Showing 195001 words to 198000 words out of 231786 words

Chapter 66 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

ya ji me tace. Sai dai bai gama fahintar waye ke tare da ita a danginsa ba, ko ma waye dai ya lura sun jima su na tare. Zai bi ta sannu har wayarta ta fado hannunsa ya dauki lamba.


"Kamar kowane dangi, akwai masu murna da ci gaban mutum da ma wadanda ba su yin farin ciki. Ba zan rantse maki cewa duka dangina su na sonki ba Zeenat, musamman abinda ya faru tsakaninmu wasu su na daukar alhakin ki cewa ke ce silar komai. Amma bangaren yan uwana kuma shaƙiƙaina, ba ki da wata matsala. Don haka ki kwantar da hankalinki. Ban taɓa fadamaki ba saboda bana son sanyaki cikin wani hali. Amma yanzu ya zama dolena na faɗa don kar ki ga wani abu a wajen wasu ki ji ba dadi. Ba zaman kowa kike ba face ni."




Wani dadi ya lulluɓeta, ta ji a duniyar nan ta kara son Mijinnata. Ba ta sadda ta rungumeshi, ya runtse ido yana ji kamar wuta ta ɗosana a fatar jikinsa.


"I love you."


Ta furta a hankali. Ramlat ce ta fado a ransa kafin ya ce.


"I love you too."


Da wannan ya shawo kanta ta mike har da batun za ta shiga kasuwa ta soma siyan tsaraba. Ya fiddo kudi zai karamata ta girgiza kai da binsa da hararar wasa.


"Ah haba, yan uwanmu ne fa. Rike abinka, da kudina zan musu tsaraba."


Ya yi murmushi kawai. Yana binta da kallo, ya lura kwana biyunnan kurajen nata da sauki sun fara mutuwa, ta dai ce na gargajiya ta soma karɓa ta gaji da zirga-zirgar asibiti. Shi dai ba abinda ya shafeshi. Kusantarta ne tuni ya bari.


***
*RANA BA TA ƘARYA!*







I just published "BABI NA HAMSIN DA TAKWAS" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1019046229?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=4ocpUEJVa%2B0bXSp4wxbK3lhNgthMCA7nB5QC2dclyyGJkYlECeIGKhiQUzgNGFlkVbskOsJU12vwNQbJIqJ2Pbn6%2F7TbXN1B%2BYmSMvxcC1P2DtDikL9OR4lEi83T5hqO












🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.


58)






Ana gobe ɗaurin aure tun da safe, suka bi jirgi zuwa Yola. Awa biyu da mintoci ta kaisu. Kamar yanda Hussein ya shirya, Kausar da AlHassan ne masu zuwa tarba. Kausar tun da ta ga Hajiya Zeenatu ranta ke zafi dakyar ta iya tankwara zuciyarta.


'Allah Ya isa.' Ta fadi a kasan ranta, Hajiya Zeenatu kuwa wani dadi ta ji ganin irin tarbar da ta samu a wurin Kausar duk da shekarun da ta ba ta. Suka dunguma a motar AlHassan zuwa gida. Bai yi gangancin sauketa a gidan Dada ba don ya tabbata Dada za ta iya kasa hakuri don ba ta iya ɓoye abinda ke ranta ba wasu lokutan sai dai ya san akwai ta da hakuri.


"Anan za ki zauna sai zuwa gobe idan an huta sai a leka dangi. Hakan ma ina ce ya yi miki?"


Hajiya Zeenatu dake karewa dakin da aka ba su kallo ta juyo tana dubansa fuskarta cike da damuwa.


"Yanzu dagasken a yau za ka juya? Gaskiya idan hakane zan jira a gidannan zuwa sadda za ka shigo garin sai mu leka dangin tare. Wallahi haka kawai na ke jin fargaba."


'Me akai da maza Zeenatu?' Ya furta a ƙasan zuciyarsa a fili kuwa murmushi ya yi kamar gaske ya shafi gefen fuskarta.


"Shikenan, yanda ki ka ce hakan za'a yi. Nima kin riga da kinsan dalilin komawar, ban larasa handling komai a wurin aikinmu ba ne, gobe juma'a in sha Allah da zarar na kammala, Asabar da safe zan taho."


Ta gyada kai.


"Babu wata damuwa. Allah Ya kaimu."


"Amin. Amma toh ko bikin ba za ki leƙa ba? Na fadamaki Cousin Sister ce a wurina."


