Showing 222001 words to 225000 words out of 231786 words

Chapter 75 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

ya kawo shi nan?"


Baffa Surajo ya dafa kafaɗar Hussein kafin ya ja hannunsa ya bishi suka zauna saman kujera dakyar. Hussein banda girgiza ƙafa ba abinda ya ke yi yana hararar inda Kawun ya ke, ganin haka Baffa ya riƙe ƙafar.


"Ya isa ɗana. Ya isa."


Kawu ya taso zai ƙaraso inda Hussein ya ke, da wata irin tsawa ya dakatar da shi.


"Kar ka sake ka ƙaraso nan! Kar ka yi wannan gangancin!"


Daidai da shigowar AlHassan da sallama, ya kalli mutanen falon ya kuma dubi Hussein mai magana ya sauke ajiyar zuciya. Ya san dama hakan za ta iya faruwa, bai ma yi tsammanin zuwan wannan ranar nan kusa ba, sai dai Allah ne Mai shiryarwa.


Ya karasa ya gaisa da Baffa Surajo da matan Kawu har ma Kawun. Ya koma gefe ya zauna gefen Hussein.


"Ka yi hakuri mu ji ta bakinsa, ya riga ya zo kuma da iyalinsa baki daya, ka tuna, idan shi ne ya yi mana laifi, iyalinsa ba su da laifi tunda shi ne shugabansu."


Da kalamai irin haka Baffa da AlHassan suka taushi zuciyar Hussein. Ya yi shiru bai kara magana ba, wannan ya ba Kawu damar soma magana cike da jin wani tsananin kunya, wato wannan a duniya kenan ma, ina ga na lahira? Allah Ya tsaremu.


"Ku yi hakuri, ku yafemin. A ƙiyayyar da na nunamaku har da sharrin zuciya da shaidan. Na sani, Innarmu a baya ita ce kan gaba wurin ƙara rura wutar ƙiyayyarku a zuƙatanmu, sai ya kasance ni abin ya zame min ciwo domin kuwa ya juye zuwa hassada da tsana. Ban ƙara jin tsanar Amina da Aminu ba, sai bayan auren Amina da mutumin da nake ganin ban kama ƙafar arzikinsa ba. Wato dai Marigayi Naziru, ban kuma gama farfadowa daga wannan bakin cikin na ci gaban da Amina ta samu ba a rayuwa, sai ga Aminun da muke tunanin ma ya mutu, ya dawo. Tun kan ya zo Kano wurina, labari ya riskeni, na yi bakin ciki sosai, Karime kanwarmu ta fadamin da murnarta ni kuwa ban ga abin murna ba a dawowarsa musamman da naji labarin ai rayuwa ta mishi kyau ya dawo har da matarsa da kuma yaransa ƴan biyu. A wannan halin sai ya kawomin ziyara duk kuwa da tarin kiyayyar da nake mishi, sai dai na gasamishi baƙaƙen maganganu wanda har ya mutu a lokacin ban yi dana saninsu ba sai ma dadi da naji a lokacin ganin ya bar min filin duniyar na ci karena babu babbaka."


Kawu ya numfasa saboda kukan da ya shaƙe shi, iyalinsa da su Dada kuka suke yi cike da mamakin irin wannan salon ƙiyayyar da bawan Allahn ke yiwa ɗan uwansa na jini. Shi kuwa Hussein ba zai ce ga yanayin da yake ciki ba, sai dai ko kallon Kawun ba ya son yi.


Kawu ya ci gaba da magana bayan ya sharce majina.


