Showing 138001 words to 141000 words out of 231786 words

Chapter 47 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

zai yimin sanadin wurin neman halal ɗina. Dama shawara zan ba ki kawai don matar Chairman ba kanwar lasa ba ce."


Don tsananin ɓacin rai ba ta san sadda wani wawan tsaki ya suɓucemata ba.


"Daga ita har mijinta basu ɗaɗani da ƙasa ba, ke kinsan ni kuma kin san halina. Bana kallon mutum irin Chairman matsayin nagartaccen namiji da ya isheni kallo ballantana har na ƙulla alaƙa ta dindindin da shi, wato aure. Ke dai da ya tsolemaki ido har ki ka kasa haƙurin bar wa cikinki gulmar sai ki je can ki ƙarata."


Daga haka ta katse wayar ta kasheta gaba ɗaya ma tsabar takaici da ɓacin rai. Har suka isa ta sauka ba ta ji sassauci a ranta ba. Ita ta soma zargin ma Halimar ce ta kwatantawa Chairman din gidansu na Yakasai. Can kuma ta ja istigfari a ƙasan ranta.


***
*
ADAMAWA*


AlHassan ke ta zuba sauri a hanyarsa ta komawa cikin babban shagon siyar da kayayyaki na Alkhairat Mall adalilin mantuwar da ya yi na wallet ɗinsa saman teburin Cashier.


Karo suka ci da wani matashi da kallo ɗaya za ka yi mishi ka san ruwa biyu ne, kamar dai ɗan Sudan kamar kuma ɗan Nijeriya.


"Sorry please." Faɗin AlHassan kenan yana dubansa a fisge, Matashin ya zaro ido kafin ya saki ƴar dariya yana nunashi da yatsa.


"Hussein!"


Daga haka ya rungumeshi yana dariyar farin ciki, AlHassan ya tsaya cak! Ya kasa magana kwakkwara, can dai ya ɗago ya dubeshi da kyau, kamar ya so sanin fuskar sai dai Allah bai ba shi ikon tunawa ba.


Rasheed da ya lura da irin kallon da yake binsa da shi, sai jikinsa ya ɗan yi sanyi. Daidai sadda wani ma'aikacin wurin ya nufosu, duban AlHassan ya yi.


"Yallaɓai ai na fita ban iskeka ba mun yi saɓani, ga wallet ɗinka ka manta."


Ya karɓa da godiya, Rasheed dai kallo yake sai kuma a sannan tunaninsa ya ba shi anya kuwa wannan Hussein ɗin da ya tako takanas daga ƙasarsa don ya gani ne? Nan da nan jikinsa ya ba shi Twin brother ɗinsa ne wato AlHassan Aminu.


"My name is Alhassan Aminu, Hussein's Twin Brother."


Rasheed ya shiga murmushi da gyaɗa kai, bai lura da yanayin sauyawar fuskar Alhassan din ba, daga yanayin farko zuwa wani yanayi na daban mai nuni da alhini da kuma sosuwar rai.


Alhassan ya nemi su ɗan fito farfajiyar wurin. Ba musu Rasheed ya bi bayansa. Ji yake kamar ya yi tsuntsuwa ya je ga Abokinnasa, shekarun da suka gabata ya yi masifar kewarsa. A hanyar ma su na tafe ƙorafi ya ke zubawa AlHassan na yanda Hussein ya kasa cika alƙawarin kawo mishi ziyara sai shi ne ya cika a karshe.


"Kusan satina ɗaya a garinnan na kasa gane gidanku, har na fidda rai don har na yi komai na komawa garinmu sai yau cikin ikon Allah muka haɗu da kai."


Duk yana maganar ne cikin harshen turanci, Alhassan ya ba shi address din gidansu kafin su yi musanyen lambar waya suka rabu. Rasheed dai ya yi mamakin dalilin da yasa bai ba shi lambar Hussein ba, ya so tambaya kawai sai ha bar wa cikinsa. Da wannan ɗokin ya nemi adaidaita ya koma masaukinsa, siyayyar da bai yi ba kenan tsabar murnar cimma abindanya kawoshi. Tun a hanya ya kira mahaifiyarsa yake labarta mata haɗuwarsa da AlHassan da yanda ya rungumeshi a zatonsa Hussein ne. Ta tayashi murna sosai sannan suka yi sallama.


