Showing 159001 words to 162000 words out of 231786 words
Chapter 54 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
ya jigata sosai a hannunsu.
"Ramlat." Ya faɗi da wani irin sanyi kusan kalar muryar Hussein da ya yi haddarsa.
Kuka sosai Ramlat ta shiga yi. Za ta nufeshi Halima ta ƙara yo baya da ita.
Juyo da Ramlatun ta yi, Ramlat ba damar gudu. Hankalinta na kan Hussein yayinda idanun ke kallon masheƙin da ke tsaye a gabanta.
"Mene ribarku idan kun kashe Hussein? Me ku ke da buƙata?"
Wata dariya Halima ta yi kamar ta yara ƙanana, ta sauya murya.
"Ubanki za mu yi! Ai ke muke nema! Ke kuma aka ce mu kashe ba Hussein ba. Kai Gwaska!"
Tana fadin haka wanda ke zaune da ta yi zaton Hussein ne ya miƙe ya yakice kyallen. Nan ta ga wata sura marar kyan kallo don kamar babu ɗigon imani cikinsa. Ya ƙaraso, yanzun ne tunanin Ramlat ya ba ta cewar tarko ne aka yi mata kuma ya faɗa. Da wani irin sauri ta ja gefe ta yunkura za ta gudu, tuni Gwaska ya damƙe ta tana kokarin ihu ya rufemata baki.
"Ki kashe ta! Me kike jira?!" Ya yi maganar a tsawance ganin Halima ta kasa sarrafa bindigar kamar yanda ya koyamata. Ta runtse idanu ta harba ba tare da saiti ba. Wata ƙara Gwaska ya saki sakamakon samunshi da ta yi a cinya. Ramlat ganin hakan ta ture shi za ta gudu, Halima ta damƙota.
"Ki kashe ta nace!" Gwaska ya fadi iyakar karfinsa yana dafe da cinyarsa. Jin haka AlHassan ya fito daga maɓoyarsa sai dai kafin ya karasa tuni Halima ta ƙara sakin bindigar wanda cikin sa'a ta samu Ramlat a kafaɗa.
"You are under arrest!"
Muryar mutum suka ji. Gaba daya suka juya, fitilun motocin da ke shigowa gurin ya haskewa Halima fuskar AlHassan. Ta zaro ido ta cikin mask din fuskarta. Hussein ne?! Hajiya dama karya ta yi da ta ce ta saka shi bacci?
Ganin haka ta yunkura za ta gudu sai dai da wani irin zafin nama na ɗaya daga cikin ƴan sandan, ya cafketa tana kiran wayyo Allah. Ramlat dake zube anan tana gani dishi-dishi hannunta na dafe da kafaɗarta da Gwaska ya samu. Ba shiri ta zube a ƙasa. Wani irin sunguma da AlHassan ya yi mata a gigice yana ambaton sunanta, amma ko motsi.
"Kai ta mota mu je asibiti!" Hisham daga bayansa ya faɗi a gaggauce. Kafin ka ce me, sun isa mota tuni rigar AlHassan ta ɓaci da jini. Hisham ya bada umarnin tafiya da su Gwaska da nufin zai je station din daga baya. Suka tafi da ɗan sanda saboda ba da shaida.
Munir wanda ya taho, suka yi waya ya ke sanarmasa halin da ake ciki, hankali a tashe ya juya kan abin hawa ya nufi asibitin da Hisham ya kwatantamasa.
Kafin su je ya riga su isa, don haka suna zuwa ya tarbesu. Shi ya karɓi Ramlat ya ƙarasa ciki da ita. Sai dai aka kammala dukkan wani sa hannu aka hau ceton rai da gaggawa.
Munir ya kira gida ya faɗawa Zulaihat wacce ke faman kiransa a waya. Jin abinda ya faru daga ita har Hajiya suka kasa zama gidan suka nufo asibitin.
"Laifina ne, meyasa na bar ta ta je ita kaɗai ban maramata baya ba?"
"Ka daina faɗin haka Hassan, rai da ajali duk a hannun Ubangijin al'arshi su ke, kaddararmu ce haka. Mu yi fatan samun saukinta." Hajiya ta faɗi tana mai sharce hawayen saman kuncinta.
AlHassan hankalinsa sam bai kwanta ba, ga tsananin son ganin Hussein da ya ke yi. Yanzun da ya san inda yake sai ya ke jin kewarsa ta ƙaru. Fitowar Likita ne yasa suka dubeshi.
