Showing 198001 words to 201000 words out of 231786 words
Chapter 67 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
uwa aka baibayesu mai hoto ya shiga aikin dauka. Kirjin Hussein banda bugu da sauri babu abinda ya ke yi, ji yake kamar ya ja ta ya sanya a babbar riga ya gudu da ita. Sai da aka kammala hotunan har da mutan Adamawa sannan Ango da tawagarsa suka fice.
Murja da Fareeda dai fasa yinin aka yi aka dunguma aka tafi yayinda Bilkisu ta daure suka zauna. Amma Salma rantsuwa take yi da ƙarawa cewa asiri ne kawai aka yiwa Hussein domin kuwa wutsiyar raƙumi ta yi nesa da ƙasa, ko makaho ya shafa Hussein ya san ya wuce aurar Ramlat duk da dai itama ba baya ba.
***
Sai wuraren bakwai na dare sannan jama'a suka soma tafiya, wadanda suka rage da zasu je Adamawa ba su da yawa. Ramlat ta yi ɗai-ɗai saman gado tana hutawa duk ta gaji don yau ba karamin zirga-zirga ta sha ba a cikin gidan kawai. Kowa ya zo sai an kirata an ɗauki hoto, wannan zamani na hoto har haushi ya ke ba ta.
"Ke kinga mutuniyarki ko? Ta kasa ɓoye abinda ke cikinta? Kai Allah Ya rabamu da hassada mugun ciwo."
Amrah ke zancen ganin duka na dakin babu bare, daga su sai Nusaiba sai Aisha sai kuwa Hunainah dake sallah.
Murmushi Ramlat ta yi.
"Ni mamaki ma abin ya dinga ban, ta madubi fa ina kallon yanda suke hararata amma da mun hada ido sai su basar."
"Ke wa ya taɓa samun daukaka idan bai hadu da yan hassada ba? An fadamaki tsakani da Allah za ta je Adamawarnan? Ni wallahi ban san sadda Bilkisu za ta sauya ba. Gaba daya a farko kamar ba za ta yi ba." Fadin Rafee'ah wacce ke shan wani youghurt da ƴan Yola suka kawo.
"Dama DAN ADAM ance mai wuyar gane hali." Aisha ta furta.
Haka aka yi ta hira, har zuwa sadda Hafsat ta shigo da sauri ta hau kan gadon gami da sanyawa Ramlat waya a kunne. Ta kalleta kafin ta tambayi waye cikin rada-rada ta ce.
"Angonki."
"Assalamu alaikum."
Ta ji muryarsa sadda ta rike wayar sosai a kunnen, amsa sallamar ta yi.
"Shi ne kika kashe wayarki ko? Gaba daya kin sa na rasa nutsuwa."
Ta sauke ajiyar zuciya, ta tuna ashe fa tun a wurin kwalliya ta kashe wayar ba ta ƙara bi ta kai ba.
"Ina neman afuwa."
"Naji, amma yanzu ki fito ina mota. Gaisawa kawai zamu yi."
"Ka..."
Bai bari ta kai aya ba ya katse wayar, dole ta cire ta miƙawa Hafsat da hankalinsu gaba daya ba ya kanta. Ta matsa kusa da Amrah ta mata raɗa. Amrah ta murmusa.
"Kar ki manta dai, yanzu miji ne a wurinki ba manemin aure ba. Umarninsa za ki bi kawai. Ki je ba komai"
Ta mike ta gyara zaman dankwalinta ta yafa gyale sannan ta fice. Tana jin yanda matan dakin suka dauki sowa murmushi kawai ta yi ba ta ko juya ba.
A farfajiyar gidan ta ga mota sabuwa dal sai sheƙi ta ke, ba ta yi zaton shi ne a ciki ba sai da ta zo giftawa ta ji ya mata hon, hakan ya ba ta damar bude kofar don ba'a ganin na ciki. Shi din ne zaune kuwa, ta shiga ta rufe sakamakon AC da ke a kunne. Kamshin motar da kamshinsa sun hadu da sanyi sun saukarmata da ni'ima a zuciya. Ta dubeshi, ya cire babbar riga hakanan hular na ajiye saman gaban motar.
"Ina wuni."
"Lafiya."
Ya furta tamkar ba ya so. Can ya ce.
"Ya gajiyar biki? Anya kin ci abinci? Sai naga kamar kin faɗa."
Ita mamaki ma ya ba ta don haka ta kasa amsawa.
"Kin yi shiru."
