Showing 174001 words to 177000 words out of 231786 words

Chapter 59 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

yi albarka sosai, sai da suka shekara kafin ta samu cikin ƴan biyu. Ta sha wuya sosai kafin ta haifesu. Sai da ƴan biyu suka shekara goma cif a duniya, Malam ya rasu bayan fama da rashin lafiya. Sosai ya gargadi Aminu kamar koyaushe akan ya je ya nuna iyalinsa a gida. Wanna tasa ana yin arba'in na Malam, shima hankalinsa ya yi gidan.


Shi ne zuwan da ya yi a yanzun, Dada ta ci kuka ta kuma yi korafin nisanta kansa da ya yi da ita har ba ya tunanin halin da ta shiga. Hakuri sosai ya ba ta, ɗan uwa rabin jiki, nan da nan kuma ta mance da komai. Ya nemi labarin abubuwan da suka faru bayansa, anan yake jin labarin mutuwar Inna bayan ta yi fama da jinya. Addu'a kawai ya yi mata tsoron Allah na ƙara shigarsa. Nan yake jin auren da Modibbo ya yi da kuma zaman da ya koma yi a Kano inda yake kasuwanci, sai Adda Salma da mijinta ya koma Gombe. Sauran yan uwa kuwa suna nan a Yola, Karime ma ta yi aure hakanan Adamu. A yaran Amarya Hajjo ma, autanta ne kaɗai bai kai ga yin aure ba sannan.


Washegari suka dunguma zuwa dangin mahaifinsu.


Sun samu tarba ta ban mamaki a wurin yan uwan mahaifinsu wannan ya kara tabbatar musu cewa dama can shakkar Inna ce ta sanya ake baya-baya da su, ko dai kuma don yanzun Dada na auren mai kudi ne shima kuma Aminu ya samu rufin asiri daidai gwargwado ne don har gidajen gona da dabbobi yana da su? Oho, ba su da masaniya.


Aminu bai yi ƙasa a gwuiwa ba sai da ya je gida yayyunsa mata duka idan ka cire Adda Salma da ke Gombe. Ya yi mamakin ganin yanda har sannan babu ɗigon kaunarsu a cikin idanuwansu, asalima sai da suka goranta masa na auren Bare a cikinsu don dukkansu auren gida akai musu.


"Kai da Amina kun fita zakkah! Gwara ita, ta auri Fulani kai kuwa bayinmu ka je ka kwaso mana. Har abada ba zamu taɓa daukarki daya a cikinmu ba. Tsana yanzu aka fara."


Wannan shi ne munanan kalaman da Gwaggo Hansatu ta watsawa Zahra da har ya sanyata hawaye.
Karime ce dai ta rasa inda za ta sanyasu don farin ciki. Ta rungume HASSAN DA HUSSEIN cike da murna da jin dadi har da kukanta.


Haka aka rabu cikin aminci, suka dunguma zuwa Mubi. Nana ba laifi an musu tarba.


Aminu bai ƙasa a gwuiwa ba sai da ya shirya zuwa Kano sada zumunci da Modibbo. Ya tarar da matansa biyu, Hajja Fatuma da Amarya. Tun shigowarsu ya dinga watsamusu banzan kallo yana gyara zaman malun-malun. Ba haka ya so ganin Aminu ba, so ya yi rayuwarsa ta lalace yanda rigar jikinsa ma zai gagareshi. Ya mishi tsanar da ko a inuwa ba ya son ganinsa sai rana. Da harshen fulatanci Aminu ya gaida shi.


"Gaisuwar ta mece ce? Ni waye a wurinka? Shekaru nawa ka tafi yawan maula, sai yanzun ne za ka je ka dawomana da SADAKAR YALLAH?"


Cikin dakiya Aminu ya amsa.


"Ba sadakar Yalla ba ce, sunanta Zahra. Matata ce."


Harara Aminu ya watsamata, ƴan biyu suka ƙara nanewa a jikinta suna bin wanda aka kira Yayan Babansu da kallon tsoro da tsana.
"Bare ce! Yanda uwarka ta shigo gidanmu tana matsayin bare, kaima haka ka je ka kwasomana abin fadi da gori! Har abada wannan matar ba za ta zauna cikin zuri'armu ba. Sai yanzun ka tuna da mu ka kwaso jiki ka taho zumunci ko? Toh ni Muhammadu, ban sanka ba! Bani da wata alaƙa da kai, ƙafarka na ƙara gani a gidana Allah Ya isa. Duk abinda na yi maka kuma kai ka ja wa kanka. Ku kuma kuma kallona kamar Mayu!"


