Showing 117001 words to 120000 words out of 231786 words
Chapter 40 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
yi shiru kaɗan yana murmushi, har ta fidda rai zai yi magana can ta tsinkayeshi.
"Amma dai kin san ni mijin mace huɗu ne ko?"
Ta dara kadan.
"Um um, ban ga alamun hakan ba. Kai da aka kafamaka ƙahon zuƙa ana bi duk inda ka yi?"
Ya shiga jinjina kai gami da kaɗan yatsa jikin sitiyari.
"Ke ba'a kada ki a magana ko?"
Ya ba ta dariya.
"I'm sorry."
Ta furta kanta tsaye. Ya kai hannu ya dauki gilashinsa baƙi ya manna a idon, ta saci kallonsa, murmushi kawai ya ke dokawa da ya ƙara masa kyau. Wani ajiyar zuciya ta sauke. Ba ta ga baƙin Hajiya na kishin wannan haɗaɗɗen ba.
Har suka isa bai ƙara magana ba banda muryar Maher Zain da ya ƙaro a waƙarsa ta Thank You Allah. Nutsuwa sosai ta yi har da kwantar da kai jikin kujera tana sauraron waƙar. Koda suka iso Sharada, shiru ta yi ta zuba ido tana so ta gani ko zai gane gidansu. Ta sha mamaki ganin ya shiga kan layin. Kamar wancan karon ta juyo ta dubeshi.
"Zan sauka anan."
"Don me? Kar saurayinki ya ganni?"
Ya furta yana tafiya a hankali a dalilin ruwan da ya cika wurin. A raunane ta ce.
"Ni wallahi ba wani saurayi, kawai dai.."
"Kar ace ni saurayinki ne?"
Ya fadi wannan karon idonsa a kanta, daga cikin gilashin yake ƙare mata kallo. Ganin kamar kallon na ƙurillah ne ya sanya shi kauda kai ya maida bisa hanya. Ita ta ma rasa ta cewa. Ganin ya tsaya daidai ƙofar gidansu ne ta fahimci rannan dai ya gane gidan da ta shiga. Dubansa ta yi, ya fidda gilashin ya dubeta.
"Shikenan?"
Tsuke baki ta yi kafin ta bude motar za ta fita ta ce.
"Nagode Allah Ya saka da alheri."
Murmushi ya yi ganin tana shirin rufo ƙofar.
"Ji mana."
Dakatawa ta yi gami da duban ƙyauren gidan a tsorace sannan ta sunkuyo kanta ta dubeshi kamar ta yi kuka.
"Mene ne?"
"Ban mukullin motarki. Zan sa a kawomaki."
Ta ciro ba musu ta miƙa masa har da godiya. Dama burinta su saba yanda za ta tunkareshi da batun ƴan uwansa. Tasan kuma tana bukatar jin ta bakin Hisham ko akwai abinda ya sani shima.
Hannu ya kai ya ɗauko lemarta da ƙullin leda ɗaya na nama ya miƙamata yana faɗin.
"Idan ba so kike mu dawo gidannan da Madam ba, riƙe ki tafi da su."
A tare suka yiwa juna dariya, ta karɓa ta mishi wani irin kallo kwatankwacin wanda ta yi don baƙanta ran Hajiya.
"Itama ta san ni din ba kanwar lasa ba ce yanzu."
Ya ɗaga gira.
"Really? Idan kin yarda za ki maimaitan kallonnan a gabanta, shigo mu tafi."
Wani irin kunya ya mamayeta, ta yi saurin ficewa ta rufemishi ƙofar, ya lumshe idanu ya bude yana kallonta, dab da za ta shige gidan ta juyo ta ɗaya mishi hannu tana murmushi, ga mamakinsa shima ɗagamata ya yi, ta juya ta shige ciki shi kuma ya ja ya tafi duk jikinsa a sanyaye.
Kamar yanda mamaki bai bar shi ba hakanan itama ta ke ta mamakin kanta. Abin mamaki har ta shiga falon Hajiya murmushin ta ke yi.
Ta tarbi yaranta har da ɗaga Affan ta juya da fadin
"Oyoyo Babyn Mami."
Suna ta dariya ta karasa ta zauna gami da fadin wash.
"Sannu, amma kin jima. Mun yi waya da Rafee'ah ta cemin kin bar gidanta da wuri. Ina kika tsaya?"
Ta ajiye mayafinta a gefe bayan ta ajiye ledar a saman tebur, lema kuwa Ummi ce ta karɓe ta nufi ɗaki da shi.
