Showing 204001 words to 207000 words out of 231786 words
Chapter 69 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
kanta. A hankali kuma ta ga ya juya ya fita bai ce uffan ba. Ta dafe kirji gami da sauke ajiyar zuciya sannan a gaggauce ta mike bayan ta fesa abinda za ta fesa. Ko ba'a faɗa ba, mijinnata yana tattare da damuwar da ya ke buƙatar kulawarta. Ta gama gane irin ɗaukar da Hussein ya yi mata kamar yanda ta soma amanna da zancen soyayyar da ya ke magana bayan aure. Riga da siket ta sanya na atamfa, ta yi ɗaurinta tsaf sannan ta fesa turare ta fita gabanta na faɗuwa. Fatanta Allah Yasa ya huce. Koda ta fito ana kiraye-kirayen sallah, har a sannan ba ta samu tsarki ba. Ba ya falon amma ya ajiye wayoyinsa da agogo, wannan ya sa ta fahimci alwala ya shiga don haka itama sai ta koma ɗaki don kunya ta ke ji ya fahimci halin da ta ke ciki. Tana ji sadda ya fice daga falon sannan ta fito. Mintuna kaɗan bayan idar da sallah sai ga Hafsat tare da Kausar. Fatima ta ruga a guje ta rungumeta yayinda Hafsat ta karasa ta ajiye kwandon abincin hannunta saman tebur. Zama suka yi aka gaisa. Nan kuma aka shiga maida zance.
"Nifa Adda Amal ba wanda ya bani mamaki sama da Kawu. Wallahi ban san rashin kaunar da yake yiwa iyayenmu da mu ya kai girman hakan ba. Ai shiyasa yau nima na rama a kan ɗansa, ya kirani har ya gaji ban ɗaga ba, karshe ma na aikamasa da zazzafan saƙo. Rasheeda fa ki ga ta kasa zama ma a gidannan ta tafi gida Adda Fati saboda kunya da kuma bakin cikin abinda Babansu ya aikata. Anti Amarya ma wai mijin ya kira ta je can yana nemanta."
"Toh ke Hafsat ai dole, amma bana goyon bayan ki wulakanta Tahir tunda ba shi ya yi maki ba. Asalima ke da bakinki kin faɗi irin zafin da ya ke ji na yanda Uban yake hana su zumunci da mu."
Kausar ke maganar kafin ta maida hankali ga Ramlat.
"Kinga shawarar da zan ba ki,wallahi ki tashi sosai ki riƙe mijinki hannu bibbiyu. Kar ki ga kin rabu da Hajiya Zeenatu ki ɗauka shikenan, ba ita kaɗai ce mayya me kwacen miji ba musamman ma a garinnan. Mijina gashinan har yau ban gama fidda ran watarana ba zai ƙaromin abokiyar zama ba don yanda ƴanmata da zaurawa ke farautarsa tamkar nama."
Suka yi dariya. Kausar ta girgiza kai ta nuna Hafsat da yatsa.
"Ba abin dariya ba ne, ke ai kin san komai. Ke za ki ba da labari, ko ƙawayenki na makaranta ba sai da na takamusu burki da zuwa gidana ba?"
Dariyar dai Hafsat ta ƙara, ita kuwa Ramlat sai ta ɗan tsunduma tunani, wato dai bayan wani yaƙin akwai wani, amma bai kai wancan ba. Motsin bude kofarsa ce ta sanya su jan baki su yi shiru don ɗazun dama sun baro shi ya shiga bangaren Dada, tare yake da AlHassan. Zama suka yi Hussein na mai kama hannun Fatima da ta yi tsalle ta faɗa jikinsa. Da wani murmushin samun nutsuwar zuci da gangar jiki adalilin nasiha da ban bakin da Gwaggonninsa suka yi mishi. Ramlat ta gaida AlHassan ya amsa fuska a sake.
"Lafiya lau Amarsu, ya kwanan baƙunci?"
Ta yi murmushi ba ta ce komai ba. Bai wani jima ba AlHassan din, bayan fitar su Kausar don ta je ta harhada kaya su tafi gida, ya ɗan yiwa Ramlat har ma da Gogan yar nasiha akan zamantakewa sannan ya yi musu sallama ya miƙe ya yi gaba. Shima Hussein ya miƙe ya dubeta, duban shauki da kauna.
"Ban mintuna kaɗan, zan je na dawo."
