Showing 165001 words to 168000 words out of 231786 words

Chapter 56 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

da ganin Chairman?"


Hunainah ta furta tana duban dariya ƙasa-ƙasa na zolaya.


"Ke Hunainah! Kin riga ni a fili amma nikam na rigaki a zuci. Ni wani kallo ma na gani kamar a duniyar romeo da juliet wallahi."


Abinda Rafee'ah ta ce ta basu dariya sosai idan ka cire Ramlat wacce ta san ba haka tsakaninta da Hussein, asalima ita ke kiɗa da rawarta. A fakaice ta share kwallar da ta cika idanunta. Shigowar Munir ya sa suka bar maganar, hakan ya fi komai yi mata dadi. Anan ya ke sanarmusu Hussein sun wuce tare da AlHassan da Hisham daga can za su biya wurin police station.


"Af, nikam Yaya su waye suka yi wannan aika-aikar? Sun yi magana?"


Ya taɓe baki jin tambayar Rafee'ah.


"Eh toh, su na ta dai walagigi da hankulan jama'a, amma ko mene idan an shiga kotu gaskiya za ta yi halinta. Mace ce, sunanta Halima. Ta dai yi ikrarin kishin Ramlatun ne yasa ta aikata hakan. Ganin za ta auri Chairman. Wannan shi ne rashin sani wanda ya fi dare duhu. Idan ma da gaske take, toh ta yi a banza."


"Ya sunanta?" Ramlat ta tambaya a hanzarce. Ya ɗan yi shiru don shi kam ya mance ma da sunan.


"Nan fa ɗaya, na mance."


"Halima?"
Ta tambaya gabanta na faɗuwa.


"Yes! Sunan kenan. Amma ya aka yi ki ka sani?"


Girgiza kai ta yi, ta ba su labarin takun saƙar da suke yi tun zuwanta ma'aikatar Revenue kafin ta bar shi.


"Amma ba na tunanin ta san akwai wata alaƙa tsakanina da Hussein."


"Ki kwantar da hankalinki ke dai, ko ma mene yanzu kam ai zai fito fili tunda an cafke ta."


Ramlat ta girgiza kai karo na biyu tana duban Yaya Munir.


"Hakane, amma ban taɓa zaton tsanar da Halima ta yimin ya yi ƙarfin da ko bindiga aka ba ta za ta kasheni ba, na yi mamaki matuƙa."


"ƊAN ADAM aka ce maki, mai wuyar gane hali. Allah Ya kyauta." Cewar Amrah. Suka amsa da Amin. Ita dai Ramlat har sannan mamaki bai sake ta ba, ta ƙara jin tsanar auren Chairman.


***
Chairman Aliyu Dikko, wanda ganin mijin Hajiya Zeenat da wani photocopy dinsa ya ɗaurewa kwanya, ya kasa haƙuri sai da ya fiddo waya ya dannamata kira. Har ya katse ba ta ɗaga ba sai a karo na biyu sannan ta ɗaga.


***


Lokacin tana gida ta hargitse tana jiran shigowar Hussein don su bar garin zuwa wata Jahar kafin lamura su kwaɓe. Ga dai tana ta kiransa ya ƙi ɗagawa. Lokacin ne kuma kiran Chairman ya shigo, kamar ba za ta ɗaga ba a farko, sai dai ta ɗaga.


"Nikam Zeenat, mijinki Hassan da Husseini ne?"


Ta saki rigar Hussein da ta ke shirin sanya wa a akwati. Gaskiyar Gora kenan da yace su na tare?


"Lafiya? Kin yi shiru?"


"A ina ka gan su?"


Daga amsar ya fahimci ruɗewarta. Kai tsaye ya ce.


"A asibiti na je duba Amaryata Ramlatu, kinsan harbinta aka yi. Shi ne na tadda su a ɗakin. Sai wani hararata yake yi kamar na kashemasa wani. Na yarda da zarginki, son yarinyarnan yake kuma kwalalensa."


Tusa Hajiya Zeenatu ta saki wanda ya tahomata da guntun kashi. Ta sharce gumi ta hau safa da marwa.


"Yanzu a can ka baro su? Wane asibitin?"


"Zan miki ƙarya ne? Nawa za ki ban idan na miki ƙaryar? Idan kina son ganewa idanunki ki taka ki je."


