Showing 180001 words to 183000 words out of 231786 words
Chapter 61 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt
"Um um, gwara ya yi baccinsa Umma. Ni gani ya yi yana juyewa zuwa kamannin Zaituna."
Umma ta yi murmushi.
"Gashinan dai, sai sauya kamanni ya ke."
Ta jinjina kai.
"Naga kin warware sosai yanzu, ko don kin ji labarin auren Chairman ne?"
Umman ta karashe da dariya, itama dayake abinda ke ranta kenan sai ta sa dariyar.
"Umma bari kawai, sosai fa na ji dadin rabuwa da alaƙaƙai."
Dariya sosai ta ba Umma.
"Kai Ramlatu ba ki da dama, wato alaƙaƙai? Ko ya suka ƙare da Kawunnaki?"
Ta ɗan taɓe baki. Chairman a farko cewa ya yi dole Kawu Bello ya biyashi kudaden da ya kashemusu, daga karshe dai ya yafemasa ya ce komai ya wuce.
"Yanzu ki ka zo?"
Muryar Amrah ta katse su. Suka dube ta.
"Yanzu na zo, sannu ya jiki"
Amrah ta amsa tana kokarin mikewa zaune, cikin sauri Ramlat ta karasa ta taimaka mata. Ita ta yi mata rakiya bandaki ta yi fitsari da kuma brush sannan suka dawo. Umma kuwa ta gyara shimfidar ta kwantar da ita.
Ramlat ba ta wani jima ba ta yi musu sallama ta fice zuwa wurin aikinta. Tana tafe tana tunani, idan har Hussein zai iya mance ta ko a whatsapp bai neme ta ba, ita kuwa meyasa ba za ta dangana ta hakura da shi ba? Ta gama saddaƙarwa babu ita a ransa, ba ya ta tata. Don haka tana ji har zuciyarta ta hakura da soyayyarsa. Da gaskiyar Auta A'isha da ta taɓa ce mata gani take kamar Hussein ya fi ƙarfinta, yanzun kuwa ta yarda kuma ta gasƙata. A hankali ta sa bayan hannu ta share kwallar da ta cika idanunta. Muddin zai faɗomata a rai to fa sai ta ji kwalla.
Wayarta ta ɗauki ƙara, ta kai duba. Baban Hanif, kamar yanda ta sanya sunansa, wani ne da ba su yi ko sati da haɗuwa ba, ta kai yara shopping, a farko ya dauka tana da aure don haka ya hakura, sai dai haduwarsu ta biyu a kofar gidan Hisham kasancewar shi gidansa a Badawa Layout yake, ya ganta. Ya san Hisham don haka bai ƙasa a gwuiwa ba ya faka motarsa ya sauko suka gaisa da Hisham, ta gaidashi ta shige cikin motarta. A bakin Hisham ya ke jin cewar ba ta da aure, anan ya nunawa Hisham yana so. Hisham ya yi shiru a sannan, a karshe ya nunamasa ba ruwansa ya nemi soyayyarta. Da kansa ya yiwa Ramlat magana ta fito daga motarta, ta tsaya ta dan saurareshi. Ita kuwa ganin tunda har Hisham bai hana ta kulashi ba, kuma aminin Hussein ne, to tana da tabbacin babu alamar Hussein na sonta. Wannan yasa ta dangana ta hakura ta ba Baban Hanif dama.
Sauke ajiyar zuciya ta yi ganinhar wayar ta katse ba ta ɗaga ba. Ya ƙara kira ta ɗaga. Bayan amsa sallama ta ba shi uzurin tuƙi dole ya hakura.
***
"Shi kika tsayar kenan matsayin miji?"
Tambayar Baba Dakta ya sa gabanta ya faɗi, kanta a ƙasa yayinda yake zaune saman darduma idanunsa sanye da gilashi yana duba wani littafi na addini. Ta haɗiyi miyau, ta hakura yanzun za ta auri Baban Hanif. Ko ba komai ta yaba da hankali da nutsuwarsa. Hatta da Hajiya wannan karon da ma yan uwanta kansu, hankalin ya kwanta da shi.
"Eh Baba."
"Ramlat, kamar yanda ki ka amince da aurensa, bana son jin wata magana ta ɓullo daga baya."
A hankali hawayenta ya zubo, ba wanda ya fadomata a rai sai Aliyu da kuma yanda aka yi gumurzu a lokacin bikinsu. Abbanta ta tuna wanda a yanzun ta ke kallon Baba Dakta kamar shi. Basu da hadi sai zumunci tun shekara da shekaru da ya kasance Baba Dakta har yana da karfin ikon yanke hukunci a kan iyalin Abbansu, kuma ta zauna.