***
*KANO*


Tana zaune bayan kammala wasu aikace-aikace, ta tuna da cewa wayarta a kashe ta bar ta gaba ɗaya yinin ranar, da sauri ta jawota ta kunna. Mintuna ƙalilan da kunne Data, saƙonni suka shiga faɗowa daga Whatsapp. Wanda ta ke burin ta ga ya aikomata saƙo babu shi a ciki, har tana shirin ajiye wayar sai ga text message ya faɗo, ta duba. Ba ta kai ga buɗewa ba sai ga kira, duk daga mutum ɗaya wanda ta daukeshi SPECIAL.


"Kashe mutum kike kokarin yi."


Ta ɗan dafe ƙirji kafin ta saita kanta tuna a inda ta ke, lumshe ido ta ɗan yi tana murmushi. A baya zabta ƙaryata idan wani ya ce za ta ko kalli wani ɗa namiji ta ji ya burgeta balle ta kaunaceshi, a yanzun kuwa tana jin Hussein a ranta. Da wani irin ƙauna mai sanyi, da wani irin so mai cakuɗe da sinadarai masu ban mamaki.


"Tuba nake yi, me na yi?"


Ya sauke ajiyar zuciya wanda ya ratsa kunnuwanta.


"Kin kashe wayarki bayan kinsan na kamu da son Beautiful Angel dinnan da kika ɗora a status."


Runtse idanu ta yi cikin son haɗiye abinda kunnuwanta su ka yaudareta da son ji. Maimakon hakan sai ta ji abu daban, cikin sarewa da sanyin jiki ta amsa.


"Ka yi hakuri, na ma manta cewa na kashe wayar. In sha Allah yanzu zan turamaka."


"Ok! Na gode, ina jira."


"Toh."


"Naji muryarki ta sauya, hope komai lafiya?"


Ta ciji leɓbanta na ƙasa tsabar haushin kanta da ya kama ta, toh mene dalilin da za ta ba shi damar fahimtar wani abu?


"Lafiya kalau, ina wurin aiki ne."


Shiru ya biyo baya can kuma sai ya amsa.


"Ok ba damuwa. Idan kin koma gida kya turomin. Thanks."


Daga nan ya katse kiran.


"Ke kam dai naga alamar da wani gwanin naki kike waya."


Ta kai duba ga Hajiya Salma, darakta din department din da ta ke. Kasancewarta mace mai raha da haba-haba yasa ake sonta. Ga ba ta da wuyar sabo. Murmushi kawai ta yi ba ta ce uffan ba. Ta faɗa whatsapp, Hussein din ma ba ya online, haka ta turamasa duk hotunan Fatima da ke kan wayarta har wanda Fatiman ke tare da Hafsat. Babu dai nata ko ɗaya a ciki.


Karfe biyar da kusan rabi ta bar Ofis zuwa gida. Gaba daya jikinta a sanyaye yake sakamakon soyayyar da ta ke yiwa kanta shamaki da ita, amma kamar zuciyar ba ta jin kashedinta. Ƙara cusa kanta take yi cikin lamuran Hussein dumu-dumu. Idanunta ga cicciko da kwalla, ta sharesu. Ya dace ta yi baya-baya da shiga shirginsa tun kafin ta yi nisan da ba ta jin kira a sha'aninsa. Ko babu Hajiya Zeenatu, Hussein ya fi ƙarfin ajinta. A ganinta, wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa.


Haka ta wuni cike da kasala, sai dab da Magriba sannan ta fito ta faɗa kicin, kunu ta dama, ta zubawa Hajiya wacce ke azumi cikin flask mai riƙe zafi. Dama ta iske tuni an yi Ƙosai. Wannan tasa ta haɗamata da lemun zoɓo da ya sha kayan ƙamshi.


Sai da ta tabbatar ta haɗa komai saman darduma kafin ta koma ɗaki, alwala ta ɗauro. Wayarta na kyallin shigowar saƙo don haka ta duba.


*"Thank You."*


Abinda ya turomata kenan. Murmushi kawai ta ɗan yi ta shimfiɗa darduma.


Misalin ƙarfe takwas da rabi suna zaune a falo tare da Hajiya, kallon Tarkon Ƙauna suke a tashar Arewa24. Gaba ɗaya hankalin kacokan yana kan talabijin, sallamar Baba Maigadi ta ɗauki hankulansu. Suka amsa. Saƙon Ramlat ta yi baƙo yake tafe da shi. Nan da nan ta ɗaure fuska, tana da tabbacin Chairman ne don dama Kawu yace ta zuba idanun ganinsa a satinnan.


Umarnin Hajiya ta bi kawai ta miƙe ta shiga ɗaki, Hijabin sallarta ta zura ta fita. Kamar dai yanda ta tsammata hakan ce kuwa, yana tsaye ya sha wata narkakkiyar shadda da aka yi mishi aiki a jiki. Ƙaton tumbinsa shi za ka soma haskowa kafin ma ka kai ga ganin komai.