Ya sanarmata asibitin, ba ta jira komai ba ta katse wayar. Banɗaki ta shiga ta sauke nauyin cikinta, ta kimtsa jiki sannan ta fito. Sun rabu da Hajiya Batool akan zasu haɗu su je wani ƙauye domin a yi musu aiki maikyau. Sai dai ba ta jin za ta jure wanzuwar Ramlat a doron ƙasa, za ta sa a karo na biyu a kashemata ita. Duk abinda zai faru sai dai ya faru.


Ta fice daga gidan gaba ɗaya.


***
Chairman da tun bayan kammala wayarsu da Zeenatu ya yi shiru yana tunani.


"Ina maka rantsuwa da Allah zan sa a kashe Ramlatu idan ni ban kashe ta da hannuna ba muddin ta yi kuskuren shiga rayuwata da mijina."


"Dakata!" Ya ba direba umarni, ganin haka direban ya ja ya yi parking a gefe.


Chairman ya fidda waya ya ƙara kiran Hajiya Zeenatu, yana ta ringing ba ta ɗaga ba. Haka ya yi ta dialing shiru, don haka ya yi saurin cewa direban ya mishi magana da daya daga cikin abokan tafiyarsa. Da sauri direban ya fita zuwa ɗayar motarya kira.


"Sir."


Chairman ya dube shi.


"Ku juya ku koma asibitinnan, ku tabbatar kun kula da marar lafiyarnan. Ina zuwa."


Ya hau lalube cikin hotunansa har ya fiddo hoton Hajiya Zeenatu a wajen wani taron biki da suka hadu. Koda wasa ban yarda ku bar wannan matar ta shiga dakin ba."


Ya jinjina kai cike da girmamawa ya karbi odar ya koma motarsa. Motar Chairman ya wuce su kuma suka juya zuwa asibitin.


***
Hussein ya yi shiru kawai yana kallon Halima wacce har sannan ta ƙi faɗar gaskiya. Sai ka rantse hankalin a kanta yake, amma ina! Zuciyarsa na wani ɓangaren, sai hura hanci ya ke yana ƙara cin magani. Garin Kanon ta fita ransa, so yake su juya tare da ɗan uwansa kawai. Sai dai kafin nan yana son nunawa Hajiya Zeenatu kurenta. Yana son maka ta a kotu yanda za ta fuskanci fushin hukuma, duniya kuma ta san da abinda ta aikata.


Wayar AlHassan ta yi ringing, gani Dada sai ya yi murmushi ya fita daga station din. Hisham ya ɗan daki kafaɗar Hussein kaɗan, dubansa ya yi kawai ya watsamasa harara ya kauda kai.


Dariya sosai Hisham ya yi.


"Ikon Allah, to ni kuma me na yi? Nasan fa me ke cin ranka"


Hussein ya gyara tsayuwa gami da ɗan lumshe idanu bai ce uffan ba.


"Kar ka yiwa kanka saki na dafe, tun kafin lokaci ya ƙuremaka gwara ka faɗamata abinda ke ranka."


Ya dubi Hisham.


"Me kake nufi? Kuma wa kake nufi?"


Hisham ya bude baki zai magana ya ɗaga mishi hannu.


"Malam bana son shirme, yimin shiru. Kai a komai sai ka sanya wasa da zolaya. To ka fita idona."


Dariya sosai ya ba Hisham. Daidai sadda AlHassan ya dawo ya dubesu yana dariya.


"Lafiya dai? Tom and Jerry?"


Murmushi kawai Hussein ya yi.


"Dada ce?" Ya tambaya. Gyada kai AlHassan ya yi yana murmushin shima.


"Yes, ita ce. Sai dai ban fadamata komai ba, na dai ce ina tafe da wani babban albishir."


Jinjina kai Hussein ya yi.


"When? Nima na ƙagu na gan ta."


"Very soon in sha Allah."


"Maiduguri fa?"
Cewar Hussein kamar zai yi kuka.


Dariya AlHassan ya yi.


"Duk za mu je da yardar Allah. Saboda rashinka na ɗauke ƙafa, ganina yana sa Hajjo kukan tunawa da kai. Wannan ta sa tsakaninmu sai waya."


"Ina son hukunta ta." Hussein ya fadi zuciyarsa na zafi, fuskar Hajiya Zeenatu ya ke haskowa da kuma cuɗanya iri-iri da ya yi tare da ita.


"Muje daga waje please. Nan ba wurin tattauna wannan zancen ba ne."


Suka dubi Hisham mai magana, su ka maida hankali ga Halima da ta yi musu ƙuri da kumburarrun idanunta. Duk hirar da ake yi tana ji, kalaman Hussein na ƙarshe ya sa tsoro ya ƙara kamata. Kada dai ita yake nufin a hukunta? Ita kam ta shiga uku. Ba ta mance shawarar da kaninta ya ba ta ba da ya zo.


