Showing 153001 words to 156000 words out of 231786 words

Chapter 52 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

Hussein, shi dai ta gani kamar yanda ya gan ta amma ya kauda kai. Wannan abu ne da bai taɓa afkuwa ba tsakaninsu. Ta ɗauki wayarta da karar shigowar saƙo ya katsemata tunani, kuɗi ne har dubu ɗari aka aikomata. Ta kai duba ga lambar mai account din. Aliyu Dikkl. Hakan ta gani a rubuce. Ranta ya ƙara ɓaci, ga babu lambar acc balle ta mayarmasa. Ta ja tsaki. Kai tsaye ta ƙara kiran wayar Hussein, wannan karon ringing ta ke yi sai dai har ta katse bai ɗaga ba. Ta kuma kira nan ma shiru, a karo na uku ma babu alamar za'a ɗaga. A na huɗu sai ji ta yi an kashe wayar gaba ɗaya.


"Meke faruwa?" Ta ambata a fili. Kawai sai ta ji zuwa wurin aikin ma ya fita a ranta, don haka ta ba kanta mintuna kusan biyar a tsaye tana jin karatun Alkur'ani tana hawaye kafin daga bisani ta samu ƙwarin gwuiwar da za ta tashi motar. Gidan Amrah ta nufa, a hanya ta kira ɗaya cikin abokan aikinta, Hindu. Uzurin rashin lafiya ta bayar domin dagasken ba ta jin dadin zuciya da gangar jikin.


***
Amrah ta yi mata duban tsanaki bayan gama sauraron dukkan bayanin Ramlat. Ita kanta kwallar ce ta cicciko mata.


"Yanzu AlHassan ɗin bai shigo ba?"


Ramlat da kanta ke jikin kujera sakamakon zazzaɓi-zazzaɓin da ta ke ji. Ta girgiza kai murya a dusashe.


"Mun yi waya da shi yanzu da zan fito, abin hawa ne ba'a kammala gyara mishi ba, yana tunanin ma bar musu zai yi ya biyo motar kasuwa."

"Kai! Wannan lamari akwai wata sarƙaƙiya a cikinsa Ramlat. Sai dai kuma ki zauna don Allah ki yi tunani ko dai akwai abinda ki ka aikata ga Hussein har ya ɗauke maki wuta haka? Ni fa gani nake da walakin goro a miya."


Cike da damuwa ta ɗago ta zauna sosai tana duban Amrah da ciki ke ƙara girma.


"Da ace akwai abinda nake jin zan ba dukkam girma da kulawa bayan iyaye, ƴaƴa da ƴan uwa, wallahi ya biyo bayan Hussein. Kin san ni, kin kuma san halina Amrah. Ina son Hussein, son shi nake yi da ban san iyakarsa ba. Akan me zan ƙuntata masa? Ni duka-duka ma yaushe rabon da ko chatting nayi da shi balle haɗuwa face to face? Ban sani ba, ban san me na yi ba. Ni dai babban burina koda zai zama abu na ƙarshe da zan mishi, shi ne na sada shi da ƴan uwansa da taimakon Allah."


Amrah ta jinjina kai, shakka babu Ramlatu na son Hussein, so mai yawa. Tana tsoron tarihi ya maimaita kansa idan har dangin uwa da uba suka dage mata akan auren Chairman. Sauƙinta ma wannan karon su Hajiya na goyon bayanta.


"Ko Hisham zan tambaya?"


Maganar Ramlat din ta maido ta hayyacinta. Gyada kai ta yi.


"Ki tambayeshi tunda amininsa ne. Ba zai rasa abinda ya sani ba."


Da haka ta danna wa Hisham kira. Yana ɗagawa suka gaisa.


"AlHassan din ya iso kenan?"
Ya nemi sani.


"Aa, wannan tsakanina da Hussein ne."


"Ina jinki Ramlat."


Ta ba shi labarin irin sauyin da ya ke mata.


"Ko akwai wani abu da ya ce maka na yi mishi don Allah?"


Shiru ya biyo baya kafin Hisham ya ce.


"Ya Salam!"


Jin haka ta gyara zama tana kallon Amrah don dama a speaker ta sanya. Suka nutsu.


"Meyafaru?" Ta tambaya kirjinta na dukan uku-uku.


"Ki yi hakuri, ina ga wannan laifina ne, yanda na ɓata kuma ni zan gyara. Kar ki damu don Allah. Zan kira ki anjima ko kuma ince zai yi kiranki da kansa. In sha Allahu."


