Showing 213001 words to 216000 words out of 231786 words

Chapter 72 - KARFEN KAFA Book 1 COMPLETE (By Rufaida Umar).txt

ɗakinta ta ɗauki zani da hijab, anan ta shimfida darduma ta yi sallar, sai da ta yi addu'a mai tsawo tana roƙarwa mijinta dukkan wata rahma da alheri kafin ta gangara ga iyayenta da kuma yaranta. A karshe ta kara nemawa Aliyu da Kakarsa gafarar Ubangiji da ma dukkan musulmai, wannan ya zamemata kamar farillah duk bayan kowace sallah.


Tana ninke hijabin tana murmushin tuna daren jiya, a karon kanta ta gama saddaƙarwa son da Hussein ke mata ya ninka ya kara ninka wanda ta ke mishi. Wasu kalaman ma da ya dinga furtawa, ita da kanta idan ta tuno jin kunya ta ke, amma ta san da yake shi din namiji ne, ko a yanzun zai iya maimaitawa. Sai kuma ta yi ƴar dariya kaɗan, ita kaɗai ta san me ta tuna. A ƙasan zuciyarta ta furta kalmar hamdala. Ta shagala cikin tunani don tuni ta kammala ninke hijabin ta koma kan zanin da ta ɗora. Ba ta ji shigowarsa ba, sai jinsa da ta yi ya jawota jikinsa ta baya, ya ɗora wuya saman kafaɗarta.


"Good morning."


Ya faɗi da muryarsa da ke hargitsata. Ta lumshe idanu tana tuna irin laushin da sumar kansa ke da shi sadda ta yi mishi riƙo son ranta.


"Ina kwana, fatan an tashi lafiya?"


"Idan na ce ban tashi lafiya ba, na yi karya. Na samu farin cikin da ban taɓa tsintar kaina cikinsa ba, na kuma yi baccin da ɓata lokaci ne tsayawa misalta daɗinsa. Kece rayuwata Ramlat, na yarda ba zan iya rayuwa da kowace mace a bayanki ba. Ba alƙawari nake daukar maki ba, kamar yanda ba da alfahari nake faɗin haka ba, abu ne da nake ji a jinin jikina. Yanayi ne da na tabbatar ke za ki fahimta. Ina miki son da babu rabuwa. A shirye nake da yi maki dukkan abinda zai faranta ranki. A yau ni Hussein na ba ki wuƙa da nama, ki yanka iyakar yanda ki ka ya yi maki, ki faɗamin burinki a duniya, da yardar Allah koda ya fi ƙarfina zan ƙoƙarta yi maki shi. Ban san farin cikin da ke cikin auren budurwa ba, amma ina da yaƙinin ba za su kai min ke ba."


Ya na maganar yana kai hannunsa duk inda ya so. Ta gama shagaltuwa da wani irin sonsa, tana ji a yanzu haka numfashinta na shige da fita ne da so da kaunar Hussein, ba ta san sadda ta juyo ta zubamishi dara-daran idanunta ba wanda ke ƙara tsumashi, kamar yanda duban nasa lumsassun idanun ke tarwatsa tunaninta har ta rasa kalar wanda za ta yi. Sai dai a wannan karon, a yanzun, a kuma wannan rana, ji ta ke ta samu kwarin gwuiwar kallon abin kaunarta tsakar ido, ba kuma don jin raini ba, aa, babu wannan tsakaninsu har abada sai wani irin kauna da ta ke jinsa daga ƙasan zuciyarta. Ba ta san lokacin da hannuwanta ya sauka saman fuskarsa ba kamar yanda ba za ta tuna sadda ta ɗora leɓɓanta bisa nashi ba. Hussein ya ji kalar soyayyar da bai tsammaceta nan kusa ba, bai ɗauka za ta miƙa masa wuya har haka ba, sai da tsayuwa ta nemi gagararsu duk kuwa da irin riƙon da ya yi mata ba na wasa ba kafin ta samu ta daidaita kanta ta rungumeshi. Daidai saitin kunnensa ta shiga magana tamkar mai raɗa.