"Idan kinsan ba da gaske kike ba Yaya Halima, ki fito ki fadi gaskiya kafin lokaci ya ƙuremaki. Nidai gaskiya ban yarda da abinda kika faɗamin ba."


Ta share hawaye tana ci gaba da kokwanto a ƙasan ranta. Ta faɗa ko kuma ta yi shiru? Ita kanta ta rasa wanne za ta zaɓa. Har suka fice tana kallonsu. Ta bi wurin kwananta da kallo, ta ja majina. Anya Hajiya Zeenatu dagaske ta ke za ta cire ta a wannan taskun? Shiru ta yi, karshe ta yanke shawara ta aika ƙaninta wurin Hajiya Zeenatu ya yi mata bayanin halin da take ciki.


***
Ramlat ta yi shiru, ita kadai a dakin, su Rafee'ah sun wuce, sai Hajiya dake bandaki ɗauro alwalar sallar Azahar.
Nos Khadija ta kwankwasa ta shigo tana jan kayan dressing din ciwo a ɗan keke. Suka yiwa juna murmushi. Ɗan zaman da ta yi a asibitin sun saba, mace ce mai kirki.


"Su kuma waɗannan ƴan sandan da aka zubamana a bakin ƙofa fa? Da alama dai Angonnaki na baki kulawar da ta dace."


Wannan ne karon farko da ta ji haushin Nos Khadija, sam ba ta son abinda za'a haɗa ta da Chairman. Tun kafin su Munir su tafi, suka zoda zummar tsareta bisa umarnin ubangidansu. Har ta soma faɗa Munir ya ce ta rabu da shi kawai. Shi ya sani. Taɓe baki ta yi ba ta ce komai ba. Daidai sadda Hajiya ta fito, suka gaisa da Nos Khadija gami da yin ƴar raha don mace ce mai tsokana da kuma ja da wasa. Tana cire Bandage din kafadar suna ta hira abinsu, bayan ta goge ta ƙara rufewa sannan ya dubi Ramlat jin Hajiya na faɗan ba ta son cin abinci.


"Ki dinga cin abinci don Allah Ramlat, haba yar uwa, ina yabonki? Ki ci yanda idan na ba ki magani ba zai sanyaki jiri ba. Yanzu zan dawo."


Ta gyada kai ba don ta so ba, ita kawai komai ma ba dadi ya ke mata.


***
Hajiya Zeenatu tunda ta doshi barandar ɗakin da Ramlatu ta ke ta hangi wasu masu kayan ma'aikata tsaye a bakin ƙofar ta yi turus. Wuƙar da ke cikin jakarta yasa ta kasa ƙarasawa, juyawa ta yi tana tunanin ina mafita? Ta ya za ta cimma burinta? Yanzun ta tabbatar Hussein ba zai kara yi mata kallon mace mai daraja da ƙima ba a idanunsa, amma tabbas idan ta bar Ramlat na yawo a doron ƙasa tofa shakka babu, wataran za ta ji batun aurensu. Abinda ba za ta taɓa ɗauka ba har abada. A kan idanunta, Nos Khadija ta shiga, hakanan a kan idanunta ta fito. Wata dabara ta faɗomata don haka koda Nos Khadija ta zo wucewa ta wurinta ta saki fuska sosai suka gaisa.


"Nace don Allah idan babu damuwa, ina son ganinki."


Nos Khadija ta bita da kallo, a shekaru ta girme mata sosai hakanan kuma ba ta yi mata kama da wacce ta fito daga ƙaramin gida ba.


"Shikenan, ba ni minti biyu."


Hajiya Zeenatu na murmushi ta gyada kai. Ba jimawa Khadija ta dawo suka ɗan fita waje.


Shiru Khadija ta yi tana jin bayanan Hajiya Zeenatu. Kirjinta ya shiga dukan uku-uku.


"Ki sani, wallahi-wallahi duk wani jin dadi na rayuwa kin sameshi kin gama matukar kika yimin aikin da na sanyaki. Zan ba ki duniya iyakar ƙarfina. Za ki taka duk ƙasar da kike so, za kuma ki shiga duk inda kike so a faɗin garinnan ba wanda ya isa ya ce maki don me?"