"Alhamdulillah an cire harsashin, ba dai ta farfaɗo ba. Amma muna sa ran komai zai zo da sauƙi. Dafin bai shiga jikinta sosai ba."
"Alhamdulillah." Suka furta kusan a tare. Hajiya ta dubi Zulaihat bayan sun gama addu'a da godiya ga Allah.
"Uwani maza ki wuce Muniru ya sauke ki gida, dare ya yi. Ni zan tsaya anan da ita."
"Aa Hajiya, ba za'a yi haka ba. Su Ummi da aka bari a gida fa?" Cewar Zulaihat.
"Ina ce Ladidi na nan? Zan ƙarasa na nemi alfarma ta kwana yau dai ɗaya. Daga nan zan haɗaku a waya idan da abinda ki ke buƙata sai na dawo na kawomaki. " Faɗin Munir yana mai ƙarashewa da mayar da akalar zancen ga Hajiya.
Suka yi na'am, Hajiya ta ƙara duban AlHassan.
"Hassan sai hakuri ka ji? A kara godewa Allah tunda a baya ma ba'a san inda yake ba. Yanzun kuma da Allah Ya nuna in sha Allahu komai zai zo karshe. Kar wannan ya dameka. Ya kamata ka wuce gida duk ka ɓata jikinka da jini."
AlHassan ya jinjina kai yana gyara zaman gilashinsa, suka yi sallama aka tafi aka bar Hajiya ita kaɗai ta na jiran likitoci su kammala su ba ta umarnin shiga.
A harabar asibitin bayan tafiyar Munir da Zulaihat, Hisham ya dubi AlHassan.
"Dama nayi mamakin ta yanda za'a ce wani abin zai sami Hussein. Ba wai ba za ya taɓa faruwa ba ne, sam aa, sai dai idan har zargina ya tabbata da hannun Hajiya Zeenatu a abinda ya faru ga Ramlat to ba zai taɓa zamtowa an riski Hussein a wurin ba. A irin son da Zeenatu ke yiwa Hussein ba za ta bari a haɗa baki a cutar da shi ko ya ya ba."
"Kai ma kana da labarin Hussein kenan?"
AlHassan ya tambaye shi da gaggawa. Ya gyaɗa kai yana duban agogo.
"Ina da labarin komai, na taƙaice maka Hussein aminina ne, bani da aboki sama da shi a faɗin duniya. Sai dai kuma ya dace ko me zamu yi kada ya wuce gobe, idan ba haka ba za mu rasa damar mu."
"Me kake nufi?"
Tiryan-tiryan Hisham ya ba shi labarin duk abinda ya sani dangane da Hussein. Ya ɗora da faɗin.
"Babu damar a yiwa Hussein zancen ƴan uwansa, ba ya so. Da zarar ka tambaye shi game da asalinsa, kansa zai ɗau zafi ya sauya gaba ɗaya. Ransa kuma idan ya yi dubu toh zai ɓaci. A ranar idan mutum bai yi dagaske ba girmansa zai iya faɗuwa a idanun Hussein."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Mace ce? Ita ta rabamu da Hussein? "
"Hum, sai addu'a." Hisham ya furta, a ƙasan ransa yana jimamin yanda AlHassan zai ji idan ya gane da sa hannun Kawunsa ciki. Hakan yasa bai faɗamasa ba har sai gaskiya ta yi halinta.
"Ya za'a yi na gan shi yanzu? Bana so su kai ga barin ƙasar."
"Kada ka damu, a gobe da safe in sha Allah zan haɗaka da ɗan uwanka. Za ku ga juna."
Murmushi AlHassan ya yi mai haɗe da dariyar farin ciki, kasa hakuri ya yi sai da ya rungume Hisham yana murna.
"Na gode, Na gode sosai. Allah Ya bar zumunci."
Hisham ya yi dariya gami da dukan kafaɗarsa.
"Ameen. Kar ka samu damuwa. Ka kara godewa Allah, sannan Ramlat. Ba karamin namijin ƙoƙari ta yi akan ɗan uwanka ba."
Murmushi sosai AlHassan ya yi tare da fatan Allah Ya ba ta lafiya.
Hisham ya amsa kafin su yi sallama, shi ya nufi gida, Hisham kuwa ya zarce Police Station don jin abinda ake ciki.