"Mota ce ta macemin a hanya wallahi."
"Ya Salam, to yanzu ya kika yi?"
Murmushi Ramlat ta yi, fuskar Hussein ke yawo a kwayar idanunta.
"Abokin Hisham ne ya ganni, shi ya kawoni har ƙofar gidannan."
"Mijin Hajiyarnan?" Yanda Hajiya ta fadi ido waje sai ya ba ta dariya.
"Shi."
"Ai shikenan ke kika sani, ki yi ta jajiɓo yaronnan idan ta zo har gidannan ta jibgeki ba abinda zan ce."
Dariya ta yi.
"Ta jibgeni fa Hajiya? A gabanku?"
"Atoh, ai naga alamar kamar alaƙar taku ƙara yin gaba ta ke."
Jiki a sanyaye ta girgiza kai.
"A'a fa Hajiya, ba komai tsakaninmu wallahi banda mutunci."
Hajiya ta murmusa.
"Allah Yasa toh."
Ramlat ta basar da zancen.
"Ga nama nan ma ya siyamin."
Daga nan ta mike ta nufi ciki don sauya kaya sai dai maganar Hajiya ta ɗan shigeta. Dagaske sabo ke neman shiga tsakaninta da Hussein. Kamar kuma irin sabonnan da ba shi ta nema ba, irin wanda ba shi suka shirya da Amrah ba.
Ta kai hannu ta fiddo wayarta daga jaka, kai tsaye ta shiga whatsapp kan dp dinta. Hoton yaranta ne, Affan da Ansar sanye da shadda iri daya, hular Affan har goshi, Ansar kuwa ta zauna ɗas a kansa. Ummi daga bayansu ta dafa kafadunsu suna dariya kamar yanda mai hoton ya basu umarni. Murmushi ta yi ta shafi hoton tana tuna kalaman Hussein. Wato dai ya san tana da yara kuma ba ta da aure? Da alama a wurin Hisham ya nemi ƙarin bayani.
'Har zuciyarki ta soma saƙa wani abu akan wani ɗa namijin?'
Wani bangare na zuciyarta ya ankarar da ita, ta yi saurin kashe wayar ta ajiye gefe, rage kayan jikinta ta yi ta faɗa wanka. A ganinta wannan kuskure ne babba. Don haka dole ta yi takatsatsan, kyakkyawan jihadin da ta yi niyya kawai za ta aiwatar akan wadannan ƴan biyun. Daga nan babu komai!
***
Washegari safiyar Lahadi da misalin ƙarfe takwas na yamma, Malam Bala ya yi sallama a kofar falon. Ita kadai ce a falon tana taimakawa Ladidi da tsintar shinkafa, yara na ɗaki wurin Hajiya,ta amsa ta leka suka gaisa. Muƙulli ya miƙomata.
"Gashinan wani ne ya kawo ya ce a ba ki inji Yallaɓai, ga motarnan an shigo da ita ma."
Ta karbi mukullin.
"Ya tafi?"
Malam Bala ya amsa da eh. Ta mishi godiya sannan ta dawo ciki ta ajiye mukullin. Wayarta ta yi ƙarar shigowar saƙo. Ta dauka ta duba.
"Mota duk ta yi datti ba wanki, gashinan, za ki biya kudin wankinta."
Abinda aka rubuta kenan, wannan ya ba ta tabbacin har wankemata ya sa aka yi. Dariya ta yi kafin ta maida mishi martani bayan ta ƙare wa lambar kallo.
"Nagode Yallaɓai, Allah Ya bar zumunci."
Ta aikamasa kenan ta ga akwai saƙon da ya shigo ba ta ko lura ba. Hilal ne. Kirjinta ya fadi, idan ba ta mance ba yau an zarta sati da maganarsu, damuwa ta sauka saman fuskarta a yayinda ta karanta saƙonsa.
"Ban sani ba ko hidima ce ta miki yawa kamar yanda ta sha kaina har ban samu zuwa akan lokacin da muka tsayar ba. Ina fatan komai lafiya? A sanyamin ranar da zan zo idan ba damuwa."
Sauke ajiyar zuciya ta yi, ta rasa ma amsar da za ta ba shi. Ita ta sani, babu soyayyar bawan Allahn nan (Hilal) a ranta face tausayi da kuma ganin daraja da ƙimarsa. Ta yi addu'ar istihara sosai amma ba ta jinsa ko kaɗan. Ta rasa amsar bayarwa don haka ta ajiye wayar kawai ta ci gaba da aikinta.