Ya maida akalar zancen kan Hassan da Hussein da suke kallonsa, duk da karancin shekarunsu, haka bai sa sun gaza fahimtar wasu abubuwan da yake faɗi ba don Hausa sak ya yi ko don ya baƙantawa Zahra.


Da wannan cin kashin da rashin mutuncin na Modibbo, Aminu ya tattara iyalinsa suka juya ko kwana ba su yi ba. A mota ya yi ta rarrashin Zahra da ban hakuri. Ita kuwa murmushin yaƙe ta yi kawai ta nuna ba komai tunda dai bai ɓoyemata alaƙarsu da su ba tun farko. Labarin komai na irin riƙon da ya samu a hannun uwarsu ta sani.


Watansu daya suka yi shirin komawa, nan fa Dada ta rikice da kuka da rantsuwar ba ta yarda ba, a karshe ta dage ma sai dai a bar mata ƴan biyu ta riƙe, dabararta na yin hakan, don kawai su dawo da wuri a dinga ganinsu. Aminu ya rasa ya zai yi da yar uwarsa, ga mamakinsa Zahra da kanta ta riƙe hannun Hassan da Hussein ta damƙawa Dada tana murmushi.


"Yarana mallakinki ne Dada. Gasunan na bar miki su duniya da lahira."


Wannan abu har gobe Dada ba za ta mance shi ba, kuka sai ya koma dariya. Har tasha suka yi musu rakiya suka dawo. Abin mamaki Hassan da Hussein ko a jikinsu don sosai sun saba da Dada da iyalinta a ɗan zaman da suka yi tare.


***
Mummunan labarin hatsarin mota da rasuwar Aminu da Zahra ya riskesu. Wannan ya yi sanadin fitar cikin Dada, ta sume.











I just published "BABI NA HAMSIN DA BIYU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1010093134?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=azuNeDf8BzRGeUbQ5hUohOGx2aTzO5EgG0sslypZUWd87KXOqPMoNqGJcWUIJ7lkGQPCJLaZwnIqw7s7g8N0NU%2BMfRV98U0i0%2BriYhHA5YJps5E19e%2B0H%2FQy%2Br8BBzme








🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.


52)






Sosai mutuwar ta girgizasu, anan suka ƙara jinjina kudurar Ubangiji. Wato dai da yanzun har yan biyun za'a rasa shikenan babu tarihin Aminu da Zahra a doron ƙasa.


Allah Ya taimaka, Aminu ya bada kwatancen inda suke zaune a Maiduguri, da haka suka karasa bayan an sallaci gawar Aminu da Zahra an binnesu a nan cikin Yola.


Yakura ta ji mutuwarnan ba kaɗan ba, dama tana cikin takabar Malam. Hakanan iyayen Zahra su kansu mutuwar ta dake su. Sai da aka yi arba'in aka raba gadon ƴan biyu. Ba wanda ya hana Dada tahowa da Hassan da Hussein.


***
RAYUWAR ƳAN BIYUN


Rayuwa mai dadi suke yi a wurin Dada da mijinta, basu san matsalar rashin uwa ko uba ba. Kaunar da Dada ke yi musu har kusan matsala ta so ba ta da Naziru don gani yake kamar ba ta kula da yaransa irin yanda take rike da yan biyu. Wannan ne dalilinta na ɓoye son a zuciyarta. Makaranta mai kyau na masu gata suke zuwa don dama sun soma firamare, ci gaba kawai suka yi.


Tafiya ta ci gaba da tafiya har ƴan biyu suka kammala firamare suka soma kokarin tafiya Sakandire. A sannan ne Dada ta danne zuciyarta ta shirya da yaranta kaf suka halarci bikin ƴar Modibbo a Kano. Yaran babu mai murna haka Dada ta yi ta lallaɓasu gami da nunamusu muhimmanci da ladan dake cikin sada zumunta.


Koda zuwansu suka sauka a gidan wani abokin Baba Naziru don yaran sun rantse baza su je kwana gidan Modibbo ba har da kukansu, anan ne Dada ta goyi bayansu, ita kadai ce ta karasa gidan dan uwannata ta sauka dakin Amarya don duk ta fi mutan gidan kirki da dadin mu'amala. Ita ke yawan ba Dada hakuri akan yanda rayuwa ke tafiya. Hajja Fatuma ta yi bakin ciki da saukar Dada dakin Amarya ganin ita ce ke aurar da ɗiyarta.