"Mtsw." Ta ja guntun tsaki tana jin kamar ta juya, dolenta ta daure ta ƙarasa. Ganinta ke da wuya, ya ƙara daidaita tsayuwarsa yana mai ƙuramata idanu ga wani haƙoransa da suka bayyana shi a dole murmushin ƙauna ya ke.


"Ranki ya daɗe Ramlatu."


"Ina wuni."


Ta gaidashi ciki-ciki.


"Lafiya kalau Hajjaju. Wato sai kika ganni kwatsam. Wallahi kasa hakurin na soma kiranki nayi saboda jina nake kamar na shiɗe jiya tsabar tunaninki da ya.."


"Ina mai neman alfarmar ka tafi kai tsaye ga abinda ya kawoka, komai nawa nakan ba lokaci muhimmanci. Da ace dai ka sanar da ni zuwannaka tun wuri zan fi samun sukunin tsakurar maka mintoci kaɗan daga lokutan da nake sa shi. Yanzu dai akwai abinda nake yi ka katsemin hanzari. Amma bari na ƙara faɗamaka haƙiƙanin abinda ke zuciyata dangane da kai. Inaga hakan zai taimaka wajen ganin ba mu shiga haƙƙin juna ba."


Chairman Dikko wanda ya zubamata idanu kamar ya haɗiyeta tsabar so, ya jinjina kai gami da gyara tsayuwa.


"Na ji abinda kika ce, ko daga yanda kika tarbeni nasan me kike nufi, kar ki manta kin faɗamin ai tun kafin na tako nan. Amma Hajiya Ramlatu, duk wasu bayananki ba zai sa ni Dikko na haƙura da ke ba, ina sonki, wani irin so da rabona da shi tun a kan Mairo uwargidata. Don haka zan jure dukkan ƙiyayya, na rantsemaki da Allah kika shigo gidana ba za ki ƙara marmarin fita ba saboda daɗin da zan jiyar da ke. Ga kuma madarar ƙauna."


Ya ƙarashe da wata shaƙiyiyar dariya. Ta bishi da kallon tsana, ta sauke idanunta kirjinta na ƙara zafi. Kasa cewa komai ta yi har ya kammala sumbatunsa, karshe ta dubeshi.


"Dare ya fara, na kuma gaji da tsayuwar."


Ya sauke ajiyar zuciya gami da duban agogo.


"Wallahi ban san lokaci ya ja har haka ba, amma nidai don Allah ki ƙara dubawa tunda dai su Kawu sun riga da sun ba ni ke. Kinga kuwa babu abinda zai hana aurenmu, ki sanyawa ranki salama ki yi tunanin alherikan da ke jiranki a gidana."


Ta ƙara ɗaure fuska, ba ta bari sun yi doguwar sallama ba ta juya ta nufi ciki. Ba jimawa da shigarta sai ga Baba Mai gadi da ledoji har uku shaƙe da kaya, da sauri ta karɓa da zummar maida mishi, babu shi babu motarsa.


"Ai ina ce miki ya wuce, ba ki ji ba."


Faɗin Baba Maigadi, cike da takaici ta dubeshi.

"Don Allah Baba kar ka kara amsar saƙon wannan mutumin."


Baba ya ɗan yi shiru, ita kanta Ramlat din sai ta ga rashin kyautatawa tunda dai Baba Maigadi ba ruwansa da alaƙarsu. Juyawa ta yi ta koma ciki.


"Wai ke wannan kumburin da kike yi, ba fa wanda ya matsa akan sai kim aureshi."


Hajiya ta furta tana dubanta. Ramlat da tuni idanunta sun cicciko da kwalla ta amsa.


"Ni Hajiya abinda ke tayarmin da hankali, bai wuce yanda Kawu ya yi saurin aminta da shi ba. Fisabilillah babu bincike babu komai? Ni nasan waye Chairman, ba abinda suka sani a kansa."


"Ke wa ya faɗamaki ana dogon bincike akan mai muƙami ko dukiya? Hum, Ramlatu a zamaninnan ba'a wannan. Bar ganin Yayyuna ne, amma na fi ki sanin halinsu. Ke dai ki dage da addu'a, muddin kuma kina son ki shafe maganarsa toh wallahi ki watsar da komai ki fiddo mijin aure. Shi ne kwanciyar hankalinki da namu baki ɗaya. Ai kin dai ji abinda Uwani ta faɗamaki. Yanzu da ace kin tsaida hankali wurin ɗan uwan mijinnata ai da yanzun sai dai wata maganar ba wannan ba."


