Showing 162001 words to 165000 words out of 231786 words
Chapter 55 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
fadamaka dama duk sadda maganar dangi ko ƴan uwa ta haɗa mu da Hussein ya kan shiga wani irin hali, ina kuma ga yau ya yi ido huɗu da ɗan uwansa?"
"Hakane, sai nake ganin kamar ba na asibiti ba ne."
AlHassan ya faɗi bayan kai karshen nazarinsa.
"Hisham, ya jikinnasa?"
Suka juya, Rafee'ah ce. Ta karaso suka yi mata bayani.
"Allah Ya ba shi lafiya. Kada ku damu, Hajiya ta aika a karɓo ruwan ganyen magarya mai addu'o'in karya sihiri, da yardar Allah komai zai daidaita."
AlHassan ya sauke ajiyar zuciya yana ɗan murmushin jin dadi da wani irin kaunar zuri'ar da ke kara mamaye zuciyarsa.
"Na gode kwarai, Allah Ya sakamaku da alheri. Allah Ya bar zumunci."
Ta yi dariya kadan.
"Ameen. Ai yiwa kai ne. Bari na koma, dama Hajiya ce ta ce na sanarmaku sannan na gano halin da yake ciki don marar lafiyarmu ta tashi hankalinta sai kuka ta ke yi."
Murmushi AlHassan ya yi yana mai hasashen wani abu da tun a jiya ya yi zaman dirshan a kwakwalwarsa.
***
TA FARU TA ƘARE...
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Halimar aka kama?!"
Hajiya Zeenatu ta faɗi tana tsaye a bakin ƙofar gidan Kakar Halima wacce ke rike da ita. Ƙanin Halima uwa daya uba ɗaya wanda daga ita sai shi, su uku iyayensu suka haifa kafin rasuwarsu, dayayar Halima, Halima sai Yusufa. Kakarsu ta karɓi riƙo. Yusufan ya share hawaye yana duban Hajiya Zeenatu.
"Wallahi ranki ya daɗe, ɗazu aka yi mana waya, naje har ofishin ƴan sandan na sami Aunty Halima, wai dumu-dumu aka kama ta da bindiga za ta yi kisa. Wannan abu ne da ko a mafarki ba mu zaci faruwarsa ba. Su biyu aka kama, shi ɗayan ko Gwaska ko wa? Yana asibiti. Yanzu Kaka na kwance ba lafiya tun da ta ji halin da ake ciki."
Hajiya Zeenatu wacce ta yi mutuwar tsaye, ta yi sauri ta dawo hayyacinta. Baki na rawa ta ce.
"Ta..ta..faɗi wadanda suka sanya ta?"
Kallon da Yusufa ya yi mata na nazari sai da ya sa ta sakin ƙaramar tusa mai haɗe da fitsari ba shiri. Ya girgiza kai.
"Abin kunya ne ace saboda ɗa namiji za ta aikata hakan. Kishi ne kawai don uban gidansu na aiki zai auri abokiyar aikinta Ramlat. Haka ta sanarmin."
Ya karashe da wani irin jin kunya. Ajiyar zuciya Hajiya Zeenatu ta sauke ta juya za ta shige mota.
"Amm..Hajiya, na ce sai dai ban sanki ba. Kema wurin aikinta ki ke ne?"
Ta juyo.
"Eh, tare muke aiki." Tana kaiwa nan ta juya da sauri ta faɗa mota, ta ja. Kiyayewar Ubangiji ce kawai ta isar da ita gidan Hajiya Batool. Itama nan ta iske ta su na dambe da surukarta. Dakyar ta raba su. Ɗan Hajiya Batool ba ya nan ya yi tafiya Dubai, shi ne surikar ta zo gidan kwana.
"Haba Hajiya, me ya yi maki zafi za ki tsaya dambe da suruka? Ke kuma don ba ki da kunya wannan ba uwar mijinki ba ce?"
Fareeda wacce ke tsaye tana huci ta narkawa Hajiya Zeenatu uwar harara kafin ta saki dariya gami da tafa hannu.
"Ahayye! Ai fa da yake daga ke har ita jirgi ɗaya ya kwaso ku dole ne ki ga laifina! Tsoffin banza da ba su riƙe girmansu ba ai ba zan ji kunyar taka su son rai ba. Kin tauye hakkin yaro kin danne kina zaune da shi! Ko an fadamaki bani da labarin mijinki? Kina kai min uwar miji yawon bin bokaye don mijina ya ƙara aure ko? To wallahi karyar ku domin tun kan a haifi uwar mai sabulu balbela ke da farin kai. Don haka idan ku na son na lulluɓe dukkan sirrikanku to ku tabbatar an fasa batun auren Mijina da kowace shegiyar kucaka. Idan kunne ya ji..." Ta ƙarashe da rike kunne kafin ta wuce tana dariya ta bar su baki galala. Bayan shigewarta ɗaki Batool ta yi gaba ta haye sama, Hajiya Zeenatu ta bi ta a baya. Su na shiga ɗaki suka sa mukulli.