Daga haka ya katse kiran. Suka dinga mamaki. Tunanin Ramlat me Hisham ya faɗawa Hussein?


"Hisham ya san batun aurenki da Chairman?"


Amrah ta nemi sani. Maganar Ramlat ji ta yi kamar an sokamata mashi a ƙahon zuci don haka maimakon amsa sai ta harareta ta ja guntun tsakin da ya ba Amrah dariya.


"Allah Ya ba ki hakuri. Mancewa nayi fa."


Ta cije lebɓa gami da girgiza kai ba ta ce komai ba.


***
MISALIN ƘARFE SHA ƊAYA..


Rubutu yake kamar wani Mango Park ba ya ko kallonsa, Hisham ya ƙuramasa idanu da mamaki. Ya sauya kamar ba Hussein din da ya sani ba.


"Malam ya ina magana ka kyale ni? Ba ka ji me nace ba?"


Ya ɗago ya dubeshi, ya ji, dukkan wani labari da ya ba shi, ya ji ba wai bai ji ba. Sai dai duk da hakan shi bai ga ta inda zai fara rage KISHIN Ramlat da ya ke ji ba. Ya soma yarda da abinda ya ƙaryata da gangan, ba kuma ya son sanya ta a matsala. Wannan ne dalili sauyawar sai dai ya ji wani sanyi kaɗan a maimakon tsananin zafin da ya ɗauka a farko duk akan lamarin aurenta da Chairman.


"Kunne ke ji, kuma na saurareka. Ka yi kokari."


Harara Hisham ya watsamasa yana danne tausayinsa.

"Shi ne za ka share ni? Nima fa takanas na taso don wanke laifin Ramlat amma ina da abin yi ai. Aikina na baro na zo."


Wannan ne karon farko da ya yi murmushi daga jiya zuwa yanzun, Hisham yana da raha. Ko ya ya ka zauna da shi sai ya sanyaya ranka.


"I'm travelling to London."


"For what?!"


Yanda Hisham ya nemi sani a hargitse, hakan ya ba Hussein mamaki har ya kalleshi, ganin ya zaro ido sai ya buɗe tafukan hannu gami da ɗaga gira cikin dakiya.


"Me akai na razanar? Tafiya ce kawai ta 3months."


"Gwara da Allah Yasa na zo." Hisham ya faɗi a fili kuma a hankali. Da ace ba su haɗu ba ba zai sani ba kenan. Lallai dole su yi komai cikin gaggawa.


"Me ka ce?"


Hussein ya tambaya. Girgiza kai ya yi.


"Ba komai. Yaushe za ku wuce?"


Damuwa ƙarara a fuskar Hussein sai dai ba ƙaramin ƙoƙorin dannewa ya ke ba.


"Ba na jin za mu wuce satinnan. Ya dai danganta da samun Visa."


Ya faɗi a sanyaye.


'Innalillahi wa inna ilaihir raajiu'un!'


Hisham ya ambata a zuciya gami da mikewa.


"Ok ok, Allah Ya nunamana. Bari na wuce sai mun haɗu anjima."


Hussein ya bishi da kallo har ya fita. Abinda ya kawo a rai shi ne damuwa ce tsantsa na ganin za su yi nesa da juna. Ya dafe kai da hannu. Shi kansa damuwar ce ke cinsa, tunanin tafiya ya bar Ramlat da Chairman kan ci masa tuwo a kwarya. Sai dai ya tabbatar furta wata kalma a kanta zai zama kamar barazana ga rayuwarta. Hajiya Zeenat ta sha faɗamasa gami da cin alwashin kashe duk wata mace da za ta shiga rayuwarsa. Ba a bayan idanunsa ba, a gabansa ta ke faɗi ya na kuma ji a jikinsa fiye da hakan ma za ta aikata. A hankali ya ɗauki waya ya kunna Data wacce rabonsa da whatsapp tun ranar da Hajiya ta kwace wayar. Saƙonni suka shigo har da nata. Ya shiga ya karanta. Gaisuwar safe ce ta mishi gami da tambayar ko lafiya. Ya dinga binyana karanta hirarsu da bai fi a ƙirga ba. Murmushi sosai ya ke yi san nan ya bude hotonta yana kallo. Ya kai kusan minti biyar ba'a hayyaci ba, tashin hankalinsa ya ƙaru. A hankali ya rufe hoton ya aikamata saƙo.


