Showing 225001 words to 228000 words out of 231786 words
Chapter 76 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
nufi ɓangarensa ya watsa ruwa. Duk tana ji, Allah Ya taimaka dama girkin ƙarashe ne don ta dafa markade ta kuma yi tafashen kazarta kafin su wuce kasuwa. Wannan yasa kawai miyar ta haɗa ta kuma dafa kuskus da ya sha karas da koren wake. Komai ta haɗa a gaggauce ta kawo falon ta jera saman ledar cin abinci.
Ƙamshinsa ya soma dukan ƙofofin hancinta, ta ɗaga kai ta kalleshi. Wando ne mai jikin cotton ya sanya sai farar tshirt mai gajeran hannu. Koyaushe Hussein ƙara kyau yake yi a idanunta, kullum ƙuruciyarsa ta ke gani. Har kullum idan zai fita daga gida hakanan sai ta ji wani kishi ya kamata. A kwanakin baya sai da ta kwashi takaici sadda wata Meena ta matsa mishi da kira, hankalinta bai kwanta ba sai da ya tabbatar mata babu komai tsakaninsu karshe ma ya rufe Meenar ta yanda babu damar da za ta ƙara kiransa. Da wannan ya samu hankalinta ya kwanta.
Har ya ƙaraso ta shagala ba ta ko lura ba sai da ya kai hannu ya shafi mafi soyuwa a wajensa. Ta dawo hayyacinta ta sauke ajiyar zuciya lokaci guda ta ɗan harareshi da wasa gami da murguda baki. Ya shafi lebbanta da yatsa hana murmushi.
"Ni kike wa haka? Tunanin me kike?"
"Ba komai."
Ya matso da ita jikinsa ya kwantar da kanta saman kirjinsa.
"Ko? Faɗamin gaskiya Malama."
Ta lumshe idanu tana shaƙar ƙamshinsa mai sanyamata nutsuwa.
"Dagaske fa ba komai. Tunaninka nake yi."
Ya sumbaci saman kanta yana murmushi.
"Uhum, faɗamin, me kike tunani alhalin ni ɗin naki ne."
Ta yi wani tattausan murmushi a hankali ta ɗago kai har hancinta na gogar sajensa. Suka dubi juna. Ya ja karan hancinta.
"Ko ba haka ba?"
"Hakane."
"To kin gani, me zai dameki?"
Ta jinjina kai kawai ta murmusa. Nan kuma ta zubamishi abincin, koda ta ce ta ci bai matsamata kan lallai sai ta ci ba.
Haka dai a kwanakin nan kusan kullum sai sun fita siyayya, sai da suka jera kwanaki uku, kafin Hussein ya murtuke ya ce abin ya ishe shi. A gaban Dada aka yi, suna zaune ne sai ga Waleeda cikin shiri ta dubi Ramlat.
"Adda Amal, muje ko?"
Ya haɗe fuska, ita kuwa Ramlat da ido ta nunamata Hussein alamar bai yarda ba. Waleeda ta dubeshi baki sake sai dai tuni ta haɗiye abinda ta yi niyyar faɗi dalilin kallon da ya yi mata. Dada ta dara.
"To kai Husseini banda abinka, ai fitar ta su ce, ɗinkinsu za su kai. Ka yi hakuri su je a auna su."
Ya mike zaune.
"Aa bari na aunata sai ita Waleedar ta kaiwa telan. Ba shikenan ba?"
Kunya ta kama Dada, ba ta kara uffan ba ta mike ta yi daki, Hussein dama ba yau ya saba ɓaram-ɓaramarsa ba. Ramlat da ta ji kamar ta nutse ta rasa bakin magana. Waleeda dake dariya ciki-ciki ta dubeshi kawai yayinda Hamida ta hau dariyarta sosai a fili don kusan sa'anni suke da ƴan biyu. Sai da ma ta faɗo duniya da watanni biyu aka haifesu.
"Me na ce ne?"
Ya furta yana neman ba'asi ganin Dada ta mike ta yi daki, su kuwa na falon na dariya.
"Au ba ka san me ka ce ba kenan? To ai Dada wuri ta ba ka idan ka auna matartaka sai ta dawo."
Ya taɓe baki yana yamutsa fuska.
"To meye a ciki? Dada dai ta so jin kunyarta ne. Idan muka haifamata jikoki ta daina. Tashi ita kuma wannan ta ɗauko abin awo."
