Showing 186001 words to 189000 words out of 231786 words
Chapter 63 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
ji Hajiya da na fadin.
"Ai wannan ba a bukatar jin ta bakina ko ita Ramlatun. Ramlatu da Amrah duk daya ne. Dukkan hukuncin da ku ka yanke a kanta nasan ba za ta taɓa yin da na sanin zaɓinku ba in sha Allahu. Balle kuma dama akwai fahimtar juna tsakanin yaran. Ni dama hankalina ya fi kwanciya da shi tunda ko ba komai ba wannan ne aurensa na farko ba. Allah Ya sanya alheri. Ya sa ayi muna raye."
Ramlat tuni ta ji wani gumi na tsastsafo mata, kirjinta ya tsananta bugu, ta ji Baba Dakta na kara godiya da yiwa Hajiyar addu'a. A karshe ma yake batun zai je takanas can Yakasai ya ga su Kawu su yi magana. Gwuiwa a sake ta juya ta koma saman gadon, Affan ya damu da kai ƙarar Ummi ta ɗauki wayar Mamin, ba ta san sadda ta dakamasa tsawar da dukkan yaran sai da suka tsorata ba. Ta ja guntun tsaki ta riƙe kai, salati kawai ta ke yi da addu'ar Allah Yasa hakan ya zamemata alheri. Ta dafe saitin kirjinta, ba ta taɓa zaton lamarin aurenta da Baban Hanif zai zo mata da yanayin ɓacin rai kwatankwacin na Hilal ba sai yanzu. Sai dai wannan karon alƙawari ta yiwa kanta, ko me zai je ya zo, za ta rungumi zaɓin iyayenta da hannu bibbiyu.
"Ki godewa Allah da zaɓinSa. In sha Allah jikina yana bani wannan aurennaki shi zai zama na dindindin duk kuwa da cewar sai an yi hakuri kuma an kai zuciya nesa saboda kananun maganganun da kan iya tasowa."
Wannan shi ne kadai abinda ta ji a bakin Hajiya, nan ta tuna wayarta a safiyar yau da Baban Hanif, inda cike da damuwa yake sanarmata irin tashin hankalin da yake fuskanta daga iyayensa game da aurenta da ya yi niyyar yi. Labari ya zo musu cewar ta taɓa yunkurin kisa a aurenta na farko. Wannan ne dalilin da yasa gaba ɗaya a kwanakin ta kasa gane inda ya nufa.
Ramlat ta dubi Hajiya karo na ba adadi tun zamanta a falon, waya Hajiya ta shiga yi da Munir, ta kasa kunne amma a karshe ma sai Hajiyar ta miƙe ta nufi ɗaki. Ranta sai ya soma ɗan baci. Ko ba komai ba wannan ne aurenta na farko ba, ya kamata ta san wa za ta aura ai. Hakan kuma bai nufin jayayya za ta yi da su. Ko kadan, ta rantse koma waye ta yarda kuma ta amince da aurenta da shi, kawai dai tana son sanin waye. A gefe guda kuma jikinta yana ba ta cewar ta yi BANKWANA DA HUSSEIN. Bankwana na har abada.
"Mami! Wayarki."
Ta sa hannu ta karɓa a hannun Ummi. Baban Hanif din ne kuwa ya kira don haka ba ta jira ya kara ba ta bi bayansa. Sai da ta shiga daki ta rufe kafin ta amsa sallamarsa. Bayan sun gaisa a gaggauce ta ce.
"Kun yi magana da Baba Dakta ne?"
"Eh ya kirani dazunnan da yamma, mun yi magana sosai da shi. Labari ya zo maki kenan?"
Ta kasa magana kawai sai ta kashe wayar gaba daya, kai ta dora saman gwuiwar ƙafafunta ta shiga rera kuka. Kukan jin zafin Hussein da ya kasa kallonta matsayin masoyiyarsa. Ta gasƙata cewa yanzun babu wani abu da zai ƙara shiga tsakaninta yanzun. Ta ji kuma ta hakura da zaɓin Allah. Dakyar ta iya miƙewa ta faɗa ɗakin yaranta, kowannensu ta gyarawa gado don yanzun ta sauyamusu da gado kanana na yara kowanne da na shi. Ta kakkaɓe, ta ba su umarnin kwanciya. Kasancewar sun saba da baccin wurin hakan yasa su na kwanciyar bayan ta sa sun yi addua, bacci ya ɗauke su.