Ita da kanta ta yi musu girki, shinkafa da miya. Tana kammalawa ta fito falon inda suke zaune ya yi daidai da shigowar Munir gidan dauke da yaransa. Daga ganin yanayin fuskarsa da irin daurewar da ya yi ka san cewa akwai matsala. Ya zauna yana gaida Hajiya a daure, ta amsa gami da jefamasa tambayar dake zuciyar Ramlat.
"Lafiya kuwa? Meyafaru na ganka da su Yasmeen?"
Ya shafi kai yana amsa gaisuwar Ramlat kamar ba ya so. Ya ba Yasmeen umarnin su shige ciki da su Ummi. Yasmeen ta ja ƙannenta uku suka ɗunguma gaba daya zuwa ciki. Da yake yarinya ce mai wayo, gaba daya itama fuskarta ta koma kalar tausayi.
"Wata ƴar hatsaniya aka yi da Bilkisu da Hunainah akan kawai yarannan su na shiga bangaren Hunainah. Ita yarinyar tana sonsu tana kuma jansu a jiki, toh ashe ita Bilkisu ranta na baci. Dama ba sau daya ba, kuma ba sau biyu ba ta ke nuna ba ta kaunar zuwan yaranta wurin Hunainah. Yau da na gaji don Yasmeen ta kwana sashin Hunainah shi ne ta kama yarinyar ta buga, ni kuma na yanke hukuncin zamansu a wurin Hunainah tunda abin haka ne, toh wai shi ne Bilkisu ta dauko wuka har da kai wa Hunainah yanka a kafaɗa ta yankamata hannun riga, wai ita ta rantse idan har na rabata da su za ta kashe Hunainah. Wannan ne dalilin da yasa ni kuma na korata gidansu na kwashi yaran na ce bari na kawosu nan idan ya so zuwa anjima sai na tafi da su. Haba! Wannan masifar ta ishe ni, Hajiya kusan kullum sai Bilkisu ta ɓullo da sabon rikici. Daga wancan sai wannan! Nikam gaskiya ta soma isata don zan iya sauwaƙe..."
"Kar ka fara! Nace kar ka fara! Idan ka yi ba da yawuna ba wallahi. Wane shashashan namiji ne zai saki matarsa ta farko kuma Uwar ƴaƴa? A'a kar na kara jin batun rabuwarnan a bakinka. Yanzu kai dama anan ba sai da na gujemaka irin hakan ba? Ban maka magana game da haɗa matannan gida ɗaya ba? Ka nunamin kai namiji ne da mace ba ta isa tankwarawa ba. Ai zaman lafiyar ake nemamaka. Toh ga irinta nan, tun ba'a je ko'ina ba ta soma yunkurin kashe baiwar Allah."
"Hajiya ɗan rigima fa ɗan rigima ne, koda ba gida ɗaya suke ba, sanin da na yiwa Bilkisu za ta iya takawa har gidanta. Toh Hajiya a hakan ma fa zargina take da rashin adalci ina kuma ace gidansu ba daya ba?"
Ramlat dai ta yi shiru tana kallonsa yanda duk ya fice a hayyacinsa.
Yanda aka banko labulen falon aka shigo yasa duk suka kalli kofar. Bilkisu ce buguzuzum da ita. Kalar mayafin daban da atamfar da ke jikinta. Da ganinta ka san ba'a nutse ta ke ba.
Kai tsaye wurin Munir ta tunkaro hannunta a ƙugu.
"Ka bani yarana tunda ba kai ka haifamin ba!"
Idanunta jage-jage da ruwan hawaye. A fusace ya mike Hajiya ta yi saurin riƙe hannunsa.
"Kai bana son hauka. Yi shiru abinki Bilki, zauna don Allah ki nutsu. Yaranki suna nan, kuma zan ba ki kayanki ki tafi da su."
Wani kwafa ta yi ta zauna tana kuka har da share majina. Ramlat ta mike ta yi ɗaki don ita takaicinsu ma ta ke ji. Mace ta riga da ta raina mijinta ko kadan ma ba ta ganin girmansa.
"Allah Ya kyauta." Ta faɗi a fili.