"Na ba ki nan da kwanaki uku, ki yi tunani dakyau, idan har kin amince ki zo ki sanar da ni. Zan ba shi damar ya turo magabatansa. Allah Ya zaɓamaki abinda ya fi alheri."
Ta kasa amsawa a fili sai a zuci, jiki a sanyaye ta mike ta mishi sai da safe ta kama hanyar gida. Kiran kenan daman, koda ta isa gida ba ta ɓoyewa Hajiya komai ba. Hajiya ta yi murmushi.
"Yaron ya san abinda ya ke yi da alama, kuma ko ba komai ɗan babban gida ne tunda Kakansa ma abokin Kakanki ne, wato Mahaifina. Zuri'ar Imam Shu'aibu Lawwali bani da shakku a kansu da yardar Allah. Kuma ke a dadinki ma tunda ba gida daya zai haɗaku ba da matarsa."
Ramlat ta yi shiru jikinta a sanyaye kawai tana sauraron Hajiya. Ta daure ta yi murmushin da bai kai zuci ba. Tana ji a ranta ko mutuwa za ta yi, wannan karon ba za ta ba iyayenta kunya ba. An yi ta kuma an ƙare.
A wannan yanayin Munir ya shigo gidan a fusace, suka dube shi. Oyoyon da su Affan ke mishi bai amsa ba. Bayan zamansa Hajiya ta dubeshi bayan amsa gaisuwarsa.
"Lafiya kake kuwa?"
Ya yi kwafa.
"Hajiya, wallahi Bilkisu ta haukace. Ba ta da hankali. Akan zama a gaban mota ta kama Hunainah da duka."
"Da cikin?!" Fadin Hajiya da Ramlat har suna hada baki.
"Na gaji! Wallahi na gaji da wannan rigimar ta Bilkisu. Haka kwanaki ta kawo wannan ƴar iskar ƙanwarta Salma, yan iskan samarinta na zuwa tafiya da ita night club ni kuwa na kora ta gidansu ba zan iya ba."
"Kai ba wannan ba, ka ce ta daki yarinya, yanzu ya ake ciki?"
Munir da har lokacin bai huce ba yana aikin karkaɗa mukullin hannunsa, ya dubi Hajiya.
"Ba ta yi mata rauni ba, ni ne dai na raunata Bilkisun, kuma na kora ta gidansu na sake ta."
"Innalillahi wa inna ilaihir raaji'un! Kana da hankali kuwa? Yanzu kai ba za ka iya hakurin zama da mace ba? Haba Muniru! Ai idan rai ya ɓaci, hankali ke dawo da shi."
Ya saki baki don mamaki, duk irin cin kashin da Bilkisu ke yi amma ana kiran meyasa ya sake ta? Hajiya sosai ta yi faɗa ta ce ta ba shi nan da gobe ya maida aurensa da Bilkisu kafin ransa ya ɓaci. Ganin bai samu goyon baya ba haka ya tattara ya fice sai gidan Baba Dakta. Nan ma dai duk kanwar ja ce, sai dai ɗan saukin da ya samu jin cewar Baba Daktan zai kira Kawu Jamilu su je gidan tare a washegari.
***
Kwanaki ukun da Baba Dakta ya ba Ramlat na cika, bai yi ƙasa a gwuiwa ba ya ƙara kiranta don jin ta bakinta. Kai tsaye cikin fawwalawa Ubangiji lamarinta ta ba shi damar yi mata zaɓi a wannan karon.
"Idan har shi ka zaɓarmin Baba, na amince zan zauna da shi kuma ba zan ba ku kunya ba."
Baba Dakta sosai ya ji dadin batunta, ya sa mata albarka karshe ya ce duk abinda ya yanke daga baya za ta ji. Da wannan suka ajiye maganar.
"Kar ki yi gaggawar amincewa da Baban Hanif." Amrah ta furta bayan Ramlat fitar Umma daga dakin kasancewar ta dawo gida an sallame su. Ramlat da ta ƙurawa Zayyan idanu, yaron Amrah, ta yi murmushi.
"Ba zan yi ba in sha Allah. Watakila shi ne alherina, na dai bar wa Allah zaɓi, duk abinda Baba ya yanke kaina shi ne daidai. Idan ya amince da aurena da Baban Hanif shikenan."
"Ba ki tunanin Hussein kan iya dawowa watarana?"
Ta hadiyi miyau a kokarinta na danne damuwarta.
"Koda ya dawo mene ne haɗina da shi? An faɗamaki kalmar so ta taɓa shiga tsakaninmu?"