Ta tuno da hakan don Kawu Modibbo ya fadamata zancen bikin don shi ne silar zuwansa garin shima. Sai dai ya gargadeta da shiga dangin gudun samun matsala don haka ta girgiza kai. Shima Hussein kawai fada ya yi don ya gwadata, amma tuni ya ji tana batun ba bikin da za ta leka da wanda suka yi waya kwanaki.


"Ka yi hakuri dai, ka ga ba'a san ni ba. Zan jira har ka dawo ka gabatar da ni a wurinsu."


Ya jinjina kai.


"Ba damuwa."


Daga haka ya rage kayan jikinsa ya shiga bandaki, can ya fito, wanka ya yi. Ya sauya kaya ya feshe jikinsa da turare. Hajiya Zeenatu ta ƙuramasa idanu, kananun kaya ya sanya. Rigar da ya sanya milk mai gajeran hannu sai blue jeans. Tsayawa suffanta kyawun da ya yi mata ta sani ɓata baki ne, mijinta kara kyau ya ke koyaushe da kuma ƙuruciya musamman gashinsa baƙi siɗik da ya kwanta a sumar kansa irin na Bafulatanin Yola wanda ke kara fiddo da zahirin waye Hussein. Ta shagala a kallonsa da jin wani irin tashin hankali da kishin zuwan da za su dinga yi Yolan yanzu, tana da tabbacin idan matan Kano ba su yi nasarar raba ta da shi ba, to wadannan kyawawan matan na fulanin Yola za su iya rinjayar zuciyarsa. Hakan tunaninta ke ba ta. Har ya kammala ya ɗaura agogo ta shagala a tunani.


"Muje mu ci abinci, su na jiranmu." Ya fadi ba tare da ya kalleta ba, jin shirun sai ya ɗaga kai yana dubanta. Ta shagala a tunani, sai da ya ɗan yi tafi kusa da ita sannan ta yi firgigit.


"Um, am..me ka ce?"


"Tunanin me kike? Nace mu je mu ci abinci daga can zan biya wurin Dada sai na wuce Airport."


Ta yamutse fuska.


"Sai zuwa anjima zan ci, yanzu bacci nake ji."


Ya ɗan ɗaga kafaɗa.


"Ok. Bari naje, idan kin yi nisa a baccin ba sai na tasheki ba. Zan wuce."


"Allah Ya kiyaye hanya."


Ya fice yana mai amsawa da wani irin nishadi a ƙasan ransa.


A falon ya yada zango, yana cin abinci su na hira da AlHassan da Kausar duk akan tsarin bikin.


"Yanzu kenan ita kadai za ta zauna a gidan? Yaushe Amaryar za ta zo nan? Don naji ana cewa tare duka za su shiga dakunansu."


Kausar ke neman sani.


"Asabar za su zo. Ke dama ai yanzu ba zancen zuwanki Kano saboda matarnan. Su Hafsat dai da saura sai su je."


AlHassan ke maganar. Kausar ta jinjina kai.


"Allah Ya kaimu."


Shi dai Hussein loma kawai ya ke, yana kammalawa ya mike ya gyara bakinsa. Koda ya shiga munshari Hajiya Zeenatu kawai ke yi. Ya ja mata kofar bayan ya dauki abinda zai dauka yana tsakin takaicin aurenta. Tare da AlHassan suka shiga gidan Dada. Kullum ta gansu sai ta ji kamar an yayyafawa zuciyarta ruwan sanyi. Tana tare da su Baba Yakura yan Maiduguri da ma sauran yan uwan mahaiyarsu. Aka gaggaisa kafin ya yi musu sallama da zummar wucewa Kano.


"Allah Ya kaika lafiya Ango. Mu dinma ai yanzu zamu wuce. Kai dai tunda a jirgi ne za ka riga mu sauka."


Ya yi murmushi jin abinda Gwaggo Lubabatu ƴar abokiyar zaman kakarsu ta bangaren Uba da ke Mubi ke fadi, ya yi addu'a akan Allah Ya kawo su lafiya sannan aka kara yin sallama ya tafi.


