soma nauyi ba kasafai ta ke fitowa ba.
***
WASHEGARI...
"Ki soma shirya kayanki. Tafiya ta zo."
Hajiya Zeenatu ta dubi mijinnata gabanta ya fadi.
"London ko ina?"
Ba tare da ya dubeta ba ya ce.
"Adamawa kafin London. Ai na faɗamaki zamu je yan uwana su ganki ko?"
Ta dan yi shiru tana tuna wayar da suka yi jiya da daddare da Kawu Modibbo. Gargadi ya yi mata a kan zuwa Adamawa don a cewarsa ya zo garin, bai kuma ga wata alama da ke nuni da cewar ta samu karɓuwa ba, asalima labarin da ake shi ne, asiri ta yi ta rabashi da mahaifarsa.
"Kin yi shiru."
Hussein ya furta gami da ɗan riƙo yatsun hannunta yana murmushin yaudara. Ta bishi da na yaƙe.
"Hum, kana ganin ba ni da matsala da su? Za su karɓe ni da hannu bibbiyu?"
Hussein ya ci gaba da bin ta da kallo, abinda ya ke zargi ya kara tabbata. Jiya ya ji tana waya kuma tsaf