-*"Ki sa ranki Hussein ɗan uwanki ne. Ya na buƙatar addu'arki a duk inda zai je. Akwai wani duhu da na kasa fita, ke na gani kin fitar da ni kin sadar da ni da haske. Ina fatan mafarkina wataran ya tabbata. Ban ce ina sonki ba, ban kuma ce ina tsananin kishinki ba, amma ina roƙonƙi akan kar ki yi garajen aure. Nemi zaɓin Allah. Ke ba yarinya ba ce. Ina miki fatan alheri koyaushe."*_

Ya aikamata ya kashe datar, dakyar ya ci gaba da abinda ya ke ransa a jagule.


***
Kawu Modibbo tsaye a tsakar falonsa. Safa da marwa ya ke yi yana ƙarawa. Babu wani cikin iyalinsa da ya yi ƙoƙarin dosar inda ya ke, Amarya kanta haƙura ta yi da kwanan ta koma sashinta ta kwana.


*_"Kamar wuta da ruwa, haka ta ke barazana ga ayyukanka. Na sha faɗanaka, ba kai ɗaya ke aikin ba, akwai masu yi. Naka kan rinjayesu ne wani lokacin, kamar yanda nasu kan rinjayi naka aikin. Ina tsoron shaida maka muddin ba'a kawar da yarinyarnnan ba, aikin shekara da shekaru zai lalace. Za'a rasa dukkan wata nasara a kansa. Abubuwan da ka ke gudun afkuwarsu a rayuwarka, za su afku!"_*


Waɗannan jawabi na Tsoho, shi ke yawo a kwanyar Kawu Modibbo suka kuma hanashi sukuni daidai da sakan. Daren jiya kasa runtsawa ya yi balle har ya samu damar baccin. Idan komai ya lalace, hakan na nufin bayyanuwar komai.


"Lokaci ya yi da za mu haɗa ƙarfi da ƙarfe da ke ZEENATU."


Ya furta a fili kafin ya samu wuri ya zauna kamar kayan wanki.


***


ƘARFE BIYU...
Ta karanta saƙon Hussein sau ba adadi, sai dai ba ta fahimci komai ba. Cewar ba ya sonta ba kuma ya kishinta wannan ya haifar mata da matsananciyar damuwa. Kukan da ta yi ya jazamata tsananin ciwon kai. Hajiya na ganin haka ta tsorata, abinda ya faɗo a ranta kada ace wani mummunan abin ya sami Ramlatu sanadin wannan yaro, bayan ta taimaka mata ta sha magani ta shiga tofe ta da addu'a. Ummi kam su na Islamiyya ba su da labarin wainar da ake toyawa.


Wuraren ƙarfe huɗu da mintuna ne. Wayarta ta yi ƙara, dakyar ta iya ɗagawa. AlHassan ne.


"Na shigo Kano, ina hanyar gidanku."


Ta amsa da toh, a daddafe ta miƙe, babu laifi kan ya daina sarawa. Ta shiga ta yi brush ta kama ruwa ta yi alwalar jiran la'asar. Fitowa falon ta yi bakinta duk jikinta ya yi mata nauyi. Hajiya na zaune tana amsa waya.


"Ita Ramlatun?!"


Hakan da Hajiyar ta faɗi ya ɗau hankalinta, ba ta katse ta ba har ta kammala wayar.


"Ke da kanki ki ka ba shi Dikko damar turo kuɗi? Yaya Bello ya shaidamin ai sun ma gama magana ya turomaki kudin aurenki ta akawun dinki da ki ka aikamasa."


Dafe kanta ta yi tana salati, kirjinta na bugu da sauri-sauri.


"Ni kuma Hajiya? Wallahi ban.."


Ɗif ta yi, sai lokacin ta tuno da kuɗin da ya turomata account. Ranta idan ya yi dubi ya ɓaci. Ta faɗawa Hajiya gami da nunamata sannan ta ƙara da faɗin.


"Amma wallahi ban san inda ya samu lambar account ɗina ba. Ban sani ba. Me ake nufi da ni wai?"


Ta karashe hawaye na son zubomata. A fusace Hajiya ta mike tana faɗa.


"Bari na je gidan! Ba su suka haifarmin ke ba don haka ba zan zauna rayuwarki ta ƙare haka ba Ramlatu! Idan shi Munirun ya kasa ni zan je na same su."


Daga haka Hajiya ta faɗa ɗaki ta bar Ramlatu da ruɗewa da kuma hawaye. Waya ta ɗauka ta kura Zulaihat ta sanarmata komai, itama hankali a tashe ta ce za ta je can gidan su Dada kar abin ya ɓaci. Hajiya ta fito ta kama hanya ta fita.