Jikin Khadija ya ɗauki wani irin rawa. Tunda take a duniya, tunda ta ke, ba ta taɓa jin lamari irin haka ba. Wani irin tsoron da ba za ta iya misaltawa ba ya shige ta. Daga yanayinta Hajiya Zeenatu ta gane babu nasara don haka ta bude jaka ta fiddo bandiran kudi ƴan dari biyar guda biyu ta miƙamata, Allah Ya taimaka babu jama'a a wurin, ta ɗago mata lafiyayyar wuƙa sabuwa fil ta nunamata.


"Ki zaɓi ɗaya Hajiya Khadija, idan ba haka ba ni da kike gani don na kasheki ba komai ba ne a wurina. Sai na ɓatar da ke da ma ƴan gidanku. Don haka zaɓi ya rage naki, na baki nan da awanni biyu, duk abinda kika yanke ki kira ki sanarmin. Kar ki manta rayuwarki a tafin hannuna yake."


'Ƙarya kike, Allah ne Mai iko da rayuwakanmu.' Nos Khadija ta fadi a fili don ba ta jin tana da kwarin gwuiwar faɗa a zahiri. Ta gyada kai kawai a fili, ta karɓi kudin ba don ta so ba ta zura a aljihun wandonta.


"Ina tsumayenki. Ga lambar wayata." Hajiya Zeenatu ta fadi karo na biyu tana miƙamata karamin complimentary card mai dauke da numbobin wayoyinta a jiki. Nan ma Khadija gyada kai ta yi.


"Je ki." Ta ba ta umarni, ta juya da sauri ta shige ciki har tana cin karo da wata mai tsohon ciki.


"Yi hakuri don Allah." Matar ta bita da kallo kawai gami da jan tsaki irin na masifaffun masu ciki. Haka ta wuce ta a mita.


Koda ta karasa dakin Nurses, ba ta tarar da kowa ba don haka da sauri ta ciro kudaden hannu na rawa ta cusa a jaka ta zuge zif. Bandaki ta shige ta soma watsawa fuskarta ruwa tana salati a ƙasan ranta. Yau da wane rashin sa'a ta fito daga gida? Kawai sai ta shiga hawaye, nutsastsiyar fuskar Ramlatu da kuma na Hajiya mai cike da dattako da kamala take tunawa. Ta ya ya? Ta wace hanyar za ta iya kashe wannan baiwar Allahn? Duk da dai idan ta so abu ne mafi sauki a aikinta, za ta iya kasheta irin kisar da zai yi wuya kafin a gane ita ce silarsa. Amma ina! Ba'a ba ta wannan tarbiyyar ba kuma ita ba haɗamammiya ba ce akan abin duniya. Kaɗan ma da ta ke samu ya wadatar da ita.


Sai da aka kwankwasa ƙofar sannan ta fito. Karo suka yi da Nos Jamila. Ta bita da kallo.


"Dije, lafiya?"


Murmushin yaƙe ta yi ta hau murza idanu.


"Ba komai, abu ne ya faɗa idanuna."


"Aa Dije, faɗamin gaskiya."


Girgiza kai ta yi, ba za ta iya ba, tana tsoron abinda zai sanadin rayuwarta.


"Ko haihuwar ki ka karɓa, don nasan halinki na tausayi."


Dariya ta ba ta.


"Oh na tuna, ashe fa ba duty naki bane yau." Cewar Nos Jamila karo na biyu.


Ita dai Khadija ta sulale ta fice daga ɗakin. Maganin ma kasa komawa ta ba Ramlat ta yi sai wata ta aika.


***
Hussein da AlHassan zaune a falon gidan Hisham suna cin lafiyayyen girkin Aisha. Gogan ci yake kamar an mishi dole.


"Wai Hussein lafiya? Ko kaima jinyar kake taya Ramlat?"


AlHassan ya fadi yana murmushi don tuni ya ɗago shi.


"Mene haɗina da ita? Kawai dai na damu da harbin ne, na kuma rasa waye zai yi ƙarya da ni ya harbe ta. Shiyasa na kasa fahimtar mai laifin, me ya sani tsakanina da ita da ya zaɓi hanyar kasheta ta amfani da ni."


"Da mamaki kam, amma ko ma mene in sha Allah nan ba da jimawa ba zai bayyana. Har wanda ake ɓoyemana."


Hisham ya furta yana kashe mishi io ɗaya, AlHassan ya yi kamar bai gansu ba ya ci gaba da kai loma yana murmushi. A yau jinsa yake kamar a duniyar gajimare tsabar murnar ganinsa zaune tare da ɗan uwansa.