"Uhm, na ci."
"Kin fa zama matata, amma na lura da ke tun dazu kamar murmushin dole ki ke yi."
Yanda ya yi maganar kamar zai yi kuka yasa ta dubansa, gaba daya ya juyo ya matsa dab da ita, ta ji nauyinsa, shi kuwa hakan yake so dama, tun shigowarta ya ke kokarin su hada ido amma hakan ya gagara. Za ta juya kai ya yi saurin riƙo haɓarta ya karkato da kan. Ta dora hannunta a saman nasa da zummar kautarwa. Sai dai ya rike hannun tamau.
"Please ka sakarmin hannu."
Ta ci gaba da kokarin kwacewa don ba ta shiryawa hakan ba. A hankali ya saki hannun.
"Na saki. Shikenan?"
Ba ta ce uffan ba.
"Ki je kawai, sai mun yi waya ko?"
Ta saci kallonsa, kamar dai fushi ya yi. To ita kuwa me za ta ce? Ina sabon da za ta sake don ya rikemata hannu?
"Kin tsareni da ido, ba na kyaleki ba?"
Yanda ya yi furucin sai ma ya ba ta dariya, ta kauda kai tana murmushi.
"Ni kike wa dariya?"
"Aa."
"Kin ma iya ki ci abinci, ni da ban ji ki ba kasa daurewa nayi da komai har sai yanzu da na zo na ganki. Idan na tsaya wassafa kalar farin cikin da nake ciki, zamu kwana mu wuni a nan."
A hankali ya jawo hannunta mafi kusa da shi ya damƙe cikinnasa. Wani yarr ta ji kamar yanda shi kansa sai da ya ji wani shock. Ya ƙurawa lallen idanu.
"Allah Ya bani ikon riƙe ki amana Ramlat. Ya ba ni ikon yi maki adalci a zamantakewarmu. Na san na ɓatamaki rai da yawa, amma ki yi hakuri. Haka nake, ban yarda da soyayya kafin aure ba, bayan aure ke kanki yanzu son zai fi maki armashi a kowace tafiya. Abubuwa da yawa ba ma sai na fada ba tunda ke ba yarinya ba ce ko?"
Ta saci kallonsa don gaba daya sautinsa ya sauya, gira ya ɗaga mata yana jifanta da tattausan murmushi. Ta kauda kai ta shiga kokarin zame hannunta.
"Na dauka zaman hakuri da biyayya kawai zamu yi ai tunda cikinmu ba wani mai kaunar ɗan uwansa."
Ba zato ya fisgota kafadarsu na gogar juna kamar yanda fuskokinsu tuni ya hadu wuri guda sai hucin numfashinsu da ke gaurayewa.
"Kina da tabbacin bana sonki? If yes, prove it."
Ta lumshe idanu tana shaƙar kamshin lemon mint da bakinsa ke yi. A hankali kuma ta yi nufin yin baya ya rike kanta kafin ba zato ta ji bakinsa a nata. Shirun kusan mintuna biyu kafin ta tureshi ya yi baya, babu kwari a jikinsa, don haka ya jinginar da kai yana kallonta da soyayyun idanunsa. Ita kuwa sai afkin goge baki da ta ke yi bayan ta zari tissue dake saman gaban motar. Ya kauda kai kadan yana dariyarnan irin na wanda aka rainawa wayau.
"Kai, ni kike gogewa baki don na taɓashi?"
Ta daure fuska ta harareshi.
"Saboda ban shiryawa hakan ba. Ai ba haka tsarin zamantakewar tamu ya ke ba."
Daga nan ta wurga tissue din a jikin motar duk dacewar hatta da kujerun baa ciremusu ledojinsu ba. Tana kokarin bude kofar ta fita ya kara yi mata wata wawuyar fisga, duk kokarinta ta kwace abin ya gagara. Haka ya taramata miyansa a baki kamar yanda bai kauda bakin ba sai da ya ji ƙarar tafiyarsa, loko da saƙo sai da ya tabbatar ya gauraye a bakin kafin ya saketa. Iyakar shaƙa ta shaƙa, ta bankamasa wata hararar. Ya ɗaga mata yatsu.
"Good night Love."
Ta bude kofar kawai ta fice, ya bita da kallo yana jin kamar kar ta tafi saboda wani tsananin kewa da ya kamashi nan take, har sai da ta shige gidan kafin ya lumshe ido da murmushi can kuma ya buga sitayari.
