Showing 171001 words to 174000 words out of 231786 words

Chapter 58 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

yanda har Hajiya Zeenatu ta yi nasara akan su.


Kwankwasa kofar da aka yi gami da sallama yasa duk suka mayar da hankali. Nos Farida ce. Suka gaisa sannan ta miƙawa Ramlat takarda. Cikin raɗa-raɗa ta ce.


"Gashinan, Khadija ta nemi da na ba ki."


Ta karɓa da mamaki ta kuma yi godiya. Daga nan Farida ta juya ta fice. Ta ɗago ta dubi mutan dakin wadanda ita suke kallo. Ta maida hankali ga takardar ta warware ta shiga karantawa.


_*Assalamu alaikum,*_


_*Ramlat ina miki fatan alheri da kuma samun lafiya. Akwai wani lamari da nake son sanarmaki. Wata mata ta yi barazanar hallaka ni matukar ban aiwatar da aikin da ta sanya ni ba, wato na kashe ki. Laifi ne da har abada bana fatan na aikata koda a kan maƙiyina ne. Ina mai ba ki shawara akan ki nar asibitin nan da gaggawa domin idan ma ni na kasa aiwatarwa za ta iya siye wani da kudi ya cikamata burinta. Taku mai kaunarku, Khadija Ashir.*_


Bakin Ramlat ya shiga rawa yayinda idanunta suka cicciko da kwalla. Tsam! Ya miƙe ya ƙaraso wurinta ba zato ta ji an zare takardar daga hannunta. Ta dubeshi, shima ita ya ke kallo cike da zargi kafin ya maida hankali ga takardar.


"Meyafaru ne?"


Hajiya ta nemi sani. Ya miƙawa Hisham, Hisham ya karanta a fili. Hussein ya sa kai ya fice daga ɗakin.


Su Hajiya suka sanya salati.


"Wai wace ce wannan matar mai neman ganin bayan Ramlatu? Oh duniya ina za ki da mu? Nikam ko maganin asibitin nan ban yarda a ƙara kawowa ki sha ba Ramlatu."


Maganar karshe na Hajiyar sai ya ba AlHassan dariya.


"Kar ki damu Hajiyarmu, ba abinda zai sami Ramlatu da yardar Allah. Sai dai ya kamata a bi shawarar Khadija, a ɗauke ta daga asibitin."


"Dama ai Likitan ya fadi, yanda take samun sauki zai iya ba mu sallama gobe ko jibi. To ai kuwa gwara a yi komai."


Can wayar Hisham ta yi ringing, Hussein ne. Hisham ya saurari bayaninsa sai ya yi murmushi ya katse kiran.


"Ga wanda ya fi mu can ma ya tafi nema maku sallama a darennan."


Da mamaki Aisha da AlHassan har su na haɗa baki wurin tambayar waye?


"Hussein." Aisha ta saci kallon Ramlat tana murmushi, itama Hajiya murmushin ta yi kawai ba ta ce komai ba.


Kamar dai da wasa, haka Hussein a daren ya yiduk cuku-cukun da zai yi har aka ba su Ramlat sallama a daren. Suka haɗa komatsansu, Hajiya da Ramlat a motar Hussein, shi kuwa Hisham da madam dinsa suna tare. Amrah wacce har ta kamo hanya, sai waya suka yi mata suka sanarmata da batun sallama. Ita kanta ta yi mamaki.


A hankali ta ɗago kai don tun shigar ta motar kan yana a ƙasa. Caraf suka haɗa idanu ta cikin gilashin kasancewar AlHassan ke tuƙin wannan karon. Ta sauke kanta, shi kuwa ya samu damar ƙarewa fuskar kallo yanda duk ta faɗa kamar wacce ta yi cutar wata guda.


A hankali ya kauda kai, suka yi ido hudu da AlHassan da ke satar kallonsa, murmushi AlHassan ya yi mishi shi kuwa ya gyara zama gami da ɗan ɗaure fuska kadan yana shan ƙamshi.


Har gida suka kai su, Ummi da su Ansar duk suka fito a guje suna mata oyoyo, za su fada jikinta Hussein ya yi saurin riƙo Affan wanda ya fi kowa kusantarta, ita kuwa ta dafe hannu tana kiran wash!


"Ba kwa ganin ciwonta?"


Ya faɗi a hankali, suka fasa rungumeta su na dariya. Ya kama hannunsu zuwa wurin mota.