Ramlat ta mishi wani irin kallo kamar ta yi kuka. Ya yi murmushi ya girgiza, kallon ya ji shi a dukkan wata gaɓa ta jikinsa. Miƙewa ya yi ya mata duban zan haɗu da ke kafin ya musu sallama ya fice wurin aiki, lokacin goma da ƴan mintuna.
"Dagaske dai mijinki bai bari ba. Ai shikenan, kawai ki ɗauko rigar da za ta yi maki daidai a yi amfani da ita."
Waleeda ta faɗi tana murmushi. Kafin Ramlat ta ce wani abu sai ga kiransa. Ta ɗaga da sallama.
"Kwalliya ta biya kuɗin sabulu, amma kallon da aka yimin yanzu idan na dawo zan zauna a yimin sau ɗari. Kuna iya tafiya, Allah Ya tsare. Drive carefully."
Daga haka ya katse kiran bai jira cewarta ba, ganin yanda ta ke zabga murmushi yasa Hamida kallonta.
"Ya bar ki kenan ko?"
Ta gyada kai, suka yi dariya. Mikewa ta yi ta koma bangarenta, mayafi kawai ta dauko sai jaka da mukullin mota ta rufe ko'ina. Koda ta dawo, Dada na zaune ta dawo falon. Sallama suka yi mata suka wuce. Wani tsadadden leshi da ya haura dubu ashirin, iyakarsu ne kawai, iyalan Dada, surukai da kuma ƴaƴa, ranar Dinnerparty zasu sanya. Sai atamfar da zaa sanya ranar wuni gaba daya dangi. Sai kuwa wata shadda ta Ramlatun da za ta sanya ranar ɗaurin aure.
***
Ana gobe za'a sanya Amare a lalle ne, ƴan Kano suka iso, dama iyalan Kawu Modibbo tun ana saura kwana uku suma dira. Ramlat ta rasa inda za ta sanya su Rafee'ah don murna. Ga yaranta, Affan ya zama babban mutum, ba kuka sai ma yawan sunkuyar da kai wai shi a dole mai kunya. Yaran sun yi wata irin ƙiba da kyau ga murjewa. Ta dauki Babyn Aisha, kyakkyawa da ita, sunan Mahaifiyar Hisham ta ci su na kiranta da Afnan. Kyau kam wane iyayenta.
"Ke kina ta cewa wasu sun yi kyau, kina kallon kanki kuwa a madubi Ramlat? Lallai aurennan ya karɓeki tubarakAllah."
Maman Twins ke maganar tana kallonta sosai. Nan fa sauran suka shiga tofa albarkacin bakinsu, ba wacce zuwanta ya ba ta mamaki sai Bilkisu don ita Hunainah ba ta zo ba saboda laulayin ciki na biyu da ta ke yi, ba ta jima da haihuwar ɗanta ba kafin ta kai ga yin wani tsarin iyalin sai ga ciki. Bilkisu kuwa wata uku kenan da dawowarta gidan Muniru, nan ma sai da ta sha baƙar wuyar rayuwa a gidansu, ta duba ta hango babu rayuwar da ta fi ta gidan mijinta dadi wannan yasa dakyar da siɗin goshi ta lallaɓa Muniru har ya sauko ya maidata ɗakinta. Tun komawarta musamman ganin su Yasmeen babu wani alamar wahala tattare da su, sai ta yi sanyi, ta kuma karɓi Hunainah hannu bibbiyu suka zauna lafiya.
Hussein sosai ya ke jan yaran a jiki, wani irin so da kaunarsu ya ke ji na musamman a ƙasan ransa har yake ji inama daga jikinsa suka fito. Ya yi amannar son da ya ke musu, ko mahaifinsu sai hakan. Ramlat kuwa banda murmushi ba abinda ta ke yi, ganinsu tare na karamata annashuwa. A ranar dai da kansa ya ce ta kwanta tare da yaran, ya tabbatar ta yi kewarsu.
Washegari aka shiga cikin biki, komai ya tafi cike da tsari. Ranar babu batun anko don kowa kayansa ya sanya, a rana ta biyu ne suka gudanar da yini da rana wanda kowaccensu ta sha ankon atamfa har su Aisha mutan Kano, don tun kafin su zo Ramlat ta aikamusu hoton ankon suka ɗinka.