"Ya Rabb!" Ya fadi cike da nishadi, soyayyar Ramlat na kara ƙaimi a ransa. Dakyar ya samu kuzarin jan motarsa, kafin ya fice daga gidan ma sai da ya kira wayar Hafsat ya jaddada mata akan ta shaidawa Ramlat ta kunna wayarta.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://www.wattpad.com/story/229538078?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_reading&wp_page=reading_part_end&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=3RG5g2a5w6izCuKU8HhNqobuQjDF3XsdSGdqdVtdShDrSoD84AKgTAv38ifr8A0P6JNqIoYXqVCm072j3Kj010bX%2FXCFmaovF0BtpPRfTxUwRF7KoTA35HGU0Qpfh9Zn
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
59)
Kusan gaba daya mutan dakin bacci suke yi idan ka cire Amrah da ke zaune tare da amniyarta tana tayata wajen shirya kaya a ƙatuwar akwati. Wasu kayayyakin kuwa su na fitarwa domin bayarwa. Amrah na lura da yanda gaba daya ba ta da sukuni, jefi-jefi takan sa hannu ta share bakinta.
"Wai ke kam lafiyarki kuwa?"
Ta dawo hayyacinta.
"Me kika gani?"
Harara ta watsamata.
"Kamar ya me na gani? Alhalin ina lura da yanda tun dazu kike wani shagala da shafa baki, saurin me kike?"
Ranta ya kara baci ta ja tsaki.
"Me kike nufi? Idan ma wani abin kike nufi gwara ki watsar tun a nan don kinsan irin zaman da na shirya za yi da Hussein."
Amrah ta jinjina kai.
"Ko wane irin zama ne ba zan hanaki ba tunda ke ba yarinya karama ba ce da zan tsaya ɓata bakina, abu daya da zan tunasar da ke, yanzu Hussein ya tashi a kowane matsayi ya hau matsayin mijinki. Idan kin gyara kanki, idan kin ɓata ma ke za ta shafa."
Shiru kawai Ramlat ta yi ba ta kara tankawa ba. Can kuma aka kwankwasa kofar dakin da sallama aka shigo. Hafsat ce sanye da riga da wando na bacci kasancewar ita ta kafe ta ƙi bin yan uwansu Hotel, hakan yasa Hajiya ta mata wuri a makeken gadonta. Hamma ta ke zabgawa duk suka dubeta.
"Adda wannan Yayannamu ya hana ni bacci wallahi, don Allah ki tausayamin ki kunna wayarki ku yi magana. Ni ga wayata ma na bar maki a nan don wallahi da zarar na soma nisa a baccin yake tashi na."
Dariya ta ba su, aikuwa ba wanda ya kai ga cewa komai sai ga wani kiran. Da sauri Hafsat ta miƙamata.
"Yauwa gashinan. Sai da safe."
Ta fice Amrah na addu'ar Allah Ya tashemu lafiya. Ita kuwa Ramlat wayar ta ɗaga ta ɗora bisa kunne yayinda Amrah ta juyamata baya ta ci gaba da aikin da tuni ma sun ƙarƙare sai tattarawa. Sallama ta yi, jin muryarta sai ya sauke ajiyar zuciya. Shiru ya dan biyo baya kafin ya tanka.
"Kin hana ni bacci Heart."
Ta ɗan saci kallon Amrah wacce hankalinta na can wurin harhaɗe kaya ba ta ce masa komai ba.
"Meyasa ba ki kunna wayarki ba? Kinsan zan nemeki, zan so na ji muryarki. Bacci ya kauracemin, ba ni da burin da ya wuce na ganki a gidana. Heart, kin yi shiru."
Ta ɗan daure ta yi magana.
"Me zan ce?"
"Ko mene ne ki fada daidai ne. Amma kar ki kara kuskuren da ki ka yi dazu, idan kuwa hakan za ki ci gaba a zamantakewarmu, za ki sha wahala a wurina."
Murmushi ta yi mai sauti.
"Dariya ma na ba ki?"
"Ko kusa, bacci fa nake ji."
"Ni kuma ban shiryamasa ba, hira na ke son mu yi. Koda dai tambayar da nake son yi maki ba ta waya ba ce, sai mun haɗu ga ni ga ki."
Nan ma ba amsa sai shirun daga wajenta, har Amrah ta mike ta fada bandaki ta dauro alwala, yana ta magana Ramlat sai uhm ko uhm uhm. Tana kallo Amrah ta kashe fitilar dakin ta bi lafiyar gado kusa da Babynta ta kwanta. Cikin takaici Ramlat ta ce.