Ta yi shiru tana kallonsu bayan ta gama kwashe shirgin kayan da suka zubar a ƙasa ta ninke kayan sif din da ya lalace. Aliyunta ne ya faɗomata, zuciyarta ta ƙara karyewa, nan ta shiga rera wani sabon kukan. A karshe don kanta ta rarrashi zuciyarta ta share sannan ta fita ta ja musu ƙofar.
"Ashe AlHassan ya zo garinnan?"
Ta dubi Hajiyar da le tambayarta, robb ta ke faman shafawa a ƙofofin hancinta.
"Ban sani ba wallahi. Yaushe?"
Murmushi Hajiya ta yi.
"Ai da Husseini muke waya, sai ya ba shi muka gaisa. Wai jiya-jiyan nan. Amma ya cemin zuwa gobe zai shigo in sha Allahu."
"Allah Ya nunamana."
Ta fadi a ɗan gaggauce don ji ta ke yi kamar ta fashe da wani kukan.
Hajiya na lura da ita kuma abin na ba ta mamaki amma ba ta ce uffan ba. Ta san dai idan ma da wani abu na daban a zuciyar Ramlatun, dole yanzu ta yi kokarin kawar da shi tunda dai bakin alƙalami ya riga da ya bushe.
***
Tun sadda Hajiya ta shaidamata cewar ana nemanta a Yakasai, Kawunnanta, kirjinta ke bugu da sauri. Affan wannan karon maƙalewa ya yi zai bi ta, dole ta shirya shi suka fita tare. Adaidata Sahu suka hau kasancewar motarta ta samu matsala.
A hanyar ma babu cikakkiyar nutsuwa tattare da ita sakamakon tunanin abinda zai biyo baya da ta sa a rai. Kiran ko kusa bai ba ta mamaki ba, ta san dama tunda har aka ce an mata miji to komai ma za ta gani. Har dai suka iso ba ta jin ta ba Affan kwakkwarar amsar tambayoyinsa na shirme da ya ke mata. Karshe ma da ya dameta cewa ta yi za ta bar shi a cikin Napep din dole ya ja baki ya yi shiru.
Ɓangaren Baba Dije ta soma shiga. Bayan sun gaisa ta ce.
"Ina tayaki murna ƴarnan, kin yi goshi wannan karon ba shakka. Allah Ya sanya alheri ya nunamana lokacin."
Ta rasa yanayin da ta shiga. Ta kasa amsawa hakanan ta kasa cewa komai don haka kawai sai ta mike ta fita tana murmushin yaƙe.
"Ayiririri!"
Guɗar da ta ji yasa ta waiga, Baba Hajara ce yayar Hajiyarsu. Su uku ne kadai mata a wurin Hajjar, Baba Hindu, Baba Hajara sai Hajiya. Mazan kuwa su uku, Kawu Jamilu, Kawu Bello da Kawu Sunusi, su ne manyan maza a ɗakin.
Jiki a sanyaye ta gaida ta kafin ta karasa ɗakin Hajja itama Baba Hajara na daga bayanta.
Hajja ce zaune tana shan fura, tana ganin Ramlatun itama ta saki fuska.
"Kishiyar ce a tafe kenan? Sannu da zuwa."
Ita dai ba ta ce uffan ba, Affan ya karasa a guje ga Hajja. Zama ta yi gwuiwa a sake kafin ta maida hankali ga Baba Hajara.
"Wai Baba lafiya?"
Baba Hajara ta zauna tana dariya, ba ta kai ga magana ba Hajja ta katse ta.
"Na rabaki, idan ba so kike tarihi ya maimaita kansa ba. Ki bari ta ji komai daga bakin Ubanninnata. Ai ba abinda zamu ce ga Dakta (Baba Dakta) sai godiya da fatan alheri. Allah Ya biyashi da aljanna. Yanda yake nunamaku kulawa kamar ƴaƴan da ya haifa a cikinsa, Allah Yasa aljanna makoma. Na ji ma ance ya kawomaku kayayyakin abincin azumi, to nan ma haka ya aikomin. Wannan bawan Allah sai fatan alheri da fatan Allah Ya jiƙan iyaye."
Baba Hajara ta amsa da amin, itama Ramlat ta amsa ta hanyar motsa lebbanta amma dukkan wata gaɓɓa ta jikinta ta yi sanyi. Can kuma sau ga shigowar saƙo. Hussein ne. Ta bude hannunta har rawa ya ke don yanzu ta kasa fahimtar komai.