Hussein din ma banda harara bai cewa Hisham uffan ba, saboda gudun zargin sai ya saki jiki ya ci abinci. Bayan sun kammala ya mike.


"Ina zuwa?"


Fadin AlHassan don ba ya son ya ji Hussein din ya matsa daga gareshi. Murmushi Hussein ya yi.


"Gidan Hajiya Zeenatu."


"Aa, bai kamata ka je kai kaɗai ba. Muje tare."


Jinjina kai Hussein ya yi cikin amincewa da zancen dan uwannasa. Suka ɗunguma suka fita, Hisham ya takamusu har ƙofa kafin ya dawo ciki. Kusan shima yau dai jinsa yake sak. Babu sauran damuwa.


***
RAMIN ƘARYA....








I just published "BABI NA HAMSIN" of my story "Ƙarfen Ƙafa". https://my.w.tt/S2N0l9OdWcb






🕯️ *ƘARFEN ƘAFA*🕯️


_*Rufaida Umar*_


Bismillahir Rahmaanir Raheem.


50)


Tun daga farfajiyar gidan ma'aikata suka dinga al'ajabin ganin ƴan biyunnan. Har dai Malam Bala mai guga ya ka sa hakuri.


"Yallaɓai ashe ku ƴan biyu ne."


Hussein suka dubi juna da AlHassan, kauna ta jini na ƴan uwantaka na ƙara ratsa zuƙatansu, banda kaddara me zai raba su? Su da suka rayu tare a mahaifa guda.


"Eh Malam Bala, we are twins."


Fadin Hussein wanda ya ƙarashe da kallon su John. Nan suka shiga washe hakora suna gaida AlHassan da fadin abinda ya bambantasu, hakan ya ba ƴan biyun matasan dariya. Hussein ya yi ciki yana murmushi, ya bar su da AlHassan. Yasan matar gidan ba ta nan kamar yanda ya ji daga masu gadin, don haka ya shiga bin ko'ina na falon da kallo. Tafkeken hotonsu shi da ita ya ƙurawa idanu kamar wani fulanin daji da bai san hoto ba.


"Ita ce. Makira."


AlHassan ya fadi a hankali, sai sannan Hussein ya juyo da rinannun idanunsa ya dubeshi.


"Idan na ce maka ban san ta ya ya na aureta na za ka yarda? Idan na ce maka ba da son raina..."


"Ba fa sai ka faɗi komai ba ɗan uwa, na maka farin sani na kuma san kalar macen da ka ke so. Ko ka mance cewa ka ban labarin haɗuwarku da tayin kaunar da ta yi maka? Ban san dalilin da yasa na kasa tunawa da hakan ba, ban kuma san dalilin da yasa na amince ka bar mu ne saboda ka auri wacce ka ke so. Amma ban taɓa kawo wa ita ce ba nasan dai babbar mace ce kamar yanda ka faɗi."


Sauke ajiyar zuciya Hussein ya yi gami da jinjina kai. Falon suka koma suka zauna. Nan kuma AlHassan ya shiga ba shi labarin abubuwan da suka faru a bayansa. Rasuwar Baba Naziru mijin Dada da kuma rasuwar ƴar uwar kakarsu da ta riƙe su kamar jikokinta da yaran cikinta suka haifamata ba su Dada ba.


"Allah Yay musu rahma. Yasa aljanna makoma. Baba Naziru ya rasu da bakin cikina."


Girgiza kai AlHassan ya yi.


"Kar ka ce haka. Wallahi har ya rasu kewar ka ya ke, ya kuma faɗa ya ƙara, ba halinka ba ne."


Hussein ya jinjina kai.


"Yaushe za ku tafi?"


AlHassan ya tambaya.


"A satinnan. Ina neman alfarma a wurinka, koda kun haɗu da ita kar ka nuna mata komai kamar yanda nima ba zan nuna ba."


Hussein ya faɗi idanunsa cikin na ɗan uwan. Da mamaki AlHassannya tambaya.


"Dalili?"


Hussein ya yi mishi bayanin duk abinda ya ke buƙatar yi, a farko AlHassan ya ji abin kamar babu amfani, a karshe kuma sai ya hau murmushi sosai.


"Good, hakan shi ne daidai."


Abinda ya ce kenan bayan gama sauraro. Hussein ya ɗan ciji leɓɓansa gami da shafa sumar kai.


Daga farfajiyar gidan kuwa, Hajiya Zeenatu ce ta shigo ta yi parking ta fito. Ta sauke ajiyar zuciya ganin motar Hussein. Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login