Amrah ta sauke ajiyar zuciya, ta sani da gaskiyar Ramlat. Hussein bai furta yana sonta ba, kuma ko a waya ba ya nemanta.
"Amma sai naga kamar yana sonki."
Ta girgiza kai.
"Tunaninki kenan, yanzu dai a bar zancen ba shi da wani amfani."
"Ai shikenan. Allah Ya yi maki zaɓi na alheri."
Daga haka Amrah ba ta kara tada zancen ba.
***
BAYAN KWANAKI UKU...
BAZATA.....
Tana kwance a saman doguwar kujera tana karatun wani littafin hausa mai suna KE ALHERI CE a wattpad, dariyar Nene ta ke yi sosai har ɗankwalinta na zamewa. Tana sanye cikin riga da siket ƴan kanti da ya yi mata kyau. Ummi da su Ansar suna farfajiyar gidan su na wasa, sai ji ta yi su na ihun oyoyo Uncle. Ta yi ƙasaƙe tana sauraro can kuma ta yi murmushi don jikinta ya ba ta idam ba Hisham ba toh Hilal. Mikewa zaune ta yi ta gyara zaman ɗan kwalin kanta, ta mike gaba daya da zummar ɗauko mayafi, sai dai sallamar wanda ta ji ya katse dukkan yunƙurinta.
"Wane ne ya zo ne nake jin...Au, Husseini?"
Hajiya dake fitowa daga daki bayan idar da sallah ta ke tambayar, ganin wanda ke tsaye bakin ƙofar suna kallon kallo da Ramlat yasa ta katae tambayar. Ramlat da sauri ta fada daki don ɗauko hijabi, shi kuaa ajiyar zuciya ya sauke ya ƙaraso ya durkusa yana gaida Hajiya da bakinta ya ƙi rufuwa. Gaba daya ya sauya sai ka ce wanda ya fita ƙasar waje, ya ƙara kyau da ƙiba abinsa.
"Dama za ka dawo ɗannan? Ni na ɗauka kuma sai dai mu bi bayanka da kayanka. Nan abokinnaka shima ya zo ya gama jajensa."
Dariya ta ba shi.
"Ayi hakuri Hajiya, na yi laifi ko a waya ban sanar maku batun zuwana ba."
"Ba komai ai."
Nan kuma aka shiga hirar yaushe gamo, Hajiya ta aiki Ummi kiran Maminta don kawo ruwa. Ta fito cikin dakin ba ta ko kalli inda yake ba ta shige kicin. Hussein yana nazarinta a hankali. Har ta kawo ruwa ta ajiye da murya ƙasa-ƙasa ya ce.
"Kin fi koyaushe kyau."
Ta ɗan dubeshi, ya watsamata lumsassun idanunsa yana murmushi. Ta kauda kai kirjinta na bugu da sauri-sauri. Zubamishi ta shiga yi a kofi hannu na rawa. Koda ta miƙa maimakon ya karɓa sai ya ɓige da tambayar Hajiya.
"Na yi zaton zan tarar an yi bikin Ramlat."
Ta dube shi ranta na zafi, wato dai yana kara tabbatar mata babu ita a shafin rayuwarsa. Ta mike ta nufi daki sadda Hajiya ta soma ba shi labarin yanda ta kaya da Chairman.
Bai katse ta ba har ta kammala.
"Allah Ya kyauta." Shi ne kadai abinda ya furta. Daga bisani ya sanyo wata hirar daban inda a karshe ya kira Dada a waya video call ya haɗa su suka gaisa, Dada godiya ta shiga yi sosai da sanyawa Ramlat albarka. A karshe ta nemi gaisawa da Ramlatun, Ummi ta karɓi wayar ta shige dakin a guje ta kai wa Ramlat da ke kwance saman gado.
"Mami, ga Dada."
Tana shirin magana sai ganin fuskar Dada ta yi saurin mikewa zaune ta maudo fara'arta. Suka gaisa har ta ba Hafsat ma suka gaisa. Godiya kam ta sha shi, tuni Ummi ta fice daga dakin. Daga bisani suka yi sallama ta katse kiran, dama a wayar Hafsat ne. Hankalinta ya kai ga hotonsa dake saman screen din, ya rungume throw pillow guda a kirjinsa yana kwantar da kai yana murmushi. Sai take ganin kamar ita ya ke yiwa murmushin hakan yasa ta yi saurin jan guntun tsaki gami da hararar wayar kadan kafin ta cillar da zummar sai Ummi ta shigo ta maida mishi.