"Batool akwai matsala!"
Hajiya Batool da ta zauna rike da ƙugu tana ambaton wash sakamakon cizon da ta sha a wurin Fareeda. Ta amsa wa Hajiya Zeenatu kamar za ta yi kuka.
"Matsala nima cikinsa kika tarar da ni Zeenatu. Kamar Gora yaudararmu ya ke yi yana cin dukiya a ɓagas. Ni na rasa kan wadannan lamuran."
Hajiya Zeenatu ta yarfar da jaka da mayafi, da sauri ta faɗa banɗaki. Can kuma ta fito ta zauna tana sharce gumi. Ta kora dukkan bayani ga Hajiya Batool gaba dayanta a rude.
"Ya zan yi ne Batool? Ga Visa ta yi wuya an ce mu kara hakuri zuwa sati na sama, ga wannan lamari na neman kwaɓemin? Ba mu ga ta zama ba Batool, ta inda aka hau dai ta nan ake sauka idan ba haka ba mai afkuwa za ta afku. Ba ni da tabbacin Halima ba za ta tonamana asiri ba. Ban san iyakar lokacin da za ta riƙe sirrinmu matsayin sirri ba. Wannan fa barazana ce garemu. Tashi za ki yi mu kama ƙafa muje mu ga Gora tun kafin komai ya lalace."
Hajiya Batool ta share hawayen takaici, yau ita suruka ke dambe da ita, ta rantse sai ta ga bayanta tunda dama ba ta haifarmata ko ƴartsana ba sai afkin ci da kasayarwa.
"Muje. Bari na lallaɓa."
Ta miƙe dakyar ta dauki gyalenta. Suka fice. Fareeda na leƙensu ta window ta yi dariya ta saki labule. A fili ta ce.
"Munafukan banza, da alama an tafi yawon abinda aka saba. Zama daram ni Fareeda!"
Ta furta tana mai zama kan gado tana dariya.
***
Tunda Hajiya Zeenatu ta sanarmasa da batun kama Halima ya gaza samun nutsuwa. Don haka ya kira Dada a waya karon farko. Hakan ba karamin mamaki ya ba ta ba don har sai da ta ce.
"Yaya lafiya dai ko?"
"Ah lafiya kalau mana Amina, ba damar na kira ki kenan sai idan babu ita? Mtsw. Ina yaran nan kuwa? Husseini? Yana gari?"
Dada ta amsa a sanyaye.
"Aa, ya shigo nan Kano wani uzuri na ma'aikatarsu, bai ƙaraso nan ba?"
Wani zufa ya karyowa Kawu a goshi, ya samu wuri ya zauna ɗabas! Sai ya ɓige da faɗan borin kunya.
"Ina na isa dama ya zo wurina? Ai ban isa ba! Kin koyawa yara tsanata da tsanar iyalina. Sai ki yi idan hakan zai haifarmaki da ɗa mai ido! Mu din dai mu ne nasu."
Daga haka ya katse wayar bai saurari ban haƙurin Dada ba. Miƙewa tsaye ya yi yana sunturi, ba zai yiwu ba. Babu abinda zai ruguza dukkan sirrinsa. Idan ya tabbata lamarin Hussein ne ya kawo AlHassan garin Kano kamar yanda Bokansa ya buga ƙasa ya bincikamasa, toh shakka babu komai ya rushe. Tonuwar asirinsa kamar jin kunyarsa ne a cikin dangi, ya san duk tsanar da sauran yan uwansa suka yiwa jinin Aminu da Amina (Dada), bai kai tsanar da ya yiwa HUSSEIN ba.
Ya dau waya ya dannawa Hajiya Zeenatu kira, haka ya yi ta ringing ba'a ɗaga ba, wannan yasa shi kasa zama ya fice daga gidan don ƙara tuntuɓar Bokansa karo na ba adadi.
***
Ya mike zaune dakyar daga saman gadon da yake kwance. A hankali ya dafe kai yana salati.