"Kai ne burina, bani da sauran burin da ya wuce kai. Ka zame min wani jigo babba a rayuwata. Soyayyarka da kulawarka su kaɗai ne abin buƙatata. Koda nayi soyayya a baya, ban ji abinda nake ji a kanka ba, ban kuma samu farin ciki kwatankwacin wanda nake ciki a kwanaki ƙalilan da nayi tare da kai ba. Idan har za ka riƙe ni da amana, ni Ramlat zan zame maka tamkar raƙumi da akala. Dama ni ce a ƙasanka, muddin rai, zan maka biyayya. Ba zan ketare ɗaya cikin umarninka ba, wannan shi ne burina. Ka tayani addu'a akan Allah Ya bani ikon cikawa."


Bai ce mata uffan ba sai janta da ya yi suka ƙara faɗuwa duniyar masoya.


***
BAYAN KWANAKI UKU..


KANO.


A hankali ta shiga fiddo bandir-bandir na dubu ɗaya daga cikin ƙatuwar ledar da ta zo da shi, Gora banda satar kallon ledar da haɗiyar yawu ba abinda ya ke yi, jikinsa har rawa ya ke dakyar ya yi kokarin tankwasa kansa. Har ta kammala ya tabbatar sun cika yanda ya ce, sannan ta mayar ledar ta miƙamasa bai ce uffan ba. Haka itama Hajiya Batool da ta tattara gwala-gwalanta ta siyar ta haɗa da siyar da motarta har ta samu suka kai milayan biyu, ragowar kudin ta adana su a banki.


Gora ya gama haɗa miliyan bakwai cif a hannunsa kafin ya kyakyace da muguwar dariya duk suka dubeshi fuskarsu a sake don sun san sun cika sharuɗɗa kuma za su ga aiki nan ba da jimawa ba. Ko ba komai su na tuna aikin da ya yi musu tun farko da suka ji dadi.


"Lallai dagaske kun shiryawa buƙatunku, toh ku sa a ranku kamar dama duk wani bala'i da ku ke gani a yanzu mafarki ne don kuwa ina mai ba ku tabbacin cewa burinku na dab da cika. Hussein zai dawo wurinki kamar yanda ita kuma matarsa za ta faɗa duniya ta lalace. Ke kuma! Ɗanki zai dawo gareki koda ace bangon duniya matarsa ta kai shi. Idan ya dawo ko a ranar ki ka ba shi umarnin ya saki matarsa, ba za ki rufe baki ba zai aikata."


Don farin ciki sai ga Hajiya Zeenatu da Batool na sakin shewa har da cafkewa. Gora ya dinga washe hakora ya kalli wannan ya kalli waccan. Can kuma ya turɓune fuska kamar gaske ya hau magana.


"A daren yau, ni da kaina zan shiga cikin dajin Falgore, anan baƙaƙen aljanun suka yi umarnin na zartar da dukkan yankan da za'ayi na mutum da na dabba. Gobe kamar war haka, ku dawo na ba ku maganin da za ku yi amfani da shi idan suka shigo hannunku."


Ba yau suka saba jin Gora na kiran sunayen dazuka ba da sunan wurin da zai yi aiki, don Gora har Sambisa ya ce musu ya shiga yin wani aiki kuma sun yi imanin hakan. Da wannan irin farin cikin Hajiya Zeenatu ta ce.


"Ina mai maka albishir da kyautar sabon gida muddin kwalliya ta biya kuɗin sabulu."


'Makira, me zan yi da gidanki? An fadamaki ni talaka ne? A banza nake aikinnan ban mallaki kadarori ba?'


Abinda ya ce kenan a ƙasan ransa yayinda a fili kuma ya kyakyace da dariya shi a lallai ya yi farin ciki da jin wannan kyauta. Haka itama Hajiya Batool ta mishi alƙawarin mota.


"Ai kun ƙara ƙarfafa gwuiwana wajen yi maku aikin da ya dace! Ku tashi kawai ku je! Gobe ku dawo ku ji sakamako!"


Da haka suka yi mishi sallama suka tafi ransu wasai, su na fita ya mike ya cire babbar rigarsa ya kwashi jakar kudaden ya yi ciki. Nan ya ba yaronsa umarnin duk wanda ya zo kawai a sallameshi a ce ba ya nan. Yaron kasancewar ya san komai kuma tare ma za su yi tafiyar ya sa bayan ya tabbatar da ɓacewar su Zeenatu a layin ya rufe ƙofar sosai yanda ba wanda zai ce Gora na nan.