_*"Ban yarda da dukkan wani so da za'a yi shi kafin aure ba. Ban kuma yarda akwai kulawar da namiji zai yiwa mace ba da za ta kere kulawar miji ga matarsa. So da kauna na gaskiya ya fi ma'ana idan aka zama mallakin juna. Ina taya junanmu murna."*_
"To wai me yake nufi?" Ta tambaya a fili bayan ta karanta ya fi sau biyar amma ba ta gane komai ba.
"Wa kenan?" Hajja da Baba Hajara har suna haɗa baki wajen tambaya. Ta ma kasa cewa uffan sai kai da ta girgiza tana sharar gumi ga kwalla cike a idanunta.
"Idan ma za ki saka ranki a inuwa tun wuri gwara ki sanya don wannan karon na tabbatar wanda za ki aura ba fetur ba, Allah Yasa tankin mai gaba daya za ki zazzaga maku, zai yarda ku mutu ƙurmus! Sawun giwa ya take na raƙumi!"
Hajja ke wannan sababin ta karashe da kurɓar furarta ta bar Baba Hajara da dariya. Ita dai Ramlat ba ta ce komai ba sai hawayen da ta shiga sharewa, gaba daya gaɓoɓin jikinta sun yi sanyi, yanzun kuma abin haushi ya ke bata.
"Yaya Ramlatu ki zo inji Kawun Zaure."
Wato Kawu Jamilu kenan wanda shi hanyar shiga sashinsa na daga wurin zauren gidan, ai ba ta ma jira Hauwa diyar Kawu Sunusi ta karasa faɗin saƙon ba ta yin zumbur ta miƙe tsaye har wayarta na faɗuwa amma ba ta ko damu da ɗauka ba. Tana ji Hajja na fadin.
"Kuma yarinya ta dawomin daki da baki kamar gonar auduga sai na yi ƙasa-ƙasa da ita. Maza Affan bani wayarnan idan mijinnamu ya zo sai ya siyamata wani."
Tana jin dariyarsu amma babu wanda ta tanka asalima baki ta turo ta ɗan ja guntun tsaki tsabar ɓacin rai. Haka ta dinga tafiya har sashin Kawu Jamilu, duk a zatonta shi kadai ne, sai ganin sauran Kawunnan da ta yi zaune ƙasan bishiya suna taɓa hira. Ta karasa gami da durkusawa ta kwashi gaisa. Suka amsa fuska a sake duk da cewar kanta a ƙasa yake amma sautinsu ya nuna hakan. Sai da aka gama gaisuwar da ɗan barkwanci kafin Kawu Jamilu ya yi gyaran murya ya soma magana.
"Toh Ramlatu, abu na farko shi ne mu miƙa godiyarmu ga Ubangiji domin Shi ya yi mana dukkan ni'ima. Ya kuma so ki da dukkan rahma da mu ɗin gaba ɗaya. Alhamdulillah."
Ya ɗan ja numfashi gami da gyaran murya sannan ya ci gaba.
"Kamar yanda ki ka ji daga bakin mutanen gida, abin alheri ne ya sameki. Babanki Dakta ya yi maki zaɓi bisa damar hakan da kika damƙa maki. Kar kuma hakan yasa ki yi zaton cewa shi da kansa ya haɗa auren, aa, shi yaron ma asali tun ana zancen aurenki da Dikko ya tunkari Baba Daktan da batun aurenki sai dai Baba Daktan ya ba shi hakuri ya kuma sanarmasa da batun Dikko, a karshe ya yi mishi kwatancen gidannan ya ba shi lambar wayar Kawunki Bello cewar yana iya zuwa nan wurinsa ya faɗamasa ko Allah Zai sa a dace. Da yake shima yaron nada hankali ya ce aa babu komai, ya yarda Allah bai kaddara ke din rabonsa ba ce. Ba ya son ya yi nema cikin nema. Wannan ne dalilinsa na janyewa bayan ya nemi alfarmar su bar maganar tsakaninsu. Yanzun ma da kika ji, magana ce ta kawo magana shiyasa ya faɗamana shi Babannaki. Sai kuma cikin ikon Allah lamarin aurenki da shi Dikko ya lalace, anan ne kuma bayan kin bar wuƙa da nama a hannun Daktan, ya ba wancan yaron iznin turo nashi magabatan bayan shawarar da ya yi da mu kuma muka amince. Alhamdulillah, Ramlatu ke ba yarinya ba ce, mun kuma sani, yanzun kin fi baya hankali. Kin kuma ƙara hankaltar rayuwa. Mun sani, wannan karon ba za ki ba mu kunya ba in sha Allahu."