"Sannu Hussein, ka tashi?" Ya dubi mai maganar da sauri, shi dai wanda ya gani a ɗazun ne mai kama da shi. Ɗan uwansa da ya daina sanyawa a idanu shekara da shekaru. Ƙuri ya yi mishi da idanu, daidai nan Hisham ya miƙamasa kofin ruwan tofi.
"Shanye duka please." Ba musu ya karɓa ya shanye tas. Kamar yanda jini ke zagaye a cikin jiki, haka ya dinga jin ruwan na zaga dukkan wata gaɓɓa ta jikinsa, a hankali hawayen da suka sauya kalar kwayoyin idanunsa suka samu damar kwaranyowa saman kuncinsa. AlHassan ya taso ya zauna a gefe gami da sanya hannu cikin nasa.
"Hussein, ka gane ni?"
Gyada kai kawai yake yi bakin na rawa amma kalmar A ta kasa fita daga bakinsa. Kawai sai ya ɗora hannunsa haɗe da na AlHassan saman goshi ya shiga kuka kamar ransa zai fita. Hisham a hankali ya juya ya fita daga ɗakin yana share kwallar dake kokarin zubowa a kokarinsa na katse ta yana mai hamdala ga Mahaliccin Sammai da kuma Ƙassai.
"Na gane ka. AlHassan Aminu Gidado."
Hussein ya furta da kakkarwar murya, jin haka AlHassan ya ƙara jan sa a jiki shima yana kukan. Zai so ace Dada na zaune a dakinnan, matar da idanunta ba su taɓa kafewa da zubar hawayen rashin Hussein ba. Kullum kiranta, amanar Allah ne su din a hannunta, koyaushe ɗorawa kanta laifin ɓatan Hussein ta ke yi.
"Ina Daa...da, Baba Naziru.?"
Hussein ya tambaya, AlHassan ya ɗago fuskarsa da wani irin murmushi mai haɗe da dariya-dariya.
"Dada tana nan, tana nan kullum cikin kuka da addu'ar Allah Ya nunamata kai. Babban burinta ta samu wani ko wata da zai kawomata kai koda labarin mutuwarka ne, ita dai ta san cewa ka mutu cikin musulunci kuma an maka kyakkyawan sutura. Da yawa ya faru bayan gushewarka Hussein, abubuda da dama sun faru garemu da baki bai isa ya buɗamaka su ba."
Hussein ya jinjina kai yana jan hanci.
"Eh, da yawa ya faru. Irin yawan da ban taɓa kawo wa kaina a rayuwa ba. Ban sani ba ko ni na jazawa kaina ko kuwa dai.."
Rufemasa baki AlHassan ya yi yana girgiza kai.
"Kar ka ce komai ɗan uwana, ka yi shiru mu ƙara godewa Allah da ganin wannan ranar da muka kwashe shekaru muna jira. Haɗuwa da Ramlatu alheri ne garemu baki ɗaya. Ina zan manta da ita da zuri'arta?"
Hussein ya ci gaba da dubansa da idanunsa da suka kaɗa. A idanun AlHassan ya gano karin bayani ɗan uwannasa ke nema. Murmushi ya yi.
"Mai hali ba ya fasa halinsa, ashe ba ka sauya ba?"
Suka yi dariya gami da ƙara rungume hannun juna gam! Kamar ance ga wani abu zai ƙara raba su. Tirya -tiryan ya ba shi labari tun daga haɗuwarsa da Ramlat har zuwa yanzu da aka harbe ta sanadinsa. Hussein ya yi shiru, ya rasa me zai ce. Ya kuma rasa wane yanayi ya ke ciki, tunani sosai ke neman shigarsa don haka ya gaggauta yanke tunanin.
"Mu je na ganta don Allah."
Ba musu suka mike, ya zura takalmansa, bini-bini za su kalli juna shi da ɗan uwansa su yi murmushi, haka suka jera idanun jama'a a kansu don ba karamin burge su suka yi ba musamman masu juna biyu, nan suka fara addu'ar su ma Allah Ya basu ƴan biyu masu bala'in kama irinsu, su gan su sun girma haka tare.
***
Gora ya duba, ya ƙara buga ƙasa ya duba, ya ɗago kai ya kalli Hajiya Zeenatu da Hajiya Batool da ke zaune gabansa cike da wani fargaba da tsoro.
"Lafiya dai?" Zeenatu ta nemi sani.
Ya girgiza kai ya ƙara maida hankali ya yi buge-buge da rubuce-rubucensa. Can ya ɗago ya dubesu yana sharce gumi.