***
CIKAR BURI..


Gidan cike yake da yan uwa da aboka arziki, tun safe ake shige da fice na dora sanwa. Dangi an cika a madafi ana aiki ana kwasar hira. Fuskar kowa ka gani cike da farin ciki musamman Hajiya da har kwalla sai da ta yi don kuwa sun debemata kewar Abba. Cikar da suka yi ya motsa zuƙatan mutan gidan da tunanin Abba, bikin ganinsa suke yi tamkar na wata budurwa ba bazawara ba. Ƴan Daura da yawansu sun zo hakanan kafatanin mutan gidan Hajja su na nan. A bangaren Baba Dakta ma, hatta Kanwarsa Hajiya Nabila da yan uwan Umman Amrah duk sun hallara. Wannan shi ne kadai karar da zaa yiwa Hajiya mace mai son mutane da kuma zumunci. Don sun shaida, Hajiya ko ba ta je sabgarka ba, to hannunta zai je. Ba ta gajiya da kyautatawa hakanan marigayin Mijinnata. A ganinsu wannan ce karar da zaa yi.


Kowa ya bude baki ya ga cikar gidan cewa ake, har ma da auren Ramlatun, shima ya yi albarka kwarai. Duk wannan shagalin da ake, Ramlat na can tare da Amrah da kuma Rafeeah a gidan kwalliya. Dama tun ana gobe daurin aure suka je aka tsaramata lalle a ƙafa da hannu na gani na fada. Hakanan duk a ranar aka yi mata kitso sirara.


Maryam Cutie ce gwanar kwalliyar, tsayawa faɗin irin kyawun da ta yi ba'a cewa komai. Kasancewar Maryam kawar Rafee'ah kuma ba ta da matsala ne yasa ba su wani jima su na roƙo ba ta amince za ta bisu har Adamawa don yiwa Amarya kwalliya ta musamman. Ba ta samu matsalar hakan daga mijinta sosai ba don shi mutum ne mai fahimta hakanan sanin da ya yiwa Rafee'ah da mijinta ne yasa bai yi ja in ja ba.


"TubarakAllah Masha Allah."


Amrah ta fadi tana kallon Ramlat baki ya ƙi rufuwa tsabar kyawun da ta yi mata. Ko aurenta na farko ba ta tsaya ta nutsu an mata kwalliya kamar hakan ba. Murmushi Ramlat ta yi jin yanda su ke koɗa ta. Farin leshin wurin Muniru ta sanya an mata dinkin gown. Maryam Cutie ta yi mata dauri na gani na fada a karshe ta yafamata gyalen kamar yanda ya dace .


"Ke Ramlatu, kinga yanda kika sauya?"


Rafee'ah da ke tsaye gaban madubi tana dauri ke fadi, ita da Amrah suma duka Maryam ta fito da fuskokinsu ba laifi.


"Ya isa kar ku cinyeta."


Fadin Maryam tana dariya. Hotuna ta shiga yi mata tana mai yin alfahari da baiwar iya kwalliya da Allah Ya ba ta. Ta tabbata fuskar Ramlat ko kasar waje za ta a haka, to fa za ta ciri tuta.


Sai wuraren sha biyu suka kama hanya zuwa gidan, ita dai Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, fatanta Allah Yasa wannan ya zama aure na karshe a gareta wanda mutuwa ce kawai za ta raba. Allah kuma Ya ba su zaman lafiya.


Koda suka shiga gidan nan ma haka yan uwa suka yi caa ana ta koɗa kyawun da Amarya ta yi, kunya ta kamata ganin Hafsat diyar Dada, sai a sannan ta kula da zuwan yan Adamawan. Hafsat ta ja hannunta zuwa can falon Abba na baya da aka kai su, suka karasa ta durkusa ta kwashi gaisuwa.


"TubarakAllah, Amaryar Hussein kyakkyawa da ita." Matar ta fadi da hausarta da ba ta fita sosai. Ita dai Ramlat kanta a kasa tana murmushin jin kunya. Sai da Hafsat ta sanya ta zauna ta dinga daukarsu hotuna kafin a karshe ta yi musu sallama ta fito tare da Hafsat. Nan fa Hafsat ta shiga cikinsu aka dinga raha kamar dama can an shaku sosai. Su Nusaiba duk sun zo, daga mai goyo sai mai ciki.


Suna zaune a daki sai ga Salma da Bilkisu, dama Hunainah ita kam tun safe tana gidan, ko sadda suka shigi tana kwance ta yi rashe-rashe a saman gadon suna kwasar hira da kanwar miji kuma aminiyarta A'isha.


"Amarya Ramlat. "


Bilkisu ta fadi tana yamutse fuska musamman jin bakin cikin ganin Hunainah ta riga ta zuwa. A ranta ta ce 'Cusa kai.'