Ta gyaɗa kai.
"Allah Ya dawomin da kai lafiya."
Ya ɗan tsaya ya dubeta na sakanni, kamar ya yi tsokana kawai kuma ya murmusa cike da jin dadin addu'ar ya fice.
***
Kawu Modibbo gumi kawai ya ke sharcewa, labarin komai ya riskeshi daga bakin jama'a, hakan yasa don ya tabbatar ya umarci Anti Amarya da dawowa. A bakinta tana kuka cike da takaicinsa ta sanarmasa duk yanda aka yi ta kara da fadin.
"Mece ce ribarka idan ka cutar da ɗan ɗan uwanka? Abu ɗaya da wannan zuri'a ta yi maka da sunan laifi, ba za ka iya tunawa ba saboda babu shi. Babu dalilinsa. Ka ji tsoron Allah tun lokaci bai ƙuremaka ba, ka tuba ka je ka nemi gafararsu."
Tana kaiwa nan ta bar shi da shi da Uwargidansa Hajiya Fatuma wacce ita kanta jikinta ya yi mugun sanyi. Ta san ba su kaunarsu saboda bakin cikin daukakar da suka samu, amma ba ta taɓa tsammanin mijinnata zai aikata wani abu makamancin wannan ba. Tambayoyi ne birjik a kwakwalwata na yanda akai ma ya san matar Hussein, har ta soma tunanin ko shi ne ya haɗa auren amma babu mai ba ta amsa, mai amsawar ba ya a hayyacinsa. Ta kara dubansa yanda ya ke faman sharce gumi sai ta kula har wani hawaye ya ke fitarwa, na nadama ne ko akasinsa, ba ta da masaniya.
"Ku harhaɗa kayanku, gobe za mu koma Kano."
Ta bishi da kallo har ya shige ɗaki, ranta ya ɓaci, wato dai ba shi da niyyar aikata abinda Anti Amarya ta ce? Ta girgiza kai don ba ta jin zata ɗara ko nan da can ba tare da ta nemi gafarar Dada da yaranta ba na irin kiyayyar da ta musu kuma ta tara yaranta su nema su ma.
***
Misalin karfe goma na dare ya shigo gidan, a lokacin Ramlat har ta gaji da zaman jiransa ga yunwa. Ƴan Maiduguri sun shigo sun mata sallama kasancewar da Asuba za su tafi. Ta sha nasiha sosai sannan suka bar sashinta.
Ta ƙarasa ta nufeshi da zummar karɓar ledojin hannunsa, hannunsu ya haɗu wuri guda, ta ji wani yarr, da sauri ta janye ta yi gaba zuwa cikin falon ta ajiye saman tebur. Shi kuwa dakinsa ya shige, har ta kammala jera kayan abincin da ruwa bai fito ba. Can kuma ba jimawa sai gashinan, daga shi sai jallabiyar maroon. Ko ba'a faɗa ba wanka ya yi don ƙamshi kawai ke tashi a jikinsa. Kauda kanta ta yi tana mamakin ma kunyarsa da ta ke ji, ta yarda dai mazan ma suna suka tara don Hussein wani kwarjini yake mata. Tana zuba abincin amma a jikinta ta ke jin ya cika ta da ido yana kallonta, gaba ɗaya sai ta rasa sukuni. Ta saci kallonsa, ita ɗin kuwa ya ke kallon babu ƙakƙautawa. Ta gama zubamishi ta ajiye a gabansa, tana shirin zuba nata ya damke hannunta. Kallonsa ta yi. Murmushi ya sakarmata.
"Wannan ya yimin yawa. Zo mu ci tare."
Ya fadi yana matso da kujera daf da shi.
"Seat." Ya fadi a hankali yana dubanta ƙasa-ƙasa. Ba musu ta zagayo ta zauna, ganin jikinsu na gogar juna ne yasa ta yunkurin ja da baya, hannu ya sa da sauri ya saƙalo ƙugun.