"Ku zo muje"


Ramlat ta bisu da idanu kafin ta juya ta bi sahun su Hajiya zuwa ciki. Shi kuwa Hussein ledojin dubiyar da ya loda a boot, shi ya ciromusu ya damƙa musu.


"Oya, maza ku je a kaiwa Mami sai ta ba ku."


Affan ya hau washe baki ganin Hussein ya fiddo alewa daga aljihu ha bude ya sanya mishi a baki. Murmushi sosai shima ya yi mishi ya bishi da kallo har ya ɓacewa ganinsa.


Bayan Hussein sun koma gida, Hajiya Zeenat ta tarbe su da fara'a tana mai danne takaicin da suka ɗuramata. Hussein ya dan sakarmata.


"Ki yi hakuri, gidan Hisham muka ci abinci ba haka na so ba."


Ganin yanda ya fadi cike da kulawa yasa nan da nan ta ji zuciyarta ta sake. Ko ba komai hanyar lafiya a bita da shekara. Yanzun dai kaffa-kaffa ta ke yi kar kwaɓarta ta yi ruwa. Da haka ya nunawa AlHassan dakinsa kafin shima ya shige nashi dakin. Hajiya Zeenatu ta yi mamakin da ya bari ta kwana tare da shi duk da bai yi mata kama ko hannunta ba, asalima baya ya juya da nufin bacci yake ji.Ta so su yi batun tafiyarsu London ammata share, har lokacin jikinta a sanyaye yake, burinta yanzu gari ya waye ta shiga asibitin da Ramlatun take ta ga ko ta aiwatar da aikinta.


"Gobe in sha Allah zan yi ƴar tafiya."


Hajiya Zeenatu ta tsinci maganar Hussein wanda ta yi zaton bacci ya ke kamar daga sama, ta mike zaune gami da kunna fitila. Har sannan ya bata baya. Ya yi crossinh hannaye a kirji.


"Ina za ka je kuma?"


"Adamawa." Ya furta kai tsaye gami da juyowa ya kalli tsaka idanunta. Duk sai ta ji ta rikice, hanjin cikinta sun kaɗa. Ta haɗiyi miyau, Hussein zai je Adamawa?


Hannunta ya ɗan riƙe ba don ya so ba.


"Ya naga duk kin sauya? Ba kya son na je na ga ƴan uwana?"


Ta yi murmushin yaƙe.


"Ko kusa aa, amma na ji haushi da ba ka shirya tafiya da ni ba, da ace ka yi niyyar muje tare za ka sanar da ni akan lokaci."


Ya yi ɗan murmushi.


'Makira.' Ya furta can ƙasan ransa. A fili kuwa ya shafi gefen fuskarta.


"Ki yi hakuri, bansan yanda za su kalli lamarin aurenmu ba. Gwara naje na yi musu bayanin komai a tsanake cewa auren soyayya muka yi. Kinga hakan zai fi armashi."


Ta ji wani sanyi kamar kankara, tana so ta yi shakku akan zancensa sai dai kuma ta kasa. Ta shiga gasƙata dukkan kalamansa. Hussein ya ci gaba da yi mata daɗin baki har sai da ta gasƙata da kanta cewar dagasken Hussein sonta ya ke yi ba wasa a ciki. Da wannan ta ji salama amma duk da haka tana tsoron a hana shi dawowa.


"Za ka dawo garinnan kuwa?"


Ya yi murmushi ya lumshe idanu.


"Wa zan bar wa ke?"


Ya fadi ba da manufa biyu, ta ji wani sanyi har sai da ta dara cike da shauƙi. Da wannan suka kwanta bacci.


***
ƘARSHEN ALEWA..!


A ranar Talata sha biyu ga watan Maris, kotu ta yankewa Halima da Gwaska hukuncin shekaru goma zuwa sha biyar a gidan yari a dalilin yunkurin kisan kai.


Halima ta yi kukan nadama sosai, karshe ta nemi alfarma wurin ƙaninta akan ya je ya nemar mata gafarar Ramlatu. Yusufa na hawaye haka suka rabu da Yayarsa aka tsitsa ƙeyarta suka bar kotun.


A can gida, Ramlat ta ji labarin komai a waya daga Hisham, kuka sosai ta yi na tausayin Halima. Haka ta dinga samun kira daga tsofaffin abokan aikinta na ma'aikatar Revenue, da yawansu sai yanzu suka san dalilin kamen da aka yiwa Halima. Sun jajantawa Ramlat gami da yin Allah wadai da son abin duniya irin na Halima wanda ya kai ta ya baro.