Ramlat kirjinta ya yi nauyi, ta share hawayen da ya soma sauka saman fuskarta. Miƙewa ta yi ba ta ko yi marmarin ganin abinda ke cikin ledojin ba ta faɗa ɗakinta. Gefen gado ta zauna gami da zabga tagumi. Tana cikin tsaka mai wuya, ita ta sani. Wanda ta ke masifar so kuma ta ke jin za ta iya aura bai san ma tana yi ba. Runtse idanunta ta yi tana mai sa hannu ta dafe kanta.


"Ya Allah!" Ta furta a fili, fuskar Hussein kawai ta ke gani cikin ƙwayar idanunta. Ta buɗe idanun, tuni sun kaɗa sun yi jazur. A hankali ta kai duba ga hotonsu na Family, Abbanta ta ƙurawa idanu. Take dukkan wani faɗi-tashi da aka yi akan zancen aurenta da Aliyu ya faɗomata. Murmushi ta yi da ya fi kuka ciwo, soyayyar Abbanta ya mamaye zuciyarta, yanzun komai ya zama tarihi. Abba ya bar ta da kewa ta har abada, hakanan Aliyu.


Ta tsinci kanta a sabuwar rayuwar da ba ta san abinda zai haifarmata a gaba ba.


***


ADAMAWA


Misalin ƙarfe biyu da mintuna na ranar Talata, Rasheed ne zaune yana faman haɗa gumi ga idanunsa da suka kaɗa suka yi ja tsabar tashin hankali. Labarin ɓatan amininnasa ya matuƙar girgiza shi.


"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"


Ya furta a fili, Dada dai hawaye ta ke yi hakanan Hafsat da ke raƙuɓe a gefe ta dora hannu saman cinyar Dada. Rasheed ya dubi AlHassan cikin harshen turanci.


"Ban ji dadin wannan labarin ba sam! Sai dai ina ji a jikina duk inda Hussein ya ke yana raye, bai mutu ba. Sannan meyasa ba ku yi cigiyarsa ta gidajen rediyo da talabijin ba? Na dauka wannan ce hanya mai sauki da za ku yi saurin ganoshi."


AlHassan ya jinjina kai.


"A farko duka mun yi wannan amma a karshe sai muka watsar mu ka fawwalawa Ubangiji. Ni kaina ban yarda cewa Hussein ya mutu ba. Amma ya zamu yi? Babu inda ba mu nemeshi ba, sai dai ba wani labari."


Rasheed ya runtse idanu cike da ɓacin rai, ransa na suya.


"Kuma babu wani abokin gaba da ya ke da shi? Wanda ku ke zargi?"


"Babu."


Rasheed ya yi shiru, so ya ke ya tuna ko akwai abinda ya manta game da Hussein. Duk iyakar kokarinsa ya kasa, a ƙarshe dai AlHassan ya shiga roƙonsa akan ko labari ya ji na abinda ya danganci Hussein don Allah ya sanarmusu. Bai bar gidan ba sai da ya ci abinci, nan ma kawai cusawa yake, ba zai ce cimarsu ta bambanta ba don shi kam ruwa biyu ne, mahaifiyarsa ƴar jahar Katsina ce. Jimami da alhinin ɓatan Amininnasa ne ke sukarsa. Da wannan ya musu sallama ya bar gidan.


Ranar dai ya tayarmusu da alhinin Hussein, wunin ranar sun yi shi sukuku ba daɗi idan ka cire Taheer da bai san me ake ba.


Burinsa kawai ya shaƙu da Hafsat kuma ta kaunaceshi, sai dai abin ya faskara.


***
KANO


Wata wawuyar dariya Hajiya Zeenat ke yi tana ƙara rungume wayarta a kunne, ƙafafunta kamar za su rabu da cinyarta tsabar girgizasu da take. Kallo ɗaya za ka yiwa yanayinta ka fahimci ko ma wane kalar labari ake ba ta ba ƙaramin daɗi ya yi mata ba.


"Kai Dikko! A ganka nan a bar ka inda kake! Da ace za ka san daɗin da wannan labari ya min za ka sha mamaki. Kai ma kwallon shege ne!"


Can kuma ta ƙara nutsuwa ta ce.