"Bana jin akwai sauran duhu da yanzu haske bai mamayeshi ba a rayuwar mijinki. Yanzu haka maganar da nake maki yana tare da ɗan uwansa. Gaskiyar magana babu sauran asiri a jikin yaronnan. Da alama akwai wanda ya tsayamasa." (Allah Ya raba mu da aikin jahilci da jahilai. Ya kiyayemana imaninmu. Ameen).
"Na shiga uku na lalace ni Zeenatu!" Ta dora hannu a kai ta kurma ihu da kuka.
"Na fadamaki ai! Duk ranar da ya yi tozali da abokin haihuwarsa aikinki ya rushe. Ko kin manta wannan gargadin? Toh bari ki ji, akwai wani babban bala'i da ke tunkaroki daga ke har Batulu, ina mai gargaɗinku akan ku gaggauta barin garinnan kafin komai ya ida lalacewa. Wallahi kun ji na rantsemaku, taku ta kare domim ruwa ya ƙarewa ɗan kada!"
Gora ya na kaiwa nan ya mike ya gyara zaman malun-malun hadi da ɓantalar goro ya hau tauna. Da wani irin tsalle Hajiya Zeenatu ta miƙe ta shaƙe wuyansa ya hau kakari.
"Karya ka ke wallahi! Karya ka ke! Nawa na kashe?! Har kabari na tona! Hatta da jariri nayi amfani da shi duk akan Husseini! Karya kake ka ce duka wannan aikin ya tashi a banza Gora! Dole ne ka nemomin mafita idan kuwa ba haka ba wallahi sai na kashe ka!"
Gora wanda ya ji shaƙa dakyar ya iya ɓanɓare hannun Hajiya Zeenatu daga wuyansa. Bai yi wata-wata ba ya kwaɗamata lafiyayyen mari da rawar hannu ya hau nunata da yatsa.
"Ni ki ke kokarin kashewa? Yau sakamakon da za ki yimin kenan? Shegiya ƴar zina! To ki sani kin taɓowa kanki tsuliyar dodo, yanzu kika soma ganin bala'i da masifa! Babu ke ba jin dadi a rayuwa wallahi. Ni na miki wannan alƙawarin."
Jin haka ta ƙara daka tsalle ta shaƙe wuyansa ta hau bori, ga hawaye caɓe-caɓe ga zani na neman kuncewa sanadin jijjigar da ta ke yi. Tana faman ikrarin ko mutuwa ta yi kaɗan ta raba ta da Hussein. Hajiya Batool ta yi iyakar yinta amma ta kasa kwatar Gora don haka ta bazama rumfar da matan aure da karuwai har ma da ƴanmatan ke bin layin ganin Gora, ta nemi ɗoki. Nan da nan suka bazama aka shigo dakyar suka kwaci Gora wanda tuni ya galabaita har ya suma. Ruwa aka watsamasa ya farfaɗo. Idanun na kyarma ya shiga nuna Hajiya Zeenatu.
"Za ki yi dana sanin wannan yunƙuri da ki ka yi na kashe ni Zeenatu. Sai na nunamaki waye ni! Na fi karfin wulakancinki!"
"Hoo! Shege tsinanne wanda ba ya kallon gabas! Ni Zeenatu baƙar ashana ce! Ka san tarihina ka kuma san asalina! Babu uwar da ban gani ba don haka ka shirya! Sai na ga bayanka da karyar bokancinka. Ba wanda ya isa ya raba ni da Hussein! Wallahi sai na kashe ko waye!!"
Da haka Hajiya Batool ta janye ta suka bar wurin zuwa mota. Hankali a tashe Hajiya Batool ke tuƙi, Allah Ya taimakesu gilashin mai duhu ne sosai ba'a ganin haukar da Hajiya Zeenatu ke yi. Ita Hajiya Batool ma ta fi ta kwanciyar hankali. Ita dai Hajiya Zeenatu kira ta ke sai ta kashe AlHassan da ma Ramlatu idan hakan ne kadai hanyar da za ta rayu da Husseininta!
***
Tana zaune daga ita sai Rafee'ah da Amrah, Hunainah da Zulaihat sai Muniru. Hajiya ta wuce gida wanka da ɗan runtsawa. Hira suke yi amma ita kam tana zaune ko abincin da aka zubamata ta kasa ci, hankalinta na kan Hussein. Kwankwasa ƙofar da aka yi ce ta sa da sauri ta dubi ƙofar. Amrah ce ta mike tana gyara lulluɓi ta buɗe. Basu damar shigowa ta yi baki sake tana ƙara kallon tagwayen masu tsananin kama. Bambancin kaya da gilashin AlHassan ne kawai ya raba su. Hisham ke bayansu.