Kayan islamiyya ta fiddowa yaranta ta ba kowanne nashi kafin ta shiga shirya Affan. Har ta kammala ta fito ta zubamusu ruwa a robobi ta basu Hajiya na ta shari'a tsakanin miji da matar. Idanunta ya kai ga Bilkisu, wata uwar harara ta watsamata, ita abin ma sai ya ba ta dariya ganin ai ba ita ta kai zoman ba, ratayar ma ba'a ba ta ba. Hijab ta sanya don ta fi kaunar ta bar musu gidan wannan yasa ta dauki wayarta ta yiwa Hajiya sallama da zummar za ta kai su Ummi makaranta daga haka ta fice don hankalin Hajiyar ma ba ya gareta kawai ta amsa da jeki.
***
Koda ta miƙa yaran ta wuce gidan Umman Amrah. Ta saki baki ganin Zaituna.
"Wai Umma har yanzu ba su ɗauketa ba?"
Umma ta dara.
"Sun dauka mana, maidomin abata suka yi. Kusan tun bikin Muniru."
Ramlat ta murmusa.
"A'a wannan dai ta zama kishiyar ta gaske. A bar maki ita kawai."
Kama baki Umma ta yi.
"Wannan Babannata ne zai bar ta?Bari kiga nan kusa za ki ganshi ya zo daukarta. Yaran yanzu da shegen son ƴaƴa, wa ya sani ma ko ita ke turoshi."
Dariya sosai abin ya ba Ramlat.
"Kema dai ɗiyata ina nan ina addu'a Allah Ya zaɓamaki miji nagari mu sha biki. Ba na jin dadin ganinki a gida da kuruciyarki. Ai ina jin ba ki yi talatin ba ko?"
Da murmushi ta girgiza kai.
"Ban kai ba Umma. Kin manta watanni kawai na ba Amrah."
Umma ta yi dariya.
"Ke da Amrah ai rigimarku sai ku, ki ce kin girmeta itama ta ce ta girmeki."
"Allah na girmi Amrah."
Ita dai Umma ta amsa da toh sannan ta mike zuwa daki tana dariya, can ta fito rike da wani littafin adduo'i ta mikawa Ramlat.
"Ki dinga karantawa, akwai adduo'i sahihai da kuma nafiloli. Kar ki yi wasa don Allah."
Ta amsa da toh, mutanennan suna da burin ta yi aure, ba za ta ce ba ta so ba. Sai dai tana duba yaranta, ba ta kaunar yin nisa da su. Aure kuma ance ba inda ba ya kai mutum.
Kwanciya sosai ta yi saman kujera sadda Umma ta mike ta wuce bangaren mijinta da ta ji tsayuwar motarsa. Wannan ya ba Ramlat damar danna waya, lambar Hussein ta bude ta ga dacewar ta yi saving. Cak ta tsaya tana tunanin sunan da za ta ɗora akan lambar, can kuma ta yi murmushi ta rubuta Mr Wuf. Ita kanta abin dariya ya bata.
Daga haka ta faɗa whatsapp ta shiga duba contact har ta faɗa saman lambarsa. Dp dinsa na wani ƙaton ocean ne sai rana da ta ɗauko faɗuwa daga sama. Murmushi ta yi ta je kan Status na profile. Busy kawai aka rubuta da alama kuma ya jima sosai a hakan.
Tana komawa kan whatsapp ta ci karo da sallamar Alhassan. Ganin yana online ta amsa da sauri. Suka gaisa ta tambayi Dada da iyalinsa. Ya amsa har da turo emoji na nuna jin dadinsa da hakan. Ya tambayi mutan gidansu shima.
_*"Ina nan shigowa Kano karshen satin da zamu shiga in sha Allah. Zan kawomaki Fatina ku gaisa idan ba damuwa. Address?"*_
Ganin abinda ya rubuta ne yasa ta saurin miƙewa zaune. Alhassan zai shiga Kano? Kodai yana da ƴan uwa a Kano?
Wannan tambaya ce da ba ta da amsarta. Ga haɗiyi wani yawu kafin ta amsa mishi.
_*"Kano na marhabin da ku, Allah Ya kawoku lafiya. Ashe muna da ƴan uwa a Kano kenan._*
Ta tambaya cike da ƙaguwa . Dariya ya aikomata kafin ta ga yana recording. Ta bude ta saurara.
"Eh toh, muna da yan uwa. Akwai yayan Babanmu a Kano. Yanzun ma biki za'a yi na samarin yaransa har biyu, shi ne zan kawo su Dada da Maman Fatima. Ina fatan za ku hadu ku gaisa?"
Abinda ya ce kenan, ta yi shiru, gaba daya ya dulmiyar da ita cikin tunani. Kenan Alhassan suna da dangi a Kano? Toh ta yaya zai yiwu ace ba su taɓa cin karo da Hussein ba? Anya zai yiwu? Ace kuna gari daya ba ku taɓa sanin juna ba. Kodai Hussein din ne bai da zumunci?