Ranar wuni direba ya kawo yaran Dada kaf. Basu samu matsala sosai ba don hidimar biki ta sanya ma ba wanda ya hadu da Modibbo sai dai a wurin yaran su Adda Salma da sauran yan uwa, sun sha hantara.


Sai da aka kammala bikin sannan Dada a karo na biyu ta kwashi yaran suka shiga bangaren Modibbo don su gaidashi su yi mishi sallama, wancan karon ya ganta sarai amma ko amsa gaisuwarta bai ba.


Modibbo zaune shi kadai a falonsa, ta samu damar shiga dalilin ranar girkin Amarya ne. Yana ganinsu ya daure fuska tamkar bai taɓa dariya ba.


"Ke har yanzu ba ki tafi ba?"


Dariya ta ɗan yi.


"Eh, amma gobe zan wuce. An yi biki, Allah Ya..."


"Dakata, ke har wani bakin alheri ne da ke? Ai ni kaf zuri'ata ba za ta ga rashin alheri ba. Tashi ki ficemin daga gida! Zaman ya isa hakanan, biki ya ƙare tunda kin zo gayyar soɗi ai sai ki tattara ku koma."


"Dada tashi mu tafi! Ba zamu kara dawowa ba! Na tsaneshi!"


Da sauri Dada ta kalli Hussein ta rufemasa baki, shi kuwa Modibbo ya mike ya zo ya fisgoshi.


"Kai! Dan iskan yaro, ni sa'anka ne? Haka aka koyamaka ka zageni?"


Ya bubbuge bakinsa kafin ya murɗe kunnensa, Hussein sai huci kawai amma kukan ma ya ƙi yi. Dada na hawaye yaran na tayata ta mike ta ja hannunsu ta fito ba ta kara magana ba.


Sosai ta gargadi yaran akan kar wanda ya fadawa Baba Naziru abinda ya faru, suna cike da ɓacin rai da jin haushin Modibbo wannan ta sa ba su amsamata ba. Ba ma kamar Hussein da ya ji duniya ya tsani mutumin.


***
Tafiya na ci gaba da tafiya, yan biyu suka kammala Sakandire, a sannan sun zama matasa, Hassan na sanya farin gilashi a sannan a dalilin matsalar ido da yake fama da shi. Wannan ne ya taimaka wurin bambance su.


Baba Naziru bai yi ƙasa a gwuiwa ba wurin nema wa kowannensu gurbin karatu a fannin da yake so, AlHassan ya samu fannin Accounting a jami'ar Oxford, London. Yayinda Hussein ya tafi AUD a Dubai.


***
Tsakaninsu da Nijeriya sai an musu hutu. A wani zuwan ƙarshe da Hussein yi hutu, don wani lokacin hutunsu kan bambanta da na Hassan. Hutu wanda daga shi kuma sai kammala karatunsu. Bisa tursasawar Dada ya ziyarci ƴan uwan Babansu. Sosai ya samu tarba a hannun Adamu da Karime kamar koyaushe, zuwa Kanon da Dada ta ƙaƙaba ya fi komai dagula lissafinsa.


"Nikam ba zan je ba." Cewar Hussein ransa a tsananin ɓace. Daƙuwa Dada ta mishi gami da harara, ya kauda kai.


"Duk rashin ƙaunar da zai nunamaka ai hannunka bai taɓa ruɓewa ka yanke ka yar ba. Mu mun san muhimmancin zumunci don haka dole ne ka je idan har na isa da kai."


Ganin yanda ta dage har da ɓata rai yasa shi lallaɓa ta ya kuma shirya tsaf ya bi motar kasuwa ya tafi har da tsaraba Dada ta shirya ya kai.


Tun a ƙofar gidan Kawun ya soma cin karo da samarin gidan, haɗe girar sama da ƙasa ya yi kamar bai taɓa dariya ba ya ƙarasa. Ciki-ciki ya yi musu sallama sai dai ba wanda ya yi yunkurin amsawa, wannan ya fi komai ƙular da shi. Wato don ubansu har sannan ba su ɗauke su wata tsiya ba. Ya yi kwafa ya karasa ciki. Ba laifi ya samu tarba daga Amarya sosai, ganin haka ya ƙi shiga ɓangaren Hajja Fatuma ya shantake har dai ta sanarmishi da shigowar Kawun daga kasuwa. Tsam ya miƙe ya nufi sashinsa. Yana zaune saman kujera ya shiga da sallama. Dubansa ya yi yana mai amsawa sai dai ganin ko waye ya karasa amsawar ciki-ciki. Hussein ya taɓe baki don dama ya shirya ganin fiye da hakan.