Tun soma sabgar biki ba ta da wani lokacin kanta balle kuma na Hussein, hira ta ragu sosai a tsakaninsu. Sai dai ta kai mishi abinci, zaman da za ta yi wurinsa bai fi na mintoci ba. Wannan abu ya kai Hussein bango, gaba daya ma sai ya daina bari su haɗu. Da daddare idan ta leƙo, ya rufe kofar gam, da safe kuwa duk irin sammakonta ya fice daga gidan, waya kam ko ta kira bai ɗagawa. Text na duniya ba ya kulata, sam ya kasa yi mata uzurin tana da baƙi kuma su na hidimar biki. Wannan damuwar ta sa a ranta, shiyasa ko ranar da ta kama na dinnerparty, kasa wani kataɓus ta yi. Tana zaune tana kallon kowa na shiryawa, maganar duniya su Zulaihat da su Kausar sun mata akan ta tashi ta shirya amma ta ce sam ta fasa.
"Adda Amal kina cewa ba za ki je ba, ga Hamma Hussein can ya ci uban kwalliya ya fita, kuma wallahi idanun ƴanmatan nan kamar su tsiyaye tsabar kallonsa."
Jin abinda Falmata yar uwar su Hussein ta Maiduguri ta fadi, ai sai Ramlat ta mike tsaye ranta na susa. Nan aka kwashe da dariya, har itama ta murmusa.
"Kishi kumullon mata, ki zauna dai kar ki je. Wallahi sai dai ki ji ana wani labarin."
Ita dai Ramlat ba ta biyewa zancen Rafee'ah ba ta shiga bandaki bayan ta rage kayan jikinta, tana ji su na mata dariya. Wanka ta ƙara yi duka rabin hankalin na ga tunanin Hussein, abinka da zuciya, sai nan da nan ta ji itama ai ya mata laifi, ta ji ya bata haushi sosai. Kwafa ta yi tana ƙara cuɗa sabulu a jikinta, aikuwa ta ci alwashin itama ko kallo bai isheta ba a wurin taron. Ta fito ta shirya, da yawansu sun fice har su Rafee'ah da maman Twins. Aisha da Falmata da kuma Asma'u diyar Hajja Fatuma uwargidan Modibbo sai wata Hannatu itama daga Maiduguri, su ne kadai suka yi zaman jiran Ramlatun don su wuce a motarta.
Leshinta da suka yi anko kalar milk kai adon golden brown ya yi masifar sama a jikinta, ya sha aikin stones shi ta fiddo ta zura. Falmata ta yi mata make-up na fitar hayyaci, kasancewar kwalliyar zamani mai kama da na aljanu bai damu Ramlat ba don ba irinsa ta fi yi ba, sai ta fito ta yi wani azababben kyau. Daman su Rafee'ah yanda suka ga ta sauya fatarta ta kara kyau da sulɓi yasa suka dinga yi mata zargin mai ciki, ita kanta sauyawar na ba ta mamaki.
"Wallahi na fadamaki wani abu? Nidai ba ki taɓa kyau irin na yau ba, ko bikinki albarka."
Aisha ce ke maganar tana dariya, harararta Ramlat ta yi ta ja guntun tsaki ba ta ce komai ba, wannan duk abinda ta yi ɗanawa Hussein tarko ta ke son yi yanda zai yi dana sanin wannan fushin da ya ɗauka da ita. Har tunani take ko wa ya sanya a gaban mota suka tafi? Nan fa ranta ya ƙara sosuwa. Ta mike ta yafa mayafinta golden ta dauki purse dinta mai kyalli shima golden, turare mai sanyin ƙamshi ta fesa kafin ta zura takalminta da ya kasance mahaɗin purse din, ta dauki mukullin motarta. Kuɗin liki kam dama tuni sun tsufa a cikin ƴar jakar don tun safe suka bada aka yi masu chanji kowacce ta adana abinta.
"Muje." Ta basu umarni, duk suka fito ta rufe ko'ina na gidan. Su Ummi na sashen Dada da yara ana ta wasa don yanzu ba su fiye wani kewar uwartasu sosai ba balle su liƙe mata.
Tana tuƙin amma fuskar ba wawalar a zo a gani musamman da ta ga dagasken dai babu motar Hussein a farfajiyar gidan. Aisha ta karanceta tsaf, ta san kishi kawai ke cin ƴar uwarta don haka ta bar janta da hira ta maida akalar hiran ga su Falmata dake zaune a baya haka har suka isa ƙayataccen ɗakin taron na FARHAS Event Centre (Dan Adam).