Abinda ta yi ta rayawa kenan,can ta tuno ba ta ba shi amsa ba, gudun kar ya yi tunanin wani abin ne yasa ta ba da amsa.
_*Wow, Allah Ya kaimu toh. Zan so na ga Fatima.*_
Suka ɗan taɓa hira kafin su yiwa juna sallama. Ita dai ta ajiye wayar kawai amma hankalinta gaba daya ya tafi ga tunanin wannan lamarin mai ban mamaki da ɗaure kai.
Ba ita ta bar gidan ba sai da lokacin tashin yaranta ya yi, ta so ta ƙi shiga wurin Baba Dakta saboda kar ya yi mata batun aure, a karshe dai ta daure ta shiga kuma har suka gaisa ta fito suka taɓa barkwanci, bai mata zancen ba.
Tana shiga da yaran falon Hajiya, ta ga babu su Munir balle yaransu sai Hajiya da Ladidi da ke tattaunawa. Hajiya na ganinta ta yi dariya.
"Ja'ira, wata kika gudu kika bar ni da su ko?"
Tana dariya ta zauna.
"Me zan ce? Na saka baki Yaya Munir ya ce na mishi rashin kunya? Ya suka ƙare?"
Taɓe baki Hajiya ta yi.
"Na yi musu dai nasiha daidai gwargwadona. A karshe sun ba juna hakuri suka kwashi yaransu suka yi gaba."
"Allah Ya daidaita lamarin."
Suka amsa addu'ar Ramlat da Amin.
***
LAMIƊO CRESCENT.
Kallon abincin ta ke kamar ta fasa ihun kuka tsabar takaici da bakin ciki. Ta dage ta yi girki da ruwan maganin tarkinta amma Hussein ya tahomusu da wasu manyan kifaye har uku gasassu da aka sanya chips a gefe da kayan tumatir albasa sai ɗan yaji a wata ƙaramar roba. Ci ya ke yana jin dadinsa ya dubeta.
"Madam tunanin me kike ne? Wannan fa don ke na siyo. Please come and join me."
Ita a dole shagwaɓa irin ta masoya, ta yamutse fuska.
"Ni a'a gaskiya, na dage na maka girki da kaina da hannuna yanzun kuma ka cemin ka ƙoshi?"
Ya yi murmushi.
"Shikenan, ki sanyamin a fridge I promise you, da shi zan yi breakfast. Hankalinki ya kwanta?"
Ta ji sanyi a ranta, murmushi ta kasheshi da shi, ya maida kai ga abinda ya ke ci. John ta kwalawa kira ya shigo sanye da rigar kuku, umarnin ya juye ya sanya a fridge ta ba shi sannan ta matso ta soma tayashi cin kifin. Sanin da ta yi Hussein ba ya magana biyu, zai wuya ya ƙi yin abinda ya furta yasa hankalinta kwance ba ta ko damu ba.
Sai dai kuma ga mamakinta da safe tashi ta yi sai filin gado ita kadai babu shi ba dalilinsa. Takardar da ta gani ta dauka ta karanta, sanarmata ya yi ya samu kiran gaggawa zai wuce Abuja meeting, abu ne da suka sanya rai har sun fidda za'a samu sai gashinan ya yiwu, ta yi hakuri idan ya yi rashin kyautawa. Hawaye ne kawai Hajiya Zeenatu ba ta yi ba. Ta kirashi a waya sai dai a kashe, ta ja tsaki ya fi a ƙirga.
***
Kuɗin take ƙarewa kallo ba tare da ta iya kataɓus ba. Ta kasa bin umarnin Chairman ɗin nata ta dauka balle har ya je jakarta. Kuɗin da ya ninka albashinta sau biyu. Da mamaki ta dubeshi, kallonta yake ƙasa-ƙasa.
"Me zan yi da su?"
Dariya ya yi, duk a zatonsa ta ruɗe ne saboda yawan kuɗin, bandir na dubu har guda uku ai ba wasa ba. Ya kara turo kuɗin.
"Dauka dai ki riƙe tukunna Madam Ramlat."
Girgiza kai ta yi.
"Ka yi hakuri Yallaɓai ka faɗamin kudin na menene tukunna."
"Kyauta ce daga gareni, wannan ba komai bane daga irin kyautar da nayi maki tanadinsu. Don Allah kar ki ce ba za ki karɓa