"Why?" Ya furta kamar mai raɗa a saitin kunnen. Ta yi ƙasa da kai ba ta ce uffan ba. Ganin haka ya saketa ya soma cin abincin yana haɗawa da sanyamata a baki. Ramlat dai ta ga ta kanta, duk wannan yunƙurin da alwashin da ta ci sai ta neme su ta rasa. Ita har wani shakka-shakkarsa ma ta ji tana yi. Bayan sun ci ya ba ta umarnin ɗauko ledojin da ya shigo da su, ta bude, kaza ce sai lemuka. Ya ja plate ya ajiye, nan ta bude kazar ta zuba, lemukan kuwa ta kai firij don akwai wani a ajiye. Koda ta dawo nan ma ya dage sai dai ya ba ta, ta gaji da wannan abin don haka ta ɗan yi kicin-kicin da fuska. Murmushi ya yi.
"Oh, ashe fa kin ce ba zaman da ki ka shirya yi da ni ba kenan ko? Sorry."
Ta ɗan harareshi da wasa, ya shafi fuskar.
"Ko me kika yi, kyau ya ke min."
Haka suka ƙarasa ci yana ta jan ta da hira. Falon ya koma ya zauna bayan ya wanke hannu ya kuma rage hasken fitilu. Ta kammala gyara wurin, sauran abincin ta sanya a firij. Niyyarta ta shige ɗaki ta kwanta amma kaifin idanunsa ya hana ta aikata hakan, dole ta dawo ta zauna.
Hankalinta ya rabu biyu, tana kallon talabijin, yayinda Hussein ke afkin kallonta. Ta gaji ta juyo fuskarta na nuna alamun gajiya.
"Me nayi don Allah?"
Yanda ta marairaice sai ta sanya shi ƴar dariya. Hannu ya miƙamata. Ɗan harararsa ta yi.
"Gulma ce fa ba na so Heart."
Ta basar.
"Wace gulma kuma?"
Hannunta ya kamo ya murza cikinnasa.
"Har yanzu ba ki tabbatar da babu ƙiyayya tsakanina da ke ba? To a tunaninki tun ma farko, don me na aureki?"
Ta rasa amsar ba shi, ita dai gani ta ke kawai rainin hankali ne yasa shi aurenta. Yanzu kuwa ya gama wanke kansa.
"Tunanin me kike ne? Na shayar da ke mamaki ko? Ni yanzu damuwata kamar ma ke ce ba kya sona."
Ta kalleshi, ya wani yamutse fuska shi a dole damuwa. Hannunta ya kai saman fuskarsa. Ta lumshe idanu sadda ya shafa tun daga sumarsa har ya gangaro saman karan hancinsa, yana tafiyar da hannun tana jin wani zuum a gangar jikinta. Hannunta ta ke kokarin ɗaukewa amma ba ta da wannan kuzarin. Tana ji ya maida yatsunta bakinsa, ya bi su ɗaya bayan ɗaya ya sumbata.
"Faɗamin meyasa ba kya sona? Tsakani da Allah nasan muna da kyau. Haka Allah Ya haliccemu kuma mun godemasa. Ba fa yabon kai ba."
Ta maze ta yi gyaran murya kafin ta amsa.
"Ka ɗauka kyau shi ke sanyawa a so mutum?"
Ya shafi sumar kai yana murmushi da dubanta idanun a lumshe kamar mai gyangyaɗi.
"Kin ɗauka bansan rashin ra'ayin hakan ne ya bambanta ki da sauran matan da ke sona ba?"
Baki buɗe ta ke kallonsa don ita mamaki ma ya ba ta. Ya yi ƴar dariya ya gyara zama sosai ya fuskanci talabijin ya matso gareta sosai. Daga yanayin nutsuwarsa ta fahimci ko me yake shirin cewa mai ma'ana ne.
I just published "BABI NA SITTIN DA ƊAYA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1023106863?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=bdvKCKOC3LLp5bowO1ooPkj4NyQWwtoNnAonSsHZp24WzPeGm2lKyYgVyvV%2Bh9gt6e1Oc%2BZqkJMVkFlQ2xAQQ3P60IL2qqoNgqvumrfhTuosHta7gVySLHczdgg1%2Fq97
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
61)
"A rayuwata, kar ki yi mamakin cewa ban taɓa soyayya ba. Ban yi ba tun ma kafin zuwan Zeenat, balle a bayanta."
Ta dubeshi, dama idanunsa na kanta, sai ya yi murmushi ya riƙo hannunta ya damƙe cikin nasa yana murzawa a hankali kafin ya ɗora.
