Showing 219001 words to 222000 words out of 231786 words

Chapter 74 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

hancinta kafin ya rungumota ta baya.


"Albishirinki."


"Goro."


"Alhamdulillah, bisa la'akari da workkng experience dina da kuma credentials, Yayanmu ya samarmin aiki a wani Kamfanin gine-gine. Sosai su ka yaba da komai nawa "


Ta juyo ta ba shi kyakkyawan sumba a kumatu. Ganin ya jefata da wani kallo ta kauda kai tana murmushi don har sannan wani lokacin Hussein dinta kwarjini ya ke mata.


"Congratulation, Allah Yasa a fara a sa'a. Ya kara daukaka."


"Ameen dearest one."


Daga haka ya jawota ya hau yi mata raɗa a kunne. Daidai sadda wayarta ta yi ringing, kasancewar shi ne a kusa, ya ɗauma, ganin baƙuwar lamba sai ya ɗaga kawai, bai kai da sallama ba muryar namiji ya ratsa dodon kunnuwansa.


"Assalamu Alaikum, Adda barka da rana. Taheer ne."


Wani irin kallo ya ke bin Ramlat da shi, Ramlat gabanta ya fadi, ta sani dai a dazun Taheer ya kira ya ce yana son magana da Hafsat zai mata wani albishir, ta ce ya bari idan ta shiga gidan sai ta kira. Shaf ta mance, kuma ba ta samu shiga ba sakamakon wankin undies dinta da ta tsaya yi. Jikinta ya bata akwai matsala. Ba ta gama tantancewa ba sai da ta ga Hussein ya miƙamata wayar ya kuma ƙuramata idanu. Ta karɓa da rawar hannu, gaba daya ta ruɗe, tunda suka yi aure ba ta taɓa ganinsa a wannan yanayin ba kuma ma adalilinta sai yau.








I just published "BABI NA SITTIN DA BIYAR" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1032619087?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=WqGcOpyrKLCeYJ2pB6S21O2rofM3hfkPhkl8xHn5YliOXRIEhSFgVvGwVllJASGRLQwGf8a%2FEFI9gUseG%2BLsfaQfid671L2Bpg0RFziPc0xIuxqo35SEHCqXV8izbKgB










🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.


65)






_*Assalamu alaikum masoyan karfen kafa. Ina ba ku hakuri mai yawa. Na so kwarai na haɗa post din nan da na karshe na aiko gaba daya, sai dai na sani kun yi hakuri iyaka, makaranta da ma sauran abubuwa ke ɓoyeni da hana ni typing. Saboda damuwar da ku ka yi na hakura zan soma posting wannan, daga shi kuma sai BABIN KARSHE in sha Allah. Ku yi hakuri, na tabbata duk wanda aka ba hakuri baa aikatamasa daidai ba. Amma kuyi hakuri. Ina kaunarku fisabilillah.*_








"Hello. Taheer ba..ta..ba ta kusa."


Daga yanayin muryarta ya fahimci akwai matsala, bai kara magana ba ya katse wayar yana mai dana sanin kiranta duk da irin gargadin da ta yi mishi akan muddin ba ita ta nemeshi ba su yi magana da Hafsat, kar ya yi gangancin kiran wayarta.


Hussein juyawa kawai ya yi ya wuce ɗakinsa, ta dage goshi tana kiran sunan Allah, shakka babu laifinta ne ko me ya faru. Ta saɓa umarninsa na hana Hafsat waya, tunda yanzun ba amfani, abinda ya ke gudun, tana yi da wayarta.


Ramlat ta numfasa, tunani take ta bishi ko ta kyaleshi zuwa anjima kaɗan? Sai dai idan ta rabu da shi, tana tsoron kada ya ƙi cin abinci alhalin daga yanayinsa kadai ma ta fahimci ya kwaso yunwar.


Mikewa ta yi tsam ta nufi dakin. Ba ya nan, alamar an kunna ruwa yasa ta fahimci yana banɗakin. Ta nemi wuri gefe gadon ta zauna, ta ɗan jima zaune kafin ya fito ɗaure da tawul a ƙugunsa sai karami a hannun yana share ruwan gashinsa. Bai ko kalleta ba ya yi gaba zuwa gaban madubin, da saurinta ta karasa ta bayansa, ganin abinda ta ke shirin yi, wato rungumoshi, sai kawai ya juyo fuska ba walwala hakan ya dakatar da ita, ta sunkuyar da kai har idanun sun cicciko da kwalla.