"Malam kowa fa ya kwanta, nima gyangyaɗi nake, ina son..."
"Be serious Heart, ko kadan ba ki tunanina?"
Ta lumshe ido ba tare da ta tanka ba.
"Talk."
Ya fadi a hankali. Ita har mamaki ma ya ke ba ta.
"Shiru ma fa magana ce ko? Inji Hausawa."
Ya kara fadi yana yar dariya, ta cije lebba don takaici, wato ma ya riga da ya fassarata.
"Kai ka san wannan, ni abinda ya tsayar da ni daban ne. Sai da safe bacci nake ji."
Ba ta jira komai ba ta kashe wayar gaba daya. Mikewa ta yi tana murmushi har ta na tuntube da ƙafar Dijen Daura da ke bacci a saman katifa. Hakuri ta ba ta sannan ta fada toilet. Alwalar itama ta yi ta nemi wurin kwanciya.
***
Tun da Asuba masu tafiya Adamawa suka tashi ba'a koma ba. Daga mai wanka sai mai sanya kaya, wasu kuwa da ba za su sami zuwan ba, sai suka fada kicin don yin abin kari. Ramlat dake bacci sakamkon tana fashin sallah, dolenta ta wartsake don ba karamin takuramata su Rafee'ah suka yi ba akan ta mike ta yi wanka. Bayan ta fito ta shirya cikin atamfar Holland kalar light blue da fari, ta yafa farin mayafi sannan ta fita wurin yaranta. Ta dauka za ta gansu cikin damuwar tafiyarta sai dai da sauki musamman ga Ummi da Ansar wadanda suka shaku sosai da Hajiya. Affan ne ma ya dan yi wuri-wuri da idanu da ya tabbatar dagasken tafiyar Maminsa za ta yi. Itama dannewa kawai ta ke amma tsananin kewarsu ta ke ji tun kan a je ko'ina. Kiran da Hajiya ta mata ne yasa ta lallaɓa Affan da ya kanainaye a jikinta ta fita. Can ƙuryar daki ta isketa. Ba ita kadai ba ce har da Umman Amrah da ta shigo tun sassafe da kuma su Baba Hajara da sauransu. Nasiha sosai suka yi mata, Hajiya a karshe ta tofa da cewar sun gama magana. Ta yiwa Ramlat addu'a kawai. Ita kuwa banda afkin kuka ba abinda ta ke fitarwa. Iyayenta masu sonta da komai, a baya ta bijirewa saboda son zuciyarta. Nan ta bude baki ta na mai kara neman gafararsu akan abinda ta aikata a baya. Murmushi suka yi.
"Banda abin Ramlatu, ai kowa ya fahimci kaddara. Ba komai kedai komai ya wuce sai da kawai yanzu ki maida hankali wurin biyayya ga mijinki."
Wata Gwaggonta daga Daura ta fadi.
***
ADAMAWA...
Hajiya Zeenatu hakanan ta ji faduwar gaba, shigar da Hussein ya yi da irin fara'arsa sai ta soma wani tunani daban. Ganinsa ta ke yi kamar wani Ango. Ya kammala ɗora agogon hannunsa bayan ya idar da sallah, murmushi ya ke tun sadda suka yi magana da Hafsat ta tabbatarmasa da isowarsu garin su ma. Dama habyar da ya biyo daban da tasu.
"Hussein."
Jin ta kira sunansa kai tsaye yasa shi dubanta.
"Duk wannan fara'ar ta mecece? Wani kyau ka yi kamar wani Ango. Gabana faduwa ya ke yi. Yaushe za mu je ka kaini mu gaisa da danginka?"
Ya yi wani banzan murmushi ya rike kafadunta.
"Kar ki damu, kin ga yau daurin auren yar uwata ake yi, ke kuma na sanki ba kya son cunkuso da wani hayaniya, ki yi hakuri gobe zamu shiga ku gaisa da kowa. Kallon banza aka yi maki Hussein ba zai rabu da mai shi ba. Sannan kina batun wai Ango, na dauka kodayaushe ni Ango nake a wurinki? Toh ki kwantar da hankalinki, babu macen da ta ishe ni kallo har naji ina sonta. Ke kinsan yanda nake."