"Barka da yamma." Ya gaida shi a ladabce.


"Kai, me ya kawo ka gidana?"


Kallonsa ya yi kyam.


"Zumunci."


Kawu ya ji wutar tsanar Hussein ta ƙara ruruwa a ƙoƙon ransa, shekaru kusan bakwai rabon da ya tako gidansa, Alhassan kan shigo koda ba ya so.


"Na lura ba ka da kunya! To ko Aminu ubanka bai isa ba balle kai! Ni na fi ƙarfin tsagerancinku! Illar auren bare kenan...


"Ubana Aminu ya rasu, gidan da ya je ba wani da zai dawwama a duniya bai je ba. Gidan biyu ne, wuta da aljan. Don Allah Kawu ka yimin dukkan zagi, banda ambatar iyayena."


Miƙewa Kawu ya yi ma matukar fusata. Jikinsa har rawa ya ke yana kumfar baki.


"Ni ka ke faɗawa baƙar magana?! Ni? Na maka kama da sa'an Uwarka?!"


Hussein caraf ya mike a fusace, bai san sadda ya soma ɗaga murya a magana ba.


"Kawu! Tsanar ta isa haka! Haba! Wadannan mutanen da ka ke zagi babu ranar da ba sa yi mana nasiha akan mu bi ku mu yi biyayya! Mene laifinsu ma zuwa a bare?! Waye bare? Ina ku ka samo wannan al'adar marar tushe?! Wallahi wallahi! Ina girmamaka ne domin Dada, darajar su ka ke ci nake ragamaka a dukkan wulakanci da cin kashin da ka ke yi! Amma... (Ya nuna shi da yatsa) Daga yau na zubar da girman a idona na take shi! (Ya yi amfani da ƙafarsa wurin murje ƙafet ɗin ɗakin) Daga kai har zuri'arka duk wanda ya ƙara gangancin cin zarafin iyayenmu sai na nunamaku cikakken ɗan halak ne Hussein! Mu zuba da ku!"


Yana kaiwa nan ya juya yayinda kalaman Kawu ke shiga kunnuwansa.


"Ni ka ke gayawa magana haka? Lallai zan nunamaka ƙarshenka!!"


Wannan kalaman tsaf sun shiga kunnensa sai dai ko kaɗan bai ji ko ɗar ba, bai tsaya sallama da kowa ba ya kama hanyar fita. A zaure suka hadu da daya cikin samarin gidan ɗa ga Hajja Fatuma, Bashir. Fiito ya soma yi yana waƙe wanda hakan ya ƙular da Hussein ya kuwa haɗa kansa da bango ya bishi da lafiyayyen mari.


"Ubanka ma ya yi kaɗan balle kai!"


Daga haka ya fice ya bar shi da ihu da kururuwa.


Ranar dai gidan abokin Baba Naziru ya kwana washegari da sassafe ya juya gida Adamawa. Kwanansu uku, ya yi mamakin yanda Kawu bai kira Dada ya sanarmata ba, shima ya haɗiye bai faɗa ba. Har hutunsa ya ƙare bai ji wani bayani ba don haka da dariyar mugunta ya bar ƙasar. Ya dai gane a baya ma Kawunnasu wuri ya samu!


***
Daga AlHassan har Hussein, kowanne ya na iyakar kokari wajen yin karatu yanda ya dace. Basu da wani buri face su fito first class ko don su farantawa uwa da uban da suka rikesu tamkar su suka haifesu rai.


Hussein saurayi ne mai daure fuska da tsauri a wasu lokutan, zai yi wuya ka ga dariyar Hussein. Ya killace kansa ya kasa yin abokai sai abokinsa daya haifaffen garin Saudiyya kuma mazaunin can, Rasheed. Sun shaƙu sosai da Rasheed wanda ya kasance ruwa biyu. Mahaifiyarsa irin Takarunnan ne dake zuwa daga ƙasashe daban-daban, sai dai ita din ƴar Katsina ce a Nijeriya. Mahaifinsa kuwa haifaffen garin Makkah ne a Saudiyya. Zama ne ya haɗasu har aka kai ga yin aure, Allah Yasa Rasheed ta hanyar aure suka haifeshi.