Ramlat ta gaidata da murmushi saman fuskarta. Ta mance rabon da ta sanya Bilkisun a idanu, gaba daya ta kara wani fari fat sabida shafe-shafe ga wani uban ƙiba da ta ke narkawa, ita kuwa Salma har tambarin baƙi-baƙi ya yi mata a fuska. Ramlat ta ja hannun Yasmeen suna gaisawa, yarinyar yanzu ta bar sakewa sosai kamar a baya don dif haka uwar ta raba ta da gidan. Yanzun ma da biyu ne zuwannata, ba ta san mijin Ramlatun ba. Ko a hanya suna ta gulmar abin suna dariya don har Salma na fadin Allah Yasa wani Alhajin ne mai mata uku da katon tumbi. A jikinsu ba su taɓa kawo wai matashi mai jini a jika zai aureta ba musamman idan an san wacece ita.


"Murja da Fareeda ma suna tafe, Hilal ya fadamusu tunda ke ba ki iya gayyata ba."


Ramlat ta dubi Amrah, Amrah ta kanne mata ido don ta san gulma ce.


"Ayya, ban yi zaton za su zo bane. Allah Ya kawosu lafiya kuwa. Ina murna."


Bilkisu ta taɓe baki ita kuwa Salma murmushi ta yi ta dora kafa daya kan daya tana girgizawa. Sai dai kyakkyawar budurwar da suka gani da aka kirata da yar uwar mijin Ramlatun duk sai suka soma shan jinin jikinsu. A hankali Salma ta yi magana saitin kunnen Bilkisun.
"Anya wadannan mutanen su na da labarin wace ce Ramlat a baya?"


Bilkisu ta ce "Oho musu, nikam daga suturar jikin yarinyar kamar dai ba karamin mutum shegiyar ta kwaso ba. Ai kuwa ƙafata ƙafarsu har Adamawan naje na ƙarewa danginnasu kallo sosai."


Salma da takaici da bakin ciki ya cika zuciyarta, ita kasa magana ma ta yi. Shekararta sama da ashirin da biyar yanzu amma ko auren fari ba ta yi ba, ga Ramlat har ta kara samun wani ɗanɗasheshan. Don jikinta ya fara ba ta hakan. Burinta yanzu a daura auren ya shigo ta karemasa kallo.


***
Yana kishingide saman kujera a gidan Hisham wanda ya shiga wanka, hotunan da Hafsat ta hankaɗomasa ta whatsapp ya ke aikin kallo, sosai ya yi zooming hoton Madam din tasa ya kasa kauda ido. Murmushi ya ke yana jin soyayya mai tsafta na kara mamaye ko'ina na zuciya da kwakwalwarsa.


Ba zato ya ji an fisge wayar, ya dan dago a ɗan razane don sam bai ji tahowar Hisham din ba. Hisham wanda ke daure da tawul ya ja tsaki.


"Aikin banza, sai afkin karewa mace kallo amma ba a iya tattali ba. To ka tashi, yanzu Yayanmu ya kira ya ce sun iso, ka tarbo su suna waje."


Hussein ya mike zaune gami da dan dafe kai kafin ya mike ya ja guntun tsaki yana gyara zaman rigarsa ta shadda fara ƙal sai dai babbar rigar na ajiye bai sanya ba.


"Ka ci gaba da shiga rayuwata. Kuma ma meyasa ya kiraka bai kira ni ba?"


"Ganin dama."


Daga haka Hisham ya yi ciki da wayar Hussein din a hannunsa don ya shirya, Hussein ya bishi da harara don sosai ya ragemasa nishadi, a bakin gate ya ci karo da su. Ganin wanda bai zata ba sai kawai ya tsaya kamar wani gunki baki a bude.


"RASHEED?!" Ya furta kai tsaye kafin da azama su yiwa juna wata wawuyar runguma da bubbuga gadon baya ana dariya. Can ya sakeshi suka kara cafkewa su na dariya. Nan da nan idanunsu suka kada kuma kamar wadanda ke shirin kuka. Tabbas sun yi masifar kewar juna. Bai ma ga sauran yan uwansa uku da ke tare da su ba sai da ya gama gaisuwar da Rasheed. Najib, Faruk da kuma Khalil duka Yola idan ka cire Faruk da ya zo daga Mubi.


"Allah Ya isa, ban yafewa matarnan."


Rasheed ya fadi sadda suka nutsu suka zauna a falo. Murmushi Hussein ya yi.