"Bayan shekaru da dama, a wani ziyara da Amina kika sa Husseini ya kawomin, lokacin ya samu hutun karatun da yake yi a Dubai. A wannan zuwan ne yaron ya ban tsoro har nake ganin nan gaba zai iya cin mutuncina a gaban ko su waye. Saboda tunda nake da ke da Aminu, babu wanda wuyansa ya taɓa yin tsaikon da zan faɗa ya faɗa, sai Husseini, ko Hassan bai taɓa yimin cin fuskar da nake ganin Husseini ya yimin a lokacin ba. Wannan ne dalilina na farko da na ci alwashin sai na tarwatsa rayuwar Husseini. Sai ya rasa dukkan farin cikinsa. Sai dai me? Kafin na kai ga aikata duk wani abu da na yi niyya, na samu labarin ɓacewar Husseini, ya gudu ya bar gida ba'a san inda ya shiga ba. A lokacin idan ka tona zuciyata banda tsananin farin ciki babu abinda na ke ji, har addu'a nayi Allah Ya dauki ransa ma. Bayan watanni uku da ɓacewar Husseini, wataranar lahadi ba ni mancewa, ni da kaina ke tuƙi a mota daga kasuwa zan koma gida, a hanya na hangi wata tsohuwar kwastama ɗita, a baya takan zo ta sararwa Hajiyarta atamfofi a shagona ko kuma yadika na maza ta tafi, a sannan tana budurwa ko kuma nace mace mai zaman kanta amma a karkashin ikon wata Hajiya mai safarar yara zuwa Makkah da sauran ƙasashen waje don aikatau ko akasin haka. Zeenatu kenan, tun a baya Hajiyar ta sha aiko ta shagona tun ban kai ma ga auren ita Maimuna ba, (Anti Amarya), tun a wancan lokacin muka saba, nakan ba ta shawara akan ta yi aure gudun kar ta ɓata rayuwarta don ni nasan wace ce Hajiya Balki uwar ɗakinta, saboda na sha zuwa gidan muyi cinikin kaya ta siyawa ƴan matan yaran da ke gabanta ko kuma ta siyar, na kuma san irin kalar sana'arta. Daga baya kuma sai na bar ganin Zeenatu, sai wata Raliya ake turowa. Koda na tambayi Raliya, ta bani tabbacin ai Zeenatu ta tafi Makkah, a sannan na ji ba dadi kwarai don ban so ta cuci kanta ba sai dai dama daga yanayin Zeenatu na fahimci maganata ba wani shigarta ya ke ba."


Kawu ya numfasa, nan kuma dai dakin tsit ya yi babu mai kuka sai jin wannan labarin mai ban mamaki daga bakin Kawu. Ya ɗora zancensa.


"Ganin da na yiwa Zeenatu a haɗaɗɗiyar mota, bai sa na kasa ganeta ba, asalima fuskarta ko kaɗan ba ta sauya ba duk kuwa da ɗumbin shekarun da aka ɗiba. Parking ta yi a gaban wani katafaren shagon siye da siyarwa na maƙulashe, na juya kan mota da sauri na faka a gefenta. Sai dai ban kai ga fitowa ba, idanuna su ka sauka akan Husseini, ba karamin razana nayi ba, sai nake ganin abin kamar a mafarki, fuskokinsu kadai ya nuna suna cikin tsantsar farin ciki. Ban karasa ba, har suka shiga suka fito, mantuwa suka yi ko mene? Ban sani ba, na ga Husseini ya fita ya koma ciki, har zan je wurinta sai naji tsoron kada ya fito ya gan ni, sai kawai na koma cikin mota na jira har ta tashi motarta ta kama hanya ta bar wurin, na bi su a baya har suka isa gidansu. Koda na ga gidan kawai sai na juya da zummar zan dawo na same ta don ba na kaunar Husseini ya gan ni. Bayan kwanaki biyu, a wani yammaci na isa kofar gidan, cikin saa na isketa tana kokarin shiga cikin kyauren, ganin ita kadai ce na yi hon ta juyo, ni kuwa na ja na tsaya na fito. Ta shiga bi na da kallo kamar na neman ƙarin bayani da kuma son tuna inda ta san fuskar, nan take ta tambaye ni. "Kamar na sanka." Na ba ta amsa da eh, kafin na ce kin manta Modibbo na Kwari? Nan da nan ta saki fuska muka kara gaisawa. Na ce "Yaushe kika dawo?" Nan ta ke sanarmin ai ta kai shekara guda da dawowa, daga nan kuma na nemi mu keɓe don mu tattauna wata muhimmiyar magana. Sai dai na tambayeta ko akwai wani saurayinta a ciki? Idan akwai na juya. Ni kuma na dadi haka don na gane irin zaman da suke yi da Husseini, burina ta cemin ba zaman aure ba ne.
Abin ya ba ta dariya. "Aa ai kuma yanzu an girma da wannan kalar rayuwar, aure nayi." Na jinjina kai ina murmushin da bai kai zuci ba don ba haka na so ba. Sai dai ina bukatar mu zauna na ji bayani sosai. Koda muma shiga ciki, ta sanya aka kawomin lemo da ruwa, abinci kuma na ce aa. Bayan mun nutsu na kara kai duba ga hoton Husseini da ita wanda tun shigowata ya dauken hankali, shakka babu aure ne suka yi. Anan na sanar da ita gaskiyar alaƙarmu da Husseini, a farko ta razana sosai har ma ya ɗaure fuska tamau. Nayi dariya sosai na ce ta kwantar da hankalinta ina bayanta domin ba na shiri da iyayensa, don haka ni ko nan da bangon duniya ma tana iya kai Husseini muddin ba za'a gan shi ba. Faɗin hakan keda wuya ta kwantar da hankalinta saboda na biyomata ta sigar da dole ta samu nutsuwa. A karshe ta ban labarin duk yanda aka yi na dinga dariyar mugunta. Ni kuma na yi mata alƙawarin ko na ji ana raɗe-raɗin an gan shi zan sanarmata, zan kuma yi asirin da zan rufe bakin duk wanda naji yana raɗe-raɗin ya ga ko mai kamarsa ne a kwaryar Kano. Na kuma kara mata da cewa dole tana bukatar asirin da zai kara jin nan duniya ya tsani a tayar da zancen danginsa ko a tambayeshi, amma ta bar komai a hannuna. Wannan ne abinda na san na aikata, ya kasance ana neman Husseini, ni kuma nasan inda ya ke, amma na yi gum. Shiyasa koda Ramlatu ta zo da zancen Husseini, na kore ta na ce ba ruwana. Ban yi ƙasa a gwuiwa ba na sanar da Zeenatu, nan muka ce kawai a kashe ta yanda babu wata hanya da za'a san labarin komai. Sai dai kuma abinda Allah Ya riga ya tsara, ba wanda ya isa dakatar da shi."