Farfajiyar wurin sai ɗaiɗaikun jama'a, sai da duk suka fita, sannan ta bi bayansu. Aisha ko jiranta bata tsaya yi ba don ba ta son a huce a kanta. Ta na takunnan mai girgiza zuciyar masoyinta kuma mijinta, wanda ya zama normal tafiyarta. Haka ta ƙarasa har ta shiga ciki. Wuri fa ya cika, gaba ɗaya kowa na zaune ana kallon MC wanda ya fiddo Amare da Angwayensu tsakiya yana basu umarnin zama saman wasu kujeru a tsakiyar wurin, wannan yasa hankalin da dama suna kansu ana dariya a nishaɗance. Sun haɗa ido, sai ta dauke kai kamar ba ta ganshi ba, wani irin tururi kanta ke yi ganin wata kyakkyawar budurwa a gefensa zaune, shi kuwa AlHassan Madam dinsa ce a gefensa sun ba MC hankulansu. Takaici ya sanya kawai ta ja kujera ta zauna ba tare da ta ƙarasa wurin su Rafee'ah ba, sai ma bayan ta zauna ta ɗago kai ta ga ashe ƴanmatan gidan kakannin su Hussein ɗin ne.
"Kai Adda Amal you look beautiful wallahi."
Ta dubi mai maganar Teema ta yi murmushin da bai kai zuci ba.
"Thank you. Kuma kun yi kyau."
Daga haka ta maida hankali da fiddo wayarta dake faman vibrating, ganin lambar Hussein kawai sai ta maida wayar jaka. Tana ɗaga kai kuwa ta hango su Kausar na ɗaga mata hannu alamar ta ƙaraso. Hannu kawai ta ɗagamata shaidar inda take ya ishe ta. Sai da aka kira dangin Ango Tahir don su yi liƙi sannan ta mike suka ɗunguma har su Teema, a hanya suka haɗe da su Rafee'ah aka shige fili, Maman twins na rantsuwar a farko ba ta ganeta ba. Sai dai su na liƙin tuni mazan suma suka taso don zazzage nasu aljihun, ta ɗaga hannu da nufin somawa ya kai hannunsa saman nata. Juyowa ta yi har fuskarsu na haɗuwa numfashinsu na gauraya wuri ɗaya. A hankali ya zare kudin a hannunta ya shiga liƙawa kaf a kan Amarya da Angon, ta juya za ta wuce ya riƙe hannun gam suka fita tare. Maimakon su koma mazauni sai kawa ya yi waje da ita har wurin motarsa. Ta fincike hannunta, tuni idanunnata sun cicciko da kwalla.
"Ka kyale ni."
Hussein ya tsaya kawai hannunsa a kirji yana karemata kallo, ta yi mishi irn kyan da baki ba zai iya faɗi ba. Tsananin kewarta da son kasancewa da ita ne ke cin zuciyarsa.
"Da iznin wa ki ka zo nan?"
Ta tsuke baki, ya kuwa bishi da kallo yana cije lebba.
"Ka riga ka san da fitar ai."
Ta fadi cike da dakiya. Bai ce uffan ba ya juya ya yi amfani da mukullin motarsa ya bude, hannunta ya kama ya zagaya da ita ya bude gaban motar da nufin sanyata ciki. Ta dubeshi da zummar magana, sai dai yanayin ɗaurewarsa ya kaɗa hanjinta ba shiri ta hadiye abinda take shirin fadi ta shiga a fusace tana huci. Sai da ya zagaya ya zauna sannan ta dubeshi.
"Motata fa?"
Bai ce mata uffan ba ya yi ribas suka fice. Ranta ya ƙara zafi gashinan ko hoto ba su yi ba da Amaren balle kuma ƴan ankon.
"Amma kasan ba kai ka kawoni ba ko?"
Idan motar ta bata amsa, toh Hussein ya bata. Wayarta ce ta shiga ringing, ta ciro, kafin ta duba ko ta ɗaga ya karɓe. Ba ta san me aka ce ba kamsr yanda ba ta san wace ce ba.
"Muna tare."
Daga haka ya katse kiran ya jefa wayar aljihun gaban riga. Ramlat dai har da hawayen takaici, ba ta bar haskoshi da waccan budurwar ba kamar yanda ta ke jin zafin raba ta da wurin bikin da ya yi.