"Ai godiya za ki yiwa Allah don yau kam duka ranarki ce. Ga shi dai an yankewa wadanda suka zalunceki hukunci, ga Kawunki Jamuli ya karɓi kuɗi, ya kuma tabbatarmin da kansa yau ba gobe ba, zai damƙawa Chairman kayansa. A yi ta ta ƙare. Ke kuma ya ce idan kima kara warwarewa ki je yana son ganinki.


Maimakon farin ciki sai ya ci gaba da hawaye jin kalaman Hajiya, dama tun safe ta karbi Atm card din kuma ta fice tare da Munir. Uwa daban ta ke, ita ta tsaya tsayin daka tare da Hajja wurin karɓar mata ƴanci.


Sallamarsu ce ta katse dukkan tunaninta. Suka dube su. Shaddar ba iri guda ba ce, sai dai kowannensu fari ƙal ya sanya. AlHassan da hula a kansa, yayinda gogan ya fidda nashi a mota, sai sumarsa kwance. Hajiya tun shigowarsu take murmushi da yi musu adduar neman tsari da kariya a ƙasan ranta.


Ita kuwa tun da ta kalle su ta sunkuyar da kai cikin sanyin jiki. Suka karaso suka durkusa suka gaida Hajiya ta amsa fuska a sake. Suka yi mata murnar shari'ar da ta gudana, ta ta yi ta musu addu'a sosai. Ana haka sai ga Zulaihat da Rafee'ah suma, sun ji labarin sallama.


Suka karaso daidai sadda AlHassan ya dubi Ramlat.
"Kanwata ya jiki?"


Ta yi murmushi. Ta gaishesu. Ya amsa shi kuwa Hussein ya yi kamar bai ji ba yana kallon twins din Zulaihat.


Bayan zamansu aka kara gaisawa su na muu godiya.


"Zamu wuce Adamawa Hajiyarmu."


"To ƴaƴana, sai kuma yaushe?"


Hussein ya amsa wannan karon.


"Nan ba da jimawa ba za mu dawo in sha Allah."


Ta jinjina kai ta yi musu fatan isa lafiya. Hakanan suka kama hanya. Rafee'ah ta yiwa Ramlat ido, ba musu ta mike ta takamusu, ba laifi yanzu hannun da sauki sosai. A daidai barandar shiga dakin ta ci burki.


"Allah Ya tsare, Ya kaiku lafiya. Na gode sosai."


"Ke za mu yiwa godiya sosai. Allah Ya bar zumunci."


Ta yi murmushi.


"A gaidamin Fatina."


Ya yi murmushi.


"Za ta ji in sha Allahu."


Daga haka ya yi gaba, Hussein ya dube ta.


"Yarinyar da kika aikomin hotonta?"


Ta gyada kai tana murmushi. Sai a sannan ta ga ya yi mata murmushin shima.


"Ina kara godiya gareki. Allah Ya ba ki miji nagari. Oh, ashe kin samu. Allah Ya nunamana aurenku."


Ya karashe yana taɓe baki. Ta rasa ma me za ta ce, ya bita da wani irin kallon da ta kasa fassarawa.


"Ki kula da shan magungunanki, kada ki tsorata, likita da kansa ya rubuta da kaina na karɓomaki. Ba za ki mutu ba."


Ta dan yi murmushin yaƙe, ya juya ya tafi. Jiki a saluɓe itama ta koma ciki.


***
HUSSEIN AMINU MAMMAN MODIBBO...




Alhaji Aminu Mamman Gidado, haifaffan garin Adamawa ne gaba da baya. Su goma sha biyar cif mahaifinsu ya haifa. Mamman Gidado yana da mata uku, uwargidansa wacce suke kira da Inna, ta haifamasa yara tara cif a duniya, sai mai bi mata Yakumbo wacce ta haifi yara biyu. Hassan da Hussaina wanda a karshe suka koma hannun Inna da zama. Hajara (Hajjo) kuwa tana da yaranta huɗu cif a duniya.


Wani irin rayuwa ake gudanarwa a gidan Mamman Gidado, rayuwar da hatta da maigidan shakkar Inna yake yi balle a kai ga mata da yara. Inna wata irin mace ce murɗaɗɗa mai baƙar zuciya, a duniya ba ta kaunar ace wani ne sama da ita koda a matsayi ko wani abin. Auren gida na zumunci aka yi musu da Mamman Gidado.
Sai kuma cikin ikon Allah ya zamana Yakumbo ta fito daga gida na sarauta a garin Mubi. Mahaifinta shi ne wazirin Sarki. Wannan girma da nasaba ta Yakumbo sai ya jazamata baƙin jini fiye da na kowa a wurin Inna.