Kawu Modibbo na kaiwa nan ya dakata ya ci gaba da kuka sosai. Falon banda salatin da Baffa Surajo ke maimaitawa cikin zubar hawaye, ba ka jin komai sai sheshshekar kukan yaran Kawu Modibbo.


"Ku yafemin, ku yafemin don Allah. Na tsaneku akan ba ku aikatamin komai ba, na cutar da rayuwarku. Na hana yarana zumunci da ku duk don bana kaunarku. Ku yafemin. Husseini ka yafemin, Aminatu, Hassa.."


Ya kasa ci gaba saboda kuka, Hussein kawai miƙewa ya yi ya bar falon, Baffa ya yi nasiha mai ratsa jiki gami da nuna ladan da ke tattare da wanda ya yi hakuri. Dada nan take ta yafemasa, ta ce komai ya wuce, hakanan shima AlHassan. Wannan abu ya yiwa Kawu da iyalinsa dadi, itama Hajja Fatuma ta nemi gafarar Dada na yanda ta dinga wulakanta ta ita mai miji dadi, Dada na murmushin da ya fi kuka ciwo ta ce babu komai ya wuce. Haka dai aka yi ta neman yafiyar juna. Taheer sai satan kallon Hafsat ya ke, ita kuwa gaba daya kunyarsa ta ke ji, a gefe guda tausayi da kaunar dan uwanta Hussein ya kara mamayeta, wato dai shi ya san dalilinsa na tsanar Kawu. Ashe mugun abu ya ƙulla masa har haka.


***
Ramlat da ba ta san hawa ba ba ta san sauka ba, ta ga mutum ya fado falon, kallo daya ta yi mishi ta gane ba lafiya. Ya zube saman kujera ya runtse idanu, fuskarsa abinka da farar fata ta koma jawur da ita. Ta shiga ambaton Allah a ƙasan ranta, miƙewa ta yi ta zauna gefensa, ba ta ce komai ba amma ta kamo tafin hannunsa ɗaya tana murzawa a hankali, a ranta addu'oi kawai ta ke karantomasa. A hankali kuma ya shiga sauke ajiyar zuciya, ya bude jajayen idanunsa ya dubeta. Sai da ta ji gabanta ya fadi, gaba daya sai ta tsinci kanta cikin damuwa mai tsanani.


"Lafiya Haskena?"