Mintuna talatin bayan fitar ta sai ga kiran AlHassan yana shaidamata zuwansa ƙofar gidan. Ta mike ta shiga ciki ta gyara fuskarta da ta kumbura. Dole haka ta haƙuranta fita hakan. Tuni an gyaramasa ɗakin Muniru na baya, ta yi mishi iso ya shiga yana bin ta da kallo.


"Lafiya dai ko?"


Ta yi murmushin yaƙe.


"Lafiya kalau. Sannu da zuwa."


Ya amsa karo na biyu, shi ba wannan ya ke da muradi ba. Labarin Hajiya Zeenatu da adireshinta ya ke da buƙata.


Abinci ta kawomishi ta kuma ce ya yi hakuri har su yi sallah tukunna. Daurewa ya yi ya amsa da toh sannan ta fice.


***
"Rai kan ga rai?" Hajiya Zeenatu ta faɗi tana murmushi da wani irin mamaki shimfiɗe a fuskarta tana duban Kawu Modibbo da ke zaune a ofishinta na A&Z. Ya share goshi.








I think you'd like this story: "Ƙarfen Ƙafa" by Rufaida-Umar on Wattpad https://my.w.tt/rSOQW4y2Gcb








🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.


46)




"Kin san dai ruwa ba ya tsami banza. Kamar yanda kin sani, na sani, komai nisan jifa ƙasa zai faɗo. Toh idan ba mu yi dagaske ba, asirinmu na dab da tonuwa."


Nan da nan ta haɗe rai.


"Me kake nufi?"


Kawu Modibbo ya gyara zama yana mata kallon ƙyar.


"Wata yarinya ta zo min da zancen da ya rushe dukkan walwalata. Tana ƙoƙarin shaidamin cewar ta san inda Husseini yake, duk da ba ta fito fili ta yi bayanin komai ba, amma daga yanda ta ambaci shi Hassan ta alaƙantashi da Husseini shakka babu akwai babban al'amarin da ta sani."


"Ya sunanta?" Hajiya Zeenatu ta nemi sani a hanzarce yayinda kirjinta ke bugu, tana tsoron kar hasashenta ya zama gaskiya. Sai dai abinda ta guda shi ya faru, sunan da ta ke fatan kar ta ji, shi dai ta ƙara tsinkaya daga bakin Kawu Modibbo.


"Ramlatu ta ce sunanta."


Wani miƙewa da Hajiya Zeenatu ta yi sai da shi kansa Kawu ya ƙara tsorata. Jikinta ya shiga rawa nan da nan idanunta suka kaɗa.


"Baƙa ce, ba ta da jiki sosai kuma.."


"Abinda ya tunkaro mu, ya fi ƙarfin mu tsaya ɓata lokaci a kan suffantawa ba. Ki faɗi kai tsaye idan kin santa."


Ya faɗi cike da ƙagara. Ta haɗiyi miyau tana goge gumin goshi.


"Tsinanniyar yarinyar da aka sha yimin gargaɗi a kanta kenan! An tabbatarmin muddin ban nisanta Hussein daga duniyarta ba, to shakka babu komai zai lalace. Kenan yanzu ta gano dangin Hussein? Wannan mayyar ina ce?!"


"Mafita za mu nema. Kin sani, baragurbin kwai idan ya fashe, yakan shafi kowa ba mutum guda ba. Za ki fi ni shiga matsala. Kin san komai don haka a bar kaza cikin gashinta. Tun lokaci bai ƙure ba ya kamata a ɗau mataki."


"Kasheta zan sa a yi."


Kai tsaye ta furta tana fidda hucin ɓacin rai. Kawu ya dubeta sosai, duk da cewar yana shuka abubuwa a doron ƙasa, bai taɓa tunanin ya kashe rai ba.


"Kina ganin hakan zai haifar da ɗa mai ido? Kisa na nufin abubuwa da dama ciki kuwa har da rabuwarki da shi Hussein don za ki ƙare a kur..."


"Dakata, ai ba ni zan kashe ba. Zan saka a kashe ne. Mace ƴar uwarta zan saka, ita kanta ba za ta fahimci komai ba. Na santa a bakin Dikko, mayyar kuɗi ce da za ta iya aikata komai saboda shi. Don haka ka bar min wuƙa da nama yanda ka ce, za ka sha mamaki nan da awannin da suka rage kafin safiya."