"Sadda Allah Ya soma haɗa ni da ke, mun haɗu ne lokacin bana cikin nutsuwata sakamakon ɓacin ran wata hatsaniya da muka yi da Zeenat, ban ji komai a kanki ba sai sadda na ƙara cin karo da ke a ma'aikatar Revenue da muka je tax payment. A hankali a hankali haɗuwarmu kan zo akai - akai, tun bana daukarki da wani muhimmanci har ban san yanda aka yi na soma kula da lamuranki ba. Na soma jinki kamar wata ƴar uwata. Ba ki ƙara burgeni ba sai haɗuwarmu a A&Z da kika nunawa duniya da ma Zeenat, akwai soyayya tsakaninmu. Duk a matan da suke bibiyata da sunan so, babu wacce ta taɓa rainawa Zeenat hankali kamar ke."
Suka yi murmushin tuna ranar kafin ya ɗora.
"Tun daga wannan ranar na ji ina son kusancinnamu ya fi haka, na dinga hasashen da ace gaskiya ne muna soyayyar ya kenan? Wane yunƙuri Zeenat za ta yi? Duk fa da cewar a sannan ina ɗan shakkarta, hakan bai hana ni tunaninki ba. Dangantakarku da Hisham ya ƙara ƙarfin shaƙuwarmu. Da tafiya ta yi tafiya, na fahimci ba wai kawai burgeni kike ba, kaunarki nake dagaske. Akwai ranar da na ji Zeenat na waya da Chairman tana kyakyata dariyar mugunta. Maganarki suke yi akan ya ci gaba da yin duk yanda zai yi ya aureki, za ta ba shi kyauta ta musamman idan hakan ta kasance. A lokacin har jaddada masa ta dinga yi kan ya yi amfani da masu gidan rana, sai kuma ga Hisham ya zo min da batun aurenki da Chairman. Bayan tsananin kishin da naji yana neman zautar da ni, sai na dinga ayyanawa a zuciyata ashe dagaske ƙarfin dukiya na saurin rinjayar zuƙata. Ban yi zaton kina daga cikin kwaɗayayyun mata ba, sai gashinan lokaci guda kin ban mamaki. Daga lokacin kuma tunanina ya sauya a kanki."
Ramlat jin haka ta bude baki za ta yi magana ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar ɗora yatsansa ba bakin. Murya a tausashe ya ce.
"Yi shiru please, labari ne fa nake ba ki, ki bari na kai ƙarshe."
Ta gyaɗa kai sai dai tuni idanunta sun cicciko, ta kasa kunne tana sauraronsa.
"Baki ba zai iya misalta maki ɗumbin damuwar da zancen aurenki da mutuminnan ya jefa ni ba. Na rasa walwalata, ke kaɗai nake ganin za ki mayemin gurbin ƴan uwana da ban san su ba, ina da su ko bani da su, ba zan tuna ba. Sai gashinan lokaci guda wani can zai rushemin hakan. A sannan har kwanciya nayi a asibiti, aka tabbatar da cewa damuwa ce. Na rage tunani. Bayan na farfaɗo na kasa samun sukuni da walwala, ban yi ƙasa a gwuiwa ba sai da na nemi gidan Baba Dakta, naje a matsayin manemin aurenki."
Da mamaki ta tsuramasa idanu baki a sake, hawayen da ta ke dannewa tun ɗazun suka zubo. Ya yi murmushi gami da sa yatsa ya sharemata.