Shi kuwa Gora da shigarsa ya hau shiri don dama ya haɗa kayansa kaf a ƙatuwar jaka. Ya shige wanka ya gyara jikinsa don jinsa ya ke ya zama Alhaji, ya sauya kaya. Sai a sannan yaron ya shigo, shima gyara jikinnasa ya yi, suka ajiye maganar barin garin cikin daren yau ba gobe ba ransu fari ƙal kamar takarda.


***
"Taheer mutuwa ka ke so na yi? Da wanne zan ji? Da ciwon da ke cin raina ko kuwa da yanda ka ƙi kwantar da hankalinka ka samu lafiya?"


Taheer a wahalce cikin jin zafin kirji ya waigo a hankali ya zubawa mahaifinnasa idanu. Duk da ramar da ya yi ba ya jin zai fahimci halin da ya ke ciki adalilin soyayyar Hafsat. Ya lumshe idanu bayan ya kauda kai daga duban Modibbo, babban damuwarsa halin da Hafsat ke ciki, wayarta ba ya shiga, ya tabbatar tana can duk abinda ta ke yi hankalinta na kansa, balle kuma shi.


"Ku bani abinda nake so, Abba kai ne ka lalata komai, kai ke da alhakin gyarawa. Ka sani, ba za su taɓa ba ni Hafsat ba, ba zan taɓa samunta ba muddin ba ka nemi gafararsu ba. Abba ka yi kuskure, ka biyewa son zuciyarka wurin nuna ƙiyayya ga ƴan uwanka da kuma abinda suka haifa. Yanzu mene ne ribarka? Kowa a dangi na maka kallo da wannan abin. Abba ka nemi gafararsu tun lokaci bai ƙuremaka ba. Tun kana da sauran numfashinka a doron ƙasa."


Kawu Modibbo da ya yi shiru kai a ƙasa yana sauraronsa jiki a sanyaye ya rasa me zai ce, ba wai nadamar ce bai yi ba, sai dai tunanin ko da wane idon zai dubi bayin Allahn nan har ya ce su yafemasa ya ke. Tun ma kafin wannan ranar ya san kalar rashin mutuncin Hussein idan aka taɓo iyayensa, balle kuma yanzu da Hajiya Zeenatu ta gama kunce masa zani a kasuwa. Kowa ya san da sa hannunsa a lamarin Hussein din. Sai dai kuma kunyar duniya ba ta kai ta lahira ba ranar da Ubangiji zai tsayar da shi da hisabi. Gwara ya tattara ya koam Adamawa gaba daya da iyalinsa ya nemi gafararsu kuma ya faɗi komai a gabansu. Da wannan kudurin ya rarrashi ɗan nasa tare da nunamasa komai zai zo karshe don za su je Adamawa. Jin dadin wannan kadai sai da yasa Taheer zama maimakon a farko da ba ya iya tashi sai an taimaka masa. Har abinci ya ci sosai, wannan ya faranta ran iyayen.


***
ADAMAWA.


A kwanaki ukun nan, kowa ya ga Hussein da Ramlat ya san ba karamin walwala su ke ciki ba ga wata iriyar shaƙuwa da soyayyar junansu. A kuma ranar ne, Hajiya Binta da Rasheed suka dawo daga Katsina inda ta ziyarci yan uwanta. A washegari kuma za ta juya ta koma Saudiya tare da ɗannata.


Rasheed ba Hausar kirki sai kame-kame yayinda ita kuma Ramlat ba larabci don haka sai kawai suka juye harshe zuwa English suka ci gaba da hira. Abinci lafiyayye ta yi musu shi da abokinnasa, sai da ta ajiye komai kafin ta ba su wuri tana kauda kai daga kallon da Hussein ke jifanta da shi yana ji kamar ya haɗiyeta don kauna.


Ta kwanta rigingine saman gadon, kewar yaranta ta ke ji wannan ta sa ta kiran Hajiya. Bayan gaisuwa Hajiya ta haɗa ta da su. Hira sosai ta dinga yi da yaran, wannan na warce waya, wannan na sako baki yana magana kamar yanda ta fahimta. Dariya sosai suka dinga sanyata jin dagaske su dai so su ke ta dawo Kano ta dinga kai su makaranta a mota. Sai ma a lokacin ta tuna da motarta, yanzun ta san sai dai Hajiya ta ajiye su dinga amfani da shi koda wata matsalar za ta taso da waccan.