Kawu ya jinjina kai, suka ƙara shawarwarinsu sannan ya fice.


A gaggauce Hajiya Zeenat ta kira Hajiya Batool ta ba ta labarin komai har shawarar da suka yanke.


"Wannan ya yi kuma ina goyon baya dari bisa dari. Gwara tun wuri a yi ta kuma ta ƙare."


Da wannan suka yi sallama ta kira Chairman a waya. Cikin gaggawa ta ce


"Ka turomin lambar yarinyarnan."


"Wa?" Ya nemi sani.


"HALIMA."


Dariya ya ɗan yi mai sauti, sanadin Halima ya san duk wani tarihi na Ramlatu, duk da cewa ya san da biyu ta faɗamasa, amma ya zamar masa tamkar ƙarin makaman yaƙi a wurin iyayen Ramlatun har ya same ta. Sanadin wannan ne ya sanya har holewa ya yi da ita na sati kafin ya biya ta da maƙudan kuɗaɗen da suka kusa zautar da ita.


"Wani abu ne ya taso?"


Ya nemi sani.


A ɓangaren Hajiya Zeenat ta ja tsaki.


"Wankim hula ke neman kai ni dare, turomin yanzu-yanzu."


Daga haka ta katse kiran ta kwashi tarkacenta ta fita. Ba zai yiwu su tattauna da Halima a wurin ba. Hussein zai iya shigowa kowane lokaci.


Tun kan ta kai motarta lambar Halima ya shigo. Kai tsaye ta ɗauka ta kira bayan ta daidaita zama cikin mota ta rufe.


"Hello."


Halima ta furta.


"Kina magana da Hajiya Zeenatu mamallakiyar A&Z."


Hajiya Zeenatu ta yi shiru don ba ta san ta ya za ta soma bayani ba. Ga mamakinta sai ji ta yi Halima ta ce.


"Lah, na san wurin ai ina zuwa lokaci -lokaci. Ai kin taɓa zuwa inda nake aiki kwanaki can kika biya kudin haraji. Na sanki sosai. Ranki ya dade, Allah Ya ƙara girma."


Murmushi Hajiya Zeenatu ta yi, dagaske ba za ta samu matsala da wannan ba. Don haka ta muskuta.


"Halima ina son ganinki, idan ba damuwa a yau kuma a yanzu."


"Aa babu wata damuwa Hajiya, ki fadi inda zan zo na sameki kawai."


Nan Hajiya ta yi mata kwatancen gidan Hajiya Batool. Ta dinga amsawa daga bisani suka yi sallama bayan Halima ta tabbatar mata yanzun za ta taho.


***
Hajiya ta isa unguwar Yakasai ranta a tsananin ɓace, ko sashin Hajja ba ta shiga don tasan tsaf za ta hanata tada kowace magana. Kai tsaye ta wuce rumfar Malam Bello inda anan ne yawanci Kawunnan ke zama a sha hira kuma a tattauna matsaloli. Da yake rana ce, aikuwa ta ci sa'a ganinsu a rumfar. Su biyar zaune, Kawu Bello, Kawu Sunusi, Kawu Jamilu, Haruna sai Usman.


Kawu Bello na ganinta ya haɗe gira, ta ƙarasa ta zauna aka gaisa.


"Sai kuma kika ji an turo kuɗin Ramlatu ko?"


Kawu Usman ya furta yana washe haƙora da duk goro ya ɓata. Ta haɗe gira.


"Na ji Yaya, sai dai sam ba'a kyauta ba. Ba ku yiwa yarinya daidai ba. Kada ku manta Ramlatu ba yarinya ba ce yanzu, addininta ya ba ta damar zaɓen miji a karon kanta. Idan ma ku ka dauke batun ta, na tabbatar ku kanku ba ku tsaya wani dogon bincike a kan mutuminnan ba saboda.."


"Saboda yana da kudi ko? Haka kike so ki ce! Wato mu gamunan mayun kudi? Rabi yaushe kika sauya haka? Kina son ki nunamana ke da Khalid ku ka haifi Ramlatu?"


Kawu Bello wanda tun zuwanta ya ke a fusace shi ne ya hau wannan kumfar bakin. Hajiya ta ɗago ta dubeshi don tuni ta soma hawayen idanun sun ƙanƙance.


"Ba iko nake nunamaku da Ramlatu ba, amma fisabilillah duk irin munin ɗabi'u mutuminnan da na lissafamaku a baya bai hana kun murzawa idanunku

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login