Idanun Ramlat ya kasa ɗaukewa a kansu, ta kuma kasa tsaida hawayen farin ciki. Kawai sai ta shiga murmushi ga hawaye na zuba.
I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/97Mzs8D3Qcb
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
49)
Gaisawa suka yi da Munir yana ƙara taya su murnar daidaituwa.
"Allah Ya kara kiyayewa, Ya yi sakayya" Cewar Munir. Da murmushi ƴan biyun suka amsa da amin. A hankali ya kai duba ga Ramlat, ganin haka ta yi saurin sunkuyar da kanta. Ya maida idanunsa ga ƴan ɗakin, kafin waninsu ya kai ga cewa wani abu, an ƙwanƙwasa ƙofar. Hisham wanda ya fi kusa da ƙofar ya buɗe. Chairman Aliyu Dikko ne tsaye daga bayan masu kula da lafiyarsa biyu, yana aikin gyara zaman malun-malun dinsa.
"Assalamu alaikum. Don Allah nan ne ɗakin da aka kwantar da Ramlatu Khalid?" Faɗin ɗaya cikin security din da suke tare. Hisham ya dubesu, yanzun ya gane ko wane. Kofar gaba daya ya buɗe. Suka dubeshi, Ramlat nan da nan ta haɗe fuska gami da gyara zaman mayafin da ya ɗan rufe jikinta. Hussein ya harɗe hannu a kirji yana kallonsa kamar yanda shima Chairman ya yi musu ƙuri da idanu. Ya kalli AlHassan kuma ya kalli Hussein ɗin wanda bambancin sutura da kuma gilashi kadai ya sa ba zai iya rantsuwar mutum guda ba ne. Ya daure ya dake yana mai miƙa hannu a yi musabaha, Munir da AlHassan duk suka miƙa banda Hussein wanda ya kauda kai, fuska a ɗaure ya dubi ɗan uwansa.
"Muje ko?"
Yana kaiwa nan ya fice daga ɗakin, ganin haka da yawa cikinsu ma suka fita, ya yi saura daga Ramlat sai Chairman. Ya zauna saman kujera gami da ba ƴan rakiyarsa umarnin tsayawa daga waje.
"Sannu Baby, ashe kuma harbinki aka yi? Su waye wadannan?"
Tun Baby da ya kira ta da shi, ta ji gabanta ya yanke ya yi wani irin faɗuwa, ba wanda ya faɗomata a rai sai Aliyunta. Ta yi mishi addu'a a ƙasan ranta kafin ta ƙara yin ƙasa da kanta, har dai ya kammala ɓaɓatunsa ya mike ba ta ce mishi uffan ba sai da ta ga ajiye bandir na ƴa dubu har biyu a gefenta.
"Bana so, ka ɗauke abinka."
Ta furta a kausashe. Ya yi murmushi.
"Haba Baby..."
"Kar ka ƙara kirana da wannan sunan!"
Ya jinjina kai.
"Na ji, lokacinki ne yanzu, ki yimin duk abinda ki ka yi niyya. Nan ba da jimawa ba za ki koma ƙarƙashin ikona."
Ta ja guntun tsaki, ya gyara zamam rigarsa ya fice. Ba jimawa da fitarsa su Amrah suka dawo ɗakin.
"Yau naga ikon Allah, wannan shi ne ƙarfin hali wai ɓarawo da sallama. Mutumin nan ba zai gaji ya kyaleki ba?"
Faɗin Rafee'ah tana ɗaga kuɗaɗen da Chairman ya ajiye. Kafin Amrahbta ce wani abu aka ƙara ƙwankwasa, da sauri Rafee'ah ta ajiye kuɗin. Ɗaya daga cikin abokan tafiyar Chairman ne, manyan ledoji ne har uku ya shigo da su. Ya ajiye.
"Ranki ya daɗe, Alhaji ya ce a miƙo. Allah Ya ƙara lafiya." Har zai juya Ramlat ta dakatar da shi.
"Maida."
Ya yi murmushi.
"Ki yi hakuri Ranki Ya Daɗe, ban isa na ketare umarninsa ba. A dai yi hakuri a karɓa."
Daga haka ya kama ƙofa. Za ta ƙara magana Amrah ta girgizamata kai, dole ta haɗiye gami da yin ƙwafa.
"Ki rabu da shi, ba laifinsa ba ne tunda dai shi ɗan aike ne. Allah Ya kyauta. Amma dai babu alamar mutuminnan zai saduda."
Amrah ta fadi bayan ya fice.
"Wai nikam Aunties, anya Hussein ba ya son Antinmu? Kun ga yanda fuskarsa ta sauya