Su na isa gidan ya sa hannu ya zare purse dinta yana kallonta tsakar ido Ta kauda kai tana tura baki. Dariya ma ta ba shi ya murmusa. Mukullin motarta ya zare ya miƙa mata. Yana unlocking kofofin ta bude ta fice zuwa sashinta ranta a jagule. Shi kuwa sai da ya ba direba mukullin da kudin mota akan ya koma idan an tashi ya taho da waɗanda suka je a cikinta.
***
Tana shiga ɗakinta ta faɗa saman gado ta shiga rera kuka kamar wata yarinya ƙarama. Ganinta kwnace saman gado tana kuka ya hau doka murmushi, kawai ji yake ya rama shariyar da ta dinga yi mishi a kwanaki biyunnan. A nutse kuma ya soma takawa har ya karasa gadon. Jin ƙamshin turarensa sai ta ɗago ta share fuska, kokarin mikewa ta ke yi ya riƙo hannunta gami da jawo ta ta faɗa jikinsa. Kanta bisa kirjinsa gaba daya fuskarta ta nutse yayinda hancinta ke shaƙar daddaɗan ƙamshin turarensa. Lumshe idanu ta yi sadda ya sa hannuwansa gaba daya ya rungumeta tsam. Sai a sannan ta kara tabbatar da cewar ta yi kewar mijinta. A hankali ya zame ɗankwalin kanta ya shiga shafa gashinta.
"Duk kawaici da kauda kan da nayi maki don naga gudun ruwanki, ba ki gane ba ko? Kin maida ni kamar wani hoto, kin nunan sabgar gabanki ya fi ni ƙima da muhimmanci. Tun soma bikinnan ba ki da lokacina, ba ki damu da ni ba. Shikenan ni kuma sai na kasa nuna ɓacin raina?"
Yanda ya ke magana a tausashe sai jikinta ya yi sanyi, shakka babu kam, ba ta kyauta ba. Ta ɗago a hankali ta dubeshi tana narkar da fuska.
"Ka yi hakuri. Na sani ban kyauta ba, amma don Allah ka yimin uzuri tunda dai ka sani biki ne ake yi, ga baƙi ina da su."
Ya kama haɓanta suka tsurawa juna ido.
"Sai kuma ki ke jin nauyin kwana da mijinki don kina da baƙi? Ki ka kyalewa wasu ƴan matan shi su samu matsugunni a nan?" Ya nuna kirjinsa yana ɗaga mata gira da murmushi.
Nan da nan kishin ya dawo sabo fil ta tureshi za ta mike, ya kara fisgota ya rike gam yana dariya.
"Na dauka kishiyar kike ra'ayi."
Ba ta san sadda ta harareshi ba, don mamaki sai ya yi dariya.
"Shiyasa na ganka da wata busashshiya kana yawo da ita a cikin bainar jama'a don ka zubarmin da ƙima a gane ni Ramlat ban da wata daraja da.."
Bai bari ta karasa ba ya tallafi haɓanta ya haɗe bakinsu wuri guda da zafi-zafi.
Tun tana yunkurin ƙwatar kanta har dai ta saddaƙar. Can kuma da kansa ya sake ta, ya mike yana dubanta da shanyayyun idanunsa. Da wata irin kasala ya miƙa mata hannu, ba musu ta miƙamasa, suka ɗunguma zuwa nashi ɓangaren. A nan kam alƙalami ba zai iya wassafa yanda masoyan suka kasance ba cike da matsanancin kewar junansu. Ranar dai dinner anan suka ci suka sha abinsu.
Koda jama'a aka dawo, ta sha tsokana sai toshe kunnuwanta ta yi kawai.
***
Sati biyu da kammala biki, jama'a kowa ya watse, an miƙa Amarya Hafsat zuwa Kano, tafiyar da ba'a yi tare da Ramlat ba don sam Hussein ya ce ita da Kano ba yanzu ba. Haka ta hakura, Rasheeda kuwa Abuja aka miƙa ta wurin aikin mijinta.
Tun bayan bikin ya kasance Ramlat ba ta da kuzari, koyaushe tana kwance, wani lokacin bacci wani lokacin kuwa yanayin jikin ne kawai ba ya mata dadi. Dada kanta ta soma fahimtar sauye-sauyen Ramlatun,