Kwanciya ta yi har sai da ta ji ƙarar shigowar saƙo a wayarta. Ta jawo ta duba, lambar da ba ta sani ba. Ta bude.
_*"Wayartawa itama raba ni da ita kike son yi yanda ki ka yimin iyaka da HEART?"*_
I just published "BABI NA HAMSIN DA HUƊU" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://www.wattpad.com/1013598891?utm_source=android&utm_medium=com.whatsapp&utm_content=share_published&wp_page=create_on_publish&wp_uname=Rufaida-Umar&wp_originator=1t7u8q%2B2i2CmVekKWI5wFx%2BLsRJJivM5TtUSxqfucEgX0H3IsSDvgfmbOaj%2FRM2R1oO3SAwAvV7%2FIJ95dbqOXcbxCoIbZ9MIciCSdP0fW4VijXfBR0gyHI42Cn5Za4Rc
🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️
_*Rufaida Umar*_
Bismillahir Rahmaanir Raheem.
54)
Ranta idan ya yi dubu to ya ɓaci, takaici ya sa ta wurgi da wayar gami da hararar wayarsa da ke ajiye ta ja tsaki. Ta rasa gane me Hussein ya ke nufi da ita, ba ta san wane matsayi ya ajiye ta ba. Ta cije lebbanta tana karkaɗa ƙafa daidai sadda Ummi ta faɗo ɗakin a guje.
"Mami, wai inji Uncle.."
Ba ta bari ta ƙarasa ba ta yi saurin yi mata nuni da wayar.
"Maza dauka ga ta can ki miƙa masa."
Ummi wacce ba shi ya aiko ta ba, ta girgiza kai sai dai ba ta fasa ɗaukar wayar ba kazalika ta ci gaba da zancenta.
"Wai ki zo zai tafi."
Harara ta watsawa Ummin.
"Ki ce ba ki ganni ba."
Ummi ta bude baki.
"Mami kin fa hana mu.."
"Kika karasa sai na buge bakinki. Naji ba zan zo ba wuce ki ban wuri."
Rai ba dadi Ummin ta fice, Ramlat ta sauke ajiyar zuciya. Kwanciya ta yi sai dai karatun littafin da ta ke yi ma ya fice a ranta. Ba zato ta ji muryar Hajiya.
"Ramlatu yaushe ki ka sauya? Baƙo ya zo domin ya gaishemu shi ne za ki aikamasa mugun kalamai? Me kike nufi da ba za ki je ba? Wani abun ya haɗa ku ban sani ba?"
Jikinta sai ya yi sanyi, Hajiya ta ba ta umarmin fita, a dole ta mike tana ba ta hakuri sannan ta gyara zaman hijabin ta fice ranta na tururi.
Ba kowa falon sai wata ƙatywar leda a gefe, don haka ta tsaya gami da juyowa da zummar komawa ciki, suka yi kiciɓus da Hajiya. Harararta ta yi.
"Ki je yana waje tare da yara. Tsaraba ya kawomusu. Ki mishi godiya don Dadarsa ta aikomin fura da nono."
"Toh." Ta amsa a ciki-ciki tamkar ba ta so sannan ta fice, ita dai Hajiya bin bayanta da kallo ta yi da mamakin wannan sauyi a fuska da gangar jikinta.
***
Yana zaune a mazaunin direba ƙafarsa ɗaya a waje, alewa ce a hannunsa yana kokarin ɓarewa Affan. Ta kauda kai daga kallonsa ganin ya ɗago nashi kan, kallonta yake da murmushi a saman fuskarsa. Sai kuma ya miƙawa Affan alawar ya dube su.
"Oya ku shiga ciki."
Dama haka suke jira musamman Ummi da ke rike da ƙatuwar ledar kayan kwalam da ya damƙa mata su je su sha. Ba ta son hararar da uwar ke watsomata wannan ta sa ita ce farkon sheƙawa a guje sauran ma suka mara mata baya.
Ta rasa dalilinsa na korar yaran don haka ta ja numfashi ta furzar. Cikin dakiya ta dubeshi kirjinta na bugu da sauri-sauri.
"Hajiya ta ce na kara miƙa mata godiya. Allah Ya saka da alheri. Mun gode sosai da ɗawainiya."
Ya murmusa yana shafa sumar kai. A hankali ya kai hannu ya bude dayan murfin na motarsa. Dubanta ya yi.
"Dan zagayo ki zauna ki ban aron koda mintuna biyar ne, magana zamu yi."
Ta yi shiru ba ta tanka ba, karshe ma ta daure fuska don ta san wani sabon rainin hankalin ne.