"Don Allah ka yi hakuri, ba zan ƙara ba. In sha Allahu an yi na farko da karshe."


Bai ce mata komai ba ya juya ya bar gaban madubin bayan ya gama abinda ya kai shi. Ramlat jikinta duk ya yi sanyi, ta sa hannu ta dauke hawayen da ya gangaro. Shi kuwa gogan, yana kammala shirinsa cikin kananun kaya ya feshe jikinsa da turaruka masu kamshi, ya fice. Ta bi bayansa da sauri ganin ya dauki mukullin mota, da wani irin gudu da ba ta san ta iya ba ta rigashi isa da ƙofar ta tare. Duban tsakar ido suka yiwa juna, kowannensu sai da yanayinsa ya sauya. Ba tare da ta dauke idanunta ba ta ce.


"Don Allah ka saurareni, nayi maka laifi ka yi hakuri ka yafemin."


Kamar ba zai tanka ba sai kuma ya kare tamke fuska.


"Tun yanzu zan yi hukunci akan abu, ki nunan bai maki ba har ma ki goyawa wannan abun baya, wane irin kallo kike son na yi maki? Ke a yanzu sai dai ki ba wani labarin abinda ya gudana tsakaninmu da uban yaronnan, duk wannan ma bai min ciwo ba kamar yanda har kika iya take umarnina. Ko ban hanaki ba, tunda har kika ga na raba ta da wayarta kin san me nake nufi. Ban wuri na wuce."


Maimakon ta matsa sai kawai ta noƙe kafaɗa gami da marairaice fuska, kallonta kawai ya ke yi. Daga yanayinsa ta soma fahimtar ya soma saukowa don haka ta sanya dukkan hannuwanta ta rungumoshi ta kwantar da kai a saman kafaɗarsa.


"Ka yi hakuri, na tuba ba zan ƙara aikata laifi irin wannan ba. Please Haskena."


Shirun da ta ji har ta fidda ran zai sauko, ta soma kokarin janye jikinta ya riƙo ƙugunta dakyau, fuskarsu ya haɗe wuri guda yana bin karan hancinta da kallo kafin ya maido idanunsa cikinnata.


"Kinsan ba na iya fushi da ke ko?"


Ta yi murmushi ta lumshe ido gami da gyaɗa kai duk a lokaci guda, a hankali kuma ya shiga aikamata saƙo mai kashe jiki. Karshe dai Hussein fitar da bai yi ba kenan, dama sanadin bacin ran da yake ciki ne ya tilasta masa son fita. Can ta janye jikinta ganin yanda ta matsu da jikin ƙofa.


"What?" Ya fadi da dusasshiyar muryarsa. A shagwaɓe ta amsa.


"Yunwa."


Ya yi murmushi gami da ɗaga rigarta ya shafi cikin. Lumshe idanu ta yi.


"Allah Yasa mun samu ƙaruwa."


Ta harareshi da wasa kawai ta juya ta bude kofar, ya biyo bayanta don shi kansa yunwar ke cinsa. Sai da suka kammala ba cikinsu hakkinsa kafin kuma ya miƙe ya shiga ɓangaren Dada. Ramlat dai jikinta ya yi sanyi don har tausayin Hafsat ya kama ta, ta tabbatar yau kam Hussein ba zai ɗagamata ƙafa ba.


Aikuwa hukuncin da ya dauka a kanta mai tsauri ne don har makaranta ya ce ta zauna sai ya yi magana sannan ta ci gaba da zuwa, amma fita dai ko nan zuwa farfajiyar gidan ce ya hanata. Ya kuma rantse muddin ta kara gangancin yin waya da Taheer sai ya saɓa kamanninta. Da wannan bakin cikin ya bar Hafsat ya fice abinsa.


***
NIJAR-KANO


Sun ɗau hanya miƙaƙƙa daga Maradi don dawowa Nijeriya, garin Kano. Zuƙatan kowannensu farin ciki ne marar misaltuwa, duk da irin wata azaba da su ke ji a tsakanin mazaunansu, hakan bai sa sun kasa yin murnar samun nasara ba. Kowaccensu ta matse kwalin aikin da ta karɓo a ƙasan ƙafafu, idan kuwa wuri ne mai gargada, sai su yi maza su riƙe dakyau a hannunsu. Har suka isa Kano tulun nan yana matse da su.