"Ka bar damuwa da ita, ta kusa zama tarihi. Momi ta zo?"


Rasheed ya jinjina kai. Yana nufin mahaifiyarsa, Hajiya Binta.


"Yes tare muke, tana can Yola wurin Dada."


Haka suka yi ta hirarsu cike da nishadi, shi dai Hussein bini-bini zai duba agogo. Ganin lokacin sallah na ƙaratowa ya dubesu.


"Ya kamata mu hanzarta wuce masallaci ko?" Lokacin sallah ya gabato."


Me zasu yi ba dariya ba.


"Lokacin sallah ko lokacin daura aurenka? Kai Malam ba ka da kunya wallahi."


Faruk ya fadi yana dariya.


"Bar shi kawai, ai idan bai yi hakan ba bai cika sabon shiga ba."


Hussein dai har ga Allah sun soma ba shi haushi, dagaske so yakeya ga an hanzarta an tashi an tafi.


"Na rantse zan muku ƙofi yanzun nan ku ga maciji."


Ya fadi yana mai mikewa tsaye suka yi dariya sosai shi kuwa ya shiga zura babbar riga yana mai tafiya gaban madubin dake falon yana gyara zamanta. Karshe ma hular ya dauka ya shiga gyaramata zama yana ji AlHassan na cewa su tashi don da alama Angon zai iya ficewa ya bar su. Nan kuma wadanda ba su da alwala duk suka dora sannan aka kama hanya bayan Hussein ya feshe dukkan jiki da turaruka masu tsada da kamshi har kala uku. Bababn burinsa Ramlat ta zama mallakinsa kafin kowane irintsautsayi ya gifta da ba ma ya fatansa.


***


Misalin karfe biyu da mintuna, dubban jama'a suka shaida daurin auren HUSSEIN AMINU GIDADO da RAMLAT KHALID MU'AZZAM akan sadaki har dubu ɗari wanda nan take aka damƙawa Babanta Dakta matsayinsa na waliyyinta.


Bakin Hussein ya ƙi rufuwa, sosai daurin auren ya tara mutane. Hilal kansa sai da ya halarta, duk da Hussein ya san shi, haka suka gaisa faran-faran suka yi hotuna. A karshe aka dunguma gaida iyaye.




***
Babu damar sallah a wurinta sakamakon tana fashinsa, sai dai ta yi sujjadar godiya ga Allah kuma ta yi addu'a sosai.


Bayan ta mike ne Amrah ta ba ta tissue.


"Don Allah kar ki ɓata kwalliyar mana."


Ta karba tana goge hawayen.


"Kukan munafunci ne kawai, mace sai ka ce yau aka taɓa dauramata aure. Aure na uku?"


Bilkisu ta fadi da dariyar kissa, Hafsat jin ta ce aure na uku yasa ranta ya ɓaci, dadinta Hussein bai ɓoyemusu komai na labarin Ramlat ba. Dama tun zaman Bilkisun da irin kallon da suke jefamata ita da abokiyar rakiyarta ta ji sun ba ta haushi.


"Ko aure na nawa ne ai aure ne. Duk wacce ta san me ta ke yi dole zuciyarta ta karye a wannan rana, ko bakomai ta san nauyin da Allah Ya ɗoramata."


Maganar Hafsat ta zo wa su Bilkisu a bazata, wato dama sun san komai? Nan da nan ransu ya kara yin baƙiƙirin musamman Murja da Fareeda da basu jima da shigowa ba, suma dai ganin kwakwaf dinne.


"Muje falo ga Angon ya zo."


Fadin Muhibbat da ta shigo, ta ja hannun Ramlat suka fice, Aisha kam ji ta yi kamar ta goya Hafsat don dadi, balle kuma Rafee'ah da ke dariyar shaƙiyanci. Sosai Hafsat ta burgesu don kanta a waye yake ba karya. Ai su Bilkisu na jin haka suka bi bayansu rii duk domin su ganewa idonsu Angon Ramlatu. Ai kuwa sun yi kyakkyawan gani da ya birkita tunaninsu.


Yana durkushe gaban yan uwan Ramlatun ana kwasar gaisuwa, sai ga Amaryar. Nan da nan tsofaffi aka sjiga guɗa da kirari. Ya kasa kauda idanunsa a kanta, ita kuwa ganin irin kallon da yake mata babu kunyar ido yasa ta yi ƙasa da idanunta.


Tsakiya aka zaunar da ita shima ya zauna, yan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login