Zufa sosai ta ke fitarwa, ta hadiyi miyau mai ɗaci, ba ta bar ambaton Innalillahi a ƙasan ranta ba har zuwa sadda Kawu Jamilu ya miƙomata damin kudi ƴan ɗari biya-biyar a baƙar leda bayan ya warware ledar ya turo kudin gabanta.
"Wannan ne kudin aurenki, dubu ɗari gashinan. Juma'a mai zuwa cikin yardar Allah za'a ɗaura aurenki da HUSSEINI MODIBBO. Ina ce haka sunan yake ko?"
Ya karashe yana duban yan uwansa da dariya, suka dara lokaci guda.
"Hakayake Yaya." Kawu Sunusi ya bada amsa.
Ta rasa me za ta ce, ta kuma rasa me za ta yi, a zaune ta ke amma jiri ta ke ji. Kanta ya yi wani irin sarawa, lokaci guda ya shiga ciwo. Hawayen da ta tsayar a ɗazun, suka ci gabada kwaranya su na ɗiga saman k
rafar ɗari biyar biyar din da Kawu ya ajiyemata. Wa ya faɗamusu sonta yake?
I just published "BABI NA HAMSIN DA SHIDA" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1017117739?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=NPwmUPq5q%2BNDXCvudnu9VtPx9xZ93DXS%2BXNO4Gp8IGMT8cs%2FH9GyIFlv%2Fhb%2BKgVVkXrnM1fZVi41cUdjwyw1cEK3IG5H1c7vZKRmCwE0POba10BIvSct65MXWSFYf6%2Fz
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
56)
'Me yake nufi da ni?' Ta jefawa zuciyarta tambayar da nan da nan ta samo amsar da ta ji wani mugun ɗacinsa. Hussein na nufin ra'ayinta ba komai ba ne, yana nufin koda ba ta sonsa ta rayu da shi. Ko kuma dai daga saƙon da ya turomata yana son ta fahimci ya gane tana sonsa amma ya dinga basarwa. Nan da nan ta ji wani haushinsa ya mamaye zuciyarta. Ta ci alwashin sai ta rama abinda ya aikata gareta, ba za ta taɓa yin musu a aurensa ba, amma ta rantse sai ya gane shayi ruwa ne.
"Allah Yasa hakan ya zamemin alheri." Ta ba Kawu amsa a hankali, gaba daya suka amsa da amin cike da jin dadi. Suka sanya mata albarka a karshe suka sallameta. Mikewa ta yi bayan ta share hawayen yanda ba za su gani ba, ba tare da ta ɗau kuɗin ba ta bar wajen. Kawu Sunusi zai magana Kawu Jamilu ya katseshi da zummar za su damƙawa Hajiya.
Ba ta wani jima cikin gidan ba ta yi musu sallama sai dai ba su fahimci komai ba don ta ɗan saki fuska kamar ba ita ba.
Koda ta koma gidan, ba abinda ta nunawa Hajiyarta. Wannan ya kwantar da hankalin Hajiyar don dama tun fitar Ramlatun ta ke cikin zullumin ta yanda za ta karɓi lamarin.
"Idan kin sauya kayan sai ki fito mu shiga kicin, na fadamaki yau Hassan zai shigo a gaisa."
Maganar Hajiya ta katse yunkurinta na shigewa ɗaki da ta yi niyya, ta juyo ta amsa da toh bayan ta haɗiyi miyau mai ɗaci.
***
Hajiya Zeenatu ta shigo falonta gaba daya jiki a sanyaye, likita ya duba ta amma ya ce bai gane komai ba, karshe aka haɗata da tests kala-kala akan ta yi ta kawo sakamako a gani. Ranta gaba daya a jagule ga wani jiri-jiri da ke ɗibanta. Turus ta yi ganin mutum zaune a falon. Ta daure ta shigo da fara'ar da bai kai zuci ba. Suka dubeta gami da amsa sallamarta.
Hussein ne fuskarsa cike da wani farin ciki sai AlHassan dake zaune yana amsa waya Madam dinsa Kausar, ganinta yasa shi yin sallama da ita.
"Ah, ɗan uwanmu zuwa babu sanarwa?"
Ya yi murmushi, sai yanzun dai ya zo gidan dan uwannasa don haka ba su hadu da Hajiya Zeenatun ba sai a yau, amma a Hotel ya sauka tare da Kawunsu Adamu wanda shi a yau da safe ya juya ya kama hanyar Adamawa.