Gidan Hajiya Zeenatu aka soma zuwa, suka rabu da Hajiya Batool direba ya yi gaba da ita. Ma'aikatan na ta kallon Madam din tasu riƙe da kwali, abinda suke ta tunani bai wuce ko meye a cikinsa ba. Ita kuwa tana shiga ɗakin ta samu wuri mai kyau ta killaceshi. Yanzu gaba daya tunaninta shi ne na tafiya Adamawa a gobe-gobennan, don ta fi son komai ta yi shi da gaggawa sai dai kuma yanda ta ke jin bayanta naaa azabar da radadi da ciwo, dole sai ta ji sauƙinsa. Don haka ba ta zauna ba, bandaki ta shiga ta haɗa ruwan ɗumi. Sai dai koda zamanta wani uban ƙara ta saki na azaba. Ranar dai wuni ta yi jiki ba dadi don har da su zazzaɓi. Haka ta samu labari daga Hajiya Batool, ita kam har wani ruwa ta ke fitarwa.


Wasa-wasa zazzaɓi ya tsananta ga Hajiya Zeenatu, har washegari da ta ke fatan tafiya Adamawa, abin ya gagara. Dakyar ta iya daukar waya ta kira likitanta. Har gidan ya zo ta kira Emma a waya ta ba shi iznin a shigo da shi. Ya karasa har dakinta, ya yi mata allura. Koda wasa ba ta bari ya san ɗaya ɓangaren na ciwonta ba, yana kammalawa ya fice abinsa. Aikuwa wani wahalallen bacci ya yi awon gaba da ita.


Ta fi awa hudu tana bacci, kafin ta farka, ba laifi ba kamar sadda ta kwanta ba, kusan ma babu zazzabin sai uban gumi da ta ke yi. Wayarta ta jawo, ta bude rututun missedcalls da ta gani na Manajanta mai kula da shagon gwal-gwalanta. Kafin ta gama shanye mamakin, wani kiran ya ƙara shigowa. Ta ɗaga da saurinta.


"Hello! Hajiya, gobara! gobara ta cinye shaguna har da namu! Ga wuta har yanzu an kasa tsayar da ita!"


Daga jin yanda ya ke zancen a matukar rikice ya ke don ba laifi shima yakan haɗa da nasa jarin ya juya. Wani irin miƙewa tsaye da Hajiya Zeenatu ta yi, sai ga ta a kan ƙafafunta, jikinta ko'ina ya ɗauki rawa, shi kenan dukiyar da ta ke taƙama da shi yanzun kaɗai a duniya.


"Me ka ke cewa Bala? Me kake nufi wai?!"


Inaa! babu kwakkwarar amsa, tana ta hello amma kamar babu service ga kuma hayaniyar jama'a ta cika wurin. Ai ko mayafi ba ta tsaya ɗauka ba, mukullin motarta kawai ta ɗauka ta fito hankali tashe. Ma'aikatan na ganinta suka nufota.


"Hajiya lafiya?"


"Ba za ku gane ba! Yi sauri budemin gate! Gobara a sabon gari!"


Hakan da ta fada duk sai suka fahimci inda zancen ya dosa tunda duk sun sani tana da shago a sabon gari, wato dai an samu matsala, da sauri Emma ya karbi mukullin ya ce ta bari ya kai ta ba ta da nutsuwar yin tuƙi. Ba musu ta miƙa masa jiki na rawa ta koma mazaunin kusa da direba. A hanya kamar za ta yi tsuntsuwa, duk irin gudun da Emma ke shararawa ba ta gani. Tuni ta nemi ciwo ta rasa.


Cunkoson ababen hawa da na yan sanda har ma da motocin kashe gobara, ya sa dole Emma sai wuri ya samu ya ajiye motar suka karasa da kafa. Hajiya Zeenatu na ganin yanda shagon ya ƙone ƙurmus babu abinda ya bari kawai sai ta faɗi yanke jiki ta faɗi. Nan fa mata da maza aka yi kanta, bakinta tuni ya karkace tana fidda yawu, idanunta kuwa kamar mai harara garke. Emma da ma wasu aka taimaka wurin daukarta zuwa asibiti, Manaja ya yi danasanin kiranta a waya sai dai hakkinta ne ta sani. Kusan ma akwai wadanda sai da suka sume, wasu kuwa banda kuka ba abinda suke yi kama su yi hauka.