"Please." Ya furta a sanyaye, sai ta ji ba za ta iya jan musu ba don haka ta zagaya ya bita da kallo har ta shigo ta zauna. Shiru ya biyo baya har dai ta ƙosa amma ba ta ce komai ba, shi kuwa yanda ta ke hura hanci ke ba shi mamaki da dariya. Ya ɗan murza karan hancinsa kafin ya soma magana cikin nutsuwa.
"Satina sama da biyu a Adamawa, ba ki samu damar yimin ko gaisuwar juma'a ba, why?"
Ranta ya sosu ainun.
"Ina tunawa da wadanda suka tuna da ni. Bana sanya ka layin wadanda suka zamemin wajibi na nema balle na gaida."
Ɗif ya yi kamar mutuwa ta ratsa, ta daurewa zuciyarta ba ta kalleshi ba sai dai ta ji wani irin sanyi a zuciyarta ko ba komai ta ɗan huce daga maganar da ya gasamata. Sai ta tsinci kanta da murmusawa. A hankali ta saci kallonsa don ganin yanayinsa, ga mamakinta murmushi sosai yake haƙoransa a waje, ya juyo rabin jikinsa ya tallafi haɓarsa da hannunsa ɗaya yana kallonta. Ta kauda kai.
"Hakan ma na gode sosai. Kin burgeni. Rashin wancan mutumin ne yasa ki ka sauya har ki ke gasan magana ko? Hum, za ki huce."
Ba ta ce uffan ba hakan yasa ya gama shan ƙamshinsa ya ɗora.
"Alhamdulillah, na sadu da iyaye da yan uwana lafiya. Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Ubangijin Talikai. Wannan yana ɗaya daga cikin dalilan da har abada Hussein ba zai mance da Ramlat ba. Na je Mubi kuma na je Maiduguri. Ban taɓa zaton zuwan rana makamancin hakan ba, komai ya faru bisa jajircewarki akan dukkan lamurana. Na gode. Ina kara godiya da fatan alheri gareki. Har abada ba zan mance da halaccin da ki ka yi gareni ba. Allah Ya ba ki abinda kike so kuma ya ke sonki."
Ta dubeshi, idanunsa a lumshe har lokacin murmushin ya ke, ganin zai bude yasa ta janye nata idanun kirjinta na bugu. Ta rasa wane irin so ne na Hussein a zuciyarta. Son da ba ta jin ya kai irin wanda ta yiwa ALIYUNTA. Idan Aliyu da dadin kalamai ya rinjayi zuciyarta, ta rasa da me Hussein ya rinjayi nata zuciyar.
"Zan tafi."
Abinda ya ce kenan.
Ta sa ƙafa kawai ta fice ta rufe mishi ƙofar ba ta ce uffan ba kamar yanda bai tanka mata ba har ta yi gaba abinta. Murmushin ya ƙara yi gami da lasar lebbansa. Allah kadai Yasan sirrin da ke cikin zuciyarsa. Ya sauke ajiyar zuciya ya tashi motar ya fice.
***
Hajiya Zeenatu ta rausayar da kai ta ƙara duban Hajiya Batool da ta saki baki tana kallonta, murmushi ta saki ta ce.
"Kina mamaki ne?"
Hajiya Batool ta furzar.
"Kema ai kin san dole akwai mamaki Zeenatu, shi Hussein din ne ya sauyamaki mota? Har ya ke tambayarki abinda kike da buri a yanzu? Kuma ya amince da ku bar ƙasar babu wata gardama? Anya kuwa Zeenatu ba wani tarkon ya ke shiryamaki ba? Ƴan uwansa kuma sun yarda da zamanku tare? Anya babu lauje cikin naɗi?"
Ɗaure fuska kaɗan Hajiya Zeenatu ta yi.
"Me kike son ki ce? Na fiki sanin Hussein, bai iya yaudara ba. Ko a baya balle kuma a yanzu. Duk isar mutum bai isa ya kawo mishi wargi ba balle ya yi ƙarya dominsa."
Hajiya Batool ta tsaya kawai tana yi mata kallon sakarya.
"Ke ba wannan ne damuwata ba, wasu shegun ƙuraje ne suka fesomin a cinyoyina. Ba ƙaiƙayi balle zafi, su dai gasunan ne kuma suna ɗurar ruwa."
Hajiya Zeenatu ta katse tunanin Batool, kusan ma katse zancen ta yi don ba ta son ji.
"Ya kamata dai ki je asibiti. Tunda dai ko ba komai za ku ci duniyarku da tsinke yanzun."
Suka sa dariya gami