Ita ta soma yiwa Yakumbo gorin zama bare a gidan don Hajjo ma ƴar aminin kakansa ce aka aura. Yakumbo tana shakkar Inna sosai, tana kuma bin ta sau da ƙafa.


Mijinsu ba karamin so yake yiwa Yakumbo ba, tana matsayi babba a zuciyarsa da bai jin ko Inna ta samu. Wannan ta sanya mutuwarta ba jimawa shima ya soma jinyar ajali. A gaban idanunsa Inna ta sha hana Amina da Aminu abinci, wataran Hajjo a sace take basu. Dangi kuwa ba'a taɓa ganin laifin Inna don a waje nunawa take nan duniya tana sonsu kuma tana riƙe da su da amana. Wannan tasa hatta ga yaranta maza da mata sun tsani su buɗe idanu su ga Amina da Aminu musamman ganin irin kyauta da gatan da ake nunamusu duk sadda suka kai ziyara Mubi suka dawo. Kayan da Inna ba ta sanyamusu kenan, duk zuwansu dama gargadi ne sosai da jan kunne ta ke musu akan kar su sake su yi yunkurin tonamata asiri.


Modibbo wanda ya kasance ɗa na bakwai a wurin Inna, kusan shi ne babban mugun da ya fi kowa tsanar yaran Yakumbo. Ya sha kama su a makaranta ya jibga ya kuma kwace abincin da Hajjo ta girkamusu. Gori na uwa da uba bai fasa yi musu ba.


"Wai meye amfanin riƙon da ake musu anan? Tunda suna tutiyar dangin uwarsu masu arziki ne, ki tattara ki maida su mana!"


Modibbo ya fadi a zafafe. Yar uwarsa kuma Yayarsa Adda Salma ta karɓe.


"Ashe ka gane, ni wallahi haushinsu nake ji,wannan Aminar ma kyanta ya yi yawa, ko makaranta muka je sai a yi ta wani zuwa ana daukarta. Ji nake kamar na shaƙeta na huta. Da zan samu reza na tsaga fuskar ma zai fi."


Sauran suka yi dariya har Inna Idan ka cire Karime da Adamu wadanda su kadai suka fita zarra akan sauran, basu taɓa nuna kiyayya ga Amina da Aminu ba.


"Allah ne Ya ba ta kyan, kuma ai..."


Buge bakinta Modibbo ya yi da ƙarfi.


"Dama ke da Adamu ina kula da yanda ku ke shishshigewa yarannan! Marasa zuciya da kishin uwa!"


***
Da wannan irin kiyayyar Amina da Aminu suka taso, boko dai basu isa su je ba sai yaran Inna, islamiyya kadai suke zuwa. A wannan rayuwar, Waziri ya fadi ya mutu, kasancewar mahaifiyar Yakumbo ta jima da rasuwa ne yasa babu wanda ya kara waiwayarsu balle ya maida hankali wurin kula da su daga Mubi. Yar uwar Yakumbo tilo, Zahida, ita kuwa tana aure a Saudiyya. Kafin ta shigo gari akan jima sosai.


Shekaru suka ja a wannan halin, Aminu ya yi saukar littatafai da dama na addini. Mutum ne mai matukar kokari da saurin daukar karatu. Lokaci ɗaya kuma ya bazama neman ilimi a garuruwa daban-daban. Inna ko a jikinta, don a ganinta ba wani ci gaba da zai samu face ya ƙare a almajiranci. A sannan babbar ɗiyarta Hansatu, ta kammala karatunta a fannin shari'a a jami'ar Adamawa. Yayinda Salma ta karancifannin Kasuwanci. Duk an musu aure a sannan.
Modibbo yana ajin karshe inda shima dai yake karantar fannin Kasuwanci. Adamu da Karime su ne a babbar Sakandire sai Hadiza, Safiya, Tahir a karamar Sakandire, Maimuna Autar Inna a firamare.


A islamiyya ba su taɓuka abin a zo a gani, gwara ma Karime, tana da kokari sosai don ta yi sauka.


Yaran Amarya Hajjo hudu, suma duka suna karatu.