Asibiti kai tsaye Emma ya wuce da Hajiya Zeenatu cike da tashin hankali, Likitan dai da ya zo mata dazun, Dakta Salisu, wurinsa suka je. Ya yi matukar mamakin ganinta a cikin wannan yanayin, anan Emma ya labartamasa komai. Nan da nan likitoci suka rufu a kanta sai dai kuma sun makaro, Hajiya Zeenatu an samu ta ɗan dawo daidai amma fa ta hadu da shanyewar ɓarin jiki hakanan tana magana a jagwalgwale miyau na kwaranya ta gefen bakin. Banda hawaye ba abinda ta ke yi, ba abinda ke yawo a ranta sai kudirinta na zuwa Adamawa. A yanda ta ke jinta, ko a wane hali ta ke sai ta je. Sai ta samu Hussein ko ta halin ƙaƙa.


Nan kuma Dakta Salisu ya ba Emma umarnin sanarwa mijinta da yan uwanta, Emma nan take ya sanarmasa cewa Ogansu ya rabu da ita. Dama kaf dinsu sai da ya bisu da alheri kuma ya yi musu sallama da zummar ya tafi kenan. Ba su ji dadin hakan ba amma sun mishi murnar rabuwa da muguwar mata irin Hajiya Zeenatu, ko ba komai sun jima da sanin munanan ɗabi'unta da yanda Ogansu ke shakkarta.


Ba wacce ta fado a ran Emma sai Hajiya Batool, ya san matar aminiyar Madam ce, don haka ya fice daga asibitin ya nufi gidanta.


Hajiya Batool na zaune tana jin wani mugun farin ciki yanda ɗanta ya kira waya yana sanarmata da cewa a gobe-gobennan zai taso saboda kewarta da ta cikashi, kuma a shirye yake da bin umarninta, dama ita kiranye aka bata, kuma har gshinan kwalliya ta biya kudin sabulu, ta kuma ci burin dole ta sanya ya saki Fa'iza ya auri wacce take so. Ta kira wayar Hajiya Zeenatu ya fi a ƙirga don ta ba ta labari amma ba ta samunta, karshe ma ta ji wayara kashe.


Tana shirin sake gwada kiran, sai ga Mai aikinta ta shigo tana sanarmata da batun zuwan Emma daga gidan Hajiya Zeenatu. Nan ta bada umarnin ya karaso, Emma bayan sun gaisa ya fadamata halin da Hajiya Zeenatu ke ciki. Hankalinta ya tashi ba kadan ba, ta kaɗu sosai. Ba shiri ta ce ya je za ta leka asibitin. A yammacin ta je, ta yi mamakin yanayin da ta riski aminiyarta a ciki.


"Zeenatu! Ke ce haka?"


Hajiya Zeenatu sai ido da kuma hawaye. Da harshenta wanda maganar ba ta fita sosai ta ce.


"Ni..ce. Batool ki kai ni wurin Hussein."


Hajiya Batool ta girgiza kai ta riko hannunta.


"Ki bari ki warke, ki nutsu kiyi zamanki a asibiti a dinga yi maki magani tukunna. Zan turo Dije ta dinga tayaki zama, za ki warke. Da kafarki za ki je wurin Hussein."


Hajiya Zeenatu dai sai hawaye, a ranta kawai bakin cikin abinda ya faru ta ke ji, da ace ta san hakan za ta faru da tun farko ba ta amsa wayar Manaja ba balle ta je kasuwar. Ji take inama ta kama hanyar Adamawa. Ta kara kallon Hajiya Batool dake ba ta labarin dawowar da ɗanta zai yi, haka kawai maimakon ta tayata farin ciki sai ta ji hassada da kishi sun kama ta, wato aikin Hajiya Batool har ya yiwu ita kuwa babu ɗaya da ta aikata, don aikin tulun ba zai yi tasiri ba sai ta je ta barbaɗawa Hussein hodar da Buzu ya ba ta. Haka tana ji tana gani Hajiya Batool ta fice daga asibitin gami da jadddamata za ta turomata Dije. Ita dai Hajiya Zeenatu gyada kai kawai ta yi, a yau ta ji takaicin rashin ajiye ƴar aiki mace da ta yi.


***
ADAMAWA


Baƙin Kano sun sauka lafiya a family house, suka yada zango a ɓangarensu, wannan karon ma an musu tarba sai dai ba kamar yanda aka saba ba. Kawu dai jikinsa duk ya yi sanyi, a ranar da yammaci ya tara manyan dattawan gidan maza da mata yana kuka yana roƙar gafararsu.