Wasu ƴanmata basu a gaban Hussein, akwai da yawa da suka yi suka gaji bai ko kallesu ba. Don ya wulakanta duk macen da ta tunkareshi ba kunya ta nuna tana sonsa, ba komai ne a wurinsa ba lokacin. Hakan yasa wasu da yawa suke komawa tsanarsa shi kuwa ya dau hakan wai harara a duhu don bai ɗaukesu da wata ƙima ba.


Ɓangaren karatu, kusan yana daga cikin ƙwarin ajinsu wadanda za'a iya kira da gifted. Allah Ya ba shi fasaha da saurin daukar karatu hakanan Rasheed.


Da taimakon Allah lokacin yayesu daga makaranta ya yi. Murna a wurinsu ba'a magana idan ka cire Rasheed da Hussein wadanda basu kaunar rabuwarsu. Sun tabbata sai ziyara ce za ta ƙara haɗa fuskokinsu, kafin ma a ziyarci junan zai iya daukar lokaci.


***
Hajiya Zeenatu Bashir wacce ta kasance marainiya, ta tashi a hannun kakarta mai son abin duniya. Sanadin hakan ne ta hadata da wata Agent mai safarar yara zuwa Saudiyya aikatau da Bara. Ta yi wannan aikin na shekaru goma kafin a karshe kanta ya waye ta samu ta tara kudi sosai ta dawo gida Nijeriya. Haifaffiyar garin Katsina ce, sai dai kasuwancinta da kuma rasuwar Kakarta a shekarun baya, ya maidota Kano da zama. Ta zama mace mai zaman kanta, sun haɗu da Ƙawarta Hajiya Batool wacce itama ta ke kasuwanci, a jirgi sadda za ta dawo daga Saudiyya. Nan suka ƙulla aminta sosai, don haka koda ta dawo Kano sai suka hada jari suka ci gaba da harkallar kasuwanci. Tana da zaurawa da dama waɗanda ta k rage dare da su,wannan a wajenta bakomai ba ne, a irin wannan harkar ne ta san da zaman Aliyu Dikko wanda a baya sun zuba lokacinsu tare duk kuwa da tazarar shekaru biyu da ta ba shi.


Haduwarta da wani ƙusa a gwamnati yasa jarinta daɗa faɗaɗuwa, ta soma fita sarin kaya Dubai tana kawowa katon shagon da ta buɗe a nan Sabon gari, kuma takan taɓa siyasa musamman wurin kamfen.


A wani zuwan karshe da ta yi ne a wani shagon kayan kwalam ta haɗu da wata ƙawarta da suka hadu a aikin Hajji, Hajiya Basira ƴar asalin garin Katsina da aure ya kai ta Saudiyya.
Da mamaki ta kira sunanta, Hajiya Basira na ganinta suka cafke suna dariya. Kowannensu bakinsa cike da hira, karshe dai tare suka fito zuwa masaukin Hajiya Basirar. Anan ne ta ke jin cewa ɗanta Rasheed ne ya kammala karatu ta zo bikin yayeshi.


"Ke dai Hajiya Zeenatu kin ƙi yin aure kin zauna kina cin karenki ba babbaka, nima fa nayi irin rayuwarnan a baya kafin Allah Ya tseratar da ni, kin fi kowa sanin yanda rayuwa irin haka ke ƙarewa."


Wani fari da murmushi Hajiya Zeenatu ta yi.


"Me kike ci na baka zuba ne? Tunda na tara abinda na tara dagaske yanzun nima aure zan yi. Kwantar da hankalinki."


Suka yi dariya gami da cafkewa.


"Yauwa, yanzu naji batu."


Da wannan suka shiga hirarsu kafin a karshe Hajiya Zeenatu ta yi mata sallama da alƙawarin goben za ta zo su je taron yaye ɗanta a makaranta.


***
Washegari kuwa ta cika alƙawari, a gidan Rasheed da Hussein suka kwana sai dai da sassafe suka koma cikin makaranta.


Hajiya Zeenatu suka ɗunguma zuwa makarantar. Wuri ya cika ya batse, dalibai sun sha kyau sun gaji. Baba Naziru ne kaɗai ya zo wa Hussein, hakan ma ya mishi dadi sosai.


"Yauwa ga ɗannaki." Muryar Hajiya Basira ya katse Hajiya Zeenatu daga kan wayarta, tunda ta ɗora idanu akan wani matashi da bai fi shekaru ashirin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login