Bayan tafiyar Aminu almajiranci da watanni biyar sai ga Hajiya Zahida da yaranta daga Saudiyya. Sun dawo kenan sakamakon sauyin wurin aiki da mijinta ya samu zuwa Adamawa. An saukeshi daga Ambasada. Kai tsaye wurin ƴaƴan yar uwata ta soma zuwa. Ranar da ta je ta tarar da Inna na jibgar Amina da sunan wai ta tsaya sauraron bare wanda kwata kwata ma ba jinin Fulani ba ne. Da biyu Innar ta yi hakan ganin yaron mahaifinsa mai kudi ne, sunan zuri'arsu ba ɓoyayye ba nema ƙasar. Ya ganta ne a hanyar dawowarta daga islamiyya.


Wannan tashin hankalin da Hajiya Zahida ta tarar yasa ta rantse ko sama da ƙasa za ta haɗe sai ta tafi da Amina. Kaca-kaca suka rabu da Inna, a karshe ta ci nasarar dauke Amina tana kukan rashin sanin inda Aminu ya tafi.


Da wannan suka wuce Mubi, sosai ta nunamusu ɓacin ranta akan yanda suka yi halin ko in kula da yaran Yakumbo, hatta aiken da takan yo a kai musu ba ya riskarsu.


Da wannan bakin cikin ta zauna, sati na cika ta tattara yaranta har Amina suka wuce sabon gidansu a cikin Yola.


Wannan ne dalilin ingantuwar rayuwar Amina wacce gaba daya yaran ke kiranta Dada. Babban ɗan mijin Hajiya Zahida (ɗan Uwargidansa da ta rasu, riƙonsa ya koma hannun Zahida) Naziru, tunda ya dora ido a kan Amina ya ji nan duniya ita yake so da aure.


Sosai abin ya yiwa Hajiya Zahida dadi, hakanan shima mijinta bai ƙi ba. A yan uwan mahaifiyarsa ba wanda ya nuna kiyayyar abin ko don irin rikon da Hajiya Zahida ta mishi, ba jimawa kuwa aka sha bikinsu. Amina ta yi kukan rashin dan uwanta a kusa, haka ta hakura ta fawwalawa Allah suka tare a gidan Naziru wanda babu nisa sosai da gidan Hajiya Zahida.


***
Bayan shekaru masu dama, Dada ta haifi yaranta uku duk mata, tana da cikin na hudu ne ba zato ba tsammani Naziru mijinta ya ɗaukesu sai gidan Hajiya Zahida. Wanda ta gani ne ya sanya ta zuwa a guje ta rungumeshi sai kuka, tana yi shima yi yake. Ta ɗago ta dubi wata mace fara ƙal da ita kyakkyawa, a gefenta wasu kyawawan yara ne su biyu da zasu girmi yaranta, komai nasu iri daya. Haka kawai jikinta ya bata wannan iyalin Aminu ne. Ta rungume matar kafin ta rungumi yaran tana cike da farin ciki.


Sai bayan an zauna an nutsu ne ya ke basu labarin inda ya je.


Ashe bayan tafiyarsa da tawagar almajirai ba inda suka yada zango sai Maiduguri, ya fada hannun wani Malami kuma barebari cikakke, Malam Banakura. Mutum mai sanin daraja da ƙimar almajiransa. Aminu bai ɓoyemishi komai dangane da Asalinsa ba. Tausayi da kaunar Aminu suka shiga Malam. Ya rikeshi tamkar ɗan cikinsa, duk da tarin Almajiran Malam, Allah bai ba shi haihuwa ba. Kuma matsalar daga gareshi ne. Uwargidansa Yakura, mace ce mai halin Dattako, ta rike yaran yan uwa da dama ta kuma aurar da su. Yara biyu kadai suka rage a hannunta sannan, Zahra da Yusha'u.


Zuwan Aminu sai ta haɗa da shi ta rikesu duk kuwa da cewar ya girmi Zahra nesa ba kusa ba. Sai dai zai iya sa'an Yusha'u.


Haka suka rayu har suka kara girma, noma da kiwo shi ne sana'ar Malam bayan koyarwa, Aminu ya tsunduma wurin taimakawa Malam. A hankali kuma Allah Ya sanyawa abin albarka. Koda shekarun aure suka kai, Malam ya fahimci irin soyayyar dake tsakanin Zahra da Aminu, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya auramasa ita da iznin iyayenta. Mahaifinta buzu ne kuma Maigadi, mahaifiyarta ce ƙanwa ga Yakura matar Malam. Kyakkyawar mace mai gashi har ƙugu, yarinya mai yawan ibada da kunya.


Zamansu ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login