"Hajjaju, Allah Ya huci zuciyarki. Nima zuwan ne ya tasomin babu shiri. Aiki na zo yi daga kamfaninmu na can. Ko shi Ogannaki haka ya gan ni babu zato ba tsammani."
Ta yi dariyar yaƙe gami da satar kallon Hussein da ya ɗora ƙafa ɗaya saman kujera hankalinsa ya koma kan waya yana zabga murmushi.
"Hakan ma ai daidai ne. Dama kuwa ina da saƙon da zan bayar a kaiwa Ɗiyata. Gwara da Allah Ya kawoka."
Ya yi dariya yana gyara zaman gilashinsa.
"Ba ki da matsala. Tana godiya."
Daga haka ta maida duba ga mijinta.
"Yallaɓai barka da hutawa."
Ta fadi da wani irin shagwaɓa wanda ya ba AlHassan dariya, sai dai ya haɗiye kawai ya miƙe.
"Bari na ɗan amsa waya." Yana kaiwa nan ya fice zuwa farfajiyar gidan, wannan ya ba Hajiya Zeenatu damar ƙarasowa ta zauna gefen Hussein. Ya ɗan dubeta da kulawa.
"Ya jikin naki?"
Cike da damuwa ta karya wuya.
"Likita ya duba ni, ya ce ba zai gane taƙamaiman matsalar ba sai an yimin gwaje-gwaje. Yanzu dai haka ya ban gwaji zuwa gobe zan koma mu gani. Amma na fi kaunar na hakura idan mun je London sai a yimin magani sosai."
Ya gyaɗa kai yana murmushin da ke ƙara tafiyar da imanin Hajiya Zeenatu a kansa.
"Saurin me ki ke? Ita lafiya ta fi komai ai. Ki kwantar da hankalinki. Tunda har kika ga na dakatar da aiki toh hakan na nufin na shirya koyaushe ne ma mu bar ƙasar. Abinda ya fi yanzu ki je goben ki yi gwaje-gwajen har a gano matsalar a shawo kanta. Gwara ki ɗan samu sauki sai mu wuce. Amma fa sai mun fara biyawa Adamawa kinga su Dada kun gaisa."
Ko ɗarr ba ta ji ba, a wautarta gani ta ke har a sannan babu wanda ya gane da hannunta a ɓatan Hussein.
"Yanda ka tsara hakan za'a yi Ranka ya daɗe."
Kauda kai kawai ya yi bai ce uffan ba, ta mike ta haye sama. Ya bi bayanta da kallo, sai kuma ya yi murmushin mugunta. Shi kadai ya san me ya bar wa zuciyarsa. Tabbas sai Hajiya Zeenatu ta kusa haukacewa idan ta gano taƙamaiman shirin da ya ke yi.
Wayarsa dake ringing ya duba. Hisham ne. Murmushi ya yi don ya san labari ya isa kunnensa.
"Kai dan iska ne fa! Wai me nake ji daga bakin My Princess? Dagaske kai ne ka kai kuɗin auren Ramlatu?"
Lumshe idanu ya yi, sunanta kaɗai idan ya ji sai tsigar jikinsa ya tashi. A hankali ya shafi sumar kansa.
"Mamaki ka ke yi? Ba haka ka ke so ba?"
Dariya Hisham ya yi.
"Haka nake so, sai dai ka rainamin hankali fa. Zan rama amma. Kar ka yi tunanin zan tayaka campaign."
Taɓe baki Hussein ya yi kamar yana kallonsa.
"Campaign after marriage? Ni zan yi abina dama."
Hisham ya ɗan dara don shi abin kam dadi ya yi mishi ba kadan ba. Addu'a ya yi da fatan alheri. Hussein ya amsa da amin kafin su yi sallama. Agogo ya kara dubawa, da sauran mintuna a kira sallar Magriba. Ya ƙagu ya ganshi a gidan su Ramlat. So ya ke ya sanyata a idanunsa. Bai zaci za ta ga saƙonsa ta shareshi ba, abin ya ba shi mamaki. Hakan yasa ya ke son zuwa ganinta da kansa.
***
Kawu Modibbo rai a ɓace ya ke amsa wayar ƙaninsa Adamu.
"Me ya kawoka Kano? Wato Adamu har wuyanka ya yi kaurin da za ka shigo inda nake ka kasa nemana? Idan kuma aka yi magana sai ka nuna ka fi uban kowa riƙon