***
_*LAMIƊO CRESCENT*_
Safa da marwa ta ke faman yi a tsakar falon, ta ɗauki waya ya fi a ƙirga. Kiran Halima ta ke jira kamar yanda suka yi alƙawari.Ta kira Hajiya Batool ya fi sau goma don ta ji ko sun yi waya amma shiru ka ke ji, Malam ya ci shirwa. Ta kara kai idanunta kan wayoyin Hussein da ke ajiye saman kujera. Baƙin kishin Ramlat ya ƙara ƙarfi a zuciyarta. Ta gwada amfani da yatsarsa ta buɗe wayar, hakanan ta gwada shiga lambobin Ramlat, HEART da ta gani a rubuce ya sanha ta saki ƙarar da har sai da John suka fito daga kicin zuwa falo. Ta dakamusu tsawar da dole suka koma.
Hajiya Zeenatu ta sauke ajiyar zuciya tana jin wani malolon abu ya tokaremata maƙoshi. Awanni biyu kenan da ta ba Hussein lemo ya sha wanda ya yi sanadiyyar baccinsa, a wannan lokacin ba abinda ta ke burin ji sai saƙon mutuwar Ramlat. Wayarta ta yi ƙara da wani irin zumuɗi ta duba. Tsaki ta ja ganin lambar Kawu Modibbo, sai da ta kalli ƙafar benen ta tabbatar babu mai saukowa sannan ta amsa a fusace.
"Ina jinka."
"Ya ake ciki?"
Ta safe goshi gami da runtse ido cikin soma gundira da tunani.
"Ni kaina na gaji da tambayar kaina. Abinda ya fi shi ne zan nemi Halima har gidansu na bincika."
"Ga dukkan alamu lamura sun ɓaci."
"Ina tsoron hakan ta kasance."
Ba ta jira cewar Kawu ba ta kashe kiran.
"Zeenat."
Da wani irin ruɗewa ta juyo tana dubansa, yana dafe da goshi a hankali kuma ya shiga saukowa daga matattakalar. Ta yi kokarin saita kanta ta karasa gareshi da murmushin yaƙe.
"Sannu, ka sha bacci."
Hussein ya gifta ya karasa ya zauna saman kujera kansa na ci gaba da sarawa.
"Me ki ka ban na sha?"
Ya tambaya ba tafe da ya kalleta ba. Ta zauna gefensa.
"Ba ka samun bacci yanda ya kamata, ga gargadin likita da ya ce ka dinga samun hutu, shiyasa na sanyamaka maganin bacci a lemu na kashe wayoyinka."
Ya dubeta da idanunsa da har sannan ba ya jin baccin ya sakeshi.
"Haba Zeenat, shi ne dalilin sanyamin maganin bacci? Meyasa haka? Wane irin hutu ne ba na samu? Cuta ba ta Allah ba ce?"
"Hakane, to ka yi hakuri." Ya mike rai a ɓace ya ɗauki wayoyinsa ya haye sama. Ta bishi da kallon munafuki karon farko a rayuwarta.
"Ka ci darajar son da nake maka Husseini, da yau sai ka gane shayi ruwa ne."
Ta furta a hankali yanda ta san ba zai ji ba. Har hango hotonsa da Ramlat ta ke yi a kwayar idanunta. Takaicinta, meyasa ba ta nemi kwararrun ƴan daba sun aiwatar mata da komai ba? Meyasa sai Halima?
Ta ja tsaki tana sharce gumin da fargabar ko Hussein ya ji wayar da ta yi ya haifarmata.
***
"Ita kuma wace ce wannan?" Hisham ya tambaya yana karewa Halima da ke faman sharɓar kuka a bayan cell kallo.
"Sharrin shaiɗan ne wallahi, don Allah don Annabi s.a.w ku yafemin wallahi nayi alƙawari ba zan ƙara ba. Nima san..."
_*"Halima, ki tabbata koda wasa aka samu matsala, kar bakinki ya yi kuskuren ambaton sunan ɗaya daga cikinmu. Ki ce kawai dai kina kishin Ramlatun za ta auri Chairman dinku ne. Ki ka kuskura ki ka yi gangancin tonamana asiri, ki sani rayuwarki ce za ta ƙare a doron ƙasa saboda za mu bar ki ki rayu kuma ki mutu a gidan yari ba tare da mun ɗauki matakin fiddoki ba. Idan kuwa ki ka bar komai a cikinki ki ka faɗi yanda na ce, toh shakka babu ina mai tabbatarmaki ko kwana uku ba za ki yi a hannun ƴan sanda ba za mu sanya a fiddo ki kuma ki bar garin. Idan kunne ya ji....jiki ya tsira."*_
"Kin yi shiru? Me ki ke son ki ce?!"