Gyara zama ya yi, bai ɓoyemata duk abinda ke faruwa ba, kawai sai ta shiga hawaye tana mamaki da tsoron lamarin mutum. Idan naka ya yi maka haka, ina hujjar da za ka ji haushin wani don ya yi maka? Sai kuma ta fahimci kuskurenta, hawayen ba zai ƙarar da Hussein da komai ba face ya kara ganin girman laifin da Kawun ya mishi har ya kasa yafemasa. Don haka ta yi azamar sharesu, ba ta kai ga magana ba sai ga AlHassan ya yi sallama ya shigo, Dada tafe a bayansa. Ta mike da sauri tana musu sannu da zuwa, Allah Ya taimaka ma tun fitarsa ta suturta jikinta sakamakon shanyar da ta kwaso a bayan gidan wurin shukoki. Ta gaida su Dada, Dada ta amsa fuska a ɗan sake. Sai dai itama fuskarta kamar na Husseini, ta yi ja, kuka kam ko ba'a faɗa ba sun yi shi, balle AlHassan.


Za ta shige ɗaki, Dada ta hanata, ta bata umarnin zama. Shiru ya ɗan biyo baya. A hankali kuma Dada ta shiga yiwa Hussein nasiha, sosai ta ke yi mai ratsa jiki tana kawomishi misalai na irin hakurin da Annabi s.a.w ya yi da yan uwansa da ma sauran mutane.


"Ka yi hakuri ɗana, ka yafemishi, idan ba ka yafe ba, da me zai ƙare ka? Me kake nema a duniya yanzu da Ubangiji bai maka ba? Babu shi, ka saka a ranka ba yanda ka iya, haka Allah Ya so ya jarabceka kuma Ya jarabta. Idan har na isa da kai, kuma har zuciyarka kana jin za ka iya yafewar, domin Allah muje ka fadi ya ji da bakinsa ka yafemasa."


Hussein wanda gaba daya jikinsa ya yi la'asar, ba shi da sauran kataɓus, miƙewa kawai ya yi suka fita tare da Dada zuwa sashinta. Ta ba Ramlatu umarnim biyo ta, hijab kawai ta sanya ta bisu a baya.


Kawu ya yi murnar sake ganin Husseini, da kansa ya mike jiki na rawa ya kasa gareshi ya rike hannunsa, kawai sai ya soma kokarin durkusawa yana kuka. Da sauri Hussein ya rike hannunsa ya ɗagoshi tsaye.


"Ya wuce Kawu, na yafemaka a bar zancen haka."


Ba wanda kalaman Hussein bai wa dadi ba, Ramlat ta gaishesu, itama dai gafararta Kawun ya nema, take kuma ta ce ba komai ya wuce.


Nan fa gida ya yi dadi amma Hussein bai wani sake sosai ba, sai da aka yi Magriba kafin su Kawu su wuce, Baffa Surajo ya ce lallai gobe duka a hadu a babban gida yana neman kowa da kowa. Ya bada umarnin a sanarwa wanda ba ya nan, na nesa kuwa a rabu da su. Da wannan komai ya wuce.


***
Washegari kuwa misalin karfe biyu, Baffa Surajo ya haɗa taron da kowa na zuri'ar Gidado dake a Adamawa ya hallara. Bayan addu'a da doguwar nasiha, ya ba Kawu damar neman afuwan yan uwansa. Nan Kawu ya ba kowa hakuri da kuma daukar alkawarin ba zai kara aikata ko makamancin hakan ba. Kowa ya ji dadin hakan kuwa, karshe kuma ya nemi alfarmar haɗa auren Taheer da Hafsat, nan take Dada ta ce ita ba ta da ja. Hussein zai yi magana ta harareshi, murmushi ya yi.


"Cewa zan yi an bayar." Maganar ta ba kowa dariya, Baffa Surajo ya yi mishi daƙuwa.


"Ai ba kai ke da alhakin bayarwar ba."
Bai ce uffan ba, Hafsat kuwa ai kamaran mata albishir da gidan aljanna.


***
MURFI....










I just published "BABIN ƘARSHE" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1035704431?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=ahGlFX6GFRN4rYLxQybIWR9WrkgGWE36szhMfA7kRFxFwQXwS03Sgp8YSmnHzMO1lgoFTgL30%2Brf0xbkWKei5hlm6ZnndGuZExstbOwboUAs%2BBmTygvZgHsBmhnEg64g






🕯️ *ƘARFEN ƘAFA* 🕯️

_Rufaida Umar_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.