"Kar ki yi mamakin ta yanda aka yi na san Baba Dakta. A hirarrakin da mukan yi da Hisham, yakan sanyamin shi a ciki don ya cemin ma a wurinsa ya soma neman auren Aisha kafin ya sada shi da Kawunnanku. Yanda na fahimta, banda ma makwafci kuma amini ga mahaifinku, kun daukeshi tamkar mahaifin. Kuna girmamashi sosai kamar yanda ya ke kula da ku. Sau ɗaya na taɓa yiwa Hisham rakiya gidansa, a wata ziyarar gaisuwar Juma'a da ya yi. Yana ɗaya daga cikin dalilin da yasa nake ganin girman Hisham, mutum ne mai son sada zumunci musamman ranakun juma'a, wataran yakan ɗauke ni muje tare, wataran kuwa shi da matarsa suke zuwa. Wasu lokutan kuma uzuri kan hana ni zuwa. Ko Hisham bai san na je gidan Baba Dakta ba, ya sa aka kai ni falon saukar baƙi, daga bisani ya fito muka gaisa. Na yi mamaki sosai da ya shaida ni alhalin sau ɗaya muka ga juna. Bayan mun gaisa sai na rasa ta inda zan fara, karshe ya dube ni da kyau ya ce na saki jiki da shi, na daukeshi kamar Uba, kar nayi shakkar komai na fadamasa meke tafe da ni. Wannan yasa nan take na ji kaunar mutumin nan. Zuciyata ta samu nutsuwa na fayyacemasa cewa na zo neman iznin aurenki ne. Ya gama saurarona, a karshe har ya yimin tambayar ko dama muna soyayya da sauransu. Duka na ba shi labarin gaskiyar yanayin alaƙata da ke. A karshe ya yimin yar nasiha game da hakuri da kuma fawwalawa Ubangiji komai, ya sanarmin cewa an riga da an yi maki miji don magana yanzu ma ta je ga Kawunnanki kuma sun karɓi mijinnaki da hannu bibbiyu. Ya bani hakuri ya kuma ce na ci gaba da addu'a duk abinda Allah Ya yi na sa a raina shi ne mafi alheri. Ba haka na so ba, amma na ji sauƙi daga radadin da naji akan batun an miki miji da farko saboda Baba Dakta mutum ne wanda ya iya kalamai masu nutsar da zuciya da kwakwalwa. Anan ne na nemi alfarma a wajensa kan yanda muka yi maganar ya zama tsakanin ni da shi. Murmushi ya yi ya nunamin kar na sami damuwa."
Ramlat kallon Hussein kawai ta ke yi, so da kaunarsa na ƙara samun matsuguni a kwakwalwarta da ma dukkan wasu sassa na jikinta. Shima idanun ya ƙuramata na sakanni kafin a hankali ya sauke ajiyar zuciya ya ɗan murza hannunta ya ɗora.
"Ramlat, na ci wuya a ƴan tsakaninnan, daga lokacin da na gane ina matuƙar sonki har zuwa sadda ake rikice-rikicen aurenki da Chairman. Ban ƙara samun walwalwa ba. Komai kika ga ina yi maki wala da farin ciki ko akasinsa, kawai yi nake. Idan na yi tunanin zan rasa ki sai na ji hatta da ke din ma haushinki nake ji. Babban dalilin da ya hana na kasa faɗamaki a lokacin, ban gama haƙiƙancewa kina sona din ba ne ko kuwa kawai tausayina kike. Sannan ni mutum ne mai burin duk matar da nake so, na nunamata son a aikace. Ya fi armashi akan mu tsaya muna ta maida martanin kalamai ta waya da zahiri. Ke yanzu abin ma bai fi burgeki ba?"
Ta sunkuyar da kai tana murmushi. Ya ɗora zancen.
"Kinsan wani abu? Nayi mamaki iyaka da na ji labarin ke ce silar haɗuwata da ɗan uwana, mamaki bai ƙara kashe ni ba sai da na ji labarin a sanadiyyata aka harbe ki. Sosai abin fa ya taɓa ni ya dakarmin zuciya. Wannan ne yasa na ƙara ƙullatar Zeenat. A lokacin kuma na kara ji a jikina babu wani abu da zan iya sakamaki duk wata sadaukarwa da ki ka yi gareni face na maidaki karshen ikona kuma mallakina. A bakin Hisham na soma jin labarin duk wani faɗi tashi da ki ka yi kafin aurenki da Hilal, har ma bayan aurenki da Aliyu. Kinsan me? Sai na tsinci kaina da wani mugun farin ciki, tausayi da ma soyayyarki a zuciyata, amma ban nunawa Hisham ba asalima haushi na dinga ba shi har ya yi fushi ni kuwa na haye mota na wuce na yi maki siyayya na dawo. Bana duba Ramlat, amma a lokacin haka kawai na dinga ji a raina da yardar Allah za ki zama mallakina. Musamman da Hisham ya ba ni tabbacin ba kya son Chairman kuma su Hajiya ma ba sonsa su ke yi ba. Abin dai daga Kawunnanki ne. Wannan ne ya sanya ni cikin annashuwa. Kinga wancan aurennaki, ke ki ka yi kiɗa da rawarki, wannan karon kuwa tunda har yan uwanki ma ba sa ta Chairman, to fa abun zai zo da sauki. Na ci gaba da addu'a da miƙawa Ubangiji kukana har zuwa lokacin da na ji labarin fasa aurenki da Chairman. Sai kuma ga wanj Baban