Yanayin da ya furta kalmar karshen kawai sai ta kara shan jinin jikinta, ga wayarta ta rasa ya aka yi ta fada ruwa balle ta tambayi Kawu Modibbo ko akwai wani labari, yanzun dai ta ƙi tashi Hussein kuma ya karɓe ya ce zai siyomata wata da kansa. Abinda ba ta sani ba, da gayya ya tankwaɓar da ƙaton jug na ruwan dake saman centre table, burinsa dama ta rasa hanyar jin kowane labari.
Bai bar gidan ba sai da ya tabbatar ya kwantar mata da hankali, har cewa ya yi ta dauko mayafi su fita tunda hankalinta bai kwanta ba, soyayyar Hussein da ganin tsantsar gaskiyarsa a yanzu ta rufemata ido ta yanda ba ta tuna komai da kowa, hakan yasa ta kasa hasaso wani abin musamman ma da ta ga ta fito falon Kausar na mishi batun bikin da ake yi. Hankalinta ya kara kwanciya bayan fitar Hussein din da Kausar ta shiga budomata hotunan auren da ake yi tana kallo tana ƙara jin sanyi a ranta. Ta na kuma kara tabbatarwa zuri'arsu Hussein kyawawa ne tsantsa.
***
Bangaren Marigayi Baba Naziru wanda ya sha gyara da fenti daga AlHassan, nan aka kai Ramlat kafin lokacin da Hussein zai yi gininsa. A sannan yan uwanta suka hau aikin jere da ma sauran abinda duk ya kamata. A ranar daga su sai su, an kawomusu abinci da abubuwan sha.
Da daddare suna zaune ana hira, wayarta ta yi kara, Mr.Wuff. Murmushi ta yi ta dan mike ta bar wurin zuwa can wani dakin da ta tabbatar babu kowa ciki.
"Assalamu alaikum." Ta furta a hankali.
"Waalaikumussalam. Fatan an iso lafiya?"
Ta dan lumshe ido kafin ta bude tana bin dakin da kallo, shima gado ne aka shimfida a dakin, don wannan karon gatan da ta samu har gado biyu aka yi mata.
"Alhamdulillah."
Shiru kamar ba wanda zai tanka can kuma ya ce.
"Kin shiryawa abinda zai biyo bayan aurenmu?"
Ta ji maganar banbarakwai.
"Kamar ya?"
Murmushi ya yi mai sauti.
"Za ki haɗu da Uwargidana mana."
Ranta ya sosu matuka, kishi mai zafi na Zeenatu ya mamaye koina na zuciyarta.
"Ina ruwana da ita? Zamana da nata ba iri guda ba ne. Ko ba komai ita ai auren soyayya aka yi kamar a cinye juna."
"Sai aka fadamaki kema ba zan iya cinyekin ba? Wai meyasa kike son koyaushe ki nunan babu soyayya tsakaninmu? Dama akwai soyayyar da ta girmi aure?"
Ta kasa ba shi amsa don har lokacin kiran Zeenatu da uwargidansa da ya yi yana mata zafi, ta rasa rashin zuciya irinta Hussein da ya iya rayuwa da matar da ta rushe dukkan wani tubalin ginin rayuwarsa saboda son zuciyarta.
"Shiru ki ka yi?" Ya tambaya.
Ta dan turo baki kamar yana ganinta.
"Bani da abin cewa."
"Saboda kin san ba ki da gaskiya ne kawai. Na dai fadamaki, ki shiryawa hakan. Tsoro ba naki ba ne, dama na riga da nasan ke jaruma ce. Amma ban sani ba ko har a fannin kishiya."
"Wanda aka damu da shi ne ake kishinsa, tunda ba na kishinka me zai dameni da matarka? Don haka kar ka samu damuwa, ita dai za ka yiwa wannan kashedin. Zan kwanta sai da safe."
Ta katse kiran ranta a tsananin ɓace. Me Hussein ya gani a tattare da Zeenatu har yake mata son da ba zai iya rabuwa da ita ba wai? Ita ta rasa dalilin da yasa duk laifin da ta yi masa ba ya ganin ko ɗaya. Wato har shaidamata yake ta shiryawa haɗuwarta da ita saboda ya san ba zai yi kyau ba.
Ramlat ta yi kwafa, ta mike da zummar barin dakin sai ga saƙonsa ya shigo.
"Kashe waya ba shi zai sauya zancena ba, ba kuma zai hana na faɗi ba. Ki shiryawa haɗuwarki da Uwargidana. Anan za ki gane so da kuma ƙiyayya."
Ta harari wayar tana jin kamar shi din ta harara, sai kuma takaici