Tana kuka sosai ta dubi Sajan da ke mata tsawa, a gefensa Hisham ke tsaye yana jiran ji daga bakinta. Girgiza kai ta yi.
"Nima sharrin shaidan ne."
"Ƙarya ki ke! Ba haka ki ka so ki ce ba!Ki fito ki faɗi wanda ya sanya ki!"
Cewar Hisham a ruɗe. Ya ja, itama ta ja. Gwaska tuni an yi asibiti da shi.
Dole haka Hisham ya hakura ya bar case hannunsu sannan ya wuce gida, lokacin sha biyu ta wuce.
***
WASHEGARI...
Da sassafe Hajiya Zeenat ta shirya. Motsinta ne ya tashi Hussein dake bacci. Ya dube ta sadda ta ke kokarin ficewa daga ɗakin.
"Lafiya? Ina zuwa haka da sassafe?"
A firgice ta juyo tana dubansa,ta wayance da yaƙe.
"Am..am..dama Hajiya Batool ta kirani ba lafiya har an kai ta asibiti ma. Shi ne zan je dubiya." Ya gyada kai kawai ya juya ya kara jan bargo, ta sauke ajiyar zuciya ta fice. Ta bar Hussein da tunanin irin nasu auren, wannan wane irin aure ne da mace ke da ikon fita ba tare da iznin miji ba? Anya kuwa hakan zai haifarmusu da ɗa mai ido?
Ya sauke ajiyar zuciya gami da lumshe idanu cikin tunanin laifinsa ne tunda tun farko haka su ke yi. Bai kuma san ya hakan ta faru ba.
Wayarsa ce ta yi ƙara, sunan Hisham ya gani yana murmushi ya ɗaga.
"Kira da safiyar Allah, bashin me na ci?"
"Haba Malam, ina ka shiga ne wai? Jiya na kira duka wayoyinka amma a kashe, lafiya dai ko?"
Hussein ya lumshe ido ya ja guntun tsaki tuno da shirmen Zeenatu.
"Share kawai, lafiya lau ne. Ya aka yi?"
"Ba ka da labarin an kai wa Ramlatu hari?"
Wani irin miƙewa Hussein ya yi gaba ɗayansa har santsin bargon na ƙoƙarin kifar da shi ƙas.
"What?"
Labarin komai Hisham ya ba shi.
"Tana wane asibitin?"
Ya sanarmasa.
"Yanzu zan zo."
Daga nan ya katse kiran bai jira komai ba.
***
MISALIN ƘARFE TAKWAS NA SAFE...
Hawaye ta ke fitarwa yayinda ta ke tariyo komai a kwanyarta. A yanzun da Hajja ke salati da tambayar wa zai aikatamata hakan? Itama a sannan kwakwalwarta ta shiga aikin tunani. Kasancewar ta juyamusu baya ya sa ba wanda ya lura da tashinta. Cikin dare dai ta farka sannan ta ƙara komawa bacci.
"Abin dai da ɗaure kai." Hajiya ta furta tana ƙara riƙe carbin hannunta da ta ke ja.
"Nifa ina zargin matar Hussein wallahi. Tunda..."
"Yi shiru kawai Rafee'ah, zato dai zunubi. Irin haka ne sai ki ga ana zaton wuta a maƙera sai aka same ta a masaƙa."
Rafee'ah ta yi shiru amma dai kam zuciyarta cike take da zarginta. Kwankwasa ƙofar da aka yi ne suka bada iznin shigowa. Hisham ne da AlHassan, suka karasa aka gaisa.
"Kada dai ace har yanzu ba ta farfaɗo ba?" Cewar Hisham.
"Aa, ta farfaɗo cikin dare, har na taimaka ta ɗan zagaya. Sannan ta yi salla da Asuba ma. Baccin ne dai ya ƙara kwasarta."
Ramlat da ke jin bayanin Hajiya sai ta runtse idanu, wani radadi kafaɗarta ke mata, sai dai idan har za ta iya jure wannan adalilin Hussein, idan har zaa iya yaudararta a kafamata tarko a kansa, toh ba karamin so ta ke yi mishi ba. Ta ƙara aminta da hakan.
"Au dama idanunki biyu?" Cewar Rafee'ah wacce ta zagayo domin gyaramata ɗankwalin kanta da ya zame.
Ta dube ta, ganin tana hawaye ta sa hannu ta shiga sharemata.
"Haba Ramlat, meye kuma na kukan tunda Allah Ya riga da ya tsare? Yi shiru don Allah. Ko za ki tashi zaune?"