*BABIN ƘARSHE*






ADAMAWA


BAYAN WATANNI BIYAR..


Amarya Ramlat ta kara kyau da ƙiba sai dai ba irin mai munin nan ba. Sanye take cikin doguwar riga na leshi lemon green an mata dinkin bubu, ta fito daga motar yayinda Hafsat da Rasheeda suka yi gaba niƙi-niƙi da kaya, ita kuwa tare suka jera da Kausar rike da wasu ledojin. Dawowarsu kenan daga kasuwa, zuwa lokacin sun yi nisa da shiryen-shiryen bikin Hafsat har ma da Rasheeda wacce za ta auri ɗan Barrister Hansatu (Babbar Yayar su Kawu Modibbo), Mujaheed.


Tun da suka rubuta jarrabawar karshe kasancewar tare suke tafiya da Hafsat a karatu, sai Rasheeda ta tubure ta ƙi zaman Kano, ta dawo gidan Adamawa wajen Dada ta yi zamanta. Wannan abu ya yiwa Dada dadi, wai yau ta budi ido ta ga jinin Kawu Modibbo a gidanta, kuma da son ran mahaifin, sai ta ji inama ɗan uwanta baban su Hussein na raye ya ga ranar da ya dinga ce mata za ta zo in sha Allah, ashe kuwan tana tafe.


Hamida babbar ƴar Dada wacce aure ya lula da ita har Saudiyya, ta jima rabonta da ƙasar don ko Ramlat tsakaninsu sai dai ta waya ko kuma idan ta kira Hussein videocall suke gaisawa. Ta dube su da kulawa tana ba karamar ɗiyarta Mama.


"Sannunku da zuwa. Kun sha wunin kasuwa."


Suka yi murmushi lokacin da kowa ke kokarin zama.


"Wash!" Fadin Hafsat tana mai kwantar da kai jikin Dada. Ture ta Dada ta yi.


"To raguwa, ni matsa ki ban wuri. Gwara ma ki tattara ki bar gidannan ko na huta."


"Aa Dada, ina hutu ba kya ganin Auta? Faɗa dai ki ke yi."


Cewar Adda Zahra, mai bi wa Hamida, ita a Lagos ta ke da zama.


Aka yi dariya. Haka kuma aka shiga bude kaya ana ganin siyayyar da suka yi na abinda ya yi saura na tarkacen kayan girki har ma da sauran kayan kicin da ba'a siya ba. Sosai an yaba da kayan, sai da suka ci abinci kafin Ramlat ta koma sashinta. Wanka kawai ta yi don wani irin zafi ta ke ji, ta sanya kananun kaya riga da siket marasa nauyi kafin ta faɗa kicin. Lissafi ta shiga yi a ƙasan ranta, su Rafee'ah bai fi saura kwanaki shida su zo ba saboda biki. Ta ƙagu ta ga yaranta da kuma Aisha da babynsu. Ta shafi cikinta kaɗan tana murmushi, tana burin Allah Ya ba ta haihuwa ko don ta ga kalar farin cikin Hussein wanda yanzu koyaushe ba shi da zance sai na baby, baby. Haka dai Ramlat tana aiki tana tunane-tunanenta. Sai da ta yi nisa, sai ga Kausar ta shigo, itama kam ciki ne da ita wata uku. Sallama ta yi mata akan za ta tafi, har ƙofa ta yi mata rakiya.


"Kai aa ki koma hakanan, ga mijinki can na baro sashin Dada, idan ya ganki haka kin fito ai ni zai ɗorawa laifi."


Ramlat ta yi dariya, sai yanzun ta tuna da kalar suturar dake jikinta. Ko ba komai daga rigar mai hannun vest har siket din wanda yake dogo amma kamar roba, duk sun matse ta.


"Toh Maman Twins, Allah Ya saukeki lafiya. A gaidamin da Fatina sosai."


"Twins dai yana jikinki Madam, amma ba ni ba. Ki bar yimin wannan fatan. Fati kuma za ta ji sosai."


Ramlat abin ma ya ba ta dariya, tana mamakin yanda Kausar ke gudun twins. Ita kam da ace za ta samu tana son abinta. Anan dai suka rabu ta koma kan aikinta. Babu jimawa Gogan ya shigo. Ganin tana kicin kawai ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login