"Kana ji na? Kar ka sake ka yi wasa! Kar ka ɗaga ƙafa, wani ganin ba ta sonka ko ta tsaneka wannan duk a banza ce muddin ta faɗo hannunka. Ka dai ƙara ƙaimi wajen sakarwa makwaɗaitan iyayennata aljihu, na tabbatar maka ƙarfin dukiya ya fi komai tasiri a duniyarnan. Don ubanta dole ma ta sarara ta aureka. Ni kuma na maka alƙawarin wata kyauta mai tsoka muddin ka mallaketa matsayin matarka."


Jin haka daga can ɗaya ɓangaren, Chairman ya shiga zuba godiya da kirari, wannan ya ƙara fasa kan Hajiya Zeenatu, har wani lumshe ido take tana murmushi, koda ta ji motsin saukowar mutum daga bene ta yi sallama ta ajiye kan wayar. Duban mijinta ta shiga yi tana murmushi sosai, ranta na wani irin sanyi kamar ƙanƙara. Shi kuwa bai san ma tana yi ba, kacokan hankalinsa yana kan wayar da yake amsawa na Hisham game da kasuwanci na haɗin gwuiwa da suke son yi.


Har ya sauko ya ƙaraso bai kammala ba, ganin irin kallon da ga ke jifansa da shi yasa shi fadin.


"I will call you back." Daga nan ya katse wayar.


"Lafiya?"


Abinda ya ce kenan. Ta yi farr da ido, ya kauda kai.


"Ba komai, kawai dai kyau ka yimin Yallaɓaina."


Ɗan murmushi ya yi bai ce uffan ba.


"Amm, dama ina son zuwa asibiti."


Ya dubeta.


"Meke faruwa?"


Cike da ƴar damuwa ta ce.


"Kwanakinnan komai na ci sai na ji kamar zan yi amai, ga yawan kasala."


Kirjinsa ya bada dam! Haka kawai zaton da ya yi sai bai mishi wani dadi sosai ba. Ya daure ya gyada kai da murmushin da ya fi kama da yaƙe.


"Ya kamata ki je, ba'a wasa da lafiya."


Ta ƙara rausaya ƙwayar idanunta.


"An gama Baby, da safe za shirya na je. Fatana Allah Yasa mu ji alheri."


Ta ƙarashe tana shafa cikinta, ya yi murmushi kawai ya maida hankali kan wayarsa. Hotom Fatima ya buɗe yana kallo, gani yake idan har Hajiya Zeenatu za ta haifamasa irinta, toh yana marhaba. Kaunar yarinyar ya ke ji sosai. Abu daya ya tuno da ya ji ba dadi, wato dai rabon da ya ga Ramlat ma a online tun ranar da ta turo mishi hoto.


"Wannan kuma wacece?"


Tambayar Hajiya Zeenatu da ya yi saurin maidoshi tunaninsa. Ya sauka daga whatsapp din ya rufe wayarsa, cikin faɗuwar gaba ya ƙirkiro ƙarya ya shirgamata.


"Ƴar sister din Hisham ce. Ta miki kyau ko?"


Nan da nan annashuwar saman fuskar Hajiya Zeenatu ya dawo, ta sauke ajiyar zuciya tana murmushi.


"Sosai yarinyar ta yi kyau. Zamu haifi fiye da hakan ma."


Ya gyaɗa kai kawai.


***
"Wai wa ya faɗamaki ina sonsa? Ni wallahi ban taɓa sauraronsa ba."


Ramlat ke faɗi a gundure, gaba ɗaya zancen Chairman ya isheta. Ta kuma lura mitar Rafee'ah ba mai ƙarewa ba ce.


"Ai shikenan, idan dai kina son a tabbatar da hakan sai ki daure ki fiddo miji. Ko kuma shawara, ki samu Baba Dakta kawai ki faɗamasa."


Cewar Rafee'ah.


Ramlat ta yi shiru, da sun san damuwar da take ciki na son maso wani da basu takuramata da zancen Chairman ba.


"An faɗamaki Baba Daktan shima zai saurareta ne idan ba wani ta kawo ta ce shi za ta aura ba? Malama ki yiwa kanki faɗa tun wuri wallahi idan ba haka ba za'a ji kunya. Baban Twins yana da labarin Chairman Dikko, ba abinda ban sani ba na tarihinsa."


Wannan karon ma shiru ta yi, Ramlat ta yi dana sanin dawowarta gidan da wuri, da ace ta san da zuwansu ba abinda zai kawo ta. Ta dawo ta iske Hisham ya gaji da zolayar ya aikomata motarta. Yinin ranar da tunanin Hussein ta cinyeshi, don dakyar ta dinga fuskantar aikin da ke gabanta, yanzun kuma ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login