Ta gyada kai. Da taimakon Rafee'ah ta miƙe zaune ta jingina da filo. Ta gaida Hajja da su Alhassan.
Wayar Hisham ta yi ƙara ya duba, shi kansa AlHassan tunda ya ji batun zuwan ɗan uwansa ya rasa sukuni. Burinsa kawai ya gan shi don ya tabbatar da komai. Aikuwa shi ɗin ne.
"Kana waje? Ok gani nan zuwa."
Yanda Hisham ya miƙe hakanan shima AlHassan ya mara mishi baya. Rike hannunsa ya yi.
"Ka yi hakuri, nan zai shigo, ka jira ya karaso ciki ka ganshi."
Ramlat da kirjinta ya tsananta bugu ta dubi Hisham a hargitse. Nan da nan wasu hawayen suka kwaranyo. Baki na rawa ta ce.
"Hussein..Hussein ne?"
Hisham ya dubeta.
"Shi ne, ku kwantar da hankalinku yanzu zan kawo shi."
AlHassan a dole ya dakata sai dai ya kasa tsayuwa wuri guda, safa da marwa ya shiga yi yana kallon ƙofa. Koda aka tura ƙofar aka shigo. Hisham din ne a gaba, a bayansa kuma Hussein. Kamar wani gunki haka AlHassan ya ja burki yana kallonsa ƙurr.
"Hussein...?" Ya furta, furucin da ya ja hankalin Hussein dake sanye da Maroon shadda da hula, ya dubeshi.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/IRx4QB4kMcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
48)
Kallonsa yake yi sosai kirjinsa na bugawa da sauri. Ramlat ta runtse idanu tana mai addu'ar komai ya tafi daidai.
Da wani irin sassarfa AlHassan ya tako ya rungume Hussein kawai sai ya soma kuka.
"Hussein." Ya ƙara kiran sunansa karo na biyu, Hussein ya yi ɗif sai hawaye da ke zuba saman fuskarsa. Ji ya yi kamar ana saramasa guduma a tsakiyar kansa, a hankali ya soma ganin dishi-dishi, lokaci guda idanunsa suka juye yayinda baƙin kwayar idanun ta ɓace ɓat. Hisham da ke tsaye a baya shi ya lura da sauri ya karasa ya rike Hussein. Jikinsa wani irin kakkarwa ya ke yi.
"Innalillahi wa inna ilaihir raajiun!"
Cewa Hisham yana rike hannun Hussein, jin haka AlHassan ya ɗago wanda saura kiris Hussein din ya zube don kuwa da jikinsa ya samu madafa.
"Riƙe shi sosai." Cewar Hisham, suka taimaka suka fitar da shi sai wurin likita. Ramlat tuni ta miƙe tsaye. Su kansu su Hajiya sun rude. Ganin tana kokarin ficewa yasa Rafee'ah riƙo ta.
"Ina za ki je? Ba ki ganin halin da ki ke ciki? Idan kin je lafiya za ki ba shi?"
Ta girgiza kai tana hawaye, ta bude baki sai dai ta rasa me za ta ce don haka ta koma ta zauna. Hajiya ce ya fidda waya don ta kira Malam ta sanarmasa halin da ake ciki. Nan take ya ce maza ta aiko a karɓi ruwan da ya haɗa da ganyen magarya ya yi addu'o'in karyewar sihiri. Ba shiri ta yiwa direbanta waya ta ce ya biya Yakasai ya karɓo mata saƙo.
***
Duk iyakar awon da likitocin su ka yi ba su gano komai game da ciwon Hussein ba. Don haka koda suka samu ya bar jijjigar, idanun suka dawo daidai sai Likitan da ya karɓi Hussein ya fito wurin su AlHassan. Suka tarbe shi da gaggawa.
"Ku yi hakuri.."
"Mutuwa ya yi?" Faɗin AlHassan a gigice, girgiza kai Likitan ya yi yana mai riƙe hannunsa.
"Ko kusa ba haka ba ne, asalima yanzu mun samu komai ya daidaita. Sai dai hakikanin gaskiya ba za mu ce ga abinda ya jawomasa hakan ba, yanzu dai halin da ake ciki, dole zamu yi mishi tests don mu gano ainahin inda matsalar take."
Suka jinjina kai.
"Ba damuwa Dakta. Allah Ya ba shi lafiya." Cewar Hisham da hankalinsa ya ɗan kwanta.
Bayan wucewar Dakta ya dafa kafaɗar AlHassan wanda ya cire hular kansa tsabar gumin da fargaba ta haifarmasa.
"Kada ka damu ɗan uwa, na