"Kinga gajen hakurin Yayanku ko? Sai da ya sauwakewa Bilkisu ya ji dadi."


Gabanta ya fadi jin abinda Hajiya ta ce.


"Kamar ya Hajiya? Me ya kuma haɗasu?"


"Uhm, wai gidan Amaryar ta je ta ja ta da fada har da kokarin dukanta, wannan ya fusata shi. Yanzu dai Kawunnanku sun ce tunda ya dauki zafi a kyaleshi kar a tursasa mishi sai ya maido ta, nan gaba itama watakila ta yi hankali. Yarannasa su na hannun Amarya."


Ramlat sam ba ta ji dadi ba, ko ya ya halin mutum ya ke, saki wani abu ne mai zafi. Cike da jimami ta ce.


"Allah Ya kyauta, Allah Ya daidaita lamuransu idan da alheri."


"Ameen."


Hajiya ta amsa, kamar koyaushe, nasiha mai ratsa jiki ta ƙara yi mata akan riƙe amanar miji da kuma kyautatamasa. Ta kara nusar da ita game da ibada musamman a watan Ramadan da ke ƙara kusantowa don bai fi saura wata guda da ƴan kwanaki ba.


"Allah Yay maku albarka, Ya ji ƙan Abbanku."


Ramlat ta amsa zuciyarta a raunane musamman tunanowa da Abbanta da ta yi, har suka yi sallama ba ta dawo daidai ba. A hankali kuma ta kwanta sosai ta juyawa ƙofa baya. Kewar Abbanta ta ke ji, ta tabbatar da ace yau yana raye zai yi matuƙar alfahari da aurenta na biyu, zai kuma ji dadi. Burinsa da kuma farin cikinsa bai wuce nata ba, ya ci alwashi a kanta a bayan aurenta da Aliyu wanda ya zamemata ƘARFEN ƘAFA, da kansa kuma ya janye sakamakon tsantsar kauna da tausayin da yake mata. Mutuwa ba ta barin wani don wani ya ji dadi. A hankali ta sauke ajiyar zuciya, ba ta san hawaye ta ke ba sai da ta ji tattausan tafin hannun Hussein yana sharemata su. Da sauri ta juyo sai dai babu damar matsawa sakamakon hannunsa ɗaya da ke tokare a gefenta a saman gadon. Ido ya ƙuramata fuskarsa na nuna alamun ba dadi.


"Habibty, meke damunki har ki ke hawaye?"


Ta girgiza kai ta sunkuyar tana murmushi.


"Ba komai, waya muka yi da Hajiya, addu'ar da ta yimin ta sa na tuno Abbana. Shi ne kewarsa ta kama ni."


Ya kamo haɓarta ya ɗago suka kalli juna.


"Kiyi hakuri, dukkanmu muna da wannan tabon na rashin iyaye duk da cewa kaso kusan ɗari, mun samu kulawar da ta dace a wurin Dada wanda ko su ne sai haka. Haka Allah ke tsarinSa a rayuwa, dukkan mai rai mamaci. Allah Ya gafartamusu."


Ta amsa da amin tana mai jin karfin gwuiwa. Ya bita da wani irin kallo yana murmushi, ta yi azamar jan rigarta tana harararsa. Mikewa ya yi ya taɓe baki.


"Wane dare ne jemage bai gani ba?"


"Daren mutuwarsa."


Ta amsa, ya yi dariya, har ya dawo da baya sai kuma ya jinjina kai ya kama hanya yana fadin.


"Ki fito ku yi sallama zai wuce."


Jin haka ta mike ta maida hijab din da ta cire, fitowa ta yi har Rasheed din ya miƙe tsaye don haka suka yi sallama don ta san ba lallai su kara haɗuwa ba tunda a yau sha biyun dare zasu wuce Airport.


***
Bayan sallar isha'i ta shiga suka yi sallama da Hajiya Binta. Mata mai kirki, haka ta sanya ta a ɗaka ta ba ta shawarwarin da za su amfaneta a zamantakewa. Kafin ta yi mata kyautar miski mai kyau marar sirki. Ta yi godiya sosai. Koda ta fito ɗakin Hafsat ta faɗa jin yanda kwanaki biyu ba ta jin ɗuriyarta. A kwance ta isketa yatsarta na dama rike da Counter tana dannawa a hankali. Shigowar Ramlat bai sa ta ɗago ba balle ta san da wanzuwarta a ɗakin. Zama ta yi gefen gadon, hakan ya ankarar da ita, tausayinta ya kamata. Yanzun Dada ta gama faɗan sauyawarta, ta kuma san dalilin tunda Hussein ya faɗamata. Hafsat ta mike zaune da sauri tana goge hawayen saman fuskarta.