"Sharrin shaiɗan ne, ku yafemin domin Allah. Itama Aminar da yaran yanzu zan je na nemi afuwarsu."


Kowa kam ya yi farin ciki da jin hakan, ko ba komai har da rashin nadamarsa ne ya ba mutane haushi. Nan dai bisa jagorancin wani ɗan uwan Babansu, Surajo, tsoho mai ran ƙarfe, suka ɗunguma har iyalin Kawun, a yammacin zuwa gidan Dada.


***
Kwance yake saman doguwar kujera, yayinda ta ke kwance saman kirjinsa. Sai cuku-cukun miƙewa ta ke yi sakamakon raɗan da ya ke mata a kunne amma hakan ya gagara. Ta ko'ina ya matse ta gam! Ai kuwa bai yi aune ba, yana kai bakinsa saitin nata, ta yi azamar kama leɓensa na ƙasa ta ciza. Bai san sadda ya sake ta ba gami da kama baki.


"Aush!"


Ramlat na dariya ta mike, daga ita sai riga sky-blue marar nauyi, da kaɗan ta wuce gwuiwarta. Gashinta wanda tuni ta warware kitson yana tufke a baya.


"Sorry." Ta fadi tana ɗaga yatsunta bayan ta ja baya sosai tana dariyar mugunta. Hussein ya lashi leɓensa ya manna mata harara.


"Zan kama ki, yau ba mai kwatar ki."


Ta narkar da fuska.


"Haba don Allah Haskena, kai ɗin ne ka ƙi hakuri ka bari na kammala girki. Nikam kana sane ka ce sai wani satin za ka fara zuwa aiki. Don.."


Ganin ya yi wani irin miƙewa ya na kokarin cafkota ya sa da wani irin gudu ta shige kicin ta rufe tana dariya. Ya jingina jikin kofar.


"Za ki fito ki same ni, na san maganinki."


Murmushi kawai Ramlat ta yi mai bayyana haƙora ta ƙarasa wurin tukunyar miyarta, ba don na wutar kaɗan-kaɗan ta ke ci ba, ta tabbatar sai ya ƙone.


Shi kuwa gogan yana shirin komawa ya zauna, aka kwankwasa ƙofar falon da sallama. Ya amsa da ba da umarnin shigowa.


Hafsat ce, gaba daya jikinta a sanyaye. Ya dube ta fuska a tamke don har lokacin bai gama saukowa daga fushinta ba. Ta gaida shi ya amsa ciki-ciki.


"Dada ce ke kira."


Ya gyaɗa kai kawai ita kuwa ta miƙe ta fice kirjinta na dukan tara-tara. Tana tsoron abinda zai biyo baya idan ya ga waɗanda suka zo gidan. Sanin halin zuciya irin nasa ne yasa Dada kiran AlHassan a waya akan ya zo gidan bayan ta mishi bayanin komai. Wannan yasa ba ɓata lokaci, AlHassan ya kamo hanya don ba tazara sosai tsakaninsu.


"Heart, bari na je Dada na kirana. Kinji ko?"


"Toh."


Ta amsa ba tare da ta buɗe ƙofar ba. Ya gyara zaman brown tshirt dinsa ya zura silifas dinsa baƙaƙe na maza na yawo a gida ya fice. Tun a farfajiyar gidan ya ci karo da motoci, wannan ya ba shi mamaki ya tabbatarwa kansa baƙi suka yi, amma daga ina? Shi ne tambayar da babu amsarta a yanzun. A ƙofar falon ya ci karo da takalman maza da mata. Haka kawai ya ji gabansa ya fadi da sauri kuwa ya karasa ciki da sallama. Idanunsa bai sauka kan kowa ba sai a kan mutumin da ya fi tsana nan duniya zaune kusa da Dadarsa su na kuka. Ya fahimci komai, ya gane kuma Dada ta sauko ta yarda da dukkan ƙarairayin da ya shiryamata don haka shi ba shi da bukata. Tsigar jikinsa gaba daya ta tashi tsabar ɓacin rai, yayinda idanunsa suka kaɗa, ya ƙaraso ciki da zummar ƙarasawa kai tsaye ga Kawun ya shaƙe wuyansa babu ko tunanin yaransa da ke zaune a falon. Da sauri Baffa Surajo ya mike ya shiga tsakani. Ganin girma da cikar haibar dattijon mai tsananin kwarjini ya sa shi kasa ƙarasawa sai hawaye da suka shiga zubowa kawai daga kwarmin idanunsa.


"Me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login