"Adda Amal, sannu da zuwa. Yanzu ki ka zo?"


Ramlat ta gyara zama sosai ta dubeta.


"Hafsat kar ki zama marar hakuri da juriya a lamarin soyayya. Ki zama mai hakuri. Kin san illar saɓawa iyaye kuwa? Na taɓa shiga makamancin halin da ki ka tsinci kanki ciki a baya. Na kuma san yanda ki ke ji, kina jin kamar ba za ki iya rayuwa babu Taheer ba, kina jin numfashinki zai iya ɗaukewa muddin ki ka rasa Taheer matsayin miji ko? Kamar su Dada da Yayyanki ba su yi maki adalci ba."


Hafsat ta kwantar da kai saman cinyar Ramlat, sai kawai ta fashe da kuka ta soma magana.


"Adda Amal wallahi hakane, na sani Mahaifinsa mai laifi ne a wurin su, amma shi me ya yi musu da za su yanke alaƙata da shi? Dada da bakinta ta yabeshi a ɗan zaman da ya yi tare da mu, ta fada ta ƙara, bai ɗauki halin mahaifinsa ba balle na mamansa, Hamma AlHassan ma haka. Hamma Hussein bai zauna da shi sosai ba da na tabbatar zai gamsu da kyawawan ɗabi'un Taheer. Adda Amal sanadin aurena da Taheer zai iya sanyawa su shirya. Babban damuwata Hamma Hussein ya kwace wayata, Rasheeda ta kirani ta wayar Dada tana kuka ta shaidamin yana asibiti kwance ba lafiya."


Hafsat na kaiwa nan ta mike zaune, ita Ramlat kallonta kawai ta ke tana fidda hawayen tuna baya, itama dama haka ta kafe? Amma ba za ta taɓa bari Hafsat ta yi irin nata ba.


"Adda Amal kimin alfarma ki ban wayarki, sau daya kawai zan kirashi, daga haka ba zan kara ba. Wallahi kawai gaisawa zamu yi na kuma roƙeshi mu ci gaba da addu'a. Har abada ba na fatan na bijirewa iyayena da yan uwana."


Ramlat ta yi jim, tana tunanin anya kuwa idan ta yi hakan ba matsala? Sai dai kuma irin magiya da nacin Hafsat ya sa ta miƙamata wayarta. Kasa fita ta yi daga dakin ta jira har Hafsat ta kammala wayar, Ramlat banda kallon ƙofa ba abinda ta ke yi. Tsoronta kar Dada ta faɗo ɗakin don ta san abu ne mai matsanancin wahala Hussein ko AlHassan su shigo ɗakin.


Da murmushi ta dubi Ramlat.


"Adda Amal."


Sai ta rungumeta don farin ciki can kuma ta saketa.


"Cemin ya yi za su zo nan da kwanaki kalilan har Babansa, zai zo neman gafarar Dada da su Hamma."


Sosai itama Ramlat ta ji dadin hakan. Ta rike hannunta.


"Toh kinga ni, don Allah ki saki ranki, kinga Dada kin jefa ta a damuwa. Ta ce ko ganin idon baƙuwarku ba kya yi, ba ki san ki danne zuciyarki da abinda ke cikinta ba. Jefa iyaye cikin damuwa masifa ce a garemu. Kuma ina mai ba ki shawara ki dage da nemawa kanki zaɓin Allah, ki rabu da biyewa son zuciya wurin dagewa akan zaɓinki."


Hafsat wacce tuni ranta ya yi fari sumul ta gyada kai.


"In sha Allah Addata. Ina godiya sosai. Sai dai Adda ba ki ban labarin da ki ka ce."


Ramlat ta murmusa.


"Kar ki damu, ai ana tare."


"Da'iman kuwa da yardar Allah." Fadin Hafsat, suka dara kafin Ramlat ta fice ita kuwa bandaki ta shiga ta wanke fuskarta. Ramlat na sallama da Dada sai ga Hafsat din, sosai ta yi mamakin walwalarta, ta karasa ta fda jikin Dadar tana neman

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login